Hausa NovelsMijin Malama Book 1

Mijin Malama Book 1 Page 3

Sponsored Links

3…..*
Maganganun Aliyu suka kusan tarwatsa mata zuciya, idanunta ya rufe kafin tayi magana ya ce “Ko a lokacin da nake yaro, ban taɓa kuka saboda wahala ba, ba kuma zan yi kuka saboda abin da zaki aikata ba, ki sawa ranki ba a haifi Aliyu domin sadaukarwa ba, amma an haifi ni domin bautawa Ubangiji da kuma cimma burukana, bana da burin daya shige zama da Malama Majeederh Abdul’aziz Khan!” Ya fesar da numfashi ya ce
“Ban taɓa neman abu na rasa ba, kin san yadda nake zama mahaukaci akan abin da nake so….,” Da ƙarfi Latifa ta ce “And so what Aliyu? Ni kuma zan tabbatar a wannan karan na zama sanadin da zaka rasa abin da ka ke nema, ka yi ta farauta wacce bata da amfani har zaki ya yi gaba da abin farautar taka, zaka san kuma kaci amanar matarka ni Latifa Omar zaka sani” tayi hanging off na kiran.
Tsakanin ita da Aliyu ba a san wanda ya fi wani shiga damuwa da baƙin ciki ba, shi yana jin baƙin ciki idan ta shegenta ɗan gidan Jeederh, yana jin tamkar gudan jininsa ta shegenta. Latifa Omar tana ganin Majeederh ta munafurceta tayi mata kyakkyawan zato ta ci amanarta, Allah kaɗai ya san lokacin data ɗauka tana bin baza, ko komai nata zai ƙare ba zata taɓa barin Bar Aliyu Sufyan Alhassan ya kasan inuwa guda da Jeederh ba.
Ta dunƙule hannu tare da kaiwa iska naushi cikin zafi ya juya yana faɗin.
“I can’t take it any longer Majeederh, dole kiyi haƙuri mu zama abu guda” shiru not respond.
Ya riƙe ƙugu cikin sauke numfashi yana son ya saisaita kan shi ya kasa ya ce. “Ina son na je wajan Dr Jamal, i have something to discuss with him” nan ma shiru sai a lokacin ya juya zai sake kiran sunanta yaga wayam! sai gado da drip yana ɗiga a ƙasa.
Baki buɗe ya tsaya cak yana ƙarewa room ɗin kallo kamar ƙungi.
“What?” Cikin sauri ya buɗe ƙofa ya fita suka ci karo da wata nurse ya ce
“Heee Nurse” “Yes, Sir how can i help you?”
Ya juya idanunsa ya yi ta kallon wajan yana son yaga ta ina zai gano Jeederh. “Sir!” Kiran ya dawo da shi hankalinsa ya ce “Kinga wata yanzu da baby a hannu ta fita?” Ta shiru alamar tunani sai kuma ta ce.
“Yanayinta?” Ya ce “She’s beautiful, fara tas yar yellow take tana da jiki zata kai 35 yrs going to 36” Ta kalli hanya ta ce
“Oh Malama Majeederh Abdul’aziz Khan?” Ya ɗaga ya ce “Exlty, where she’s?” Ta ce “She Left, alright”
Ya yi baya a fili ya ce “Innalillahi wa’inna ilahir raji’un, why? why Jeederh mun shiga uku daga ni har ke” da gudu kuma yabar world ɗin ya nufi reception har zuwa parking lot na hospital ɗin amma babu ko mai kama da ita.
Motarshi ya shiga tare da yi mata key kamar zai tashi sama haka yabar cikin asibitin bakiɗaya wanda ya yi kwana Uku ciff a cikinsa.
Dr Jamal na zaune a office ɗinsa yana operating system sai gumi yake duk da sanyin A.cn dake office ɗin. Bell aka danna ya ce “Come in” buɗe Ƙofar akai tare da shigowa.
“Dr Jamal wai meke faruwa da kai ne, kwana uku baka cikin hayyacinka” ya share zufa ya ce “Tajju ina cikin damuwa”
“Problem?” Tajju ya maimaita. Dr Jamal ya gyara zama ya ce “Ka san Malama Majeederh Abdul’aziz Khan?” Gaban Tajju ya faɗi hakan ya tuna masa da wasu memories ya ce “Uhm, ina jinka” kai tsaye Dr Jamal ya ce “Ta haihuwa, kuma yanzu an nemeta an rasa, kwana kenan bana barci kullum sai na duba all scanning da na taɓa yi mata, wallahi tsayin shekara biyu result bai taɓa nuna mini Majeederh nada ciki ba ko da wasa, infact results ɗin na nuna she’s Good, sai a satin nan dana sake mata wani ya nuna mini ƙari ne a cikinta shi ne ya haddasa kumburin Cikin, sai gashi kuma wai ta haihu harta gudu” cikin wata kalar hausa Tajju ya ce
“Innalillahi, subuhana”
Ya yi ta maimaita wa kafin ya ce “Amma tayi aure?” Dr Jamal ya ce
“Ko engagement ba tayi ba balle aure, bata taɓa aure a zahiri ma babu wani ɗa namiji daya taɓa cewa yana son ta”
Tajju ya miƙe ya shiga kai kawo cikin office ɗin da sauri kuma ya fice yana cewa “ina zuwa”
Yana fita mota ya shiga ya nufi gidan shi dake cikin Nassarawa. Tun da ya shiga bedroom yake tunani,akwai muhimmin abu da yake son tunawa amma ya rasa mene? Dr Jamal abokin Tajju ne gabaɗayansu likitoci ne.
A hankali ya ce “Malama Majeederh Abdul’aziz Khan? Ya Allah!”
Kwanciya ya yi nan take barci kuma ya ɗauke shi.
Can cikin barcinsa ya ci wasu maganganu na tashi a kunnenshi a firgice ya farka yana haɗa zufa jikinsa na rawa ya ce.
“Gang” ya miƙe ya ce “Gang team!” a haukace Tajju ya dinga fito da kayan wardrobe nasa cikin sa a wata envelope ta faɗo ya ɗauka da sauri yana dubawa, har yanzu wani sassan yan ƙamshi ke tashi jikin envelope ɗin, ya duba da kyau idan har ba zai manta ba shekaru biyu kenan da bashi saƙon ya bawa Majeederh, shi kansa ba zai iya tuna abin da ya mantar da shi ba. A hankali ya duba jikin envelope da aka rubuta.

*_No words to explain, no words to describe, no words to as your forgiveness, Wait for me, I’ll be back sooner or later, Please Jee_*

Tajju na gama karantawa ko gyara bedroom ɗin bai ba ya zari key ɗin mota tare ficewa daga cikin gidan, tana ina zai fara? Ina zai ga Malama Majeederh har ya bata wannan saƙon? A fili ya ce “Allah na tuba, ban san me ya mantar dani ba” haka yaci gaba da driving.
Tun safe Majeederh take tafiya fuska rufe babyn ya yi shiru a jikinta, kamar mahaukaciya haka ta zama bata gane komai bata bambance komai, kiran sallar Magriba ya yi daidai da tsayuwarta a gefen wani shago a lokacin kuma babyn ya kama kukan yunwa, ta samu waje ta zauna ta shiga kallon fuskar jaririn ko Allah zai sanya ta gane dawa yake kama, amma abin mamaki komai nata ne, kamarsa ɗaya sak da ita idanunsa ne kawai da bai fiya buɗewa ba yasa bata gama gane ƙwayar tawa ba, ganin kukansa zai sanya hankalin jama’a ya dawo kanta ya sa ta zura shi cikin hijabi bata san me zatai masa ya daina kuka ba can ta tuna abincinsa yana jikinta ta ɗaga rigar asibitin dake jikinta tare da sanya masa nono a baki, babu ruwa ko kaɗan zai azabar zafi, haka ya dinga jan fata jin baya shan komai ya cika ya dinga tsala ihu. Sai a lokacin ta fashe da kuka take rungume shi ta ce.
“Asstagafirullah Ya Allah, ba san komai, na yarda da ƙaddara, Allah ka kawo mini ɗauki albarkacin Annabin rahama” a hankali ta dinga tattaro yawun bakinta tana bawa jaririn yana sha, tun tana bashi har yawun ya ƙafe bai kuma daina kuka ba. Ta miƙe riƙe da shi tare da ƙara sawa wajan shagon tayi sallama can ƙasa kafin tayi magana ta ji saukar muryar Abbu a kunnenta ta juya da sauri ta kalli T.v dake shagon, fuskar mahaifinta tar a t.v yana yi wa ƴan jarida bayani ya ce.
“Me kuke son sani?” Ɗan jaridar ya ce “Shin da gaske ne ƴarka Malama Majeederh Abdul’aziz Khan kan ta haihu? bayan duniya ta san bata da aure? Ko dai tayi aure a ɓoye ne, ko kuma zargin da ake a kanta ya tabbata?” Abbu ya yi dariya sosai yana kallon Ɗan jaridan ya ce.
“Ina da ƴa Majeederh, amma tawa yarinyar ta zama gawa tun tuni bata raye, ban kuma san yarinyar dake amfani da sunana da kuma sunan familyna ba, zan yi amfani da wannan damar wajan yi mata Allah ya isa har abada, zan kuma shaidawa duniya duk inda suka samu yarinyar nan mai amfani da sunana su jefe ta ko kuma suyi mata bulala akan laifin aikata zina, su kuma ɗauki mataki akan amfani da rigar Muslunci tana aikata alfasha”
Ɗan jaridar ya kalli Abbu sosai, da alama ya firgita da maganganun shi ya ce. “Kenan Malama Majeederh ba ƴarka ba ce wacce muke tunani?”
Cikin tsawa Abbu ya ce
“Yara biyar ne kaf duniya, tawa Majeederh ta zama gawa tun da jimawa bana son wata tambaya bayan wannan” a firgice Majeederh ta dafe ƙirjinta da yake wani bugawa jajirin ya nemi suɓucewa ta shiga kokawa da numfashinta, wani abu mai nauyi ya tsaya mata a ƙirji Idanunta suka tsaya ƙam akan fuskar mahaifinta tunani take ko dai da gaske bashi ya haifeta ba? Mai shagon ya girgiza kai ya ce.
“Kai duniya, kai duniya wai yanzu aikata zina ya zama ruwan dare? Matan aure su aikata zina, ƴan mata su aikata zina, zawarawa su aikata zina, mijin aure ya nemi matar wani, matar aure ta nemi mijin wani? ga Fyaɗe daya ya waita, ga matsalar tsadar abin duniya, ga rashin nefa ga rashin ruwan sha, albashi wannan sai a shige wata ba a biya, wani lokacin ma a rage albashin, ga yawan aibata Musulunci yanzu Fisabilillahi a kaf garin nan waye bai san Malama Majeederh Abdul’aziz Khan babbar malamar musulunci ba ce? waye bai san irin tallafin da take bawa Muslunci ba, waye bai san wa’azin da ta kewa masu aikata alfasha ba, sai gashi ana zaton wuta maƙera sai gata a masaƙa, shi ya sa ake cewa kayi amfani da faɗar Malam kada kayi amfani da abin da yake aikatawa, wallahi ko ki aka bani dama sai na jefe wannan shaiɗaniyyar” Lawan ya girgiza kai ya ce “A’a Bala, amma dai Allah ya kyauta!” Bala ya ce “Amin, shi ya sa taƙi aure tana ta zuba alfasha, kasan daman duk wani mai aikata zina aure bai dame shi ba, kuma ko ya yi aure ba zai daina yin abinda ya saba ba”
Malama Majeederh bata tsaya neman ruwan ba, ta juya da sauri tare da barin wajan a lokacin ji take kamar ta shiga duniya, kamar ta zama ƙaruwar da suke danganta ta da ita, ji take kamar ta zama sanadin lalata sunan mahaifinta dana familyn da yake nesa ta da shi gudun kada ya ɓaci, zuciyarta ta ƙe ƙashe duk damuwarta ta tsaya, lokaci zuwa lokaci take jan numfashi ta sauke sbd abinda ya tsaya mata a saitin zuciya da maƙo shinta. Tayi tafiya mai nisa sosai kafin ta samu wani waje kusa da wata bola ta zauna ta rungume yaron wanda ya yi shiru, jikinsa ya ɗauki zafi. Ji take kamar ta rataye kanta, ga jinin haihuwa daya gaba ɓata mata jiki a haka barci ya ɗauketa.
Tsaye suke gabaɗaya a parlour Hajia ta girgiza kai ta ce “Me kayi haka Zaki? Me ka aikatawa kan ka haka Aliyu?”
Almustapha ya kalli news paper ɗin ya ƙara ware idanunsa akan photon Bar Aliyu Sufyan Alhassan da kuma photon Malama Majeederh Abdul’aziz Khan dake zaune fuskarta rufe da liƙab. Almustapha ya shiga karanta headline ɗin jaridar. “Bar Aliyu Sufyan Alhassan shi ne ya aikata zina da Malama Majeederh Abdul’aziz Khan, tare da saninta domin su wulaƙanta matar Aliyu wato Latifa Omar kasancewarta aminiyar Jeederh” ya karanta a fili cikin zafin nama da faɗa Almustapha ya ce “Wanne shirme da hauka ne haka Aliyu? Zina? Ɗan shege?” Aliyu ya kalli yayan nasa ya ce..
“Ba shege bane” “To uban mene? Aurenta kayi?” Aliyu ya ce “Ko ɗaya, ina son ta am ready to marry her, ɗa kuma ba shege ba ne” Almustapha ya ɗauke Aliyu da mari ya ce
“Mahaukaci, to kayi gaggawar zuwa gidan jaridar nan ka ƙaryata rubutun su, ina da tabbacin kuma matarka Latifa Omar ce tayi wannan aikin ai a gidan jaridar take aiki”
“Tayi dubun su, ba zai sauya mini ra’ayi ba”
Cewar Aliyu. Almustapha ya ƙara ɗaga hannu zai mari Aliyu,cikin sauri Aliyu ya riƙe hannu ya ce
“Kasan Allah ka ƙara marina zan karya hannunka,ka bar ganin kai yaya na ne, idan kun shirya korata kamar yadda Mahaifin Majeederh ya koreta fine I’ll leave the house” abu kamar wasa dambe ya sarƙe tsakanin wa da ƙani cikin ɓacin rai Hajia ta zabgawa Aliyu mari ta ƙara zabga masa mari ta ce “Ka nutsu Zaki, ka nutsu” Aliyu ya fashe da kuka ya rungume Mahaifiyarshi ya ce
“What should I do Hajia? Dame zan ji ne? Wallahi idan kuka matsa mini zan iya aikata komai, Hajia I love Majeederh don Allah ki nemo mini ita, hajia hajia….,”
Da Hajia da Almustapha su kayi kan Bar Aliyu Sufyan Alhassan wanda ya faɗi a ƙasa sumamme…

Related Articles

Government House
Labarai ake ta ko’ina gabaɗaya kuma akan Malama Majeederh Abdul’aziz Khan ne, Human rights sun shiga maganar, ƙungiyar mata ta shiga maganar, shugaban ƴan hisba. Ya sauke ɓoyayyiyan numfashin tare da juyawa kaɗan ya kalli tulin jaridun da aka wallafa, gefe guda kuma yana mamakin gidan Jaridar Hausa lastest News, domin sun fi ko wanne gidan jarida ɗaukan zafi da kuma aibata Malama Majeederh. Sama sama yake kallon photon ta, bai taɓa ganinta ba amma muryarta kullum tana yi masa amsa kuwwa a kunne. “Ham…mad” Hammad ya yi sauri ya rusuna ya ce
“Your excellency” “Waye me wannan Shirman?” Hammad ya ƙara yin ƙasa ya ce “Wata ƴar Jarida ce, Latifa Omar”
Abu-turab ya ce.
“A dakatar da gidan jaridar” with so much respect Hammad ya ce
“With pleasure Your excellency” ya jinjina kai kawai, Hammad ya juya cikin sauri. Kai tsaye akai sanarwar da yawun Gwamna tare da bada umarnin rufe gidan Jaridar. Abu-turab ya kasa komawa gida, tun safiyar yake jiran ya ji ance an samu Malama Majeederh Abdul’aziz Khan amma shiru har biyar na yamma ya yi. Tajju ne ke driving hannunsa riƙe da Envelope yana ta yawo amma bai samu Majeederh ba, gashi har an kwana wani daren na shirin yi kamar ance masa ya juya idanunsa ya sauka akanta tana nan zaune bakin bolar ta ƙanƙame jaririn kamar za a kwace mata shi, ta fita hayyacinta duk jini ya ɓata jikinta, cikin sauri Tajju ya gangara gefen titi tare da yin parking yana Hammadala a ransa ya fito,bai san mene a envelope ɗin ba amma yasan dole yana da alaƙa da wannan jaririn babu ko tabbata musamman yanzu daya tuna wata rana. Yazo daidai tsakiyar titin yana ƙoƙarin tsallakawa wata ƙatuwar tifa tayi awon gaba da shi….

#Bar Aliyu Sufyan Alhassan
#Dr Jamal
#Abu-turab

Na’ima Sulaiman Shu’aibu
08119237616
Not editing*🌈 MIJIN MALAMA🌈*

Nimcyluv Sarauta

*_Please kuyi following Acct ɗina a arewabooks🫰🏿_*
https://www.arewabooks.com/u/nimcyluv

*AN SAMU MISTAKE, WANNAN SHI NE FULL PAGE NA 4 KUYI SHARING, A GOGE WANCAN🙏🏿*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button