Hausa NovelsTayi Min Kankanta Hausa Novel

Tayi Min kankanta 20

Sponsored Links

20*

 

Wasa-wasa tsawon sati guda kenan,likitoci na tsaye kan hammad amma ko alamun farkowa bashi da ita,
Hankalin iyayensa dana zahra yayi matuƙar tashi,ko kaɗan basu cikim natsuwa.

Related Articles

Duk yadda mummy tayi da zahra kam ta koma gida ƙi tayi,ko wanka bata zuwa gidan tayo sede tayi a asibitin akawo mata kaya ta sauya.

Koda su daddy suka tambayeta me ya haddasa masa ciwon,ce musu tayi faɗa sukayi da abokinsa jameel,sosai su daddy sukayi mamakin afkuwar hakan a tsakaninsu,

Daddy jameel ya nema a waya,dan jin abinda ya haɗasu,cikin girmamawa jameel yace”daddy wannan saɓanine yashigo da rashin fahimta,da taimakon shaiɗan,kar ku sa kanku aciki mu mukayi faɗanmu kuma da kanmu zamu shirya”ya faɗi cikin girmamawa.

“to amma jameel ga fa shi abokin naka a asibiti rai a hannun Allah,tun ranar da kukayi faɗan yake a sume a asibiti,baka ganin akwai buƙatar mu shigo ciki dan ɗinke ɓatakar da ta shigo tsakaninku?”

“Daddy bansan bashi da lafiya ba,amma zanzo in dubashi bana garine nima tun ranar ina lagos,”jameel ya faɗi cike da tausayawa abokin nasa,tabbas yasan hammad farin sani,masoyinshi ne na haƙiƙa,dole ze shiga wani hali aduk ranar daya gano gaskiya,duk yadda yaso yayi fushi da hammad ɗin baze iya ba.sabida shima yana matuƙar ƙaunarsa,kuma ko shine hakan ta faru abinda zeyi kenan.

A cikin sati na biyu ne hammad ya farka gaba ɗaya ya rame yayi baƙi ya fice hayyacinshi.yazama abun tausayi.

A hankali ya kai dubansa gefen da zahra take tsaye tana share hawaye,a hankali ya miƙa mata hannu alamun tazo gunshi,ba musu ta taka a hankali ta isa gareshi.

Janyota yayi batare daya ji kunyar su mummy ba ya haɗeta da ƙirjinshi ya rungumeta yana hawaye.

Su mummy ficewa sukayi daga ɗakin,sabida ya basu kunya.ɗago kanta tayi a ƙirjinshi tana share masa hawayen tace cikin shagwaɓa”yaya kayi haƙuri karkayi fushi damu,don Allah ka samu lafiya banason ganinka baka da lfy”ta ƙarasa maganar cikin kuka.

Ƙara rungumeta yayi ajikinshi yana ci gaba da zubar da hawayen,ya kasa magana.tsawo mintuna talatin ya kwashe rungume da ita,turo ƙofar da akayine da sallama yasa yakai dubansa gun me shigowar,

jameel ne.

Wata matsananciyar kunya ce ta kama hammad,maida kansa yayi ya kwanta,sannan ya lumshe idonsa ya juya baya.

Sosai jameel ya karanci aminin nasa,yasan kunyarshi ce tasa yayi hakan dan haka ajiye kayan hannunsa yayi sannan ya ƙarasa gunshi.

Cakumo rigarsa yayi yace”ɗan iska mara mutunci,har da wani dukana rannan,to wlh baka daki banza ba zuwa nayi in rama”yana kaiwa nan shima ya shiga kirɓarsa,ta yadda yasan baze cutar dashi ba.

A galabaice Hammad ya buɗe idonsa,ya haɗa hannayensa gida biyu hawaye na bin idonsa,alamun tuba ga jameel ɗin.

Shima jameel ɗin hawaye yakeyi,da zafin nama ya janyo hammad ɗin jikinshi ya rungumeshi,shima rungumeshi yayi dukansu hawaye sukeyi.

Muje zuwa

Surbajo for life.
[1/6, 10:15 AM] Zahra Surbajo: 🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀 *TAYI MIN ƘANƘANTA*
🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button