Gidan Uncle Hausa NovelHausa Novels

Gidan Uncle 76

Sponsored Links

Kawar dakai Hajiya tayi tace “toni meye nawa a lamarin nan Hameed tsakaninku ne babu wanda zaiyi ma Umaimatu dole kaje kaci gaba da jarraba sa’ar ka idan rabonka ce zata sauko ku daidaita amma abin da ciwo kuma Umaimah bazata fahimceka ba sai kayi da gaske saboda haka Allah yabada saa” tana fada masa haka ta shige dakinta ya buga kansa da kujerar kusa dashi yanajin wani ciwo a zuciyarsa baisan meyasa son Umaimah yaqi qyale rayuwarsa ta hutaba tabbas so masifa ne yanzu badon ta fahimci yana sonta ba da bazata fada masa mgnr nan ba amma babu komai a juri zuwa rafi.

 

Miqewa yayi daqyar ya shige dakinsa ya fada gado yaci gaba da rera kukansa ya kasa control tear dinsa akan lamarin daya shafi Umaimah kuka yafi masa komai sauqi akan lamarinta baitaba zubarwa da mace hawaye ba sai akan Umaimah miqewa yayi yayi sujjada yace “Allah ka mallakamin Umaimatu a karo na biyu Allah banyi zato ba ka bani ita a karon farko Allah kada kabata ikon wahalar dani” yana addu’ar yana kuka me shiga jiki.

Related Articles

 

Haka kwanaki sukayita shudewa duk ta inda Hameed ya biyo Umaimah gocewa takeyi duk wani wanda yasan zai hadata dashi ta saurareshi ya hadata dashi amma taqi sauraron kowa kalmarta daya ce tagama zaman aure da Hameed.
Wannan kalma tana caccakar zuciyarsa da haka har lkcn da aka bashi a gurin aiki ya qare ya juya California zuciyarsa taf da damuwa Umaimah tana neman fin qarfinsa qarfi da yaji ana ya gobe zai taho ne yayi mugun ganin da ya daki zucciyarsa ya rabonsa da sanyata a idonsa kwanaki uku kenan daya bita makaranta ta zage ta cire girmansa da nasabarsu ta debe masa albarka tsaf har tana fada masa ta tsaneshi ya fita daga rayuwarsa ranar yayi nadamar zuwanshi duniya da kasancewarsa namiji haka ya koma gda jiki babu qwari.

 

Sai yau a karin banza ya ganta tsaye da wani qato Alh Jabir a shopping suka hadu ya gigice ya rinqa binta tana yagashi hardai ya samu ta saurareshi ya biya mata kudin siyayyar da tayi naira dubu tamanin sannan ya karbi compliment card dinta sukayi sallama ta shiga motarta shima ya shiga tasa suka tafi ranar sai gashi yazo gdan suna tsaye suna hira yanda take bawa Alh Jabir amsa kawai ya isar masa ya gane ba shine a gabanta ba amma ya kasa ganewa daidai lkcn Hameed din ya fito tsayawa yayi turus gabansa na tsananta faduwa mutum na uku kenan da yazo ya tarar da ita da maza mabambanta suna hira suna dariya amma shi da yayi mata mgn sai ta daure fuska wannan abu na cizonshi ba kadan ba to ranar ma daurewa yayi yaja qafarsa yace gurin yayi mawa Alh Jabir sallama ya amsa tare da miqa masa hanu suka gaisa ya kwantar da murya kamar mutumin kirki yace “am duk da nasani yarda da amincewa ka samu daga gurinta amma bazan fasa fada maka Umaimah nine zan aureta ba kayi hqr ka rabu da ita Allah zai mayar maka da wadda tafita”

 

Kallonsa sukeyi dukkansu da mamaki musamman Umaimah da ta fara gajiya da wulaqancinsa tayi saurin kawar da kanta tace “am manta dashi Alh na yanada yar matsala ne kawai dai yanzu zan sanar da Daddy yanda mukayi dakai saika turo ayi mgn amma wlh da banida niyar aure kawai dai takura dasa idone banaso” tana mgnr tana sanya hanunta ta cire hanunsa daga na Alh Jabir.

 

Sosai wannan wulaqancin ya girgiza nutsuwarsa da kwanciyar hankalinsa harma da lfyrsa wato qiyayyar Umaimah gareshi har takai wadda zatake dangantashi da hauka? Tambayar daya rinqa yiwa kansa kenan yana kuka jikinsa yana rawa duk ya rame yayi duhu saboda damuwa da azabar kishin da yasawa ransa koda yake ba laifinsa bane kishi halitta ne bare a Shuwa’arab ba mazansu ba matansu wannan dalilin yasashi dole ya hada komatsansa cikin dare yayi booking na jirgi da asuba zakara ya bashi saa saboda Idan ya zauna a 9ja tsaf Umaimah kasheshi zatayi da baqin cikinta.

 

Watansa daya a California ya kasa hqr ya juyo gda 9ja saboda kiran duniya Idan ya kira wayar Umaimah bata dagawa ko WhatsApp ko SMS idan yayi Mata bata bashi amsa abun ya fara fin qarfin tunaninsa da farin cikinsa ya isa gdan ko driver bai kiraba saboda zaquwar da yayi yazo yaga sanyin ruhinsa gabansa ba qaramar faduwa yayi ba ganinta da balaraben da yataba ganin sun jera da ita a makarantarsu idonsa har lumshewa yakeyi saboda bala’i ya isa gurin kamar zaiyi musu mgn sai kuma ya fasa ya shige gdan fuuuuu yana shiga yayi watsi da system dinsa da wayoyinsa ya zube a gurin yana kiran “ya Allahu ya hakimu ya razzaqu ya rahamanu ya rahim” yama rasa meye zaice qarar faduwar kayan ne ya sanya Hajiya da Daddy fitowa da sauri daidai lkcn da Nawwas ya fito yanz rarrafe ya shige jikinsa qanqame yaron yayi yanabin iyayen nasa da kallo zuciyarsa na ciwo yace.

 

“Fisabilillahi Daddy adalci kenan kubar Umaimah ta rinqa kwashe² kowanne kare doki yanzu wannan kuma me yazoyi gdan nan?” Hajiya ce ta tafa hanu tace “Heee Allah na dawo inji dan cirani yanzu Hameed sanyata zamuyi a gaba mu kwadata muci ko kuwa hanata zabin ranta zamuyi shita kawo tace tanaso mgn har tayi nisa ma aure saura sati daya kayi hqr ka rungumi sorry Umaimah ta daina yayinka….” Daga mata hanu yayi a fusace ya miqe kamar mahaukaci yace “ya isa Hajiya basai kin kasheni ba naji naji abinda kikeso kice amma wlh tallahi bai isa ya auri matata ba nagaji da binku din da nakeyi kuna neman turani kabari nine na farko kuma nine na qarshe ko Sulaiman don babu yanda zanyi ne na barshi yayi shuka a gonata amma wannan kodadden balaraben bai isaba wlh saidai muyi mutuwar kasko zan saceta nabar qasar da ita idan yaso kowa ya huta kuma wlh Idan na dauketa guba zan dura mata sannan nima nasha tunda naga Allan ma bazai kasheni na huta ba gara na kashe kaina da kallon wannan ta’addancin da akeyimin ni banida gata banida masu sona bani da wanda zai tausaya min bayan kunsan komai….”

 

Katse mgnr yayi saboda numfashinsa da yake sama da sauri ya dafe qirjinsa yayi waje a guje da sauri Daddy yabi bayansa ya riqo hanunsa ya juyo da sauri zuciyarsa na tafasa idanunsa na fitar da hawaye yace “ka qyaleni Daddy wlh kasheta zanyi na kashe kaina kowa ya huta na gaji Daddy na gaji wanne irin rarrashi ne banyi yarinyar nan ba wanne irin qasqantar dakai ne banyi mata ba koda ace a cikin hayyacina nayi mata laifin da take iqirarin nayi mata indai tanada imani ya kamata ta tausayamin….”

 

Daidai lkcn sukayi sallama Prof Khair ya shiga motarsa ya tafi ita kuma ta tako cikin takunta na isa ta raba ta gefensu zata gifta ya cafko hanunta da qarfi ya finciko ta ta fada jikinsa babu kunya yasa hanu ya matseta yace “wlh tallahi billahillazi La’ilaha illah huwa babu wanda ya isa ya rabani dake don kece rayuwata Umaimah ko zaa kasheni kuma ko zan rasa komai nawa a yau sai an dauramin aure dake idan kuwa akaqi wannan karon zan saceki sacewar da babu wanda zai sake ganinki har abada” yana fadin haka ya fizge hanunsa daga na Daddy Hajiya tayi saurin riqeshi tace “Alh kayi wani abu kace wani abu wlh Hameed ya haukace baa cikin hayyacinsa yake ba zai iyayin komai Alh yaronnan mukaishi asibitin mahaukata a duba kwalwarsa” daga mata hanu yayi yace.

 

“Babana shiga gda zaayi yanda kakeso a yau da wani bacin ran gara wani Umaimah zo inason ganinki” sakinta yayi ya zube a gurin yana kuka me gigita tunanin kowa da ban tausayi yace “babu inda zani Daddy ni zakayi wa wayo wlh yau saina kwana da Umaimatu kota halin qaqa nasani tana sona toshewar qwalwarta yasa ta kasa fahimtar hakan waye zai aureta ya riqe mana yayanmu idan bani ba so take dole saita tozarta amanar Allah so take dole sai twince sun tashi sun fuskancin cewa su marayune meyasa zata bijirewa saqon zuciyarta bayan nasan babu son kowa a cikinta sai nawa meyasa bazaku kalli idonta ba kalli Daddy Hajiya kalli idonta wlh sona kawai nake hangowa a ciki so take ta kasheni ta kashe kanta bayan tasan ba cikkakiyar lfy ce dani ba itama kuma nasani zuciyarta ta kamu da irin ciwon da yake damun tawa zuciyar”

 

Daqyar Daddy da Hajiya suka bambareta daga jikinsa suka jata suka shiga da ita gdan suka kulle parlourn ya miqe yana buga qofar da qarfi yana cewa “ku bude bude Daddy zan balle qofarnan wlh saika bani matata ai donni kadai aka halicceta bazan yarda ku rabani da matata ba…..” Surutai dai rututu na rashin kan gado haka Hameed yakeyi kamar zautacce yana dukan qofar kamar zai balleta saida ya gaji ya hqr ya fita ya shiga motarsa ya nufi gdansa ya bude dake an gama aikinsa tsaf har ya zuba komai na amfani ya fada daya cikin dakunan ko qofar bai rufeba jikinsa yana bari zuciyarsa na tafasa yana dafe qirjinsa da qarfi yana nishi da kakarin aman wahala.

 

Shi kuwa Daddy yana shiga da ita ya zube akan gwiwarsa ya ruqo hanunta yace “badon ni ba badon na isa dake ba don girman Allah Umaimatu ki duba maraicin twince da wasiyyar mijinki Sulaiman ki bani dama ta qarshe na daura auranki da Hameed yaron nan ya garu sosai sonki zai kasheshi Umaimatu ya zakiyi da haqqin ran dan’uwanki idan ya mutu saboda ke bayan kinada yanda zakiyi ki taimakesa….” zubewa tayi ta rungume Daddy tana kuka me ban tausayi tace “kada ka qara roqona akan wannan Daddy zan iya bada rayuwata na fanshi taka balle wannan wlh indai hakan zai zama farin ciki a gareka na amince da auren Abdulhameed indai hakan zai zama farin cikinka na amince wlh na amince Daddy” tana fadin haka ta miqe da sauri ta fada daki saman gado ta fashe da wani kuka me ciwo tana cewa “Allah ka yafemin laifin da nayi maka ka sake jarabta ta da auren Abdulhameed Allah ka dubeni ka kawomin dauki cikin buwayarka Allah na roqeka kabani ikon yima mahaifina biyayya”

 

A wannan daren Daddy bai zauna ba yana fita ya kira Yusuf da mijin Aunty Zarah a masallaci bayan sallar magaruba ya fadawa limamin cewa yanada daurin auren yayansa biyu yabada komai aka daura auran akan sadaki dubu dari biyu suna shiga gdan ya fadawa Hajiya takuwa rangada guda ta daga hanu sama tace “Allah na gde maka daka sake gwadamin wannan rana Umaimatu na matar Hameedu na wayyoh dadi kasheni na huta” tasowa tayi zata fito taji mgnr Hajiyan ta koma da sauri ta zauna tana fadin “Hasbunallahu wa ni’imal wakil Innanillahi wa innah ilaihirraji’un Allahummah ajjirni fi musibati wa’akalifni khairin minha yanzu nice matar Hameed mutuwa ta tazo ya zanyi da jarabar Hameed” shigowar Hajiya ne yasata dagowa ta dubeta hawaye nabin kuncinta tace “Hajiya yanzu shikenan an daura aurena da Hameed Hajiya kwanana ya qare nama sani bazan iya dauke lalurarsa ba kamar yanda na dauka a baya Hajiya ki taimakeni….”

 

Rufe mata baki tayi da hanunta tana girgiza mata kai tace “kiyi hqr Umaimah Hameed zai canza baza kiyi irin zaman da kukayi a baya ba wlh ni kaina da farko banyi farin ciki ba amma yanzu ina farin ciki sosai saboda na yarda kuma na gasqata Hameed sonki yakeyi da gaske baso irin na sha’awa ba” da wadannan kalaman tayita rarrashin ta har ta samu ta saurara da kukan dama ta fara shiryata da magungunan su kasancewar saura sati daya aurenta da prof Khair saboda haka ta dora daga inda ta tsaya tunda tariga tasan halin dannata ba sauqi gareshi ba.

 

Yusuf ne ya nufi gdan Hameed din da nufin yi masa kyakkyawan albishir get man din ya tambaya ko megidan yana ciki yace masa eh yayi parking ya shiga yanata kiransa yana cewa “dallah malam ka fito haukanka yayi rana Allah dai ya yarda kuma ya amsa addu’ar ka Umaimatu ta dawo garek….” Tsayawa yayi cak mgnr ta maqale a maqogaronsa saboda ganin Hameed din kwance a qasa cikin amai yayi kaca² sauri ya saki ihu ya matsa ya dagoshi yana jijjigashi yana fadin “mun shiga uku Hameed kada ka mutu Daddy ya baka matarka ya daura aurenku…”

 

Riqeshi yayi cikin wata wahalalliyar murya yace “yay…ya daura in…ina Umaiman tak…” Muryarsa ce ta sarqe daidai lkcn Daddy suka shigo da gudu suka qarosu suna salati suka tattageshi sai asibiti likitoci suka rufa a kansa suna ceto rayuwarsa bai farka a ranar ba sai washe gari ya farka da qwarinsa saboda yasha drip babu qarya qyam ya miqe yana layi Daddy ya riqeshi ya kalli Daddy yayi murmushi yace “idan naje gdana yanzu zan tarar da bloody tana jirana?”

 

 

 

 

*UMMUH HAIRAN CE…✍🏻*
[2/5, 9:08 AM] UMMUH HAIRAN CE…✍🏻: *_GU_*

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button