Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 34

Sponsored Links

PAGE THIRTY-FOUR*

 

Hajiya ce tayi gefe ta zauna a qasa ta dafe kanta tana zubar da hawaye tana maimata kalmar innanillahi wa Innah ilaihir raji’un ta zubawa Hameed din ido mamaki takeyi na labarin da Dr Saleem ya sanar dasu ko a mafarki kuma ko a hasashe zuciyarta bata taba raya mata hakan ba ashe gaske ne baka bada shaida akan dan zamani komai zai iya, da wanine ya bata wannan labarin ba Dr Saleem ba kuma ko shidin dabai nuna musu shaidar bayyane ba ta hoto me motsi wato video da yayima Hameed din da Umaimah lkcn da suke qalubalantar junansu akan cikin ba da bazata taba amincewa Abdulhameed dinta zai aikata haka ba kuma tasani tabbas laifinta ne tunda dagashi har Umaimah sun tabbatar Mata dako an rabasu bazasu rabu ba yanzu gashi garin gyara tayi gagarumar barnar da zataci gaba da yado har qarshen zuri’arsu.

 

Maganar Kaka ce ta dakatar da ita daga tunanin da takeyi tace “banga laifin Hameed ba laifin Umaimah ne tunda ita mace ce yakamata ace tayi qoqarin kare kanta amma ita da kanta ta gudu daga gdannan saboda haka itace ta fara bashi qofa kuma bisa sahalewa da jagorancin ki Zulaiha da kinbi komai a hankali kamar yanda muka tsara tun farko duk da baa kawo wannan matakin nadama da fargar jajinba”

 

Hawaye ne yakebin kuncin Hajiya ta miqe tana hada hanya ta zari mayafinta ta dubi Hameed tace “katashi ka kaini inda ka boyeta wawa kawai” bata jira abinda wani cikinsu zaice ba ta fita Daddy ne da Hajiya Kaka suka biyota sai Hameed da yake tafe kamar wanda kwai ya fashewa a ciki yana zazzare idonu kamar wanda aka tsayar hisabi🤣

 

Shiga motar yayi gabansa yana faduwa ya tasheta Suma suka shiga yajata a hankali suke tafe babu wanda yake iya cewa da wani qala tsakaninsu kowa da abinda yake ayyanawa a ransa.

Shi Daddy mamaki nema ya cikashi da suka shigo unguwar ko a Ina Hameed din yasan unguwar koshi da yake ubansa jin sunan anguwar yake amma bai taba shigarta ba parking yayi a qofar gdan ya bude ya fita ya bude get din ya dawo ya shiga motar sosai Daddy yake binsa da kallon mamaki wato saboda tsabar bai yarda da kansa ba ko megadi baisa a gdanba suna shiga yayi parking a dan qaramin parking space din da baifi na mota biyu ba budewa sukayi duk suka fito zama yayi a cikin motar bashi da niyar fitowa saida Daddy ya doka masa tsawa ya fito simsim ya bude musu qofar parlourn suka shiga sun jima suna qarewa parlourn manyan hotunansa da Umaimah da sukayi da gani kasan suna cikin shauqin qaunar juna lkcn da sukayi hotunan su Hajiya ta zubamawa ido tana mamakin lamarin juyowa tayi ta watsa masa jajayen idanunta tace.

 

“Ko babu halin nuna mana inda hamshaqiya mandiyar me wanke qafa da sosan qarfen takene”🤣🤣
Ba Hameed ni kaina da ace naga alamun rahma a gurin Hajiya babu abinda zai hanani darawa amma Ina babu dama sumsum ya wucce ya murda jamlock din qofar ya bude ya shiga suka rufa masa baya tana nade cikin bargo tana sharar baccinta saboda magungunan daya bata kafin ya fita harda na bacci kallon kallo aka shigayi tsakanin Hajiya da Daddy da Kaka shikam gogan zuba mata ido yayi yanda take baccin da gani kasan bana dadi bane na wahala ne saboda shida kansa yasan tsakanin jiya da yau ba qaramin kashi ya bata ba ga zazzabin da take fama dashi.

 

Yama manta dasu Daddy a gurin ya haye gadon ya yaye blanket din data rufe jikinta dashi daga ita sai harp vest rabin qirjinta duk awaje yake hanunsa ya dora a saman cikinta yana sauke ajiyar zuciya tare da dora daya hanun a tudun boobs dinta da sauri Daddy ya kawar da idonsa tare da qwallah masa kira yayi firgigit ya dago tare da kallon iyayen nasa ya sosa kansa a kunyace yace.

 

“Oh sorry Daddy tashinta zanyi fah” Hajiya ce tace “dan ubanka haka ake tashin mutum a bacci wato gwada mana zakayi a gabanmu mugani ko zaka sauka a gadon kosan na dagargaza maka kai shashashan banza da baisan kansa ba” miqewa yayi a sanyaye ya koma gefe ta haye gadon ta fara tashin Umaiman shure² ta farayi tana qunquni tana cewa “nifa ka qyaleni banason takura wlh baccinma bazaka bar mutum yayi ba kai kullum baka da aiki sai jarrab…..”

 

Dukan bakinta Hajiya tayi tace “kinci uwarki keda jarabar dan ubanki tashi nice dai da kika gudo kika baro saboda inason qwata miki yancinki shashashar banza” ai suman kwance Umaimah tayi saboda tsabar tsoro da firgici batasan sanda fitsarin da takeji tun dazu ya kwace mata ba don tasan yau kashinsu ya bushe daga ita har Uncle din nata🤣🤣🤣

 

Finciko Hajiya tayi dan guntun fitsarin da take matsewa ya qarasa zubowa tayi baya luuuuuu zata fadi yayi wani kukan kura ya rungumeta yace “ke kada ki zubarmin da ciki wlh ranki baci zaiy….” Wani lafiyayyen naushi Daddy yayi masa a baki tare da fincike Umaiman daga hanunsa ta fada jikin Daddyn saboda nanne kawai take tunanin sauqi ta lafe a jikinsa ta saki kukan munafurci tana cewa “wlh Daddy bansan ya akayi hakan ta faru ba don Allah kada ku kasheni wlh bazan qaraba zanyi muku biyayya wayyoh Allah mamana wayyoh Abbana….”

 

Rufe mata baki Daddy yayi ya daka mata tsawa yace “zakiyimin bayani ne dan qaniyarki Hajiya ce ta bude wadroop ta zaro mata hijjab ta cillah mata tasa Daddyn ya figeta zai fita da ita Hameed ya riqeta da sauri yace “Daddy Ina zaka kaita?” Juyowo yayi ya watsa masa daquwa yajata shima ya kuma riqeta sai yanzu da yaga da gaske zaa rabasu sannan yaji zuciyarsa ta fara tafasa yace “amma Daddy kasan akwai shaquwa tsakanin mu ku barmin ita harta haihu don Allah ku barta na kula da dana batasonsa zata iya zubarmin dashi fah” finceke hanun nata Hajiya tayi Daddy yana riqe da ita a parlourn yaga mukullin motar daya kawosu ya dauka ya jefa Umaiman ciki Hajiya tashiga Kaka ce ta fito itama ta shiga yanabinta yana bata hqr akan ta fada musu su barsa da matarsa harsai ta haihu inyaso duk hukuncin da zasuyi sai suyi amma itadinma babu wani sauqi.

 

Jan motar Daddy yayi a guje da sauri Hameed din yayi baya suka budeshi da qura yana ganin sun fita ya zube a gurin ya saki wani ihu yanata da qura kamar zararre.
Daqyar ya iya tashi ya shiga gdan ya fada saman kujera yana saqawa da kwancewa tabbas akwai buga March tsakaninsa dasu Daddy saboda shidai yasan bazai taba iya rayuwa babu Umaimah ba to waima wanne munafikin ne ya sanarwa su Hajiya Umaiman na gurinsa?……..

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[1/19, 9:39 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *GIDAN UNCLE*

 

Ki biya kafin ki karanta idan kinaso ki kira number nan; 09031307566:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button