Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 27

Sponsored Links

NIMCYLUV
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *_Arewabooks@Nimcyluv_*
Bayan sun sauka a harabar gidan Khalil ya sake tura wheelchair ɗin fuskarsa ɗauke kwantaccen murmushi, suka haɗa Idanu da Rohaan ya harare shi, Rohaan ya ce “Yaro ya girma” Khalil dai a nutse yake tura ƙyakƙyawar wheelchair ɗin da Bafullatanar matar ke zaune kai cikin wata dakakkiyar abaya mai laushi da taushi, speaking calmly ya ce “Are u okay?” Ya faɗa a hankali yana leƙa fuskar matar ganin tayi saurin riƙe hannunsa lokacin daya gangara da ita zuwa cikin entrance, ta zuba masa idanu ba tare da ta ce komai, Mai martaba Ajlaal Sultaan ya ce “Don mind her, kwana biyu haka rigimarta ke tashi” Khalil ya yi shiru sai kuma ya kwaɓe fuska irin bai ji daɗin nan ba, a haka suka nufi gidan Ƙhulud Arzaan ta dinga kallon gidan cike da sha’awa ganin yadda tsarin yake kamar a Turai a haka suka shiga….. Few minutes Khalil ya sake ɗago kansa with different things in his heart ya ce “hope everything goes well?” Mai martaba Ajlaal Sultaan ya numfashi cike da yanayi na kamala da riƙe yana kallon yadda ƴar tasa take ya mutsa fuska a hankali a taushashe yana fidda zallar kwarjini dake lulluɓe a jikinsa ya furta “Allhamd” Khalid ya jinjina kai, gabaɗaya hankalinsu yana hospital gangar jikinsa ce kawai a nan, amma nutsuwa da wani kuzarin da kan riƙe kan shi da shi ya yi nisa tare da ƙaura a jikinsa, ganin kamar tunaninsa da zuciyarsa ta Kaɗaita da inda suke ya sanya Ƙhulud ce wa أخي أنا” زوجتك” Bi ma’ana ‘akhi ‘ana zawjatuk. Ya ɗan rausayar da kansa gefe yana watsa hannu clamly ya ce “What?” Ƙhulud tayi dariya ta ce “Kana mijin Malama baka iya larabci ba? Ya zama dole naci tarar Hawwa’u, ina matar ka?” Ya lumshe gajiyayyun idanunsa masu ɗauke da wasu masifaffun sinadarai zuciyarsa na masu nauyi ga wata kyakkyawar faɗuwar gaba dake riskar shi tana shigar dukkan wata ƙofofin zuciyarsa da suka bubbuɗe gabaɗaya tare da amsar fargabar a gaggauce da yanayi na sauƙaƙe wanda yake shimfiɗe har saman fuskar tashi. Ya ɗan fiddo ido ya ce “She’s in the hospital” A kusan tare cikin zullumi da yanayi na makake na rashin sanin cikakken halin da zuciyoyin nasu suke ciki, Zaytoon ta juya ta kalli Mai martaba shi kuma ya yi saurin girgiza mata kai a kamalance yana mata nuni da tayi shiru karta ɗaga maganar, Ƙhulud ɗin ma ba tayi magana ba, tayi shiru tana kallon Zoya da Zohal da suke lumshe idanunsu za su yi bacci, Mai martaba ya kalleta ganin yadda ta zuba masa Idanu kamar mai karanto gaskiyar dake zuciyarsa wacce dauriya da kamala ta rufe su ta hana fuskarsa nuna, ya dubeta da kyau a nutse ya ce ماذا تريدين أيتها الأميرة؟ “madha turidin ‘ayatuha al’amiratu?” Ma’ana me kikeso GIMBIYA? Ta rirriƙe hannun Ajlaal Sultaan sosai hawaye na bin fuskarta ga zufar dake tsastsafowa daga goshinta jikinta ya yi sanyi ƙallo, kanta dake cinyar Ajlaal ya shafa a hankali, yanayin yadda take marairaicewa Ajlaal zaka fahimci matsananciyar Soyayyar dake tsakaninsu shi da Gimbiya domin tuni ya fara birkicewa ganin yanayin nata ya riƙeta sosai a hankali kuma yake goge mata zufar, Khalil ya zame Idanunsa daga kanta yana daga zaunan kuma ya ɗauki remote ya ƙure Acn dake cikin haɗaɗɗan part ɗin da suke zaune, Gimbiya tayi shiru tana sauke numfashi, a hankali ta juya kallonta ya sauka kan Khalil….
Majeederh na kwance idanunta rufe ba bacci take ba, amma yadda tayi shiru zaka ɗauka baccin take, tunanin abinda ya hana Khalil dawowa asibitin take tun safe, bata son zuciyarta ta raya mata yana wajan Debeka domin fahimtar hakan daidai yake da samun rauni a zuciyarta, jin ƙarar buɗe ƙofa ya sanya tayi saurin buɗe ido tana juyawa ganinta ya sauka akan General Alpha Bello khan, ya yi tsaye cikin sabuwar shigarsa ta farin voyel na ƙanan zane a wannan karan bai saka hula ba hannunsa zube cikin aljihu ya ɗan ƙara kallonta sai ya ɗauke kansa gefe, don tunda ta nemi sumewa data gansa bai ƙara shigowa cikin room ɗin ba, duk da kasancewar yana cikin hospital ɗin, ya nemi waje ya zauna yana danna wayarsa yana jin yadda idanunta ke yawo a kansa, can ya buɗe baki ya ce
“Lafiya? Wannan kallon fa? Kina bina wani abu ne ko na taɓa yaudarar ki? Akwai abinda kike so ne wanda kika gani a jikina? Kada ki cinye ni” Majeederh ta ware Idanu a ranta tana cewa “Mr arrogant, a tambayi mutum komai banda hali” Alpha ya ɗago kai gabaɗaya yana kallonta ya haɗe fuska sosai ya ce “Kin sanni ne?” Tayi shiru sai kuma a sanyaye ta ce “Who are you?” Ya kalleta sai ya miƙe gently zuwa inda take ƙwance ya zauna tare da miƙa hannu zai kama nata tayi saurin janyewa tana yaƙe a hankali ya ce “Why? Why are doing this to me?” Ta ware Idanu cikin rashin fahimta ta ce “Me na yi?” Ya ce “Stop answering my questions with a question Zabiya” Tayi masa shiru daman idan masifa ce no 1 ne shi, ya runtse idanu ya buɗe muryarsa na rawa sosai ya ce “You couldn’t wait for my return, you married someone else” Da mamaki take kallonsa ta kasa cewa komai ba, ya ce “Me ya sa? Kin taɓa tambayar kan ki rashin dawowata?” Ta girgiza kai Idanunta na kawo ruwa ta ce “Am sorry Yaya, but is no my fault yaya da bakinka ka ce baka so na idan ka aureni zaka iya mutuwa ko ka kashe kanka ko ni” Muryarta ta fara rawa sosai tana shassheƙa ta ce “Na rasa yadda a lokacin ji nake na rasa komai nawa, u left me yaya” Sai kuma ta sunkuyar da kanta tana riƙe kukan dake shirin ƙwace mata abubuwa da yawa suka shiga dawowa mata a kanta kamar lokacin suke faruwa da ƙyar ta ce “Yaya na tashi da kulawarka ban san damuwa ba idan ina tare da kai, tun ina ƙarama kake kula dani ka ɗauke ni da hannayenka, hakan yasa na tashi da soyayyarka na ɗauka kawai zumunci ne, sai dana girma na fahimci saɓanin hakan” Ta fashe da raunataccen kuka, Alpha ya yi shiru a hankali ta ce “Bayan na girma na san sonka nake da gaske, na fahimci ba haka a ranka domin babu alamun soyayyata a wajanka bisa dole na haƙura, sai kuma gashi lokaci ɗaya ka dawo mini da son ka sabo na saka rai da aurenka zan mallake ka, amma ƙaddara ta shata mini layi da samun abin da nake so ka sanya ƙafa ka shure al’ƙawarin da ka yi mini, duk da har lokacin You never said that you love me, you just said that you will marry me and then you went away and left me, na wanzu da ciwo da zafin abun a raina na kuma ƙara jin cewa da gaske na zama mujiya a idanun maza tunda naga aya akan ɗan uwana” General Alpha ya daddafe kansa yana komai na sara masa bai san ta yadda zai fahimtar da ita ba, babu wasu sauran kalamai da suka rage masa a bakinsa, ya sassauta murya ya ce “U misunderstood, ki bani dama” A tsorace ta ce “No way” Tayi murmushi ta ce “Maganar dane, yanzu na jima da share tantanma na gane a cikin maza akwai nada ban” Calmly ya ce “Wannan nada ban ɗin ni ne” Ya zame tare da durƙosawa a gabanta tunda ba zata iya tashi ba, she’s in serious sick ya ce “Kin taɓa tambayar kanki me ya sa na fifita ki da ƙanne na? Da sauran ƴan uwanki mata? Kin taɓa tunani me ya hanani aure bayan Ubangiji ya bani ikon yi? Kin taɓa tambayar ko da wasa bana maganar wata ƴa mace?…,” Tayi shiru ya kalleta murya ƙasa ya ce “I did this because of you” Ya yi ƙasa da murya underneath his breathe ya ce “I love you, i so much loves you Hawwa’u i love you” Kuka take sosai kafin ta ce “Am sorry Yaya, Ina son mijina” Da sauri ya ɗaga kansa ya ce “Liar, a rashina kika so shi, a babu ni kika amshe shi, sbd na yi nisa dake kika kusance shi, sbd na raba hannu dake kika riƙe nasa, yanzu kuma na dawo” Ta kasa cewa komai sai kallonsa da take da ƙyar ta ce “I love Khalil Yaya” Da ƙarfi ya ce “Stop saying this to me, ba zan taɓa yarda dake ba kamar yadda kike so na, har yanzu har gobe har ƙiyama ta tashi you will still loving me….,” Daga bakin ƙofa suka ji an ce “Loser” Muryarsa ta fita da ƙyar Majeederh bata buƙatar sanin ko waye ƙamshin turarenta ya wadatar ya shaida mata cewa shi ne, Alpha ya Khalil dake cikin wata fitinanniyyar Shadda dark blue ya harɗe hannu a ƙirji, Ubangijin ne kaɗai yasan adadin daya kwashe tsaye yana jin su, idanunsa ya rine har baka ganin ƙwayar idanunsa sosai slowly ya ƙarasa shigowa ciki ya nufi inda Majeederh take kai tsaye tayi saurin rufe Idanunta tunaninta dukanta zai yi, sai ta ji saɓanin haka ya saka hannu tare da ɗaukanta cak ta buɗe idanu tana saurin riƙe shi a hankali taga ya miƙar da ita tsaye kamar sai saketa tayi saurin saka hannu ta rungumesa tana kwantar da kanta a ƙirjinsa a shagwaɓe ta ce “ba zan iya tsaiwa ba, I feel dizzy” Khalil ya kalleta sai kuma ya yi murmushi mai kyau ya ce “I’m hear with u Madam” Tayi murmushi domin harga Allah tama mance da batun Alpha a wajan, a hankali a nutse Khalil ya rungumeta tare da janta zuwa bakin window ya yaye labule da hannu ya nuna mata ƙyakƙyawar motar dake wajan an saka flowers tare da yin rubutu “For u wife” daga gefe aka ce “Thank you so much” Ya juya da sauri tana kallon Khalil murmushi fal fuskarta ta ce “For me?” Ya jinjina kai ya ce “Yes Wife” Sosai take mamakin yadda a kalaman Khalil babu i love you, a hankali ta shige jikinsa tare da rungumesa sosai tayi masa small kiss a wuya ta ce “Thank you, Allah ya ƙara ariziƙi” Ya shafa cikinta yana sauke numfashi a hankali ya ce “Ya ƙara alrdy” Ya nuna mata hancinsa ta kalle shi ya ce “Kiss me” slowly tayi kissing wajan ya nuna baki ya ce “Not small, a special kiss Madam” Ta ja hancinsa a hankali kuma ta haɗe bakinsu waje guda ta shiga sauke masa wani irin masifaffan hot kisses ta mance da wannan ɗan ƙwaninin yaron take tsaye ta mance suman da tayi na bata so da ƙaunar shi, da wani irin ƙarfin ta ji an fisgeta har sai da tayi ƙara tana ƙanƙame jikinta jikin Alpha duka rawa yake, A tsorace Majeederh ta ƙwace hannunta Alpha ya yi kneeling down a gabanta ya ce “I know I did you wrong, karki hukunta ta wannan hanyar u hurting me” Sai kuma ya fashe da wani irin kuka ya nufeta kamar zai rungumeta ya ce “I love you so so much &most, i so much loves you Hawwa’u, wallahi ni ne wanda kike so ba shi ba, idan taƙamar kin rai ne shi ni na ni na raineki i sacrificed alot sbd ke i love you Hawwa’u ki tambayi Abbu shi ne shaida” Da wani irin zafin nama Khalil ya nufi kan Alpha ya shaƙi wuyansa sam Alpha bai attempting kare kansa ba, Khalil ya shiga zubawa Alpha wasu tagwayen maruka yana sakar masa naushi a ciki, Majeederh ta runtse idanu tana jin saukar marukan har zuciyarta da ƙarfi ta ce “Khalil!” Ta kira sunan shi da ƙarfi, ya tsaya cak sai kuma ya juya yana kallonta ta ce “Stop” Ya saki Alpha ya ce “Jee stop kika ce? Akan shi?” Ta girgiza kai ta ce “Ba a kansa bane, bana son wani abu ya faru ace kai ne” Ya dinga kallonta sai kuma ya yi wani irin wannan Alpha ya tsaya gaban Khalil ya ce “U see? Ka dai gani hakan zai tabbatar maka da gangar jikinta kake aure ba zuciya ba, kaga zahirin True and enternal love” Khalil ya sake juya ya kalli Majeederh za tayi magana ya ɗaga mata hannu ya juya da sauri ya fice daga cikin room ɗin yana buga musu ƙofa da ƙarfi, wani irin jiri Majeederh ta fara ji sbd tashin hankali da ƙarfi kuma ta saki ƙara tana dafe mararta kafin ta faɗi Ajlaal dake shigowa ya taro ta faɗa jikinsa a sume….
Tun shigowar shi emergency ɗin yake tsaye ya kasa ko zama, a hankali kuma Uncle Isma’il ya ce “Alhji Abdul’aziz ka shiga mana?” Ya ɗan girgiza kai ya ce “No, Allah ya bata lafiya” Maman Alpha dake zaune ta ce “Amin” Sai kuma ta juya ta ce “Yaya Bilkisu, Hajiya Asabe Here is my neighbor Zuleehart ku gaisa” Yaya Bilkisu ta ce “Sannu Zuleehart ya gida” Tayi murmushi ta ce “Allhamd, ya mai jiki?” Ta ce “Lafiya Allhamd, ya kuma yara?” Ta ce “Suna can tare da driver” A hankali Zuleehart ta gaisa da kowa har Khalil kana ta ce “Ance maka da lafiya kai ma? Allah ya sauwaƙe” A hankali Alpha ya ce “Thanks” Ya faɗa without looking at her. Daidai nan likita ya fito hannunsa da paper ya ce “Ku canki jinin waye ya yi daidai dana Malama” Uncle Isma’il ya ce “Kowa ya san nawa ne” Uncle Bello ya ce “haba Yaya ina laifi ni ma” Jawaad ya ce “Ai nawa ne ma” Dr ya ce to bari na kira results ku ji ya ce “Alhaji Isma’il” Uncle ya ce “Yes” Dr ya ce “Doesn’t match” Ya kira Uncle Bello ma haka, haka Jawaad duk ba daidai bane A hankali ya ce “Dr Ibrahimul-khalil Abraham” Khalil ya sauke numfashi a ɓoye Dr ya ce “Congratulations na jima banga jini da ya yi daidai irin naka da nata ba” Jawaad ya ce “Wow! What love” Dr ya ce “But am sorry to say ba zamu saka mata naka ba, jikinka ya ɗan hau kana buƙatar hutawa” Khalil ya kasa cewa komai Dr ya kalli Alpha kana ya juyawa ya ce “Ajlaal Sultaan?” Mai martaba Ajlaal Sultaan ya ɗan ware idanunsa bai ce komai ba, ya ce “Congratulations” Ya kuma cewa “General Alpha Bello khan? I congratulate you” A ɗan hargitse Khalil ya ce “Ban so, ban son jinin kowa a jikin matata” Da sauri Alpha ya ce “To bari naga ko zaka hana” Shi ma Khalil ya miƙe yana tattare hannun riga ya ce “To bari naga uban wanda ya isa a saka mata jinin da ban so” Abbu dai na tsaye, Zaytoon na zaune haka Ƙhulud Gimbiya daman tun zuwan su take bacci a cinyar Ajlaal har zuwan Abbu da sauran mutane duk bata sani ba, Uncle Isma’il ya yi saurin shiga tsakiya a fusace da sauri Khalil ya saka hannu ya ɗaga Uncle Isma’il cak ya matsar gefe yana kallon Alpha ya ce “Idan kai isa kuma ka haifo ka je a saka mata jikinka, zan nuna maka kai ƙaramin ɗan iska ne” Alpha ya ce “Ni ne ɗan iska?” Khalil ya ce “In capital letters ƙaramin ɗan iska” Daidai nan kuma Zizi ta shigo da sauri ta nufi wajan Khalil tun kafin ta ƙarasa ya daka mata tsawa, a hankali President Denial David ya shigo daidai lokacin kuma Gimbiya ta buɗe Idanunta kai tsaye kuma ganinta ya sauka akan Daddyn Khalil jikinta ba wani irin rawa da ɓari ta dinga kallonsa, Ajlaal ya riƙeta ta fisgi cikin mamaki al’ajabi da wani irin tu’ajjuji Ajlaal yaga Gimbiya ta miƙe tsaye akan ƙafafuwanta laɓɓanta na rawa ta shiga nuna Dad da hannu da wani irin ƙarfi ta ce “Denial.., Denial where’s my son?” Sai kuma ta fasa wata gigitacciyar ƙara tayi baya Khalil dake tsaye bai san lokacin da ya yi kanta a gigice a kuma kusan tare da shi da Ajlaal suka nufi kanta cikin rashin sa a Khalil ya saka hannu ya ture Ajlaal Gimbiya ta faɗa jikinsa a sume daidai nan kuma Abbu ya juyo idanunsa ya sauka akan kyakkyawar fuskarta…..

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button