Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 18

Sponsored Links

Dakatar da ita tayi ta hanyar ɗaga mata hannu tace “bansan ke mahaukaciya bace sai yau to ta yaya zan cireshi a raina ta yaya zan fara faɗa min ta ina ake farawa Hanisa” gaba tayi ta barta a gurin ta biyo bayanta tace “kiramin shi ta wayarki” shiru tayi kamar bazata kirashi ba ta kuma cewa mgn fah nakeyi miki Aneey ki kiramin Abdu ta wayarki”
Badon ranta naso ba ta kirasa bugu ɗaya biyu ana uku ya ɗaga yace “Ya akayi Wyf ajiyar zuciya ta sauke tace “Yaya Hasina keson mgn dakai”

 

Murmushi yayi yace “Ok haɗani da ita” miƙa mata tayi ta karɓa ta ƙara a kunnenta memakon tayi mgn kawai sai ta fashe da kuka shima yayi shiru baice mata komi ba saida tayi me isarta sannan tace “yanzu Abdu irin adalcin ka kenan ashe dama rayuwa zata iyayin juyin da zaka watsar dani Abdu meye yasa ka kasa sona saboda Allah ne nasani ni na fara sonka nice na nace maka amma ko babu komi ya kamata ace zuwa yanzun na samu gurbi a zuciyarka Abdu wa ka aura ka watsar da narkon dakon soyayyata Abdu wace tafini matsayi da daraja a gurinka har kakejin bazaka iya rayuwa da ni ba ita zaka iya da ita wacece ita Abdu ya sunanta a wanne gari take?”
Numfashi yaja da har Aneesah dake gefe saida tajishi bata zaci zaiyi mgn ba taji yace “Kinga Hasina tsakaninki da Allah yaushe na taɓa yi miki alƙawarin aure? Tunda nake bantaɓa yima mace alƙawarin kaina ba domin banji a raina na haɗu da macen da zan iya saita rayuwata da tata ba sai cikin watanni takwas ɗin nan banci mutumcinki ba kuma ko ba so bazanci mutumcinki ba Hasina saboda har yanzun kinada sauran ƙima a idanuna dalilin kin kasance sanadi na samun abinda na daɗe ina farauta Hasina ƙanwarki Aneesah itace cikon farin cikina itace zaɓina da ita naji zan iya rayuwa in ƙare miki zance ma har na gabatar da ita ga Parents ɗina dukkansu sunyi na’am da zaɓina harma sun aminc……”

 

Wata ƙara Hasina ta saki tare da sakin wayar ta dafe kanta tana faɗin Innanillahi wa Innah Ilaihirraji’un Wayyoh Allah na ni Hasina na shiga uku na lalace lallai na yarda Aneesah ke micijin ƙaiƙayi ce wato duk wannan abinda nakeyi kallo na kikeyi ashe kece babbar yar iska…..” Da sauri Hanisa ta katseta da cewa “Haba Yaya meyasa kike wannan kalamin me nayi miki?” Wata damƙa takai mata ta shaƙeta ta haɗata da bango tana dukanta ta ko ina tana kuka tana cewa “Wlh baki isaba Hanisa kinyi kaɗan kici amanata nabarki” kokowa sukeyi sosai Hayaniyar Hasina ce ta fito da Mama da Baba Suka ishe su sunata faman kokowa Hasina na dukan Hanisa ita kuma ta kasa ramawa sai kuka takeyi da ƙoƙarin ƙwatar kanta.
Daƙyar aka rabasu Hasina ta zube a gurin taci gaba da kukanta me ciwo Hanisa ma kukan take ta kwanta a jikin Baba tana cewa “Bantaɓa jin a raina wannan ranar zatazo da idanun ƴar uwata zai rufe ta kasa tsayawa ta saurareni ba tunda muka taso irin wannan ranar da za’a shiga tsakaninmu bata taɓa riskarmu ba sai yau kuma akan namiji Yaya meye Abdu da zaki zaɓi cutar dani akansa meye ya faɗa miki da zaki kasa tsayawa ki saurareni har kika iya yanke hukunci da kalaminsa……”

 

Sake zaburowa Hasina tayi tace “Na rantse da Allah akan Abdu ko rana ɗaya mukazo duniya saina kasheki maci amana azzaluma mayaudariya maci amanar ƴan’uwantaka kullum na tambayeki tsakaninki da Abdu sai kicemin Abota ashe rusheni kikeyi kina kafa kanki tabbas kin shammaceni Aneesah kuma nima zan shammaceki kamar yanda kika rusamin farin ciki nima saina tarwatsa naki”.

 

Murmushi Hanisa tayi tace “ni kuma inada burin har gobe ki samu farin ciki koda zan rasa nawa kije ki rayu da Abdu Hasina bantabajin a raina zan rayu dashi ba domin bantaɓa yi masa kallon masoyi ba bakuma zanyi masa ba badon bai isaba a’a saidon farin cikinki ya samu”
Baba ne yace “Wai meye yake faruwa?” Sai yanzu hawaye ya zubowa Hanisa tace “babu ruwanku Baba kawai dai idan hukuncin da zan yanke yayi maku ƙunci ku yafemin zanyi ne don cikar farin cikin ƴar uwata inason ta rayu cikin farin ciki ne yasa na ɗauki wannan matakin” sulalewa tayi tayi ɗaki ta zauna gefen katifarsu ta haɗe kai da gwiwa ta rushe da kuka me gunji a tsakar gdan tana jiyo Muryar Hasina tanata bala’i tana faɗawa Mama abinda yake faruwa memakon ta tattarasu tayi musu nasiha kawai saita biyewa Hasina suka rinƙa ɗebewa Hanisa albarka kukanta ya ƙara ƙarfi ta dauko mayafinta da wayarta da ATM ɗin ta ta fito idanunta na tsiyayar da hawaye ta tsaya tace “Koda kike cewa na munafurceki na ɓoye miki wani abu Ni kaina bansan meke zuciyar Abdul-Ahad ba sai jiya kuma ban ɗauki abin da muhimmancin da zanji zan iya faɗa miki ba kiyi hƙr Yaya insha Allahu daga yau bazaki ƙara ganina ba harsai burinki ya cika” tana faɗin haka ta juya zata fice Mama tace “Eh aje wannan abin kunyar baza’ayishi a gdana ba banda tsabar iskanci ma tayaya hakan zata faru sun gama lole junansu da Yayarki sannan saboda ke watsattsiya ce ya dawo gurinki ki karɓesa sai aje wannan dai yafi ƙarfin ki aje abawa wasu suci shidai wannan na Hasina ne zanyi maganin ɗan iska”……..

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_

Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍“`♡♡

 

*OUM HAIRAN*
[12/16, 2:33 PM] Oum Hairan&Affan: *WATA KARUWA*

 

*OUM HAIRAN*

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button