Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 11-12

Sponsored Links

Free Page 11-12*

★★★~~~★★★~~~★★★

 

Related Articles

Ankai ruwa rana kafin su fita daga Hayin Fulanin Saida aka shigar da jami’an tsaro sannan suka samu suka fita da Habeeb daga garin da sharraɗin Habeebah zata zauna a gdan Liman zuwa wasu kwanaki kafin mijinta ya dawo ya ɗauketa.
Inda su Jimo sukaci alwashin muddin suna raye wannan aure bazashi ko inaba shidai Habeeb bai bawa mgnrsu muhimmanci ba yaja ƙafafunsa suka bar ƙauyen cike da kewa shauƙi da ƙaunar matarsa.
Itako Habeebah lkcn da taji hukuncin da aka yanke da kuma furucin da mahaifinta yayi akan aurenta sai duka jikinta yayi sanyi bataso aurenta ya kasance a haka ba bataso ace ta samu matsala da iyayenta ta dalilin aurenta ba Shikenan sun sallamata babu su babu ita saboda Habeeb?”
Hawaye ne ya sulalo mata ta zauna a shimfiɗar da Hajjo matar Liman tayi mata ta zuba uban tagumi hawaye wani nabin wani zuciyarta tayi ƙunci duniyarta tayi duhu.
Tunda ta taso takejin iyaye mata suna cewa duk matar data ɗauki namiji uba saita mutu marainiya! Yanzu ita meye ribar da zata samu data amince tayi baram baram da iyayenta akansa? Waye shi??Meye yake ma nufi da aurenta??? Meye yasa ya tsallake matan dake birni yace sai ita?.

 

Tambayoyi barkatai marasa amsa tunanin Jumme ya faɗo mata ta kuwa rushe da kuka me gigita tunani da taɓa zuciya yanzu Shikenan bazata sake ganin Jumme ba? Ta rabu da mahaifiyarta me ƙaunarta da ƙaunar farin cikinta har abada?
Kuka takeyi sosai me taɓa zuciya, a haka Hajjo ta ishe ta ta tafa hannu tana salati tace “Haba yarinya Meye kuma abin kukan ai gdy ya kamata kiyiwa Allah daya baki mijinki me sonki da tausayinki gashi Allah ya ɗaga darajar ki zaki tafi birni”
Ɗagowa tayi ta dubi Hajjo fuskarta taf da hawaye tace “Waye Allah?” Da sauri Hajjo ta kalleta da mamaki tace “Allan ne baki sani ba ƴar nan tab to wannan wanne irin aure ne shi mijinki naga ai musulmi ne….”
Har yanzu idanunta nakan Hajjo ta kuma cewa “shima kina nufin yasan Allah?” Jinjina mata kai tayi tace “tabbas yasan Allah domin kuwa alama ta nuna bayan sanin Allah har tsoron azabarsa yanaji Habeebah kinason sanin Allah?” Saurin ɗaga mata kai tayi tayi murmushinta ta dafa kanta tace “Zakisan Allah harma ki bauta masa yanzu Meye abin da kike bautawa?” Sunkuyar da kanta tayi tace “Uwa me tsarki ita nake bautawa kuma ita ce abar dogaro na itace take bani nasara akan komai nawa sannan yanzu itace tayi fushi dani harma tasa iyayena sukayi fushi dani yanzu Shikenan rayuwata bazatayi albarka ba…..”

 

Murmushin tausayinta Hajjo tayi ta mike ta zari buta tace “bari naje nayi sallar magaruba sai mu zauna” nan ta zauna tana kallon yanda Hajjo take sallarta kamar yanda ta taba ganin ɗan birni yanayi, bayan Hajjo ta idar ta sako musu tuwo da man shanu suna ci Hajjo na bata labaru masu ban dariya sai gashi ta saki jiki tana ta dariyarta da haka Liman ya shigo ya taddasu yaji daɗin yanda ya samu Habeebah tanata dariyarta abin ya matukar faranta masa rai ya mika mata wayar hannunsa yace.
“Mijinki ne yakeson mgn dake” ƙasa tayi da kanta cike da kunya Hajjo ta karɓi wayar tace “kekam da a cikinmu akayiki bansan irin halin da zakiyi ba kawai daga mijinki na kira sai kiyi ƙasa dakai to ko yaranmu ai sun daina wannan kunyar”
Tana mgnr tana kara mata wayar a kunnenta tayi shiru tana jinsa yanata mgn taki cewa komai har ya kashe ya sake kira Hajjo ta tashi ta nufi garken shanu hakan ya bata damar cewa “Ɗan birni….” Ajiyar zuciya yayi yace “har yaushe zaki daina cemin ɗan birni kike kirana da sunana Beebah?” Ajiyar zuciya tayi tace “kaje gdane?” Gyara kwanciya yayi yace “ina kwance a gadona inajin dama kina kusa dani da kin ragemin kewa ko tausa kyayi min….”

 

Wani gwauron numfashi ta sauke daya sanyashi tambayarta “Meye” a kunyace tace “Kunya kabani ai babu kyau sashi ya rinƙa taɓa sashi” dariya sosai mgnrta ta sanyashi yace “Har yanzu?” Ɗaga kai tayi tace “Eh” murmushi yayi yace “idan nazo ɗaukanki nan da sati biyu zaki maimaita min am kinsan me?”
Girgiza masa kai tayi tace “Aa” yaja fasali yace “Hajiyata tana gaisheki na sanar da ita komai daya faru ta sanyawa aurenmu albarka sosai tayi mana fatan alkhairi” dariya tayi tace “Hajiyanka mahaifiyarka kenan?” Jinjina kai yayi yace “Eh tayi murna da samuwarki cikin alhinta Habeebah mahaifina Sarki ne a garinmu Sarki Khalil na ƙasar Dutse shine ya haifeni mahaifiyata kuwa Hajiya Kilishi wato Ummusalma haifaffiyar Masarautar Daura ce mu bakwai mahaifiyarmu ta haifa maza biyar mata biyu nine ƙarami a maza a dakinmu sai mata biyu da suke ƙanne a gurina matan mahaifina uku Hajiya Zulai wato Hajiyan soro tanada ya’ya Hudu uku mata ɗaya namiji Nasir kenan sa’anni muke dashi sai Hajiya Hauwa Hajiyan ƙofa yaranta biyu dukka maza Fahat da Salim gidanmu bamuda matsalar ƴan ubanci duk da dai ba’a rasa shi ko yaya ne tunda ya shiga gidan Annabi ma bare mu bayin Allah, abu ɗaya ne matsalar family ɗina munada ƙabilanci duk wata mace da yayyuna suka aura to ta fito ne daga tsatsonmu haka matan ma ba’a kaisu ga waje a cikin dangi akan auraddasu kasancewar mahaifinmu da ƴan uwansa sunada yawa sannan suna ƙyamar talauci wannan yasa musu gudun bare saboda sunce daga bare za’a samu musu musakai a gwamutsa musu zuri’a da datti”
Numfashi yaja ya sauke yaci gaba da cewa “Habeebah nasan zaki fuskanci ƙalubale zama da zuri’armu domin kece kika fara shigowa wannan zuri’a tamu matsayin mata kuma kika zo a wani yanayi da mai ƙaramar ƙwaƙwalwa bazai mawa rayuwa uzuri ba”

 

Numfashi ta sauke hawaye ya zubo mata tabbas wannan shine an gudu ba’a tsira ba anyi gudun wuya an haikewa wuya har ta fara kukan tausayin kanta na kasancewa matar Habeeb tun yanzu wannan wanne irin dangi ne da basa ƙaunar bare?
Muryarsa ce ta katseta da cewa “kiyi hƙr da yanayin da zamu ɗan samu kanmu nasan zamu fita babu wani yanayi da yake dawwama Beebah da wasa nake Miki bazan iya barinki kiyi dogon Zama a garin nan ba zuciyata bazata nutsu ba gobe xansa Azo a tafi dake” zaro ido tayi tace “gobe?” Murmushi yayi yace “ko baki shirya ba?” Sunkuyar dakai tayi tace “Amm….” “Shetttt” yace mata sannan yace “amma me? Banson jayayya karki fara kinji?” “to” ta amsa da ita sannan yaci gaba da janta da hira tana ƴar dariyarta har zuwa wani lokaci sukayi sallama Hajjo ta nuna mata makwanci ta kwanta bacci ya ɗauke ta cike da mafarkan Ɗan birni.
Washegari da wuri batama tashi daga kwanciyar safe ba Liman yazo yace tazo tanada baƙi taja ajiyar zuciya ta miƙe ta ɗauki hijjab ɗin da Hajjo ta bata jiya tasa ta fito tun daga nesa ya kafeta da manyan idanunsa tayi masa kyau da shigar Muslim women sai yaji ta ƙara shiga ransa ta ƙarasa gabansa kanta a ƙasa ta tsugunna tace “barka da hanya” numfasawa yayi ya sanya hannu ya ɗagota ya sanya hannu ya lakaci hancinta yace “Sannu matar Prince Habeeb kina lfy?” Sake sunne kanta tayi tana ajiyar zuciya yajata ya shigar da ita motar yaja suka bar gurin a guje.

 

Yanda ta ɗago da alamun firgici yasashi kallonta yayi mata murmushi yace “zaki koma rayuwa a inda aka halicce ki don gurin” nandanan jikinta yayi sanyi ta mayar da idanunta ta lumshe tare da kwantar da kanta a kujerar wani zazzafan hawaye ya zubo mata yabita da kallo hakanan yaji ta bashi tausayi.
Sun jima suna tafiya tana rera kukanta batare daya ce mata ƙala ba bawai don kukan baya damunsa ba sai don bashi da kalmar dazai iya rarrashinta da ita, dole tayi kuka rabuwa da dangi ƙawaye da garinka rabuwa ta har abada batare daka shirya ba dole ne ya taɓa zuciya da gangar jiki.
Bai nufi gdansu da ita ba wani Unguwa ya nufa yayi parking ya fito ya buɗe get na gdan ya shiga da motarsa yayi parking sannan ya kamo hannunta yaja fasali yace.
“Kiyi hƙr Beebah nasan kinajin ciwon rabuwa da makusantanki ne wlh ban rabaki da danginki don cutarwa ko zalumci a gareki ba sai don hakan shine yayi daidai da tsarin rayuwarki,
Dukkan wata mace a duniya a ƙarƙashin haka take ko yanzu ko gobe ko jibi sai kinbar gdanku kin tafi gidan aure so ki kwantar da hankalinki insha Allahu nayi alƙawarin baki kulawa saikin zama abar alfahari ga danginki baki ɗaya”

 

Hannunsa yasa ya share mata hawayen yace “kukan ya isa haka muje na baki ruwa kiyi wanka ki canza kaya ki bani lbrn kuruciyarki”
Fitar da ita yayi a motar suka nufi ƙofa ya buɗe suka shiga ta tsaya tana ƙarewa falon kallo sake da baki da kuma bayyanannan tsoro ta dubeshi yayi murmushi ya sake riƙe hannunta yakai bakinsa ya sumbata ya ɗago idanunsa da suke lumshewa kamar me jin bacci ya zubasu akan fuskarta yana ayyana abubuwa da yawa a ransa saidai shi kansa baya ƙarfafawa zuciyarsa gwiwa wajen aiwatar da abinda take muradi.
Zubewa yayi a kujera kallon Beebah na saukar masa da wata kasala me narka lakar jiki ya miƙa mata hannu da nufin tazo gareshi ta noƙe cike da tsoro yayi wata miƙa ya miƙe yace “ok muje bamuda lkc” batayi masa musu ba suka nufi wata ƙofa ta buɗe ɗakine harda gado kato na alfarma ta kuwa lalace a kallon gadon bataji sanda ya zare mata hijjab dinta ba saijin hannunsa tayi a ƙirjinta ya sanyata cikin jikinsa ya rungumeta da wani salo me narkar da cikakkiyar mace, itakam Beebah yanda taji yana sama da hannunsa saman ƙirjinta yasa ƙirjin nata dukan uku² tayi saurin juya masa baya ya kasance ƙirjin nata ya koma ƙirjinsa hakan ma daɗi yayi masa yasa hannu ya tallafi mazaunanta.
Nan take jikinta ya ƙara ɗaukar rawa ta janye da sauri zatayi mgn yasa hannunsa kan bakinta ya lumshe idanunsa da suka kada sukayi jawur yace “Mijinki ne ni Beebah akwai bambanci da irin mazan da kike tsoro muje na nuna Miki yanda zakiyi wanka bamuda lkc na faɗawa Hajiya na daukoki idan munje don Allah kada ki bani kunya duk abinda kikaji na faɗa a matan gda da Mai martaba ki gasƙata hakan kinji?”

 

 

Ɗagansa kai tayi ya jata suka shiga bathroom ɗin dake batada duhun kai batasha wahalar gane komai ba ya fita ya barta tayi wankanta dama jiya da dare Hajjo ta tsefe mata gashinta tasa klin ta wankeshi tas gashinta yanada muguwar cika ga tsayi ta sharceshi da matajin data gani a gurin ta sake shi ta fito sanye da hijjab ɗinta yana kwance a gado ya rungume hannunsa a ƙirjinsa ya lula sama jannati yaji ta shafa fuskarsa ya sauke ajiyar zuciya me ƙarfi ya sauke idanunsa akanta tayi masa murmushi tace “Tunanin me kakeyi?” Tashi yayi zaune ya kuranta ido har Saida ta tsargu sannan ya janyo ta ta zauna kusa dashi karon farko data fara zama a abu me laushi dangin katifa ya tallafi fuskarta yace “A matsayin ƴar aiki zan kaiki gdanmu….”
Wani kallo tayi masa na sosai tace “Ƴar aiki baiwa fah kenan?” Numfashi ya sauke yace “Hakane zaki tsaya iya bangaren mahaifiyata Hajiyata tasan matsayinki a gurina Habeebah bawai don kaskanci ba a’a saidon kareki daga duk wani abu da ka iya faɗowa bayan bananan zan kaiki matsayin ƴar aikina karki damu shekara ɗaya kawai zanyi na dawo kasar nan gabaɗaya nayi ƙoƙarin tafiya dake na hasaso asirina zai tonu domin babu wanda yasan da aurena dake sai Hajiyata nabarki gurinta amana kuma zanyiwa Khalisa da Hudah kashedi akanki bazaki samu matsala da kowa ba kiyi hƙr kinji…..”

 

*share please*
[4/16, 7:49 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2–iGyJfTwItSzAnGg

*Paid book*
Kunata cewa promo ɗin dana baku yayi kaɗan to gashi nan na ƙara daganan zuwa jibi zaku sameshi a 200 PC 500
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241 ƴan Niger kuma zaku tuntuɓi wannan number don biyan kuɗinku +227 95 04 58 22.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button