Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 46

Sponsored Links

Ta bisa da Idanu kamar yadda yake kallonta gudun kada ya zaro mata wani zancan ta yi shiru, Khalil bai fasa kallon duk inda idanunsa yake son gane masa ba clamly yana ƙasa da murya ya ce “Yanzu ƴan uku zaki haifa ko?” Ta kalle shi ya ɗaga mata gira ta ce “Kawo kunnenka na faɗa maka” Ya matsa yana riƙota dragging her more closer to himself ya ɗora kunnensa a bakinta ta ɗan yi baya tare da saka hannu ta murɗe kunnen ya ce “Auchhhii” ya ɗan yi wani erotic and emotional sounds yana rufe ido a hankali ya ce “Faɗa mini” Ta ce “Eh, da Bad boy, Abraham, the one whose Love always tortures my heart..” Wanda kullum soyayyarsa ke azabtar da zuciyata. Idanunsa lumshe ya ce “Who? Waye?” Ta saka hannu ta shafa fuskarsa tana jan gemunsa muryarta na fita a hankali ta ce “My love, Ibrahimul-khalil” Ya buɗe ido ya kalleta sai bai ce komai, ba wanda ya ƙara magana har suka isa gidansu na lafiya Round wanda tuni Khalil ya bada umarnin a gyara, driver ya yi parking a parking lot na harabar ajjiye motoci na gidan, Khalil ya wani soja ya buɗewa ƙofa, ya fito a hankali ɗaya vangaren ya nufa bayan ya tabbatar Majeederh ta gama gyara liƙab ɗinta ya buɗe mata ƙofa ta fito a nutse, ta ɗan tsaya tana kallonsa ya ware mata manyan idanunsa alamar ya akai? Sai kuma ta ɗauke kai ta nufi entrance na gidan ya bi bayanta, tana isa cikin main parlour ta cire liƙab ɗin da duguwar rigar daga ita sai ƙananun kaya ta ce “Man me za a dafa maka?” Bai kalleta ba, domin yasan abinda kallon zai haifar yana haurawa upstairs da sauri da sauri ya ce “No, thank you” Ta bisa da ido sai ta maida kanta wajan fridge tana tunanin ko akwai drinks a ciki, miƙewa tayi saman kujerar ta kwanta tana jin wani irin nutsuwa na saukar mata gata ta dawo gidan mijinta hakan na nufin babu wata damuwa data rage mata, harta fara bacci ta ji ƙarar shigowar saƙo ta ɗauki wayar saƙon ta gani daga kalli magana ce bata huce biyu zuwa uku ba, kamar haka;
“Wifey i want to see u in a special and sexy dress” Majeederh ta saki wani lallausan murmushi tana jin a ranta yau akwai rigima kenan ta dinga karanta text ɗin nasa sai kuma ta ajjiye wayar tana tunani me yake shiryawa? Ta miƙe cike da nutsuwa ta nufi part ɗinta, komai yana nan killace ita dai bata san wanda ke gyarawa ba, amma ta tabbatar ba haka aka bar gidan ba, wanka tayi da ruwan zafi ta ƙasa jikinta sosai, kafin ta shafa lotion ta fara ɗaukan turaren sandal ta kunna ta ɗora kayanta akai yaƙin ya fara ratsasu, ta ɗauki sauran turaren na icce ta turara jikinta sosai, ganin location zai ɓata mata lokaci ta ɗakko haɗaɗɗiyar kwalacca ɗinta mai azabar ƙamshi wacce ta gigita bedroom ɗin lokaci ɗaya, fara ce tas kwalacca ɗin kana shafawa fatar wajan na glowing tana sheƙi ta mulke ko’ina na jikinta duk wani sashi na musamman sai data goga a wajan, fatarta tayi shinning luwai-luwai so masha Allah.
Body spray ta ɗauka tabi dukkan gabɓanta da shi zuwa bayan kunnenta da wuyanta, wajan wardrobe ta nufa kamar zata ɗauki inner wears ta saka sai kuma ta mayar ta rufe white ɗin duguwar rigar cotton ce mai wuyan net ta saka da ƙaramin hannu, rigar tabi jikinta ta kwanta shap ɗinta na asali ya bayyana, ta kama sumar kanta ta tufke da ribbon jelar ta dawo da ita gefen wuyanta na dama, wata siririyar necklace ta saka sai ɗan kunne ta ɗauki flat shoe ta saka da sarƙar ƙafa, kana ta fesa MONIQUE Midnight ta zauna gefen gado hannunta riƙe da waya a karo na farko bisa dalilin nutsuwar zuciya data samu ta kunna network ta shiga facebook domin tafi duba muhimman abubuwa a can ɗin, kai tsaye offline ɗinta ta shiga ta duba a nan take ganin yadda followers ɗinta suka ƙaro da yadda aka dinga tagged da mentioned, shiga tayi wajan “What is on your mind?” tayi posting na magana guda uku mai muhimmanci ta ce
“Halitta mara adalci wa gangar jiki, tsarkakkiyar ga mai ƙyakƙyawan nufi,ka wanke mana tamu ta tsarkakken nufinmu” tana yin posting kiran Khalil na shigowa tana ganin kiran taƙi ɗauka a kira na biyu ta ɗauka bayan ta gama saita muryarta cikin yauƙi ta ce “Naga…,”
Ya katse ta a taƙaice wajan furta “Ki zaman yanzu” Ta ce “A ina?” Bai bata amsa ba ta kashe kiran yana tura mata direction na inda yake a gidan, ta miƙe tana tafiya harta shige garden daga can ta hango wani part shi ba hall ba shi ba club ba, kamar special waje ne a gidan na Dr Ibrahimul-khalil, ta nufi shiga wani irin sanyi ne ya ratsa saman fatarta zuwa ilahirin gangar jikinta, yana mamaye dukkan wani tsatso na naman zuciyarta ta tsaya cak tana bin haɗaɗɗan wajan da kallo dake bata hasken blue da green da red, ta ɗaga idanunta zuwa sama inda aka rubuta “Happy Anniversary Mr and Mr Dr Ibrahimul-khalil” ta furta a fili a hankali taji an tsaya a bayanta kafin ta juya taga waye zuciyarta ta sanar mata da cewa gwarzon mijinta ne Khalil ya saka hannu zuwa ƙugunta ya saƙo tare da mannewa da nashi ta baya ya fita tsayi tuni ya zartata, ya rungumeta tsam yana ɗora kansa a kafaɗarta ya kalli inda take kallo ɗin, kafin a hankali ya ce “Amincin Allah ya tabbata ga ruhin Dr Ibrahimul-khalil”.
Majeederh ta kasa cewa komai lokacin da idanunta ya sauka akan makeken photonsu, ita, Khalil, twins da Baby Khalil a rubuta One single family sai wani kuma ita dana Khalil, sai nata da tayi masifar kyau an rubuta.

“I don’t know what I have done to deserve such an amazing wife like you, but I do know that I love you more than anything. I appreciate everything that you do for our family, honey, I love you wife i love you i love you” Ta juya da sauri ta kalle shi ya ɗaga mata gira yana kashe mata Idanu ɗaya, a hankali in a romantic style ya sake manne mararsu waje guda hannayensa zube a faffaɗan ƙugunta, Majeederh ta kasa furta komai sbd bakinta ya yi kaɗan wajan furta abinda zuciyarta ke ji game da mijin nata Khalil, wani irin rauni, rauni na mace zuwa ga mijinta ya mamaye zuciyarta ya yiwa gangar jikinta inuwa, yana fuskarta murfi, a hankali ta sake juyawa ta kalli haɗaɗɗan cake ɗin dake ajjiye saman wani farin Glass an wadata shi da kayan kyalkyalin, pictures ɗinsu ne manne a jiki. A sanyaye ta saka hannunta ta zare hannunsa daga jikinta ta taka a hankali zuwa anniversary Inbox gift ɗin take tana zuwa tsakiyar wajan ta ji an saki red ɗin flowers ta tsaya idanunta rufe tana shaƙar ƙamshin furanni, cikin yanayi na ɗaukan hankalin mutum ta shiga sauya taku tama mance Little ne a gabanta, Little ɗin da aka ce ba za a taɓa so ba, balle mafarkin aura, ɗan yaron nan, wannan gwaninin. Abubuwan data gani suka girmi zaton da zuciyarta take ta juya da sauri ta kalli Khalil yana tsaye harɗe da hannayensa, sai a lokacin ta kalli shigar jikinsa wata farar Floral jacquard one button suit ce a jikinsa white colour, kansa ya sha saloon an tufke shi a tsakiya shanyayyun idanunsa sun yi wani haske tas sai laɓɓansa da suke jajur, ƙafarsa cikin Leather shoe black colour, hannunsa maƙale da Rolex mai kyau da tsada sai ƙamshin perfume ɗin Boadicea The Victorious daya hargitsa wajan, kyan kayan ya fallasa tsadar su a fili.
Jee ta durƙoshe a wajan sbd nauyin da zuciyarta ke mata, tayi expecting gani wani abu daban, tasha gani,ta kuma san yadda mijinta Khalil ke sonta, sai dai, bata taɓa sanin girman son da yake mata mizaninsa ya kai har haka ba, bata ɗauka ta shiga jerin irin matan nan masu sa a, a rayuwa har haka ba. Ashe haka zuciyar Khalil take? Ashe zai iya komai sbd ita ɗin kamar yadda idanunsa suka sha faɗa mata? Jikinta na wani irin rawa ta ƙarasa kaiwa ƙarshen saman qiwwoyinta, tana jin wani abu mai kama da zazzaɓi na kamata, zazzaɓin daba na komai bane sai na soyayyar mijinta Khalil. Kunya na hanata yiwa Khalil abubuwa da yawa, amma a yanzu ta fahimta ta kuma gane babu wata kunya tsakani zaman auratayya na tubalin kasancewarku miji da mata. Idan ta ce kuka za ta yi; wanne kala zatai?
Khalil dake tsaye yana kallonta, cike da nutsuwar dake alamtawa cewa jinin ke gudana a jikin nasa, duba da wanzuwar kamala da tarin haibar fuskarsa wacce ke sauka zuwa jikinta tana zame masa wani abu mai kama da (A man’s personality, his appearance).
Zubin halittar Khalil da kamalar shi ba zaka ɗauka na ƴan 22yrs bane, yana zuwa ya saka hannu ya miƙar da ita tsaye yana zuba ƙwayar idanunsa cikin maiƙatattun idanunta ya buɗe nasa rikitattun idanun a fili cike da kasala ya ce “Wonder Woman” Ta yi ƙasa da kanta sbd kunyarsa daya mamaye mata zuciya ya daki kafaɗarta ya ce “C’mn ke Matana ce, abokiyana, my supporter and adviser” Ta kalle shi zuciyarta na kasa riƙe dauriyar rungumarsa da take azalzalar ta da tayi, a hankali ta shige jikinsa tana ɗora kanta a ƙirjinta wani irin kuka ya ƙwace mata, kuka na zallar farin ciki da samun abinda zuciyarta ke so da muradi na har abada.

Khalil ya matseta a ƙirjinta gudun zuciyarsa na ƙara yawa da ƙarfi yana ƙoƙarin kasa riƙe kansa, shi kansa da zai iya kukan zai, sai dai jarumtar shi da ƙarfin zuciyarsa bana kuka bane a gaban matarsa, kukansa zai iya kassara gabɓanta, ya raunata zuciyarta, ya makarantar da ita bayan kasancewarta mai Idanu, ya doɗe jinta, ya zautar da ƙwaƙwalwarta, a hankali yake ɗan bubbuga bayanta can ƙasa yek furta “shiiiyy, shiiiittt” ita kanta ba ji take ba, ya tallafo fuskarta da hannayensa yana kifa tasa fuskar saman tata ya murza hancinsa akan nata a hankali ya fara sauke numfashi yana ƙarewa lip’s ɗinta kallo wanda suka jiƙe ga lamp lipstick a bakinta, jikin kukan yaƙi tsayawa gashi bashi da wani option na rarrashi wanda ya a shige “Kiss” a nutse yana sake rungumeta numfashinsu na sauka zuciyarsu na bugawa a daƙiƙa guda ya shiga sauke mata wasu special kisses asalin sumbata kukan ya tsaya ta kalle shi kamar yadda shima ke kallonta a hankali ta rufe Idanunta zuciyarta na buɗewa, gangar jikinta na janta akan linzamin zuciyarta da wani irin firgitaccen sihirtaccen yanayi suka shiga kissing juna da sukkan su da ƙauna mara algus irin son da akewa laƙabi da (eternal true love, pure purity built for God).
Khalil ya yi mata murmushi still yana riƙe da fuskata ya ce “Not every husband is lucky enough to have a wife like you. My whole life I have dreamed of getting a woman like you, The woman who is a perfect homemaker, lovely mother, a successful manager, and the best wife is not a myth; it’s YOU. Thanks for everything, INA SON KI”
Jee ta girgiza kai ta ce “Na fi kowa dace da sa a Khalil, i love you more than anything, Ubangiji ya wadata lemanka ya sanya alheri a ciki, ya rabaka da haramun ya sadaka da halak ya tsarkake zuciyarka a kullum ya baka ikon kula damu, I love you so much &most MAN”
“MAN?” Khalil ya furta yana ware idanu irin sunan bai kwanta masa ba ya jata zuwa wajan cake ɗin tana dariya ta ce “Yes, my stubborn husband mai karya jama’a for know reason” Ya ware Idanu ya ce “No reason? A taɓa ruhin babban likitan kice no reason” Ya miƙa hannu zai damƙota tayi baya ya ce “Funny woman” Ta rungume shi ta baya tana ɓalle maɓallar rigarsa hannunta a kwance a ƙirjinsa ya lumshe gajiyayyun idanunsa ya ce “Sexy mama”
A ranar Majeederh taga hauka wajan Khalil hauka na soyayya idan ta ce cikinta zai iya zubewa babu mamaki, domin wani irin ciwo mararta keyi na azaba da sun haɗa ido da Khalil yake kashe mata idanu a lokacin ya faɗa mata dukkan wasu plans ɗinsa na cikin watan Ramadan da yadda zai yi handling ayyukan shi ta sake bashi shawara wacce ya ji daɗinta sosai ya sake rungumeta yana faɗin “Thanks Malumana”
12:00 aka buga bindiga daga gidan sarki wacce ake shaidawa al’ummar musulmi ganin jaririn watan Ramadana, zuƙata su kwanta da niyar ɗaukan azumi, tun a lokacin daga Khalil ya yi zukuɗi ya zama abin tausayi ta san kuma abinda yake tunani a ransa ta dinga masa dariya bai kulata ba can ya mirgina cinyarta ya ce “Kwana nawa ne ma?” Ta ce “Wata guda ne cif mijin Malama zai azumi” bai kulata ba ta ce “Dame za ka yi shur?” Sbd ya huce haushin da take bashi ya ce “Towon shinkafa miyar kuka a saka man shanu, sai farfesun kai da ƙafa” Ta shafa kansa ta ce “Done” tasan ba zai taɓa cin wannan da daddare ba. Tana fita ya gyara kwanciya bacci ya ɗauke shi na gajiya, ya jima bai yi bacci mai daɗin wannan ba, yana ji tana tashinsa amma ko Idanunsa ya kasa buɗewa Majeederh ta zuba masa idanu ta jima da sanin nauyin baccinsa a hankali ta saka hannu ta jawo tafin ƙafarsa jin ana jan shi ya buɗe ido ba can ba ya ce “What?” Ta ce “Shur” Ya girgiza kai ta ce “pls dear ka samu ladan shur ɗin” Ya miƙe gabaɗaya ya nufi bathroom ya sakarwa kansa ruwa ya fito da towel ya kalleta can ya ce “To time ɗin da a shiga?” Ta girgiza kai sai kawai ya damƙota yana kashe switch ɗin bedroom ɗin. Washegari miliyoyin musulmai dake duniya banda wasu sassan garuruwa suka tashi da azumin watan Ramadan a bakinsu, gari ya sauya yana yi na ibada ya bayyana, tun safe Khalil ya fita sbd zakkar da za a fitar da maganar kayan sallar Orphans ɗinsa da abinda za ayi musu ya kashe kuɗi miliyoyin da bai san kan su. 11:00 ya dawo ya ɗauki Majeederh zuwa Arewa24 akan program ɗin Mata a yau da aka gayyaceta.
Kowa na azumi gaban iyayensa, wasu gidan mazajan su ita kuma ƙaddararta azuminta na farko a gidan yari, bayan fitowarsu kowa da uniform na jikinsa an raba musu aiki, wani gandiro ba ne yazo yana tambayar “Latifa Omar?”
A hankali ta ce “gani nan” ya ce “Kina da vistor” tayi shiru sai kuma tabi bayansa, tsaye ta samu Barrister Aliyu Sufyan Alhassan cikin wani tattausan voyel ya ƙara yi mata kyau fiye da ko yaushe Gandirobar ya ce “5 minutes sir” Aliyu ya ce “Thank you” magana sukai da Latifa a nan yake shaida mata an ɗauke ta daga gidan prison ɗin san zuwa Ikot Ekpene Prison dake Akwa ibom, Latifa Omar ta dinga kuka kamar ranta zai fita daga nan kuma mota aka zuba su ita da wasu akai gaba da su. Lokacin da suka isa gidan yarin tana shiga was the first data tara gani shi ne Mr President..
[10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: *MIJIN MALAMA*
BOOK2

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button