Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 50

Sponsored Links

Yana mgnr yana qoqarin janyota jikinsa janyewa tayi tayi qasa da sauri tare da shigewa daki ta fada saman gadon ta saki kukanta me sosa masa zuciya, shigowa yayi ya tarar da ita a kwance ya matsa kusa da ita ya zauna ya ruqo hanunta yace.

 

“Bansan meyasa kullum ni nake zama me laifi a gurinku ba bansan meyasa rayuwata dake ta kasa samun farin cikin daya dace ba Umaimah Allah ma shaidane inasonki sonda ban taba yiwa wata ya mace ba matsayinki dabanne a gurina tunda kinada qualities din da babu macen da zan aura tabani irinsu amma bazan boye miki ba rayuwata dake bazata dore a haka ba tun iyayenmu suna cewa cutar dake nakeyi inaqin yarda har ankai lkcn da ni da kaina nake fadawa kaina zamana dake akwai cutarwa Baby bazan iya rayuwa babu keba amma zanyi abu daya wanda nake fatan zaki fahimceni a cikinsa Umaimah zanyi aure…..”

Related Articles

 

Duf ta dauke wuta na wasu sakanni bai kula da halin da take ciki ba yace “banida raayin zama da mace sama da daya amma qaddara ta zabamin Salmah tsohuwar budurwa tace tun ta quruciya kafin haduwata da Sadiya ita muka fara soyayya da ita tun bansan ma abinda son yake nufi ba take sona aure ne ya rabamu da yaran ta uku yanzu haka suka rabu da mijinta so tun kafin na kwanta rashin lfy muka hadu da ita har mukayi musayar number kafin na fara jinya munyi mgn da ita har nayi Mata alqawarin zan tura ayi mgnr aurena da ita kuma sai wannan abin ya faru so yanzu dai nace mata cikin satinnan zaaje ayi mgn kuma harna fadawa Daddy”

 

Tunda ya fara mgnr numfashinta yake bugawa da qarfi tanayi masa wani irin kallo da bazata iya cewa ga irinsa ba harya gama mgnrsa ya ruqo hanunta yace “nasan bazan samu matsala dake ba Ummuh Shurafah zaki bani hadin kai shiyasa banyi darr din sanar dake ba kuma nasani bazaki samu matsala da Salma ba saboda tanada kirki da sauqin kai kuma tanasonki tun bakisan kanki ba tasanki saboda duk wanda yasanni yasanni dake yasan matsayinki a gurina Umaimah ban boye Mata ba na fada mata matsayinki a guna kedin ta dabance saboda ke amanace a gurina kuma ke farin cikina ce……”

 

Kallon da yaga tanayi masa ne yasashi hadiye mgnr sa daidai lkcn wayarsa tayi ring ya daukota da sauri ya duba tare dayin murmushi ya kara a kunnensa yace “yar halak yanzun mgnrki nakewa Hearty ashe kema ina ranki” shiru yayi sannan ya kuma murmushi yace “to alhmdllh nanda sati biyu kin zama tawa kenan ok bari anjima zamuyi mgn” yana fadin haka ya juya gurin Umaimah da duk yanda takai da saurin kukanta yau hawayenta sun qafe qaf sai zugin zucci da tafasa da zuciyarta takeyi abinka da shuwa masu kishin gado.

 

Kallon kallo suka tsaya sunayi kafin tayi qarfin halin miqewa zatabar gurin yayi saurin riqota shima ya miqe ta juyo ta zuba masa jajayen idanunta jikinta da bakinta sai rawa yakeyi sai yanzu hawaye suka samu nasarar zubo mata cikin in’ina tace “Sak…keni Abu Shurafah…” tana fadin haka ta fincike hanunta ta dauki yarta data tashi daga bacci ta nufi bathroom da ita ta cire Mata kayanta ta sanyata a cikin bath din amma hakanan tunda ta durqushe ta kasa tashi jin zuciyarta takeyi kamar zata faso qirjinta wai ita Umaimah ita zaayiwa kishiya kishiyar ma kusan saar yayarta Jameelah kuka ya kuma kwace mata wannan karon harda shshsheqa ashe da gaske ne da mata suke cewa ko labarin mutuwa baikai na kishiya ciwo ba “Allah ka kasheni na huta” abinda ta furta kenan jitayi an sanya hanu an dagota ta daga kanta ta dubeshi da sauri shima itadin yake kallo idanunsa sun kada sunyi jawur.

 

Har cikin ransa yakejin ciwon kukan Umaimah ya rasa meyasa kullum shine yake zama sanadin kukanta kullum shine sanadin baqin cikinta ya rasa yaushe ne zai zamewa Umaimah farin ciki a rayuwa yaji komai daya faru tun daga kwanciyar sa jinya har kawo yanzu a gurin Aunty Zarah yasani sarai ba raayinta bane sake rayuwar aure dashi tausayinta gareshi da sadaukarwarta da kuma gudun bacin ran iyayensu shine yasata aminta da sake auransa towai shi meyasa ma yakeson qara auren ne iyakar saninshi shi ba meson tara iyali bane kuma babu abinda yakeso a gurin mace wanda matarsa bata dashi to wai meyasa yakasa bijiirewa auran Salma ne?………

 

 

 

_Kuyi hqr wutarmu ta lalace Ina fama da matsalar charge insha Allahu zaku jini anjima idan baku jini ba kuma kuyimin uzuri._

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/26, 3:14 PM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *G.U*

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button