Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 25

Sponsored Links

25…..

_this novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi, pay anan or pay achan, your choice_

_masu fitarmin da novel waje kuda Allah_

Related Articles

_in kinason this novel zaki turo 300 ta 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

_you can also send MTN card ta watsapp na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_

 

Har Aabid yajashi yafitar dashi daga dakin wani irin faduwa gabanta yakeyi takasa daina kallon kofan kirjinta nawani irin bugawa tanajin wani irin tsoro, ihun dataji na Aadil yasa ta dafe chest dinta danjin ihun tayi har karkashin zuciyan ta, sakejin ihun tayi tareda kuka hakan yasa tawani irin zabura ta sauka daga kan gadon tai hanyar kofa dagudu. “auchhhh” tai wani irin kara sabida yanda taji allauran dake jikinta yawani irin chakanta, ita gabaki dayama ta manta dashi, komawa da baya tayi ahankali jikinta na rawa sosai tasa hannu ta cizge kanulan dudda hanunta na jini amma ko damuwa batayiba, tai hanyar kofa tabude ahankali kaman wacce tazo sata tana kallon ko’ina, tunda take bata taba ganin hadadden palo hakaba, hanyar inda taji kukan Aadil sosai tayi zuciyar ta namata wani irin rawa babu kowa a shashin daidai gaban kofan datakejin kukan sosai ta tsaya takasa budewa. “kai mahaukaci ne, Aadil kai mahaukaci ne bazaka taba aure ba danba abinda kasani kanajina, u are mentally unstable, kai pagal ne stay away from my Jewel kanajina mahaukaci” da sauri ta runtse idanunta ta dafe bangon da sauri harcikin zuciyarta taji zagin. “she’s my wife, Hamida is my wife” taji muryan Aadil saikuma taji wani irin karan saukan belt ne ko bulala oho, ihu da kukan Aadil taji sosai yafashe da kuka itama kukan tasaki batare data saniba ta daura hanunta akan kofan tanajin wani irin radadi da ciwo aranta, kwas, kwas, karan takalmi da alamun gudu dataji yasa arude tafara waige waige tana kuka sosai jikinta na rawa tana neman inda zata buya, wani babban hadadden flower verse silver data gani gefen kofar su ga hadaddun flowers aciki yasa tai sauri taje bayan verse din ta tsugunna talabe ta daga kanta ta flowers tana kallon kofan dantaga wazaizo ya wuce, Mami ce tazo da gudu hartana neman faduwa ta bude kofar dakin ta shiga da gudu taji Mami ta kwala kara. “Aabid, innalillahi wa innailaihi raji’un, Aabid zaka kashe dan uwanka ne” wani irin taushe bakinta tayi da hannayenta duka biyun dan bataso kukan datakeji yafito, karan bude kofan datasake ji yasa tasake dagakai ta leka ta tsakakanan flowers wani tsoho tagani da dan magidanci sun shiga dakin cike da tashin hankali, taji muryan namiji yace “Aabid kana hauka ne?” kukan Aadil tacigaba da ji dake fita da kyar kanajin sautin kukan zakasan ya galabaita bana wasaba, muryan Mami taji tace “ka dakemu tare kaji Aabid”….

 

Rafkamai sandar Baffa yayi akafa da karfi, hakan yasa Aabid da idanunshi sunyi jazur ya dago kai ya kalli Baffan dan yaji zafin bugun, wani irin mari Baffan yadauke shi dashi kafinma ya farga. “pa, pa, pau” yamai guda uku, dafe kucinshi Aabid yayi ranshi a mugun bace kanshi akasa, Baffa ya nunashi da sandarshi yace “kasheshi zakayi Hussain? Nace kashe shi zakayi? Koma meyamaka bazaka iya hakura ba sanin halin dayake cikiba, jibi irin dukan dakamai saikace ubanshi ne kai, bai girmeka ba?!” Baffa ya dakamai tsawa yace “Hassan yarigaka shan iskan duniya sanan saigaka kaima kafito, kai wani iri ne, bakada imanine Hussain? Uban wa yataba dukanka haka aduniyan nan tunda aka haifeka? Hassan dake bala’in sonka kama mahaukacin duka haka Hussain?” Baffa yay maganan yana nunamai Aadil dake kuka sosai jini nabin gefen pink lips dinshi bama ya iya kuka tsabagen kukan dayaci sai ajiyan zuciyan kuka yake ajikin Mami, Abie kuma yadauko first-aid box yana kokarin budewa dan sharemai jinin dakenbin lips dinshi, shatin jini-jinin da Mami tagani ta jikin white shirt din dake jikinshi yasa ta daga Aadil din daga jikinta da saura taja riganshi sama shatin belt dahar dan jini jini ke fita daga fatanshi, daga ita har Abie dagokai sukayi suka kalli Aabid din da kanshi ke kasa, hawaye Mami ta share ta kira sunanshi cikin wani irin raunanniyar murya. “Aabid” dago kanshi Aabid yay ya kalli Mamin da jajayen idanunshi, hawaye ta kara sharewa tasake rungume Aadil din dake nishi da ajiyan zuciyan kuka ko motsin kirki baya iyawa idanunshi a kulle yay lamo a kirjinta yarike mata hannu gam yana nishi, ahankali tace “Aabid d…dan uwanka kama dukan mu…g…” kasa magana tayi sabida wani irin kuka dayazo mata sosai bakaramin tausayi Aadil din yabata ba jitayi da ita Aabid yama dukan nan dayafi mata sau dubu akan Aadil mara lafiya wanda baimasan zafin kanshi ba, yaron da kullun suna hanyar asibiti dashine yama wanan dukan rashin imanin, share mata hawayen daya kasa daina zuba Abie yayi tsabagen bakin ciki da kuncin datakeji, kana Abie shima kasan ranshi abace yake, janye hanunshi yayi daga fuskar Mami bayan yagama share mata hawayen yace “is okay, barshi” ya dago kai yama Aabid din wani irin mugun kallo yace “wuce katafi abunka” kasa daga kafa Aabid yayi yafita daga dakin ko motsi yakasa saima kanshi dayakai kasa, cikin wani irin ihu Mami taja belt dinshi dake gefenta ta wurgamai belt din yafada kanshi tace “ance ka wuce kafita daga dakin nan, kozaka hada damune kadaka eh zalim?” dan dago kai yayi ya kalli Mami zuciyarshi namai wani iri da sauri yajuya yafita daga dakin kaman zai tashi sama yay tsakar gida ya shiga mota yaja motar yabar gidan da shegen gudu.

 

Ahankali tafito daga bayan verse din tana kuka sosai ta tsaya abakin kofan so kawai take taga Aadil din da zuciyarta ke mugun kwadayin ganinshi.
Gogemishi jinin gefen bakin Abie yayi yadan bude ido kadan yana kuka ahankali ya rirrike Mami, kiss Mami tamai a goshi jin yanda jikinshi yadau wani irin zafi sosai kaman an sakashi a oven, tsugunnawa Baffa yayi shima yana kallonshi yamika mai hannu alamun yazo kaman yanda akema yaro yana kallonshi, ahankali Mami tadaga kanshi daga jikinta tace “zakaje wajen grandfather, oya go” wasu irin hawaye ne suka bulbulo ta gefen idanunshi yana wani irin nishin kuka da karfi kaman mai asma dan abun nawani irin sosa mai rai, cikin muryan kuka sosai yace “Bid beat me Mami” yay maganan wasu sababbin ruwan hawaye na zubomai daga ido, dasauri Mami tawani irin rungumeshi tsam tsam tana jijjigashi sosai Aadil weak point dinta ne sosai, batason abunda zai taba innocent boy dinan, tunda tahaifi Aabid baitaba bata mata raiba irin nayau, sosai take jijjiga kanshi a kirjinta tana bubbuga bayanshi jin yanda yake wani irin kuka tace “is okay, ya isa kaji, mekamai yadake ka? Karka sake kashi” cikin kuka sosai yanayi kaman zai suma yace “Bid hate me Mami” da sauri Mami ta girgiza maikai tana neman yin kuka dan daurewa kawai take tasa hannun riganta ta sharemai fuska tace “no, no no, dont say that, Aabid bai tsanake ba, yana sonka sosai ko Baba” ta tambayi Baffa dake kallon Aadil din, gyadamata kai Baffa yayi yace “Aabid na sonka sosai kaji dan kirki” girgiza musu kai yayi zaiyi magana saikuma yafashe da kuka sosai tafada jikin Mami, tashi Baffa yayi da sauri dan wani irin zafin dukan da Aabid yamai yakeji yajuya yay hanyar kofa yana dogara sandarshi, ko kadan bataji alamun tafiyan mutum ba sabida kukan datake sosai tana sharewa da bayan hannu, yanda Aadil keta maganganu yanatasa zuciyarta nawani irin karaya jitake kaman ta daukemai ciwon dukan, bude kofan Baffa yayi arude tai baya tana kuka sosai ta saukar da kanta kasa tana kokarin tsayar da kukan datake data kasa, binta da kallon mamaki Baffa yayi wearing a smile akan fuskarshi kafin ahankali yace “bakuwa kin tashi ya karfin jikin?” gyadamai kai tayi tadan dago kanta ta leka Aadil ta gefen Baffa dake tsaya abakin kofan, hangoshi tayi jikin Mami dake kallonta asanyaye da Abie daidai lokacin Aadil din yabude idanunshi dake buduwa da kyar sun kumbura sunyi jajir ya kalleta innocently, lumshe ido yayi ya budesu ya miko mata hannu daga inda yake da kyar tsabagen zazzabin dake cinshi, dawata irin murya dabata da kara sosai yakira sunanta yana mika mata hannu yace “My H..Hamida” fashewa tai da kuka sosai tana share idanunta da bayan hannu tana kallonshi yanda taga fuskarshi ya kumbura da lips, takasa koda motsi daga inda take ta daura hannayenta akan bakinta tana kuka, wani irin tausayin shi takeji bana wasaba, sosai Baffa ke kallonta yana karanta wasu abubuwa tattare da ita kafin ahankali ya juyar da kanshi ya kalli Aadil din dake kuka ahankali yana kiran sunanta agalabaice yana mika mata hannu yana lumlumshe ido kaman mai shirin yin bacci, ahankali Baffa yasake juyowa ya kalleta yace “ki shiga ciki mana yarinya kin tsaya anan” gyadamai kai tayi tana share hawayen datakey, Mami ma murmushi tayi tana kallonta tama kasa magana, ahankali tafara tafiya Baffa ya matsa mata ta shigo dakin Abie yay shiru yana kallonta harta karaso tsakiyan dakin ta tsugunna ata gefe tana kallon Aadil din tana kuka, wani irin tashi Aadil din yayi daga jikin Mami ya rarrafo da kyar yakaraso inda take ya tsaya gab da ita yana kallonta, fashewa tai da kuka sosai tana kallon fuskanshi, fadawa yayi jikinta yasaki kuka sosai itama kuka tasaki tana girgiza mai kai, ahankali ta ciro kanshi daga jikinta tai cupping face dinshi tana kallonshi, lumshe mata ido yayi hawaye suka zubo, murya chan kasa ta kuka yace “Bid beat me” yasake sakin mata wani kukan, girgiza mai kai tayi takai hanunta ahankali ta sharemai hawayen dake zubowa tace “stop crying okay” make mata kafada yayi yawani narke mata hakanan yaji yanajin wani iri farinciki sosai, ahankali tana kuka sosai dan kawai tasashi murna tace “where is my chocolate?” ware manyan kumburarrun idanunshi yayi yace “i don’t know, I’ve lost it wen Bid was beating me” gabaki daya tama manta dasu Mami na wurin burinta kawai yay shiru yadena kuka yadawo normal Aadil daya iya damunta, hararanshi tayi ta murguda mai baki tace “find it” wani irin bude ido da baki yayi yana kallonta saikuma ya leka nose dinta kaman ba shine yaci duka yanzun nanba yace “ur nose is a robotic nose” murmushi tayi sosai daya bayyana dimple dinta da sauri ya daura hanunshi kan hancinta yaja yana dariya yace “do it again, saikin kara yimin” dariya tayi ta fizge hancinta shima yay dariyan yana clapping hands dinshi, Mami, Abie da Baffa duk sukai shiru suna kallonsu kowa da abinda yake kawowa aranshi daidai lokacin Suleman yazo wajen, hanunshi Baffa yaja batare daya bari ya shiga dakin ba suka bar wajen yace “Baba har yarinyar ta tashi ne” gyadamai kai Baffa yayi suka karasa falon Baffan, zama Baffa yayi akan kujeran zaman yi yay dan shiru nayan sakanni, shiru Suleman yayi dan yasan inhar Baba na tunani bayason anamai magana, dan ajiyan zuciya ya sauke ya kalli Suleman yace “Sulemanu” da sauri yace “na’am Baba” gyara zaman shi yayi yace “inaso kamin binciken yarinyar nan, wanan bakuwan data taimaki Aadil, inaso nasan wacece ita, sanan inaso nasan iyayenta dakomi nata daga nan zuwa gobe” gyadamai kai Suleman yayi yace “shikenan Baba angama, amma Baba mezakayi da information dinta haka?” shiru yayi saikuma yay murmushi yace “time will tell, kaidai kamin abinda nace”.
_🌹IN BANI 🌹_

Maman Abd Shakur

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button