Hausa NovelsYanci da Rayuwa Hausa Novel

Yanci da Rayuwa 5

Sponsored Links

*YANCI DA RAYUWA*

©️®️HAFSAT RANO

PAGE  5

Related Articles

****

“Please karki ce a ah, idan kuma house number ba zai samu ba, give me your number.”

_”Yafi sauki.”_ zaciyar ta, ta raya mata da sauri ta mika masa hannu alamun ya bata wayar sa, dan dama tunanin yadda zata zille masa take. Sai da ya kalli hannun nata sosai kafin ya mika mata wayar bayan ya cire passcode din. Karon farko da ta fara rike irin wayar ta rubuta masa number sannan ta mika masa.

“Thank you.” Yace yana kallon number murmushi shinfide a fuskar sa.

“Zanyi saving I will call you sai kiyi saving nawa, please idan na kira ki daga kinji?”

Gida masa kai tayi sannan a hankali tace

“A sauke ni anan.”

“Mesa? Mu karasa school din mana.”

“Nan yayi, zan karasa.”

“Shikenan, promise me idan na kira zakiyi picking.”

“Zanyi.”

“Ok, sai kin dawo.”

“Nagode.” Tace kanta a kasa sannan ta sauka. Jingina yayi da jikin kujerar yana jin wani irin feeling mara misaltuwa.

“Take me back.” Yace ma Uber driver din yana dan kishingida a baya cikin farin ciki.

Sauke shi yayi, yayi masa transfer kudi me tsoka ya dinga godiya ya wuce gidan cike da karsashi da farin ciki. He’s deeply in love. Ruwa ya sakar ma kansa ya fito ya shirya cikin shirin fita kamar kullum, be tsaya yin breakfast ba ya je part din Mum ya gaishe ta, sannan yayi mata sallama ya fito.
Yana kwance a bayan mota ya tuna be fada ma Mum maganar dawowar Rafeeq ba, wayar sa ya dauka a dan box din dake kusa dashi ya kira Neesa dan yasan Mum bata bude wayarta da wuri. Tana kwance tana bacci bata da lectures sai ten, wayar sa ta katse mata baccin, sai da ta bata fuska sosai kafin ta dau wayar dan tun ranar da yayi mata fada akan abinda tayi ma house help din nan take fushi dashi.

“Neesa kina ji?”

“Umm.”

“Idan kin tashi ki samu Mum ki fada mata feeqq zai nan da three days…”

Mikewa tayi gaba daya da saurin ta, dan guntun baccin da ke kanta ta neme shi ta rasa

“Mantawa nayi kuma zan dawo gida late gobe kuma next day da wuri zamu fita zuwa Kano so bana so na manta gaba daya.”

“Da gaske Ya Asim?”

“Ban sani ba.”

“Wow, bari naje na fada mata yanzu. Nasan dole akwai shirin da zatayi masa na musamman.”

“Ok.”

Kashe wayar tayi, ta zura slippers dinta ta yo waje cike da murna da farin ciki. Part din Mummyn ta wuce ta same ta a kwance tana hutawa tana ganin yadda ta shigo mata dakin sai da tayi mamaki.

“Lafiyar ki kuwa?”

“Good morning Mum, Ya Asim ne yace na fada miki nan da 3days Yaahh zai dawo.”

“3days, Saturday kenan.”

“Eh haka yace.”

“Yayi. Wuce ki sauya wannan kayan na jikinki ki kama kanki kuma bana son wannan shegen rawar kan naki.”

“Kai Mum, I’m just happy ne fa, nayi missing dinsa sosai.”

“Ke da happy din zan hada na kakkarya na watsar nan, wai ke da Asim waye yafi son Rafeeq ne ni Halimatu?”

“Ni, nafi Ya Asim.”

“Fita ki bani waje.”

Tace tana jefa mata pillow. Da gudu ta fice tana dariya. Tsaki taja bayan fitar aneesan, bata taba ganin irin wannan kaddarar ba. Kwafa tayi ta jawo wayar ta, ta kunna ta sannan ta soma laluben number Hajiya Luba.

***A gurguje ya shirya saboda yadda lokaci ya tafi, duk da ya gama komai tun jiya amma sai da AJI ya sake sakashi wani aikin a yau da zai bar kasar hakan ya jawo masa bata lokaci sosai gashi baya so yayi rescheduling na flight din ya riga yayi making mind dinsa yau zai tafi dan haka baya jin ko kwana daya zai kara a kasa. Contract din gidan da yake ciki tun kwana uku ya kare dan haka dole ya tattaro ya dawo main house nasu ya karasa kwana ukun.
Mubarak da Robin ne suka raka shi train station daga nan ya wuce airport yana zuwa baa wani dade ba suka tashi sai kasa me tsarki. Tunda yaje ya dukufa da adduar neman zabin Allah a duk abinda ya saka a gaba da dukkanin damuwar dake damun zuciyar sa.
Ranar da zai taho Nigeria da sassafe Asim ya kirashi a time din Nigeria duk da su akwai banbancin two hours tsakani. Murmushi yayi kiran na shigowa dan tunda yazo ya ajiye batun gadgets dinsa a side abinda ya kawo shi kasar kawai yayi sai yau ya bi ta kan wayar aikuwa dama yasan dole zai kirashi haka ma Aneesa ta kira kuma ta bar masa sako a WhatsApp. Number Mummy da ya gani a jerin wadanda suka kirashi ya saka shi jin wani iri wanda zai iya rantsewa a iya zaman sa kiran da tayi masa gaba daya ba zai fi goma ba idan ma ya kai, duk abinda take so sai dai tasa Asim ya yi mishi magana daga nan ita kuma sai taji. Share tunanin yayi ya daga wayar Asim din dake neman katsewa sukayi magana kadan yayi korafin da zai yi sannan suka aje wayar a tare. Bashi da time din bin kiran nasu sai kawai yayi ma Aneesa reply ya maida wayar flight mood gaba daya bayan ya kira line din AJI ya jishi a rufe, ya tabbatar baya kasar ma watakil dan ba zama yake ba sosai a Nigeria din yafi zaman Ethiopia itama Mummy dan kasuwancin ta da siyasar da take yi ne yasa dole take zaune anan din.

***Sabbin chefs ne su biyu mace da namiji aka kawo, a falon da ake ajiye baki irin su aka ajiye su sannan Hassy ta kira landline din part din Mummy din ta sanar mata sun karaso. Sawa tayi a kira mata Noor kafin ta fito Ben ya kira wayar ta lokacin tana zaune a dakin ta, tana karatu kamar kowanne lokaci idan bata da aiki. Sau kusan biyar Asim na kiran wayar Allah yasa normal line dinta ta bashi ba wanda Ake neman ta dashi a gidan ba sai kawai ta kashe line din gaba daya dan fargaba da tsoro da firgici ba zasu taba barin ta, ta daga wayar ba sam. Zatayi iya kokarin ta, ta yi avoiding haduwa dashi bare har ya gano in da take daga nan labari ya sauya. Da saurin jiki ta tashi ta yi shirin da ta saba idan zata shiga ciki ta fito ta wuce part din da Ben din ya fada mata nan zata je.
Suna zaune ta shigo suka kalle ta itama ta kalle su sai ga Mummy nan ta fito cikin shiga ta alfarma ga wani irin masifaffan kamshi da ya mamaye ilahirin falon. Kasa sukayi da kansu har ta karaso Hassy na rike da handbag dinta da sauran wayoyin ta. Bata zauna ba dan ta yi late daga tsayen ta kalle su suka gaishe ta dukka da mutuntawa ta amsa musu kadaran kadahan tana dan kallon Noor da kanta ke matukar kasa sosai.

“Taro ne damu a gidan nan, babban yarona zai dawo yau da yamma. Dan haka nake so ku shirya mana abinci na musamman, ka shirya komai a garden din baya tare da taimakon sauran masu aikin gidan, duk abinda za’a bukata akwai shi sannan Ben zai baku list na abincin da nake so ayi, ku tabbatar kunyi aiki me kyau kuma ku kula matuka dan bana so a samu matsala. Karku manta duk abinda ku keyi akwai masu sa ido akai sannan duk wani lungu da sako na gidan nan akwai CCTV tana kallon su.”

“In sha Allah, zamuyi abinda ya dace.” Noor tace da sauri

“We will do our best ma.”

“Yayi kyau.”

Tace tana yin gaba, Hassy da Hindatu suka bi bayan ta da sauri. Tashi Noor tayi sannan tace su biyo ta. Kitchen din suka wuce Ben ya bata list na komai ta duba sannan ta soma fiddo abubuwan da zasu bukata suna tayata.

***Da wajajen la’asar motocin alfarma suka soma shigowa gidan, duk motar da ta shigo sai ka zata ka gama ganin me kyauwun ta sai kaga ba haka ba, a hankali harabar gidan ta cika da motocin duk kuwa da mutane ba wasu masu yawa bane ba sai dai kusan kowa da motar sa yazo. Yawancin su kawayen Mummy ne da yan uwanta kadan da na AJI, duk da yadda zuciyar ta take cike da takaicin dawowar Rafeeq din amma haka zata danne tayi abinda zai bar mutane da magana ko dan siyasar da take ciki. Zatayi komai domin samun cikar burin ta dan haka idan ka ganta a ranar zaka dauka tana cikin matukar farin ciki mara misaltuwa.

***A gajiye yake sosai sanda suka iso Abujan, ya riga ya gama tsarawa kansa sai ya fara zuwa ya huta a gidan sa sannan ya dawo gidan nasu da wannan plan din ya zo dan baya da bukatar wata hayaniya a yau din. Be san da shirin Mum din ba duk da zata aikata koma menene amma be taba tunanin hakan ba.
Motoci ne guda uku suka zo tarbar sa,babu motar sa ko daya duk na gidan ne daya ma sabuwar motar da mummyn ta siya ne kwanan nan a ita ta aiko a dauke shi. Ba Saddam ba yaran sa ko daya, Dariya ma abun yaso ya bashi sai kawai yayi murmushi ya fada bayan motar kawai dan yayi tunanin ganin Asim duk da har suka gama waya dazu be masa maganar zai zo daukar sa din ba.
A jajjere suka gaishe shi hade da sannu da zuwa sannan suka dauki hanyar gidan kamar yadda mummyn tayi umarni.

“Apo zaku ajiye ni.” Yace yana kara relaxing sosai a bayan motar.

“Oga hajiya tace muzo gida farko, ta shirya maka surprise ne.”

“Surprise? Na me fa?”

“Surprise ne Sir.”

“Tell me.”

“Anyi inviting mutane ne, more like a dinner dai Sir.”

“Oh ok, harda Asim aka hada baki ko, shisa be zo ba.”

“Oga Asim baya gari Sir.”

“Ohh.. ok.”

Daga nan be sake cewa komai ba, yayi relaxing sosai yana ayyana yadda zai yi ruining suprise din da aka ce an hada masa, bashi da bukatar wani suprise wanda ya riga ya san dalilin hada shi, sanda suka karaso unguwar sai kawai yace suyi parking a baya sannan ya sauka a nutse ya dauki backpack dinsa ya nufi gate din bayan dan bashi da bukatar ganin kowa a yanzu har sai ya huta sosai. Tsaye sukayi suna kallon sa har ya shige cikin rashin sanin me ma ya kamata suyi dan tabbas Hajiya sai ta yi musu fada abinda suke tsoro kenan.
Kusan duk bayan wata daya zuwa biyu sai an sauya yanayi da paint din gidan nasu, be yi mamaki ba dan yaga sauye sauye har da karin wani sabon gini da aka kara a bq.

Tana tafe cikin hasken fitulun gidan da suka haske wajen sosai suka hade da duhun farkon magriba da ya fara kawo jiki,a gajiye take tikis dan tunda tazo gidan bata taba wahala irin yau ba duk kuwa da akwai help amma itace akan kusan komai dan bayan sun gama sai da Hajiyar tace su sake an kara samun wasu mutajen, dan haka sam bata lura da mutum ba, dan ba hanyar wucewar mutane bace ba, sai kawai ji tayi ta bugi mutum plate din hannun ta, ya fadi kasa abincin ya watse a wajen.
Da wani irin zafin nama ya riko ta ganin tana neman kai wa kasa, hannunsa ya hadu da nata a take wani irin shock ya shige shi. Da wani irin sauri ya janye hannun nasa
Karasa kaiwa kasan tayi ta durkusa sannan tace jikinta na rawa

“Dan Allah kayi hakuri, wallahi ban ganka ba.”

Kallon yanayin da ta shiga yayi, duk da fuskar ta dake rufe amma yana iya hango tsantsar tashin hankali da tsoro a tattare da ita. Samun kansa yayi da jin babu dadi, a hankali cikin muryar sa me cike da amo da daddadan sauti da nusuwa yace

“Baki ji ciwo ba?”

“Banji ba, kayi hakuri dan Allah.”

“Get up.” Yace yana mika mata hannun sa alamun ta tashi, kallon hannun tayi ta girgiza kai da sauri, da sauri shima ya janye hannun ya tura shi cikin aljihun wandon sa.

“Tashi kije.” Yace mata sannan ya raba ta gefen ta ya wuce kawai ba tare da ya sake cewa komai ba.

 

#Thelovetriangle💓🥰

🔥🔥 *ZAFAFA BIYAR* 🔥🔥

*MAMUHGEE* and *HAFSAT RANO* OF ZAFAFA BIYAR sundawo muku dauke da Wani sabon labarinsu me suna *AMATULMALEEK* By Mamuhgee and *YANCI DA RAYUWA* By Hafsat Rano!!!!!

Masoyan Mamuhgee and Hafsat Rano Dama masoyan zafafa gabaki daya kuzo ga damar karanta sabon labarai dazasu shiga cikin ranku sosai sbd zafin dasuke dauke dashi tareda nishadantarwa, ilmantarwa harma da qaruwa acikinsu,

Labarin AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA labaraine dazai burge ku yakuma kamaku kaman yanda kuka sani zafafa never disappoints,
Soyayya me sanyi da nutsuwa,
Nishadi me sanyaya Rai,
Qaruwar gaske,
Mamakin rayuwa da abinda take kunsa,
Kaman dai yanda kuka sani labaran zafafa Basa wasa.
Me kuke Jira?
Just pay 1000 kiyi joining tafiyar sanyayyun labaran AMATULMALEEK and YANCI DA RAYUWA 🙌🤝🫶

YANCI DA RAYUWA
Hafsat Rano

AMATULMALEEK
Mamuhgee

Guda biyun 1k
Guda Daya 500

Pay at
0022419171
Access bank
Maryam sani
09033181070
07040727902

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button