Hausa NovelsMijin Malama Book 2 Hausa Novel

Mijin Malama Book 2 Page 31

Sponsored Links

10/12, 2:09 PM] Aisha Baby Novel: ~_*Arewabooks@Nimcyluv*_~ 82
Kafin Khalil ya ƙarasa Jee tayi saurin shiga tsakiya idanunta akan shi, wanda shi kuma yaƙi yarda ya haɗa nasa idanun nata, muryarta na rawa sosai ta ce “Me kake shirin yi?” Ya yi shiru da kuma sauri ya sanya hannunsa guda biyu ya ɗagata zuwa gefe cikin ɓacin rai ya nufi kan Dad, ita cikin sauri ta ƙara shigewa tsakiya idanunta akan shi ta ce “Idan ka taɓa shi zan zubar da cikin nan na jikina” Khalil ya juya a ɗan miskilance yana kallonta da yanayin dake nuna _“You are kidding”_ A karo na biyu ya ƙara saka hannu ya ɗauketa cak ya matse kafaɗarta idanunsa a warwaje ko magana ya kasa sbd masifar yadda yake jin zuciyarsa, sai kuma ya saketa ya matsa wajan Dad yana haɗe ƙirjin su waje guda kai baka ce mahaifinsa bane ya ce “Idan ita matar taka zaka kashe go ahead, i don’t care daman ban santa ba” Ya wani cije baki Dad na jin yadda duk jikin Khalil ɗin ya ɗauki rawa kamar wanda wuta take ja, ya saka hannu ya damƙi wuyansa ya ce “Amma, da wasa ka ce zaka taɓa mini sister zaka san ku duka biyun na fiku zafin zuciya, I’ll kill you” Majeederh dake tsaye ganin yadda Khalil ya shaƙe wuyan Dad ya sa da ƙarfi ta saka hannunta ta shiga dukan cikinta, Maman Alpha ta miƙe tana cewa “Majeederh wanne irin shirme ne haka? Kashe kan ki da baby zaki?” Maganar daya jawo hankalin Khalil kenan, ya saki wuyan Dad tare da juyawa ya zubawa Majeederh idanun ganin taƙi bari Maman Alpha ta riƙe ta, idanunta rufe take dukan cikinta ga wasu irin hawaye da suke bin idanunta masu zafi, a hanzarce Dad ya fice da cikin parlourn hannunsa riƙe da waya yana ɗagawa, Gimbiya na zaune ta harɗe ƙafafuwanta tun bayan maganar da Mr President ya yi na cewa Khalil has a sister, ta nemi waje ta zauna fuskarta haɗe ba wargi as always, ko tari ba tayi ba, duk wannan abun kuma ba zaka ce tana wajan ba, inda direction ɗin Majeederh yake bata ma kalla ba. Majeederh ta saki raunataccen kuka ta ce “Ki barni tunda baya jin magana, Khalil baya ji yanzu idan ya kashe Dad shi ma kashe shi za ayi ya yake so na yi da rayuwata? Da abinda zan haifa, ko farin cikin dana fara samu ne baya so….,” Ta kasa ci-gaba da maganar, Maman Alpha ta ce “Haba Majeederh, taya tunaninki zai iya baki cewa Khalil zai kashe mahaifinsa? Shi fa ya haife shi, duk wutar gabar dake tsakani ba za a taɓa rasa soyayyar juna a zuƙantan su ba, tsakanin uba da ɗa sai Allah, muna fatan wannan abun ya zo ƙarshe” Majeederh ta girgiza kai tana runtse Idanunta jikinta duka ɓari yake ta ce “Ki faɗa masa karya ƙara cewa zai yi kisa, wlh aka kashe Khalil mutuwa zan yi” laɓɓanta duka karkarwa suke, fuskarta ta rine tare da yin jajur musamman tsinin hancinta, yadda take kuka kaɗai zai sanya mutum hawaye, Maman Alpha ta ce “Ba zamu ga wannan ranar ba, In sha Allah Khalil ko sauro ba zai kashe ba balle mahaifinsa, har kuma a jawo a kashe shi” Majeederh ta riƙe hannun Maman Alpha sosai ta ce “Mama mutuwa zan yi idan Khalil baya raye, zan mutu zan bisa, ina son Khalil, ki faɗa masa ya daina maganar mutuwa haka ya yi mita a hospital, wlh zan kashe kaina idan Khalil baya duniya..!” Tsananin mamaki ta tausayi ya wanzuwa a zuciyar kowa, Maman Alpha ta saki Majeederh tare da kifa kanta a saman armchair ta saki wani irin kuka na matsanancin tausayin Majeederh da Khalil, sosai Maman Alpha ke kuka, wanne irin so ne wannan? Tunda Majeederh ta shafawa idanunta toka a gaban kowa take faɗin haka to lallai abun ya yi tsamari, a hankali Zaytoon ta yi ƙasa da kanta hawaye na zuba cikin idanunta, Mai martaba bai iya zama ba, ya miƙe yana jin jiri na ɗaukar shi a daddafe ya nufi waje yana mai kiran Rohaan daya fito da Zaytoon she’s crying. Gimbiya yadda take a zaune haka ne a gareta har yanzu, domin ko yatsanta bata motsa ba, da kunne take jin komai bada Idanu ba, Abbu daya riƙe kansa da hannu bibbiyu yana tunani ya ɗago yana kallon yarinyar tashi, yanzu da ace da gaske ya hana auren nan ina hakƙin wannan son zai kai shi? Ko iya rabo ya isa ya kashe duk wanda ke ja da auren Khalil da Majeederh, tun ba a je ko’ina ba ga ciki ya bayyana, Abbu ya fahimci duk wannan ƙalubalan da kuma rashin auren da Majeederh ba tayi ba, da kuma yadda ya wahalar da Khalil, da fitowar Majeederh daga gidan Abuturab, da rashin auren Barrister Aliyu, da kuma rashin dawowar Alpha ba komai ne ya haddasa hakan ba sai RABO, rabon cikin dake jikinta, wanda kuma shi ne sanadin kawo jinkimar mutanen biyu wanda suke ƙoƙarin ruguza farin cikin MIJIN MALAMA da ita kanta malamar. Abbu ya miƙe jiki babu kuzari ya nufi inda Majeederh take durƙoshe, a hankali ya saka hannu ya miƙar da ita tsaye, a taushashe cikin nutsuwa da kamala ya riƙo hannunta tare da tallafo fuskarta a hankali ya ce “Hawwa’u” Ta kalle shi ta kasa cewa komai sai hawaye ya saka hannu ya goge mata hawayen ya ce “Meyasa sai kin nuna ke ƴar fari ce? Meyasa baki da wayo da dabara? Kin girma uwa zaki zama, kece wacce zaki taimakawa Ibrahim wajan ganin komai ya daidaita, kin raba shi da zafin zuciyar dake ɗawainiyya dashi, kin kawo silar daidaituwar shi da iyayensa, kin shirya su, kin zama silar sauke jinkimar su” Sharr hawaye ya sake sauka a Idanunta, Abbu ya fahimci rauninta akan mijinta Dr Ibrahimul-khalil Abraham, muryarta na rawa ta ce “Abbu, Khalil ba” Ya yi rufe mata baki ya ce “it’s okay, ba bu abinda zai faru sai alheri just pray” Ta jinjina masa kai a hankali ya furta “Come closer” A hankali ya shige jikin Abbu ya rungumeta yana jin yadda take sauke ajjiyar zuciya, a yanzu kuma hadda kewar jikin Abbun nata ke damunta, sun jima haka kafin ya ce “I am sorry dear, ki yafe mini” Ta ce “Baka mini komai ba Abbu” Ya ce “Allah ya yi muku albarka ya baku zama lafiya, haƙuri da juriya da kau da kai” Ya kama hannunta har zuwa wajan Khalil dake tsaye kamar an dasa shi, ya kama hannun khalil ya haɗa dana Majeederh ya ce “Gata nan halak makal” Uncle Bello ya ce “Ka kula karta mace don soyayyar mijin Malama” Khalil a hankali ya damƙe hannu Majeederh, bashi da wata kalma da zai iya yi mata bayani ko ban haƙuri, he just need a hug ko zai samu nutsuwa, ji yake kamar ya jata ya rungume amma ko mutuwa na Kunyar Idanun mahaifi balle soyayya, a hankali Mami ta ce “Ibrahim kuje” Ya yi jim kansa a ƙasa sai ya ce “Ƙasar zamu bari” Sai a lokacin Gimbiya ya buɗe dara-daran kyawawa idanunta ta kalli Khalil tana jin kamar sbd ita ne zai bar ƙasar, Maman Alpha ta ce “Wacce ƙasa zaku to Khalil? Majeederh ba zata jure zirga-zirgan jirgi ba, sbd cikin jikinta” Shi dai ya yi shiru ba alamar zai yi magana, da sauri kuma ya damƙe hannu Majeederh tare da yin waje gabaɗaya suka bisu da kallo tare da addu’ar kiyayewar Ubangiji.. Tunda suka ɗauki hanya ba wanda ya ce komai, kowa da tunanin zuciyarsa, suna bayan mota driver na jansu, har suka isa lafiya Road lokacin ajjiyar zuciya kawai Majeederh ke saukewa a hankali, driver na yin parking ita ta fara fita Khalil ya bita da idanu, ko ba tayi magana ba yasan fushi tayi, a hankali ya bi bayanta suka samu Debeka zaune a parlour tana waya, tana ganin su tayi saurin kashe wayar kanta a ƙasa sai kuma ta kalli Khalil da sauri ta miƙe ta ce “Wclm sweetheart” Tayi kamar zata rungume shi, Khalil ya ɗan kalli Majeederh data ɗan saci kallonsa sai ya yi peaking kumatun Debeka ba tare da ya ce komai ba ya shige part ɗinsa, kansa ne kawai yake sarawa yana buƙatar tunani, sanin son waye asalin mahaifinsa Mr President ya ɗarso a zuciyarsa, da yadda zai yaje ya dawo da biyuninsa zuwa gare shi, a fili ya furta “Who is she? Ni ban san kamarta bama” Ya furzar da iska daga cikin bakinsa yana ƙara narkewa a jikin haɗaɗɗan bed ɗin nasa, cikin nutsuwa ya sake mirginawa a lokaci na babu adadi, yasan ko da wasa Dad ba zai ajjiye masa biyuni a Germany na, ƙasar kuma da yafi zuwa suna da yawa, taya zai iya suggestion wacce ƙasar ya kaita? Ya miƙe tsaye tare da nufar bathroom ya sakarwa kansa shower ruwan ya jima yana dukansa kafin ya kashe ya ɗauki tooth brush da Colgate ya wanke bakinsa ya fesa Rose Petal marmalade mint a bakinsa, time ya duba yaga lokacin sallah da saura, har ya zauna sai ya miƙe zuwa Library ɗin shi ya zauna saman chair yana ɗan jujjuyawa. System ce gabansa ya shiga searching sunan President Denial David, nan da nan aka watso masa bayanai akan mahaifin nasa, ya dinga dubawa amma babu abinda ya gani na ba daidai ba, information ɗin abubuwan da suke similar da abinda yake nema aka sake zubu masa, gently yake dubawa one by one har yazo kan wani suna DDMASTER BOM. Duka bayanan akan Fataucin mutane, Human trafficking; the unlawful act of transporting or coercing people in order to benefit from their work or service, typically in the form of forced labour or sexual exploitation. Daga nan kuma haramtattun miyagun ƙwayoyi, wanda suke taka rawa wajan lalata ƴan mata da matan auren da suke gidan su, hankalinsa ya tashi domin hadda ɗaya daga cikin wanda aka bawa Majeederh, hankalin Khalil ya tashi haka kawai yake son kawo ƙarshen zaluncin mutumin, domin ɓarnar yake sosai musamman ga al’ummar Nigeria da kulli Shaye-shaye yake ƙara yawa ba mata ba maza, ga violence everywhere. Ya yi jim ganin an rubuta a ƙasan sunan mutumin _A dangerous person_ Khalil ya yi shiru tunani fal ran shi, idan har zai kawo ƙarshen wannan dole sai ya zama jami’ai gashi he’s not interesting, ku magana zai yi da Hukumar da ke yaƙi da fataucin mutane ta Najeriya, NAPTIP?. Miƙewa ya yi ya nufi waje yana fita yaga still Debaka na nan kuma a upstairs take ya juya da sauri ya tuna yau a ɗakin ta yake, sai kuma ya shafa kansa ya ce “Allah ka yafe, na tuba” Ya murza ƙofar dake jikin part ɗinsa wacce kuma kai tsaye ta tafi har bedroom ɗin Majeederh.

Jingina ya yi a jikin door yana zubawa gadon bayanta idanu, wanda yake da glowing gwanin sha’awa musamman da ta shafi kwalacca, ga Ƙamshin MORESQUE Midnight dake ratsa hancinsa, Khalil ji ya yi kamar bai taɓa jin ƙamshi mai masifar daɗi irin na yanzu ba, duk da yana masifar son turaren shi, yana jinsa daban amma da alama dai yanzu ɗan kwali yaja hula, he can’t stay any longer domin ji yake kamar ana fusgar shi ne, Majeederh na tsaye tana ƙoƙarin shafa kwalacca ɗin a wuyanta zuwa ƙasan hammatarta, a hankali ta ji an rungumeta ta baya a ɓoye ta sauke ajjiyar zuciya, bata kula shi ba tana ji yana shasshafata can ya amshe kwalbar kwalacca ɗin ya sun shine da sauri ya kalli Majeederh ya kalli kwalbar sai kuma ya rausayar da kansa kamar yaro clamly a hankali can ciki ya ce “Duk wacce ta baki wannan je bata imani” Ta kalle shi ta ce “A sbd ta kashe wani?” Ya kwaɓe mata fuska ya girgiza kai ya ce “Eh” Ta harare shi ta ce “Wa?” Ya ce “Mijin Maluma” Tayi masa shiru tana ji yana tura kansa gabaɗaya wuyanta inda ya manta ne kawai bai shan-shana ba a jikinta, ya yi ya kwanta lamo ta fahimci da gaske ba shi ɗin ta kashe ta shirya tsaf ta ce “Malam fita” Ya mirgina ya ce “Zunubin naki ya yi yawa” Ya ware idanun sai kuma ya sanya ƙafa kamar zai ɗaga rigarta ya fizgota ta faɗo kansa saman ƙirjinsa ta ce “Fita matarka na jira” Ya lumshe idanunsa yana sauke numfashi a hankali ya ce “Naje ina?” Tana kunce gaban rigarsa ta ce “Ban son takura” Ya mirginata zuwa ƙasa ya yi mata rumfa sosai daidai kunnenta yana mata raɗa ya ce “Ya muke da Ayyu” Ta yi wani irin murmushi ta ce “Ohho” Ya yi squeezing bakinta ya ce “Kina son rabauta? Kuka a cikin jama’a?” Ta rufe Idanu ya ce “Ba gwara ki sani gaba ki cinye ba tas da wannan kukan? Ai kin san na miki yawa ma” Ya yi ya rungumeta sosai sune jima a haka ta ɗauka bacci yake can ta ji ya ce “I won’t do it again, sorry” Ta yi shiru ya marairaice sosai ya ce “Ban sakewa” a hankali ta ce “It’s ok” Ta juya shi itama zuwa ƙasa ta kwanta saman shi a nutse ta ce “Khalil” Ya ware idanunsa a kanta alamar dai yana jinta ta ce “Listen to your mother please” a ɗan zafafe ya ce “Waye mother ɗin?” Ta ce “Ummi” Ya ɓata fuska ya ce “Ni ban san wata Ummi ba, na ɗauka mother ɗin sunan wata ne” Ta daki ƙirjinsa sosai ya ce “Auchhhii” Ta ce “Ka gane me nake nufi, ka saurari mahaifiyarka don Allah” Ya lumshe idanunsa ya ce “I don’t have a mother” Idanunta ya cika da hawaye ta ce “Don Allah” Cikin faɗa ya ce “Wai ke da zaki damu da ita ni damuwa ta yi dani ne? Idan sun yi faɗa da mijinta ni mene laifina da zata barni eh? Me na yi mata ta barni a gantale she left me bata san ya nake ba all this year’s bata san waya bani tarbiyya ba, ilimi karatu, ko ɗan iska ɗan daba na zama ko kidnapper duk ita Ubangiji zai hukunta ta wofintar dani, she left me…..,” Saukar bakin Majeederh cikin nasa ya tsayar da shi daga masifar da yake zubawa ya yi shiru yana sauke numfashi sbd yadda yake jin tana….
[

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button