Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 28

Sponsored Links

Hasina tunda ta dawo Kano take shige da fice akan taga ta shiga tsakanin Aneey da Abdu sannan ta karkato da hankalinsa kanta sun ɗinke sunci gaba da rayuwa ko ta bayan fage ne tasha wahala kafin ta samu abinda takeso satinta ɗaya da ƙarfafawar gwiwar Mama ta koma da shirinta tayi Sa’a kwananta uku da dawowa Aneey ta kama jinya harda suma aikuwa hankalin kowa ya tashi musamman Abdu suka kaita asibiti kwananta huɗu a asibiti ya zamana komai na gdan Hasina da Maryam keyi a wannan lkcn ne Hasina ta samu damar aiwatar da shirinta magungunan da aka bata da surkullen duk ta aiwatar dasu yanda akace sannan ta miƙe ƙafa jiran lkc.
Aneey ta ji sauƙi suka dawo gda da sabbin abubuwa sauyi sosai take fuskanta gurin Abdu duk da cewar bai rageta da duk abinda yakeyi mata ba amma ya ɗauke mata wuta ya daina sauraronta sosai shida suke faɗa dashi akan abubuwa sai gashi ya nema ma baya nema da farko ta zaci tausayinta yakeji shiyasa ya daina takura mata sai a hankali ta rinƙa fahimtar canjin nasa na gayya ne musamman daya shiga ɓoye mata abubuwan da suka shafeshi sai tayi kamar ta sanar da Hasina sai kuma zuciyarta ta hanata hakadai ta rinƙa haɗiye abin tana dariyar dole.
Zuwa lkcn Hasina ta tattataro nata ya nata ta dawo sashin ƙanwar tata wai taga ta fara nauyi ne tana buƙatar mutum a kusa da ita koda yaushe harga Allah Aneey taji daɗin yanda ta nuna damuwarta da lamarinta sukaci gaba da rayuwarsu a haka idan dare yayi duk da baya kulata haka zatayi wanka tayi kwalliyarta ta nufi ɗakinsa ta zauna tana jansa da mgn wata ya amsa mata wata yayi mata shiru.

 

Yau Laraba ce daren Alhamis kamar yanda ta saba tayi wankanta ta shirya cikin shirinta ta nufi ɗakin nasa bayan ta gama yi masa tanadi hakanan yau ta tsinci kanta da bala’in son kasancewa da mijinta taje ɗakin nasa ta buɗe yana kwance idanunsa akan silling ta zauna kusa dashi ta ɗora hannunta kan shaffafen cikinsa tace “barka da hutawa Own” ajiyar zuciya ya sauke ya sauke idanunsa akanta yace “Kina lfy?” Murmushi tayi tace “gata da sauƙi sai kewar mijina nikam bansan laifina ba a faɗamin nasani na nemi yafiya”
Tashi yayi zaune yace “kinsjin kinyi wani laifi ne?” Ɗagansa kai tayi yaja numfashi yace “To me kikayi?” Ƙasa tayi da idanunta tace “ka canzamin baka kulani Prince dama nasan meye laifina kaga zan gyara bansan yaushe mijina ya canza ya koma riƙe abu a ransa ba nikam ina neman tuba” jinjina kai yayi ya janyota jikinsa yace “Ok Wyf bakiyi komai ba kawai wani yanayi na keji na ƙuncin zuciya share dai kawai Ina Hasina?” Fasali taja tace tana ɗakin baƙi tana assignment kaɗa kai yayi suka kwanta yaja musu bargo sosai Aneey taji daɗin yanayin inda shi kuma ya rinƙa daurewa da gaske abin kullum ƙara ta’azzarar masa yakeyi baya sha’awar matarsa sai yayarta yanata ƙoƙarin gujewa faruwar komai amma kullum juriyarsa ƙarewa takeyi.

Related Articles

 

*Ki tausaya karki fitar mana dashi in kin siya ,Inkin san siya zakiyi don kiyi sharing don Allah karki siya mun hutashsheki,Haƙƙin mallakar marubutanne su kaɗai,Ki tausaya masu plz ,Inkinga wani pages na yawo to na sata ne ki runtse idonki karki karanta ki biyo ki siya.*

 

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_

Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
*08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍“`♡♡

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button