Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 35

Sponsored Links

 

Baya Khalil ya yi idanunsa ƙirr akan Dad ɗinsa dake numfashi da ƙyar jini na malala a jikinsa, Dad ya ce “Ba zan yarda na mutu ni kaɗai ba, sai mun tafi tare ko ba komai na raunanawa Gimbiya zuciyarta” Dad ya furta a wahale, babu kowa a wajan kuma sai su kaɗai, domin jami’an tsaro na Pakistan sun yi nesa da wajan, duk da cewa suna hanya kafin ƙarasowar su wajan komai na iya faruwa da rayuwar duka su ukun. Clara ta tsaya cak saboda lissafinta ya kunce har wani shock kanta ke mata kamar wanda aka sanyawa na’ura, idan ta juya ta kalli Khalil dake kwance jini na wata kalar zuba har da tsartuwa a ƙirjinsa ga wata kumfa a bakinsa kamar wanda ke fidda dafara, jikinsa na rawa yana kar! Kar! Kar! Sbd tsananin azabar shigar wuƙar zuwa ƙahon zuciyarsa, da yadda allurar paison ɗin ke ratsa jijiyoyin jikinsa tana bi tare da kassara su, sai kuma ta juya ta kalli Gimbiya dake ɗaure da Bom, ta rasa wa zata fara taimako a cikin su, ta zama abar tausayi, Gimbiya idanunta akan Khalil, yadda ƙwayar Idanunta tai wani masifaffan sauya launi daga asalin fari zuwa rinannen jaa zaka san ta shiga tashin hankali fiye da tunanin mai fahimtar ta, Khalil numfashinsa na fisga yana wata iriyar miƙewa idan ya yi salati a hankali kuma yake furta “My wife, Jeena, maluma” Daidai lokacin kuma wasu manyan rukunin ƴan ta’adda masu yiwa Ddmaster bom kuma Mr President aiki suka kunno kai a wata jibgegiyar mota, hankali tashe Clara ta yi kan Gimbiya ta shiga lalata Bom ɗin wanda daman aikinta ne ta ƙware a wajan, duk abinda take a gigice take musamman yadda ta hango Khalil babu abinda ke motsi a jikinsa, kafin rukunin ƴan ta’addar su ƙaraso wajan su Khalil, wata mahaukaciyar mota mai bala’in gudu ta ƙaraso wajan, tana zuwa akai parking wani mutum ya fito ya shiga jan Khalil har ya sanya shi cikin motar ya rufe, a gigice Gimbiya tayi kan motar tana furta “Khalil! Khalil karka tafi ka barni, your wife Khalil, ur unborn child, ur family Khalil” Duk yadda take ƙoƙarin zuwa wajan motar abun ya gagara Clara ta riƙeta da kyau, ita kanta ta firgita da wannan ƴan ta’addar, Motar data ɗauki Khalil ta juya da wani irin azababben gudu nan take ƴan ta’addar suka rufawa motar mai ƙirara RAM-RAM baya, sun yi nisa sai motar ta shige wani layi, da sauri kuma motar ta fito daga layin ai kuwa sukai kan motar gadan-gadan, Clara ma binsu take a baya bayan ta saka Gimbiya a bayan motar, akan idanunsu motar da aka sanya Khalil ciki ta hantsila tare da kifawa, dalilin harsashin bindigogi daya farfasa tayar motar, wata kyakkyawar juyawa motar take tana gangarawa ta daki wani tsauni nan take wata gigitacciyar mahaukaciyar wuta ta tashi, motar ta fara ci da wuta kamar hauka, Gimbiya ta saki wani ƙara da ihu “Khalil! My son” Sai kuma numfashinta ya ɗauke cak ta tafi baya ta kifa babu numfashi, Clara ta zubawa motar Idanu, akan idanunta tana ji tana ganin ɗan uwanta abokin haihuwar ta, biyuninta ya mutu ya zama toka, wuta ta cinye shi murus. Ajiyar zuciya kawai take saukewa, a daidai lokacin ne kuma Helicopter ya sakko wasu manyan sojoji suka dinga sakkowa, gabaɗaya suka kewaye ƴan ta’addar, tare da komawa wajan Dad da bai ƙarasa mutuwa ba, suka tattara sukai gaba dasu. Wani Helicopter ɗin ne ya sakko daban, a gigice kuma cikin wani irin rikitaccen tashin hankali wanda ya ruftawa Mai martaba Ajlaal ya fito daga cikin Helicopter ɗin, duk yadda yakai da jin kansa hargitsatsen tashin hankalin bai hana shi jin wata ƙwalla mai azabar zafi ta shiga sakko masa ba, ya dinga kallon ragowar wutar da Khalil ke ciki da bata ƙarasa mutuwa ba, jikinsa na ƙyarma da ɓari da wata kalar rawa ya durƙoshe saman ƙafafuwansa, wanda suka gaza ɗaukan gangar jikinsa, few minutes gabaɗaya jami’an tsaro suka kewaye wajan, aka yayyafawa tokar ruwa aka kwashe a leda tare da bawa Mai martaba Ajlaal, wanda tun fitowar Khalil akan idanunsa ya kasa samun sukuni har sai daya samu cikakken bayani, a gigice ya sanya aka tashi private jet zuwa Pakistan yana sauka kuma ya tafi office na hukumar Pakistan ɗin, daidai nan ya samu labarin yadda ake ciki domin yaga komai ta jikin camera ɗin Khalil ya saka a jikinsa, ya ji komai, ya kasa motsawa Khalil ya mutu? Ashe bashi da rabon rayuwa mai tsayi da mahaifiyarsa? Da danginsa? Ya matarsa zata ji? Majeederh won’t take it, tuna yadda al’amarin zai risketa yafi komai gigita Mai martaba Ajlaal da kuma cikin dake jikinta, ya Zaytoon zata ji? Data ɗauki soyayyar duniya ta ɗorawa Khalil lokacin? Innalillahi wa’inna ilahir raji’un! Khalil died? Baya duniya? He’s no more. Da ƙyar aka tattara su har da Clara wadda ta shiga Shock ko motsi ba tayi bata fahimta da idanu kawai take ganin komai, Gimbiya bata farko ba har aka tattara su cikin Helicopter ɗin zuwa airport da niyyar komawa Nigeria da mummunan labari wanda zai tarwatsa zuciyar mutane da dama.

Kafin ƙarasowar su, Mai martaba ya turawa Uncle Isma’il saƙo ta mail, kancewa su shirya zai turo private jet ya ɗauke su, urgently, hankalin Uncle Isma’il ya kasa kwanciya daman sai faɗuwar gaba yake kwana biyu,ya nufi gidan Uncle Bello ya shaida masa “Yaya kana ganin lafiya?” Uncle Isma’il ya shiru kafin ya ce “Ina zan sani Bello? Ina fatan ya kasance lafiya ɗin” Uncle Bello ya ce “Ubangiji ya sa Yaya, gabana faɗuwa yake sosai” Uncle Isma’il ya ce “Ba kai kaɗai ba Bello, jiya ban iya bacci ba” Ya ce “Ina General” Uncle B ya numfasa da ƙyar ya ce “Kasan suna ta fama da juyin mulkin nan da na ji ana ƙishin ƙishin ɗin yi” Ya jinjina kai yana miƙewa ya ce “Ba lallai ya samu damar zuwa ba” Ya ce “Haka ne Yaya, amma zan sanar masa” Sallama sukai daga nan ya nufi gidan Abbu. General Alpha na tsaye cikin wasu haɗaɗɗun kayan sojoji, na Uniform ɗin General waya yake dannawa a hankali kafin gently kuma ya yi kamar zai shiga gidan su sai ya faɗa na maƙociyar su, yana shiga wasu fararen yara masu kyau babba da ƙarami sukai wajensa da gudu ɗaya na cewa “Abbie, Abbie” General ya ɗauki ƙaramar yarinyar Dina yana rungumeta ya ce “Mamana” Zuleehart ta fito daga kitchen a sanyaye ya kalleta ganin bata da walwala ya sanya ya zauna saman kujera ya kalli Waheed ya ce “Ina Bilal?” Bilal ya fito ya ce “Wlcm Abbie” Ya nuna masa ƙannen shi Waheed da Dina ya ce “Kama su kuje, be careful” Ya ce “Yes Abbie” A hankali ya kalli Zuleehart ya ce “Are you okay?” A hankali ta ce “Haba General kamar is not necessary ma ka tambaye wannan, how can i be okay? Secret marriage over year’s?” Ya kwantar da murya ya ce “It was destined wife, ƙaddara da rabon su Bilal ya ƙaddara aure na dake ba tare da sanin kowa nawa ba, bani da zaɓi dole ta sanya na rufe aurenki ki ci-gaba da haƙuri komai zai daidaita” A hankali ta ce “When?” Ya ce “I don’t know, bana ce ba, kawai dai komai ya faru ƙaddara ce daga Ubangijin sammai da ƙassai” Ta girgiza kai tana hawaye ta ce “I am tired General, na gaji i need freedom to live my life, kullum ina ɓoye Bilal saboda kamar da kuke gudun kar a ganshi kasan yaro har ya fara tambayata Maama meyasa kike ɓoye ni? Wanne irin aure ne ko saboda kana son matar wani shi yasa ka kasa nuna ni wa danginka?” Ya kasa ce mata komai domin deep down na zuciyarsa gani yake a koda yaushe first love ɗinsa zata dawo gare shi ba zai yi sacrifice a banza ba, dole zaiyi rayuwa da majeederh wannan wani al’ƙawari ne na sashin zuciyarsa.
Kamar yadda Mai martaba Ajlaal Sultaan ya yi al’ƙawari haka jirgi ya kwashi su Uncle Isma’il, banda ƴan matan dake gidan mazajan su, saukar su kuma ya yi daidai da fitowar su Clara daga cikin jirgi kai tsaye kuma motar ujila aka kira ta asibiti aka tafi da Gimbiya tare da Clara, Uncle Isma’il jikinsa ya yi sanyi, Abbu kuma tunda yaga Mai martaba haka ya ji gabansa ya yanke ya faɗi, basu ce komai ba suka nufi Palace. Zaytoon na zaune tayi jigum lokaci zuwa lokaci kuma Roohan ke kallon ta, can ya ce “Zaytoon tunanin me kike?” Ta ce “Roohan rayuwa, rayuwa Roohan, na yi farin cikin yadda iyalaina suka dawo gareni Roohan, babban burina kuma d’ana jinin Gimbiya Khalil ya share mini komai na damuwata….,” Bata ƙarasa ba taga Ajlaal ya zube a gabanta, sauran familyn Khan suka shigo hadda Maman Alpha da Mami, Zaytoon ta ce “Khalil ya mutu?” Ajlaal ya kasa cewa komai Uncle Isma’il ya ce “Wanne irin Khalil kuma? Baya nan ne?” A raunace ya ce “Zaytoon, Khalil died, Ibrahim ya rasu” Daidai nan Majeederh ta fito daman wanka tayi ta zuba uwar kwalliya ta haɗa lunch na musamman saboda Khalil, Khalil love sakwara miyan egusi tana zaune kuma bacci ya ɗauketa, wanda ta gwammace ba tayi ba, domin wani irin mummunan mafarkin tayi wai ga Khalil kwance baya motsi an shimfiɗa masa farin abu, tana kuka tana cewa kar ya tafi shi kuma yana mata murmushi yana cewa “Bye bye” Tana farkawa ta fito a hargitse taga ko ya dawo ya sameta tana bacci ne? Sai dai tayi imani da Allah Khalil ya ganta tana baccin yamma sai ya tasheta ta dole ya ƙirƙiri abinda za tayi masa domin ya ce baccin yamma gamai ciki is not good for the health, fitowarta ya jiye mata wani sauti wanda har ta koma ga mahaliccinta ba zata taɓa daina jinsa ba, “Khalil died?” Sai kuma ta ƙarasa tana daga tsaye take kallon Zaytoon, wacce tayi shiru Maman Alpha kallon Majeederh kawai take Innati tayi shiru haka Yaya Bilkisu,Mai martaba ya ce “Mun rasa Khalil, ko gawar shi babu sai toka” Majeederh ta ce “Ikon Allah wanne Khalil?” Ya ɗago ya kalleta da kyau rauninsa ya ƙara bayyana a fili, ya miƙe da ƙyar ya rasa me zai ce mata saboda mutuwar miji musulmin mutuwa ce, a hankali ya kama hannunta ya ce “I am sorry na kasa kula da shi, ban je akan kari ba, Khalil ya rasu” Majeederh ta ce “Wanne Khalil? Allah ya jiƙansa” At this time Majeederh tama mance sunan mijinta Khalil balle ta fahimta, ya saka hannu ya girgiza ta ya ce “Khalil ya mutu Hawwa’u” sai ta saki dariya kamar mahauckiya tana ƙyaƙyatawa ta ce “Khalil ya mutu Khalil ya mutu wanne Khalil? Nace Allah ya jiƙansa” Ta ɗan juya tana leƙa waje sai kuma ta ce “Ina man? Where’s my Husband? Ina Khalil?” Uncle Isma’il da idanunsa ya yi jajur ya ce “Ka barta, Yaya Bilkisu shigar da ita ciki” Mai martaba ya girgiza kai ya ce “Ba buƙatar rufeta, ko ɓoye mata dole ta san baya duniya gudun kada ta zauce” Ya ƙara matse kafaɗarta ya ce “Your Husband Khalil mijinki, mijin Malama Abraham baya duniya ya rasu Khalil Died!” Wata ajjiyar zuciya ta sauke tabi Mai martaba da kallo bata cewa komai, ya fahimci brain ɗinta ce tayi hook ya ɗauki ruwan sanyi mai ƙanƙara ya sheƙa mata ta sauke ajjiyar zuciya a gigice kuma ta ce “Mutuwa? Ta rasa wa zata ɗauka sai Khalil? Ai ko ita kanta mutuwar ta ji nauyi da girma da kunyar zuwa ta ɗauke mini miji, Khalil ba zai taɓa mutuwa ya barni ba” Wani irin kuka Yaya Innati ta fashe da shi ta ce “wallahi tallahi ta haukace, wallahi kululu ta haukaci mun shiga uku” Majeederh ta shaƙe wuyan Mai martaba tana zare Idanu jikinta na rawa ta ce “Khalil bai mutu ba, ba zai taɓa mutuwa ya barni ba sai dai mu mutu tare, wallahi mijina bai mutu ba ka faɗawa mutuwar ƙarya take….,” Sai kuma ta sulale tare da kifawa kan Ajlaal babu numfashi, daidai nan kuma aka shiga kiran number Ajlaal a gaggauce yana ɗagawa ya ce “What? Where?..
[

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button