Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 4

Sponsored Links

Tuni firgici ya shiga Mama ta matso da sauri tace “Ya Hayyu meye ko al’ada zakiyi” hannunta takai jikinta taji jikin zafi zau tace “Na shiga uku Ni Indo Hanisa ruwan nan kika bari ya dakeki wannan muguwar cutar taki me cin kuɗi take neman tashi ko?” Fita Hasina tayi da sauri tace “Ai dama da naga hadarin saida nace ta taho mu tafi taƙi yanzu ai ga irinta nan bari na juye miki ruwan can da na ɗora zanyi wanka saiki watsa zakiji daɗin jikin”
Ficewa Mama tayi hakan ya bata damar miƙewa daƙyar ta nufi bayin tana dafa bango ta shiga ta watsa ruwan ta zauna cikin bahon tana yarfa hannu saboda azabar da takeji hawayenta naci gaba da tsiyaya ta mike ta daura zaninta ta koma ɗaki daƙyar tayi sallar Isha tasha maganinta ta kwanta har zuwa lkcn shassheƙar kuka takeyi me taɓa zuciya.
Daidai lkcn Hasina ta shigo gabanta ya faɗi jin shassheƙar kukan ƴar’uwar tata, da sauri ta kunna fitilar su ta ɗakin ta ƙarasa inda Hanisa ke kwance tanata rawar sanyi tace “Wai jikin ne har yanzu Hanisa meye ne yake damunki haka?” Sake gyara kwanciyarta tayi taci gaba da kukanta batare data iya bata amsa ba. Ganin tayi shiru yasa Hasina zama a kusa da ita tace “Duk da munsha bambam ta wajen ɗabi’a da halayya Hanisa karki manta munyi alƙawarin duk rintsi duk wuya bazamu ɓoyewa juna damuwarmu ba zamu faɗawa juna matsalarmu mu samawa kanmu mafita, shin meye yasa kikeson karya alƙawarin nan Ƙanwata?”

 

Ɗora kanta tayi saman cinyar Hasina ta sake rushewa da kuka Hasina ta kwanto jikinta yanda takejin kukan ƴar uwar tata tasan daga zuciya yake fita itama kukan ta saki tace “Don Allah ki cireni daga tashin hankali Hanisa ki faɗamin matsalarmu”
Tashi tayi zaune ta buɗe idanunta da suka kaɗa sukayi jawur tace “Kiyimin alƙawarin zaki rufamin asiri Yaya Hasina banason wannan mgnr ta fasu don Allah” riƙe hannunta Hasina tayi tace “Wlh ko kisa kikayi zan rufa miki asiri ƙanwata bare ma nasan bazai taɓa zama hakan ba” rungume kanta tayi cikin cinyoyinta ta sake rushewa da kuka tace “Fyaɗe akayimin Yaya Hasin…..” “Me?” Hasina ta faɗa da ƙaraji sai kuma tayi saurin rufe bakinta da hannunta tare da komawa inda ta tashi da sauri jikinta na ɓari tace “Garin yaya Hanisa waye yayi miki wannan aika²r?”
Cikin kuka ta zayyane mata komai Hasina ta miƙe tana zagaya ɗakin kanta da zuciyarta na bugawa da ƙarfi wasu hawaye masu ɗumi suka rinƙa sintiri a fuskarta jikinta na rawa daidai lkcn da wayarta tayi ring takai hannu ta ɗauka ganin sunan Abdul yasata ɗagawa muryarta na rawa tace “Abdu….” Katseta yayi da cewa “Ina Anisah?” Ajiyar zuciya tayi tace gatanan a zaune” shima zuciyar ya ajiye yace “Ina fatan tana cikin aminci?” Dake Hanisa ta sanar da ita shine ya taimaketa ya kawota gda batayi mamaki ba tace “Eh sama² dai Abdu tabbas yau tafimin kowacce rana muni cikin rayuwata wlh bantaɓa jin ciwon rasa budurcina ba domin Ni ganin dama nayi na bayar dashi Abdu zuciyata zafi takeyi saboda abinda ya samu ƴar uwata meye yasa Hanisa rayuwarta take a hargitse ne duk abinda take gudu yafi samunta?”

Related Articles

 

Sauke wani Gwauron numfashi yayi yace “Bani ita inason magana da ita” miƙa mata wayar tayi ta karɓa jikinta na rawa tace “Abdul-Ahad” cikin sanyin murya da kasala yace “Na’am Anisah ya jikinki?” Da shassheƙa tace masa naji ƙarfin jikina da nayi amfani da ruwan zafi kamar yanda kace sannu fah na gde ubangiji yabar zumunci”
Shiru yayi zuciyarsa ta lula masa duniyar tunani saida ta kuma cewa “Abdul-Ahad ka Taimakeni ka rufemin sirrina wlh muddin sirrin nan ya fasu bazan iya zama tare da Baba ba na gwammace na shiga duniya saboda kullum Baba roƙona yakeyi na kiyaye kaina na riƙe darajata yana yawan faɗamin ba talla ne matsala ba masu tallan ne da masu siyan matsalar nikam zanji kunyar ranar da asirina zai tonu baba yasan nima na rasa ƙimata”
Murmushi yayi me ciwo yace “kina nufin abar Lawwali yaci bulus gobe ma ya samu damar aikatawa wata irin abinda ya aikata miki?” Shiru tayi a ranta tana jinjina ƙarfin halin mutumin yace “Anisa tun ganina dake na farko zuciyata ta ɗarsu da tausayinki inaji a raina idan ƙanwata Maryam hakan ta faru da ita zan iya bari kuwa, Anisa bazan bari ba saboda haka kema bazan iya bari ba kedai kawai kija bakinki kiyi shiru”

 

*OUM HAIRAN*
[12/16, 2:33 PM] Oum Hairan&Affan: *WATA KARUWA*

 

*OUM HAIRAN*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button