Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 41

Sponsored Links

Aisha Baby Novel: Wata kyakkyawar runguma Jee ta yiwa Khalil gani take kamar zai sake guduwa ya koma cikin kabarinsa ne, ta ɗauki niyyar idan haka ta kasance sai dai su koma tare, lokaci guda suka sake ƙanƙame junansu, bugun zuciyoyinsu na hauhawa yadda Jee ta riƙe Khalil dole ta baka tausayi riƙewa ce dake nuna shi kaɗai ya rage mata a nan gidan duniya.
Duk yadda Khalil yaso riƙo fuskarta a hannayensa hanawa tayi tana ɓoyeta a ƙirjinsa, magana take son furtawa amma rawar da zuciyarta keyi ya sanya ta kasa, idan taji kamar Khalil sai saketa sai ta sake ƙanƙame shi cikin kalar muryan mai tsananin tsoro da firgici ta ce
“Don’t leave me, don’t” Gently ya girgiza mata kai a hankali ya furta “Tunda na sake baki ciki na 2nd time i won’t leave u” Su kaɗai suke magana domin ko John ba zai iya cewa ya ji komai ba, wayarsa kawai yake dannawa. Ta ɗago ta kalle shi da jiƙaƙƙun idanunta wanda hawaye suka kasa tsayawa shi ɗin ma idanunta yake kallo yana hango wani so da ƙauna da kewar shi zalla tsagwaronsu a cikin idanun nata.

“Ba zaka koma kabarinka ba?” Khalil ya zare fararen Idanunsa, yana Kallonta sai kuma ya yi murmushi yana girgiza kai ya ce “Me?” Ya faɗa so calmly. Majeederh couldn’t speak saboda bata taɓa ganin kyan Khalil irin na yau ba, yanayinsa ya fara rikiɗewa tamkar na Ajlaal saboda cikar suffa da kamar dake wanzuwa a jikin nasa, yadda yake cike da tsantsar nutsuwa yanzu ba zaka ce shi ne wanda ya aikata abinda ya yiwa su Innati da General ba. A hankali cikin ƙasa da murya yana sake janyo waist ɗinta yana mannawa da nashi ya furta “Your Husband is alive, he never really died, ina can U.s”

Ta kalle shi da sauri, ya ɗaga mata gira tare da saka hannu ya fara zagaye laɓɓanta a hankali kuma ya kifa fuskarsa a nata yana goga mata hancinsa can ƙasa ya ce “Sure hub, ba zan mutu na barki ba” zamewa Majeederh tayi daga jikinsa tare da durƙushewa a gabansa saman ƙafafuwanta ta fashe da wani irin raunataccen kuka wanda bashi da maraba da farin cikin da take ji. Uncle I da B Kallon ikon Allah suke haɗi da buwayar shi, sannu a hankali suka fara ɗan fahimtar wani abun dake faruwa a Yanzu. Khalil ya taka a hankali tare da durƙusawa daidai inda take ya saka hannu ya miƙar da ita, ta shiga dukan ƙirjinsa tana kuka a gigice take cewa “Why? Why? Why…? Me ya sa ka barni? Tare da yaranka ka barsu cikin maraici, me ya sa ka barni bayan kasan ba zan iya jurewa ba?” Baiyi ƙoƙarin hanata ba, dukan ƙirjinsa take kamar zautacciya, Alhassan dake da ɗan banzan wayo ya shige tsakiya gabaɗaya a iya qiwwarsu ya tsaya idan ya kalli Khalil sai ya kalli Majeederh, ganin yaron na son fahimtar wani abu ya sanya Khalil saka hannu ya ɗauke shi tare da bawa John shi ya yi masa alama da su shiga ciki, idanunsa a rufe yake bai damu da su Uncle’s da suke wajan ba, ya saka hannu ya fisgo majeederh ta faɗa jikinsa ya rungumeta suka zubawa juna Idanu a hankali kuma yana kallonta yana matsar da fuskarsa zuwa nata, lura da abinda yake son yi Jee tayi saurin matsar da nata fuskar tare da haɗe bakinta dana Khalil, Khalil ya yi saurin rufe ido yana yin baya a hankali kuma yake sauke ajiyar zuciya.

Related Articles

Uncle Isma’il da Uncle Bello da Maman Alpha saurin ɗauke ido sukayi lokaci ɗaya, ganin abinda basu taɓa gani ba, ko wannensu direction ɗin da yake kallo daban, sun jima da sanin Khalil baya iya ɓoye abinda zuciyarsa ke ciki, sun saba ganin ire-iren rashin kunyar shi amma wannan da dukkan zuciya ɗaya yake aiwatar da abinda yake yi ɗin, ba su taɓa ganin makamancin irinta ba. A hankali suka juya tare da shigewa cikin parlon jiki a sanyaye. General wani irin azababben tari ne ya taso masa ya turniƙe shi lokaci gudu ya fara yi a gigice tare da nufar garden yana tare jinin dake zuba ta cikin bakin nasa wanda ya ƙara fidda rauninsa a fili ƙarara, ganin zuciyarsa na gab da kamuwa da ciwo mai wahalar warkewa da magani.

Majeederh ta zame tana kallon Khalil, da wani irin love and emotion cikin tafiyarsa ta nagartattun maza ya nufeta da Idanun zuciya, idanunsa na fallasa ainahin abinda zuciyarsa ta kasa ɓoyewa, da yadda rauninsa ya bayyana asalin kewar shekaru biyu da wata shidan da sukayi basa tare, ya riƙe kansa da kyau gudun yin abinda zuciyarsa ke azalzalar shi da yi ɗin, ya ƙara damƙo fuskarta ƙofofin zuciyarsa na ɓoyewa suna amsar uwarnin na soyayya daga zuciya zuwa ƴar uwarta, ƙara ƙanƙameta ya yi while yana sake kissing ɗinta a gaggauce idanunsa rufe wani irin siririn hawaye na biyo gefen idanunsa suna saukar a fuskar Jee, wani irin FRENCH KISS yake mata yana sake riƙe ƙugunta yana shigar da ita jikinsa kamar wani zai ƙwace masa ita.
Romantic kiss yake mata irin Neck Kiss wanda ke nuna tsananin kewa da son da yake mata, gabaɗayansu hawaye ke fita daga cikin idanunsa musamman yadda Kspider ya nemi rusa jarumtar nata, wani irin best kisses yake bata sweet, light kisses on her cheeks, forehead, jaw line. A hankali ya sake fuskarta yana rungumeta sosai domin shi ma a yanzun ji yake zai iya mutuwa babu ita.

Jee was about to loose her mind, numfashinta na fita da ƙyar, yadda yake kissing nata da yadda ya rungumeta kamar zai ɓallata gida biyu ya sanya ta kasa kwancewa, tsananin shock ne har yanzu bai gama sakinta ba, domin a zahiri ta riga ta sallama ta saduda ta fidda rai da sake ganinsa a rayuwarta har abada, abu ɗaya tayi imani da shi, yana nan zaune daram a zuciyarta kamar zanen rubutu akan dutse saɓanin ruwa, ta gane ko baya tsagenta a nan duniya dole su kasance tare da ruhinsa, zatonta ya wargatse ganinsa a yanzu, da jikinsa, da numfashinsa, da ƙamshinsa da take a yanzu a gabanta ya sa ta gane poor darling enternal husband ɗinta is back, he’s back with full of love and confidence, ya dawo da shirin bata farin ciki na har abada.
“I am sorry Hubb” Tayi masa wani kallo cike da faɗa wanda bai taɓa gani daga gareta ba ya ji tayi baya ta ce “Sorry? Khalil ni kake cewa sorry? You left me, ka barni da ciki You didn’t even care akan halin da zan shiga? Ance mini mahaukaciya, ance Aljanu sun shige ni zuciyata ta kasa ɗauka na kusa zaucewa, na raini yaranka cikin maraici da kaɗaicin uba, a tunaninsu babansu ya riga daya mutu, all this thing shi ne zaka ce sorry? Keep your sorry to urself my dear” Faɗa take amma a sanyaye saboda bata saba da yi ba, yana kallon yadda take dafe kai da runtse idanu alamar ita kanta faɗan hawar mata kai yake. Ta nuna shi ta ce “Mai martaba, Rohaan, Zaytoon, Ƙhulud, your sister and more especially Ummie ka taɓa tunanin halin da zasu shiga na rashin ka Khalil? Musamman da komai ya faru kan idanun Ummie?” Faɗan ya nuna asalin abinda zuciyarta ke faɗa ne ya nufeta Gadan-gadan domin kansa ya fara juyawa zata juya ya yi saurin cafkota tare da raba k’afafunta da k’asa a hankali ya ce “Ni kikewa rashin kunya wife?” Ya saka hannu ya yi squeezing bakinta tare da kissing at the same time, ta ce “Get me down”
“Ki barni ni da na san yadda ake faɗa na yi, da kuɗina siyan faɗa nake” Ta haɗe fuska tana jin wani son shi na ƙara shiga zuciyarta ta mance da wani auren General Alpha dake kanta.Ya kalleta ta hararesa ya rausayar da kansa a hankali ya ce “I love you”
A nutse ta ce “I need you” Khalil ya saki dariya ta zaki gane kuranki ta ce “Meye?” Ya girgiza kai bai ce komai ba, duk yadda tayi akan ya sauketa ƙi yayi ya ce sai ya ƙarasa ladan shi. Suna shiga parlon suka samu John ya gama basu labarin komai, Uncle Isma’il da Uncle Bello wani irin farin ciki suke ciki sai yanzu suka gasgata maganar Majeederh, lokaci zuwa lokaci suna kallon Khalil idanunsa shi kuma akan Alhassan da Al’hussain da suke wasa domin kuka Al’hussain ya fara shi ma irin kayan Alhassan, gashi ƙananun kaya kawai suke dashi, aka cirewa Alhassan aka saka musu iri ɗaya, a hankali kuma ya Kalli takwaran shi baby khalil daya girma abinsa ciwo kawai ke damunsa bashi da damuwa ko kaɗan, yadda Khalil ke jin su Alhassan a ransa haka yake jin Baby Khalil, ya kalli Majeederh dake miƙewa zata kitchen ya tuna cikin jikinta ya lumshe idanunsa a hankali ya ce “I love you wife, i so much love you Hawwa’u”. Uncle Isma’il ya ce “Khalil batun fatalwa fa?” Khalil ya ɗan shafa kansa kaɗan yana nutsawa cikin kujera a hankali ya lumshe idanunsa ya buɗe kamar anyi masa dole wajen magana ya ce “No!” John da ya san komai ya saki dariya ya ce “Ai kamar ba fatalwa yanzu ko? Khalil da kansa shi ne fatalwa shi ke zuwa wajan matarsa, duk wanda ya ce yaga fatalwa to ranka ya daɗe ya gani” General dake sakkowa ya tsaya cak, yana jin wata kunya tana rufe masa iliharin jikinsa, ya kasa motsi don takaici yana jin babu abinda zai hana shi rama abinda Khalil ya yi masa duk da cewa bai faɗawa su Abba da babarsa asalin abinda ya same shi ba. “Shikenan bari kaci abinci we’ll talk later” John ya miƙe ganin matarsa na kira ya ɗauka da sauri ya ce “Right now baby” Ya kalli Khalil ya ce “Ranka ya daɗe matata tayi kira” Khalil ya jinjina kai ya ce “Alhassan muje?” Ya kuwa ɓata fuska yana hayewa bayan Khalil ya yi lamo.

Fitowa tayi daga kitchen bayan lokacin data kwashe ta gaji sosai ga laulayi ga kala-kalan abincin data shirya, tun kafin ta ƙaraso take jin hayaniya a hankali ta saka hannu tare da turo ƙofar bedroom ɗinta, cak ta tsaya tana kallon yadda aka sauyawa ɗakin kama, komai an sauke shi ƙasa, bedsheet an cire humura da kwalacca nata Duk an zubar da su a ƙasa, chocolates da ledar su birjik gasu tarkacan kayan wasa, hatta glass window an sauke shi, ta juya ba kowa sai Al’hussain bakinsa duk butter da chocolate ta kalle shi kamar za ta yi kuka ta ce “My friend who did this?” Ya kalli ƙarƙashin gado suna haɗa idanu da Alhassan ya girgiza kai, Khalil ya kwaɓe fuska, ya kalleta bai ce komai ba inda ya kalla Majeederh ta nufa ta ce “Ku fito to” jiki a sanyaye Khalil ya fito kansa a ƙasa yaƙi yarda ya kalleta, ta kalli Alhassan Exlaty yadda ubansa ya yi haka shi ma ya yi ta juya zuwa waje, Khalil ya kalli Alhassan kamar zai kuka ya ce “Friend, Umy ta ji haushi” Alhassan ya nunawa Khalil window, daidai nan Majeederh ta shigo hannunta da abin mopping da broom kafin ta ƙaraso Alhassan ya miƙe da gudu ya kama window ya dira Majeederh ta zare ido tana zama ta ce “Na shiga uku” Khalil dai ya kwaɓe fuska yaƙi kallonta ta miƙa masa broom ɗin ta ce “Share abubuwan da kuka lalata” A hankali ya kalleta ya ce “To ai ban iya ba” Ita ta rasa me za tayi akan mijin nata sai yanzu ta fahimci yadda akai Alhassan ya koyi haura window..
Wajan magariba da ƙyar Khalil ya bar Jee ta huta tayi wanka ta fito shi ko kunya baya ji wanka ya yi ya saka wasu ƙananan kaya masu kyau, suka samu hadda Abbu a parlo Khalil ya gaida kowa a taƙaice, Uncle Isma’il ya ce “Khalil Majeederh nada ciki” clamly ya ce “Na sani” Innati ta ce “Ka sani kuma? Tayaya ina yau ka dawo” Ya kalli Innati sai ya lumshe idanunsa ya ce “Na sani, tunda cikina ne, ni na yi cikin…..
[

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button