Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 48

Sponsored Links

48

Ajiyar zuciya ya sauke mai sanyi sannan ya dauke idonsa daga binta da yayi da kallo sanda ta gama shigewa cikin hostel din nasu,a hankalibya sauke hannauensa ya shige motar da tuni aka bude masa murfinta,sauran suma suka shiga tasu suka tashi motocin suka bar wajen.

A tsaye ta sameta a varender din dakunan nasu ita da wata maqociyar dakinsu surayya,da alama hira suke,saidai idanunta na can farfajiyar harabar da motocin khalipha sukayi parking kafin su tashi
“Idonki kenan?” Hanan ta fada tana murmushi gami da jifan ayshan da hararar wasa kafin daga bisani ta nufota
“Kedai bari kawai hanan….sabgogi ne suka sako kai sai godiyar Allah” karbar daya daga cikin qaramar jakar dake hannunta tayi
“Dakin ba dadi gaba daya,kullum hunaifa na bakin gadonki”
“Allah sarko daughter na,yau dai zan ganta” ayshan ta fada tana zama gefan gadonta
“Inafa zaki ganta uwarta ta maidata wajen kakanninta saboda tsabar cin zali,idanu aysha ta zaro
” kai hab,badai yaye ba ai bata rufa shekara biyu bafa”
“Hmmm,kefa mmn huanifa dadi miji” dariya suka saki baki daya kafin daga bisani hanan ta tsagaita
“Ke tsaya….idanuna sun gano gulma fa,wanne handsome dinne ya ajeki haka da jerin motoci?,ko zancena ya tabbata ne?” Murmushi aysha ta sani tana tuna khalipha,yadda da fari yayi kaman baisan sunzo ba,bai bude mata qofa ba bare shima ya fito sun jima zaune a haka
“Yaya na ne” idanu hanan ta zaro
“Da gaske?,….kai amma ma sha Allah,hala dai duka gidanku kyawawa ne” ta tambayi ayshan tana dariya,tsaki ayshan taja itama tana dariya
“Ban sani bani,naxo baki bani komai ba kin cikani da tambaya?,me zan samu” dariya hanan ta saki
“Kinzo a sa’a kuwa,dazu saddiq ya tafi,ungo ci iya cinki” ta fada tana miqa mata wata leda daje saman drower dinta.

Related Articles

Hira suke sosai a haka mmn hunaifa ta dawo daga lacture ta taddasu
“Saura qiris na biyo sahu ko zancan hanan ne ya tabbata wani ya qwamushe mana ke” dariya sosai aysha tayi
“Harda ke mmn hunaifa?”
“Eh to ai gaskiya ne,budurwa mai kyau da aji kamar ke ai dole a samu ‘yan takara da yawa” ta fada itama cikin raha,sun jima zaune a nan suna hirar yaushe gamo,aysha nata yiwa mmn hunaifan qorafi kan baro hunaifa gida da tayi
“Yana iya,abbanta yace na barta itama kakartata tafison haka”
“Ai shikenan” aysha ta fada tana dan bata rai.

A hankali ya tura qofar falon sannan ya kunna qayayen wutar haske ya gauraye wajen,takawa ya dinga yi a nutse har ya isa cikin falon ya zube saman kujerar cike da gajiya.

Hakanan yake jin sashen duka ya masa wani iri,sai yaji ya masa girma,a hankali idanunsa suka kai kan takardunta da tayi amfani dasu jiya dake aje a wajen,sai yaji kamar shi daya yake rayuwa,idanunsa ya lumshe yana futar da iska akai akai daga bakinsa,dalili kenan daya sanya ya dade sosai hira wajen anni,a haka ya shafe wasu lokuta kafin ya miqe ya tarkata ya shige bedroom dinsa.

Sai daya gama komai ya haye gadonshi sannan ya rasa abinda yake damunsa,saiya juya daya side din idanunsa kan side din da take kwanciya ko yaushe,filonta da abun rufarta yana nan a wajen,hannu ya miqa ya janyo filon ya cusa kanshi a ciki,qamshin turarenta ya shaqa har cikin kanshi,qamshine mai sanyi da tsayawa a rai,sai ya mirgina ya koma side din nata,baisan me yake damunsa ba rashinta a dakin ya tsaya masa a rai,miqewa yayi ya zauna dirshan kan gadon,ya lalubo wayarshi ya kunna ya tafi nemo lambarta.

Dai dai lokacin da itama take kwance rub da ciki kan gadonta,dakin ya dauki shuru,mmn hunaifa tayi bacci,sai muryar hanan dake waya da take iya jiyowa kadan ladan,duk da bata jin me take fada,littafinta ne a gabanta tana haskawa da torch din wayarta son sun kashe wutar dakin tana duba amsoshin tambayoyin data amsa dazu.

Gida biyu hankalinta ke rabuwa,ko daya bata jin dadin kwanciyar bare karatun da takeyi,bata wuce sakan goma bai fado mata a rai ba,saita aje wayar da takardar hannunta ta qanqame filon da take kai tana sauke ajiyar zuciya.

Qarar wayar tata ce ta sanyata daga kai taga mai kiran,kamar tasan number,haka kawai gabanta ya fadi,ta kira sunan Allah sannan ta jawo wayar ta daga gami da karawa a kunne,sallama tayi cikin sanyin murya,boyayyar ajiyar zuciya ya saki sannan ya amsa mata ya dora da
“Idonki biyu?” Gyara kwanciyarta tayi zuwa rigingine tana sauke numfashi,muryarshi na ratsata
“Eh,baccin baixo ba”
“Saboda me?” Ya tambayeta kai tsaye
“Karatu nake”
“Uhmmm,ban yarda ba,wanne karatu ne har dare haka,kuma ma ai karatu bai hana barci ko?” Murmushi ta saki kadan,batasan wacce amsa zata bashi ba
“Ina anni?”
“Tana nan qalau,na barta zata kwanta”
“Nayi kewarta” ya sani cewa har cikin zuciyarta ta fada,yana alfahari da irin soyayyar dake tsakaninta da annin,ya sani cewa Allah ne ya masa baiwa da samunta,saidai yana ganin kamar a binda shi yake ji ko yake fata daga gareta babu shi
“Dazu ta gama zancanki….” Shuru ne ya ratsa tsakani kowa yayi shuru yana jin fitar numfashin dan uwanshi,shi ya kasa aje wayar kamar yadda itama ta kasa
“Anni kadai kikayi kewa?” Ya tambayeta da wani salo,’yar kunya taji,idan da kara kam baici tace anni kadai tayi kewa ba
“Harda su haidar…”
“Haidar?” Ya tambayeta yanayin muryarshi na sauyawa,take yaji kishin haidar sosai ya kamashi,itama sai data fada din sai taga kaman hakan baiyi tsari ba
“Harda kaima” tayi saurin fada,amma data duba kiran sai taga ya katse,duk sai taji babu dadi a ranta,ko babu komai akwai sadakinsa a kanta,shi ya soma tsamo ta ya kawota cikinsu,shi ya kamata ta fara nunawa damuwa da kulawa bayan anni.

“Ana soyewa ne,ban taba ganinki kina wayar dare ba sai yau,Allah yasa ta samu” inji hanan wadda ta sauko daga gadonta da niyyar shiga toilet saboda fitsarin daya matsota,murmushi ta mata duk da a duhu ne
“Ke kam Allah ya shiryeki hanan,jeki fitsarinki kawai”
“Aiko nayi zan dawo nabi qwawqwafi,ban yarda da wannan canzawar da naga kinyi ba,tun dazu naga kin saka waya a gaba kin kasa karatun arziqi,gwara naji labari tunda wuri na shirya qawata da kyau,don naga batasan komai game da soyayya ba” bilhaqqi hanan ke maganar,yayin data baiwa aysha dariya sosai,bata sake cewa komai ba ta wuce tana murmushi.

????????????????

Qarfe takwas da rabi na safe tana shiryawa don tafiya lacture tana duba wayarta,hakanan hankalinta ya karkata data kirashi,rabuwar jiya bata ji tayi mata ba sam,har ta gama shiryawa ta hada tea a cup zallarshi ta kurba donta dumama cikinta hankalinta bai bar kan wayar ba.

Sanda zata fita hanan tuni ta fice mmn hunaifa ce tayi saura tayi mata sallama ta fice,tana kan varender dinsu wadda zata kaita inda zata sauka daga saman ta ciro wayarta,saita samu kanta da rubuta masa saqon barka da safiya ta maida wayar tata jaka taci gaba da takawa,jefi jefi tana dan haduwa da wadanda ta sani tana tsayawa suna gaisawa,don zuwa yanzun itama ba laifi tana da mutane da abokan arizqi,da haka har ta qarasa theater din da zasuyi karatun ranar bata ji dawowar amsar saqon ba,basu bar aji ba sai uku na rana.

To hakama washegari kusan wuni sukayi,har a sannan tana zuba ido shuru ba amsa,sai ta soma tuhumar kanta kaman ta zaqe da yawa da saqon data tura mishi,a ranar ma sai wajen uku da rani ta koma daki,bandaki kawai ta wuce ta sake wanka saboda ranar da aka d’ana a ranar,doguwar rigar material mai hade da mayafinta ta zura,tana gyara kanta tana qorafi saboda yadda ya isheta da zafi,neman mai kitso kawai takeyi,’yar madaidaiciyar kwalliya tayi ta feshe jikinta sosai da turare,sosai material din yayi mata kyau saboda dacewa da yayi da kalar fatarta ya haskata qwarai,sallah la’asar ta tayar ganin lokaci ya cimmata,saboda tsabar gajiya ko yunwar ma tayi nata gu,gashi dama bata karya ba ta fita,hakanan ta dawo ta tadda dakin ba kowa da alama dukansu suma ba wadda ta dawo bare tasaka ran samun abinci,dole saita idar kafin tayi tunanin me zata dafa musu.

Hudu da rabi na yammacin motocinsa suka shigo cikin makarantar,kamar yadda suka saba duk inda motocin suka ratsa sai ido ya bisu hakance ta kasance ya riga daya saba da irin wannan har takai ma ga baikulawa zuwa yanzu,wani sakayau yake ji cikin zuciyarsa da wani nishadi kadan kadan yana ratsashi har suka samu gurin daya dace da tsaiwarsu duka suka faka,motar da yake ciki ce kadai ya bata umarnin ci gaba da tafiya har zuwa wajen da yake ganin zai iya tsaiwa,qasan wata bishiya data wadata da inuwa da iska mai sanyi.

Tana saman abun sallar bayan ta idar taji anyi knocking,izinin shigowa ta bada,daya daga cikin security nasu mata ne,suna mutunci da aysha hakanan tana ganin girman ayshan sosai wanda ita batasan dalili ba,bayan sun gaisa da ayshan take gaya mata tayi baqi,cikin mamaki take maimaita baqi kuma?,anya itace kodai hanan,murmushi tayi tace mata itace
“Gani nan” ta amsa tana miqewa gami da qissima su waye zasu zo nemanta?,mayafin doguwar rigar ta sake nadawa sosai a kanta,fuskarta da babu komai sai powder da man lebe ta fito tayi kyau,ta zira takalmi plate,zata dauki wayatta taga alewar da hanannta bata jiya da daddare saita dauketa ta jefa a bakinta waiko zata rage mata rashin dadin da bakinta ke mata saboda yunwa da takeji sannan ta fito,kafin ta sauka ta hadu da laila da zahra duka maqotansu ne suka gaisa sannan ta wuce.

Tun daga nesa rake duban motar cike fal da mamaki,tasan dai tabbas ire iren motocin khalipha kenan,saidai kuma me zaya dawo dashi bayan kwanaki biyu da dawo da ita da yayi,uwa uba ma tana zaton yau ko gobe shina zao wuce cyprus,a hankali yaci gaba da takawa tana duban motar,yayin da shi kuma dake zaune a cikin motar yake qare mata kallo ta cikin baqaqen gilasan da motar ke dashi ba tare data sani ba,tun daga sama har qasa yake kallonta yana jin wani yanayi yana ratsashi.

Qanqame hannunsa yayi waje guda,ya Allah,anya kuwa ba fara son yarinyar nan yayi ba,abinda yakeji a zuciyarsa game da ita bai taba jinsa akan wata diya mace ba,idan baso bane meye wannan?,tun shekaran jiya daya karanta saqonta da safe yaji ya kasa samun nutsuwa cikin zuciyarsa,kasa dauke idanunsa daga kanta yayi har ta qaraso dab da motar ta tsaya tana duban wani sashe daban,da alama neman baqin take.

A hankali ya sauke gilashin motar,qamshin turarensa da sanyin ac dake motar ya soma busowa zuwa waje,wanda hakam shi ya dauki hankalinta,qamshin turaren da take tunanin kamar ta sanshi,a hankali ta waiwayo zuwa sashen da take jin qamshin,idanunta suja sauka cikin nashi,faduwar gabar nan da’a koda yaushe takanji idan ta ganshi ita ta soma ziyartarta,sai kuma mamakin abinda ya kawoshi makarantar,duk ta watsar da wannan cikin sakanni ta sakar masa murmushi bisa shawarar zuciyarta,saita soma takowa a hankali zuwa bakin motar
“Sannu da zuwa” ta furta cikin nuna girmamawa,shima martanin murmushin ya maida mata yana mata nuni data zagayo cikin motar,ba musu ta zagaya daya bangaren ta shiga,saidai tabar murfin motar a bude,tuni drivern dama ya koma can wajen sa saura sukayi parking ya zauna a cikinsu.

Wani yanayi ne ya dinga ratsasu dukkansu tsahon mintuna ashirin kafin ya bude wani waje dage sit din gabanshi ya ciro laptop ya aje a tsakiyarsu
“Yau da daddare zamu tashi in sha Allah…..ga wannan kiyi amfani da ita a madadin waccar” sosai system din ta burgeta,da alama rahamalls sun iya kawo kaya masu kyau da inganci,don wannan tafi waccar tata kyau da tsada nesa ba kusa ba ko a ido ma
“Akwai abubuwa na akan waccan ina sonta na saba…..”
“Shshshsh…” Ya fada yana dora yatsanshi kan lebanshi idonsa cikin nata
“Waccan haidar ne ya siya miki bana buqatar kuma ki amfani da ita,ni khalipha nine a haqqu da komai naki,so da wannan nakeso ki amfani,duk wani naki mai.muhimmanci na cire daga kai an dawo miki dashi nan,karma ki sake maganarta don already na riga na bayar da ita” hannu ta sanya ta dauka,bai cancanci musu ba sam sannan tace
“Na gode,Allah ya saka da alkhairi ya qara budi”
“Ameen” ya amsa yana lumshe idanunsa
“Ban amince kuma naga hoton kowa ba akai” saita daga kai tana dubanshi,sam ta mace hoton haidar ne akan screen din waccar,to me kenan?
“Uhmm,zan wuce me zan samu?” Ya fada idanunsa cikin nata,
“Ba komai” ta fada tana murmushi
“Shikenan” ya fada yana daga kafada duk da bai daina kallonta ba,saita motsa kadan ta fidda qafafunta waje sannan tace
“Allah ya tsare hanya ya bada sa’a” sam kasa amsa mata yayi ba,bayason ta wuce,bayason ta tafi,hannunta ya riqo cikin xafin nama da hanzari ganin da gaske ficewar zatayi,sannan ya miqa hannunshi ya rufe murfin motar,fuskarta ya sanya a cikin tafin hannunshi ya hada tsinin hancinsa da nata,cikin sakanni kadan ya kashe mata jiki gaba daya,a hankali cikin muryar dako cikin motar kake baka isa kaji me yake cewa ba yace da ita
“Ba haka nake buqata ba,sallama nakeso irinta masoya,so nake naji ya suke ji duk lokacin da rabuwa tazo…..” Idanunta ta runtse gam,wani nauyi na sauka cikin zuciyarta da gangar jikinta ma gaba daya,gaba daya ya gama saukar mata da kasala,bugun qirjinta ya dadu wanda yasanya numfashinta shima sake gudu wajen fita,qamshin lemon dake fitowa daga bakinsa yana ratsa hancinta wanda ya gauraya da turarensa,tattausan lebanta dake gogar nashi ya sanyashi kama leban nata da haqoransa yadan ciza kadan ta yadd ba zata ji zafi ba.

Knocking din qofar da akayi shi ya sanyashi sakin fuskar tata da yayiwa ruqon tsauri,kowannensu ya janye a hankali,ta bangaren aysha ake knocing din saboda haka ta juya ta dannan madannin sauke glass,gilasan suka sauka qasa,hanan ce a tsaye rungume da litattafanta
“Ina can ina bulayin nemanki,keys din daki zaki bani ban fita da nawa ba mmn hunaifa na bari a dakin”
“Ohkey” ta fada cikin sanyi tana yunqurin lalubo maqullin da tuni ya subuce qasan kujerun motar,dagowa tayi ta miqa mata idanun hanan din na kanta,kana kallon fuskarta kasan dariya take hadiyewa,kallon na kamaki ba yadda zakuyi takewa ayshan itama ta fuskanci me take nufi,saboda haka saita waiwaya sashen da khalipha ke zaune cikin sanyi tace
“Meet hanan,my roommate” cikin fara’a hanan din ta gaida khaliphan,shima a sake ya amsa mata yana tambayarta karatu tace komai lafiya
“Ranka ya dade aikinka na kyau fa,saidai a dan sassauta mata karta gagara hada masters din tata” da sauri ayshan ta kalli hanan dake dariya,maganar tata saita baiwa khalipha dariya,can cikin ranshi kuma yana mamaki kan lafazin hanan din,idanu ya kafe aysha dashi
“Wai haka humairaaah?”kunya ta mata dabaibayi sosai,tana kada kai kamar zatayi kuka tace
“Tsokana ce kawai takeyi,batasan waye kai a wajena bane” dariya sukayi hanan din da khalipha,sannan tayi sallama dasu ta wuce
“Waye ni a wajenki?” Ya jefo mata tambayar data rasa amsar daya dace ta bashi
“Matsayin daka dade da baiwa kanka”
“A yanzun idan na sauya matsayin zuwa mataki na gaba yayi dai dai?” Shuru tayi tana nazarin maganarsa,kalma ce mai harshen damo dake da buqatar nazari,hannunta taji ya kama ya sumbata na tsahon sakan goma sannan ya sake mata hannu
“Zan wuce,ki kula da kanki” sai a sannan itama taji wani iri babu dadi,addu’a tayi masa sosai sannan ta zira qafarta ta fito daga motar,harta rufe idanunsu nakan nakan na juna duk da kunyar abinda ya mata dazu dake addabarta
“Baki bani komai ba da zan dinga tunawa dashi” sadda kanta tayi tana murmushi qasan ranta,tome yakeso ta bashi?” Bata gama wannan tunanin ba ta jiyo muryarshi mai taushi
“Allah ya bamu alkhairi,saina dawo”
“Ameen” ta furta,saita kasa tafiya taci gaba da tsaiwa a wajen har ya ryfe gilasan motar ta daga tabar wajen,shi dinma ta cikin mirrow yaci gaba da kallonta har suka bacewa ganin juna.

[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha: *_Mutane masu son zuciya ma sunada rana a gareka, koba komai zasu tara maka ladansu ka kar?a a ranar da kowa ke fafutukar neman ?ari a littafin ayyukansa. Dan haka karkai ba?in ciki da zaluncin azzalumi, koda ?atanci yay maka bisa son zuciya ribace a gareka, shi ko bai gane fa?uwace a garesa sai randa babu wata ?ofa ko damar da zai ro?i gafarar ka._*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button