Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 20

Sponsored Links

20

 

 

Cikin satittikan da suka biyo baya duka mummy shirin biki take haiqan,ba qaramin buri ta ciwa bikin ba,bama ita kadai ba har sauran yayyen asma’un,karma su aunty halima suji labari,gwara ma aunty safiyya ita da yake ba shiri tsakaninta da amaryar sosai,babu wanda yake ta aysha…babu wanda ya damu da lamarinta,anty safiyya ce kawai mai tsomota cikin lamarin.

Da yammacin wata ranar laraba anty safiyya tazo gidan,suna zaune a parlour ita da mummy da asma’un,mummyn na cinikin wasu magungunan mata da asma’un tace tana so,ta kira matar takanas kuwa har gida ta kawo mata,saboda tasan cewa zata maida uwar kudinta cas harma da riba,mummy na dauka asma’u na duddubawa tana zaba da kanta,anty safiyyan na gefe tana kallon ikon Allah,tun tana shuru har ta gaza yin shirun kasancewarta mai zafi da rashin son raini da wargi,kai tsaye ta yiwa asma’un magana saboda tasan idan ta mummy ne ma aikin banza ne a wajenta
“Wai asma’u meye haka?,wannan wacce iriyar muguwar dabi’a ce?”kai ta daga tana kwabe fuska saboda tasan halin anty safiyyan tsaf
” yanzu kuma meye nayi?,tunda kika zo gidan nan na kasa qwaqqwaran motsi na sake saboda nasan ki da dan banzan chellang din mutane da cin gyaransu”
“Akan gaskiya ba….ke ko kunya bakiji ki zauna kina zabawa kanki magungunan mata gaban babarki?” Matar ce ta saki dariya tana cewa
“Yo hajiya meye?,ai yanzu haka akeyi,idan ba’a mata a gidansu ba waye zaiyi mata?,’yammatan yanzu ma kansu ya waye,idan ba’a miki ba ni da kansu suke zuwa su siya abinsu kafin bikin suyi amfani da shi…meye a ciki ai gwara su gyaggyara ko” dauke kai safiyya tayi daga bangaren matar,donta fuskanci ita kudinta takewa campaign da kayanta,ba ruwanta da batun kunya ko al’ada ta dubi mummy
“Mummy….ko magani za’a bawa asma’u ba irin wannan take buqata ba,maganin sanyi da basir ya kamata ace an soma nema mata,baya ga haka ma akwai abubuwa da yawa daya kamata ace su aka fara dora ta akai bawai magani zalla ba da sauran qyale qyale,akwai abubuwa data rasa,mummy ina mai tabbatar miki babu abinda asma’u ta iya dafawa,hana rantsuwa indomie,komai a gidan nan yiwa asma’u ake bata san ta yiwa kanta komai ba,a haka zata zauna gidanta duka ba’a kula da wannan ba,wannan gata ne mummy?,duk macen data shiga gidan miji a haka ko hurul’een ce ita ba zata taba daraja ba” bacin rai qarara ya fito a fuskar asma’u,badan badan ba da tace anty safiyya na cikin ‘yan baqincikinta,don dai kawai ciki daya suka fito,ta jima rabon da aci mata fuska irin haka,badan tasan bata daukar wargi ba ba abinda zai hanata gaggaya mata magana kota sheqa mata ma zagi
“Banda abinki safiyya duka mai ya kawo wannan maganar kuma,zancan koyon aiki kema kinsan inda zata je ai,bata da matsalar girki da sauran gyaran gida tana da masu yi mata”
“Barta kawai mummy,don ke baki da mai aiki kinqi daukar kowa kin hadawa kanki wahalar aikin gida kowa haka zai zauna kamar wani dan wahala?,already mun gama magana ni da hamid ina da masu yimin komai baya buqatar na wahal da kaina wajen dauke koda tsinke ne” asma’un ta fada cikin bacin rai tana ci gaba da duba kwalin magungunan abinta
“Idan kana da kyau asma’u ka qara da wanka,ni yar uwarki ce dole na gaya miki gaskiya koda kowa ya kasa gaya miki saboda tsoron ko shakkar rashin kunyarki,duk arziqin mijinki akwai wani abu da yake buqata matarsa ta iya tayi masa ita da kanta,ba burgewa bace kana jibge kaman kayan gwanjo wata ke miki aikin gidanki,duk ladarki kin tattara kin bar mata,bautar ubangijin da akace zakiyi cikin aure ke baki ma santa ba kenan,saidai kici ki sha kiyi wanka”
“Au dama bauta aka ce miki no zanje nayi?,tabdijan su bauta manya,ni gidan ‘yanci zan shiga gidan soyayya”ta fada tana tabe bako,don ta soma kaiwa bango,gab take da yiwa mata rashin kunya,bata son ayi fito na fito da ita kwata kwata kan nata ra’ayin,tafiso a qyaleta tayi yadda takeso ta kuma tsara
“Rayuwarki ce kiyi duk yadda kike ganin ya dace,amma karki kuskura kimin rashin kunya,kin sanni bani da dadi wallahi” ta fada cikin fushi qarara bayyane a muryarta
“To ya isa haka don Allah,ni bana son wannan rigingumun naku” mummy ta fada tana turawa matar kayanta,tattarewa tayi ta soma maidawa cikin jakarta suna lissafi da mummy,tashi safiyya tayi ta wuce kitchen saboda bacin rai da takaici,kome asma’u zatayi batasan me yasa mummy bata iya tsawatar mata ba,ita a ganinta sam wannan ba soyayya bace,duk duniya kowacce uwa na son danta,amma duk sanda kikayi sakacin da baki iya tsawatar masa a sanda ya aikata ba dai dai ba to la shalla zakiyi kuka gaba da hawayenki,bahaushe yace ka saka danka kuka kafin shi ya saka ka,hakanan kaza tana sane take take danta badon bata sonshi ba,a’a sai don ta koya masa darasin rayuwa.

Sanda ta fito daga kitchen din matar ta wuce,hakanan asma’un bata falon,zama tayi kusa da mummyn dake latse latsen waya
“Mummy…don girman Allah ki daina biyewa asma’u a duk lamuran da tace tana so,mummy wannan fa ba gata bane,gidan wani zata je fa,yadda kika saba mata haka zata ce zata yi musu,bayan ita rayuwa ba tabbas gareta ba”
“Kai safiyya kai…wallahi kin cika qorafi…magana ta riga ai data wuce ko,maganin duka qwaya biyu na daukar mata sai kuma meye yayi saura?,nifa kinsan bani son takura kwata kwata” kai ta jinjina
“Shikenan mummy…kiyi haquri” daga haka ta soko maganar data kawota gidan,kan wani abun adon daki da za’a yiwa asma’un,saidai yadda taga mummyn na lissafin na mutum daya ne
“Mummy aysha fa…nayi zaton duka daddy ya bayar?”
“Eh…ina da uzuri da nata kudin ne,idan na samu wasu kudin ko kafin biki ne ayi mata tunda kamfani ne ba za’a rasu su available ba koda yaushe” shuru kawai safiyyan tayi,tunda ta fadi haka kawai ta sani banda ita,batasan me yasa mummy take irin haka ba,aysha ta cancanci a siya mata ma ahana asma’u,don yadda mummy ke morar aysha mo asma’un bata mata rabin wannan morar ko kusa ko alama.
(To gareku mata masu riqon yaran wasu,walau marayu dan kishiya ko masu iyaye…mu sani rayuwa bata da tabbas,baki da tabbacin kema zaki rayu da naki,idan kin rayu da naki jikonki fa?,duk abinda ka yiwa yaro na cutarwa yana sane abun yana kanshi,komai dadewar shekatu wallahi Allah yana sane da abinda kayi masa,wani ma a sanda zai tuna miki tsufa ya cimmaki ko qarfinki ya qare kema kina qarqashinsa ko qarqashinta,a sannan shi kuma Allah ne kadai yasan arziqin da yayi masa,a lokacin da zai tuna mikin Allah ne kadai yasan kunyar da zaki sha idan ma kina raye kenan,idan ma bai yada maganar a sanda kike qarqashin qasa ba,wallahi duk wanda ka zalunta duk qanqantar zaluncin Allah bazai taba yafe maka ba sai ya fiddawa kowa haqqinsa,da kike fifita yaranki a kanshi shima haihuwarsa akayi iyayensa na sonahi,qila da suna tare da shi gatan da zasu nuna masa yafi wanda ke kike nunawa naki yaran,hakanan yaranki na kallon me mike kina koya musu aqidar banza ne idan Allah ya basu aron rai suma akai zasu dora,shi sharri dan aikene maishi yake dawowa,hakanan alkhairi danqo ne baya faduwa qasa banza,Allah yasa mu dace,yasa mufi qarfin zukatanmu)

A tsakanin wannan lokacin mummy suka tafi dubai ita da asma’u da anty halima,batasan me da me suka tsarawa daddy ba,saidai baiyi fada kan tafiyar da sukayi babu ita ba,itama sabgarta kawai take,a yanzu gaba daya addu’o’inta sun karkata ne kan Allah ya sanya auren ya zama alkhairi a gareta duniyarta da lahirarta,bata jin motsin wani daga cikin ‘yan uwanta bare yace wani abu kan aurenta ko zata ji dadi,tasha tasa wayarta a gaba tana kallon lambar umminta,ta sha kwatanta kiranta,tasha qissimawa a ranta inama ta wayi gari watan wata rana ta tsinci koda miscal ne akan fuskar wayarta,zata so Allah ya gwada mata wannan mafarkin nata koda sau daya ne tak a rayuwarta kafin tayi qaura wa duniya,abun mamaki da lantana mai aiki suka tafi,tana jin mummyn na cewa
“Gwara muje da itan,saboda daukar kaya da sauran ‘yan wahalhalu” bata sani ba kota fadi hakanne saboda kar ayshan ta zargeta,itadai ko oho bata masa inda zancan nata ya dosa ba,don bata iya riqe magana ba a rai,ita kadai suka barwa gidan sai mai gadi,a lokacin daddy shima yayi tafiya,tana tsoron gidan sosai amma haka ta zauna babu yadda ta iya,idan tayi addu’a ta koma dakinta bata sake fitowa sai safiya,

Ba qaramar siyayya suka yo ba,har jikokinta sai data yi musu tasu tsarabar,kayan fitar biki nata dana asma’u,hakanan ta jido kayan business dinta,saidai babu ko tsinke da Allah yasa aysha taga gilmawarsa da sunan nata ne,kaya masu yawa haka aka jibgewa asma’u a store din gidan,a haka ma da wasu suna nan qarasowa.

Kwana biyu da dawowarsu taji mummyn na waya da wani mutum dake amsar kayanta a kantin kwari kan tana son kaya,da daddare sai gashi ya kawo din kuwa,a sannan yasha tana daki tana gyaran kumbarta lantana ta shigo ta kirata,kaman ko yaushe ta saka hijabinta ta fita
“Aisha ga kaya nan saiki zabi kalar wanda kikeso,daddynku ne yace a siya muku na fitar biki” kai ta tada ta dubi kayan
“Duk wanda kika dauka min yayi”
“A’ah A’ah ni babu ruwana kinsan halin daddynku,tare da asma’u muka je ta zabi wanda takeso to saboda kayan kar suyi yawa suja kilo shi yasa ba’a sai naki ba,dalili kenan daya sa nace nuraini ya kawo miki daga shagonsu kema ki zaba da kanki,tunda suma kayan su masu kyau ne”
“Mtsweew….mummy sai dana ce miki ba sai kin kirata ba,ina laifi ba ma da za’a siya mata,kawai ki zaba ki aika dasu wajen dinki ta bada size dinta,amma ai bama girma bane ki tsaya kuna wani maida magana ke da ita”
“Shikenan zabar mata,’yar uwarki zata zabar miki”
“Na gode” ta fada kawai tana miqewa tabar wajen,asma’un ita ta zaba mata atamfa da laces,kusan kayan ma mummyn ce ta sarosu kudin ya sake dawowa inda ya fita kenan,dinki ne kawai mummyn ta kai inda ake mata bayan ta dauki hotunan kayan ta turawa daddy da sunan kayan da aka siyowa asma’u ne da aysha.

Satin da suka dawo kwana hudu tsakani aka soma shirin amsar lefen asma’un,ko ba’a fada ba mai karatu yasan waye a gaba idan ba hanci ba,tun ana sauran kwana biyu a kawo lefen aka hana ayshan tsugunnawa,tamkar wasu jinin hurul ini ne zasu zo haka ake tsara komai,a randa zasu zo din kuwa kayan masu kawo lefe kawai da aka hada abun a tsaya a kalla ne,komai cikin girma harma da nuna fariya a lamarin haka aka jibge musu kaya ana jiran isowarsu.

Tabbas hamid yayi lefe irin wanda ya dace da tsarin asma’u,akwati talatin ne cif,goma pink,goma purple,goma brown,kowanne danqare yake da sutura ta alfarma,sai kayan sakun lalle,kama ga buhunhunan shinkafa,suger gero da sauran kaya,’yan uwan asma’u kaman su taka rawa banda anty safiyya data kama kanta tun sanda taga yadda ‘yan uwan hamid ke bubbuda hanci suna kallon ko ina da kowa d’ai d’ai,don ko zama ma basuyi ba atsaye akayi komai,tukuicin kuwa da aka basu cewa sukayi sun gode basu amsa ba,wanda kana ganin yadda sukayi din sun raina ne,saidai da anty safiyyan ta fada asma’un rigima ta saka tace dama can bata qaunarta ita da hamid shine yanzu zata yiwa ‘yan uwanshi sharri,ita ta rasa me yasa tana ‘yar uwarta bata qaunarta,ta lura da da hali canzata zatayi da ayshan don ta lura tafi sonta da ita,sai abun yaso ya koma kaman ashan ce tayi da yake tafi rainata akan kowa,shuru kawai tayi musu daga qarshe saboda yadda taga sun dauki zancan tsakanin asma’un dasu anty halima,babu ma wanda ya kula da abinda ita tace ta hango din,duk idanunsu ba wannan yake kalla ba,abinda kawai suka dubawa dukiyar da aka jibgowa asma’un.

A sannan aysha na falon ta zuba ma anty halima da anty kubra abinci ta aje musu,saboda basu tafi ba har isha’i suna falon suna hirar yawan kayan da kyansu tare da yi musu d’ai d’ai suna sake kalla,tana shirin juyawa anty kubra tace
“Ke yaushe ne kawo naki lefen?naji har yau baki ce komai ba” Kanta a qasa tana murza tafin hannunta tace
“Idan zai kawo din zai fada…..dama ya riga daya gayamin zaiyi bakin qoqarinsa ne idan sun samu,saboda ranar bikin da aka sama tayi mishi gajartar da zai iya shiryawa a tsukin” wani mugun tsaki anty halima ta saki sanda take kai lomar abincin bakinta
“Kema kubra da neman magana kike wallahi…..har wani lefe kike jira a kawo mata….saikiyita jira ai….ke tashi ki bamu waje” ta fada tana hade rai gami da kafeta da ido,asma’u dake zaune gefe ta samu nayi,dariya ta dinga harda qyaqyatawa
“Yaron oga ne fa,sai abinda oga ya gutsuro ya bashi da shi zaiyi hidiman bikin,ku bishi dai a hankali kar ya fece,dai dai ruwa dai dai qurji”
“arziqi da talauci dai duka na Allah ne,kuma zaman lpy da mutunta juna ake nema ba tarin dukiya ba”cewar anty safiyya aysha ta jiyota tana fada,a sannan tuni ta isa qofar kitchen tayi shigewarta abinta,itakam ko cikin tunaninta bata wani saqa zancan lefe,mata masu ‘yanci suke bidar lefe,ita wani abu ne ya rage mata,sam bama shine damuwarta ba a yanzu.

Washegari da daddare daddy na falonshi zaune ana nuna masa kayan,asma’un na zaune gefenshi suna kallo tare,duban mummy yayi
“Banga aishatu ba yau….ina tayi ne?” Baki mummyn ta tabe
“Allah dai ya kusa raba yari da barawo” ta furta a ranta
“Tana ciki…..ka santa gwanar zama a daki sam batason zaman falo bansan me ya sa ba” asma’u ya kalla
“Jeki kira min ita” hakanan ba don taso ba ta miqe ta tafi kiran ayshan,sanda taje ayshan na kwance rub da ciki saman gadonta tana karanta wani littafin addu’o’i,ta qara yawan haddar addu’o’inta sosai saboda kariya da ingantuwar tata rayuwar
“Saiki taso kizo….kwarkwasa fidda mai giji” ta fada tana watsa mata harara sannan ta juya ta koma,a nutse ta miqe ta sanya hijabinta sannan ta zura slippers ta fito.

Cike da nutsuwa tayi sallama hannunta dauke da jug na glass wanda ke cike da lemon guava data hadashi dazun nan,fuskar daddyn ce kawai qunshe da murmushi,ta isa gabanshi ta aje cikin nutsuwa
“Daddy sannu da hutawa”
“Yauwan indon baffale….sannu kadai” ya furta yana duba jug din
“Yau kuma me na samu?” Murmushi ta saki tana sunkuyar da kanta sanda take komawa da baya tana lalubar mazauni,da kanshi ya zuba sannan ya soma kurba yana kallon kayan da asma’u ke dagawa daya bayan daya,ganin shuru daddyn baiyi magana ya sanyata fara yunqurin miqewa a zatonta ba wani abu bane sai ya dakatar da ita har sai da suka gama kallon kayan tsaf,duk da aysha jifa jifa take daga kai ta kalla ta maida kanta qasa ta saddar.

“Ma sha Allah….yanzu sai biki kenan gaba daya ran ashirin ga wata” dif sukai daga mummyn har asma’un saboda anzo wajen,anzo wajen da ba zasu yarda daddy ya hada musu biki da ayshan ba,ko komai sun daure basa jin zasu haqura da wannan din
“Daddy” aysha ta kirashi cikin sanyin nan nata
“Na’am aishatu…”
“Daddy don Allah ina neman alfarma…”
“Tame indo?” Dan jim tayi kadan sannan tace
“Ina neman alfarmar idan babu damuwa a qyale anty asma’u tayi nata bikin ashirin ga wata din…ni ranar litinin din da aka gama bikinta ina son na tafi qauye ayi nawa bikin a can,daddy……” sai kuma ta danyi jim
“Inason idan an tashi daukoni a daukoni daga tushena…inda na girma na kuma rayu a can”.

Shiru daddy yayi yana auna kalamanta,yarinyar nada nutsuwa sanin da kamata,ya tabbata da wata ce cikin ‘yammatan zamanin nan masu son abun duniya son qyale qyale da qyamatar tushe babu abinda zai sanyasu yin zancan asalin nasu ma bare akai ga batun zuwa can biki
“Kin tabbatar haka kikeso,baki kuma da matsala da hakan?” Daddy ya tambayeta yana dubanta
“Eh daddy..” Ta fada tana gyada kai alamun tabbatarwa
“Shikenan to,babu damuwa” kanta ta duqar qasa
“Na gode daddy…Allah ya saka da alkhairi ya qara girma”
“Amin amin aishatu” ya amsa yana jin dadin addu’o’inta,ficewa tayi ta barsu a nan.

Tana shirin tada sallar wutiri bayan ta gama shafa’i wayarta ta dauki tsuwwa,dakatawa tayi don bata riga ta tayar din ba ta duba mai kiran,Aliya ta gani…take hannunta ya fara kakkarwa tana kokawar daga kiran kamar wadda ke dambe da wani tsabar rudewa da jin dadi,lallai Aliyar tazo mata a dai dai sanda tafi buqatarta fiye da kowanne lokaci
“Aliya..”
“Aysha” suka kira sunan juna a tare,qatuwar ajiyar zuciya aysha ta sauke,sannan cikin mutuwar jiki ta koma gefan gadonta ta zauna tana cewa
“Haba Aliya…haba..ya zakimin haka don Allah fisabilillahi…..bayan kinsan duk duniya bani da abokin shawara..kin tafi a lokaci mai tsada da muhimmanci a rayuwata kinyi dif kamar baki duniya…?” Ta qarashe fada lafuzanta na bayyana tsantsar damuwar dake maqare a zuciyarta
“Kiyi haquri sashin…wallahi dake nake kwana nake tashi…saboda ke naqi zama a nijer,kin ganni shigowata gida kenan ko zama wallahi Allah banyi ba na soma da kiranki….gayamin meke faruwa?”ajiyar zuciya ta sauke,cikin karaya tace
“meye ma bai faru ba,babu abinda ma bai faru ba sashin” idanu Aliya ta zaro kamar tana wajen cikin fargaba
“Me ya faru dake ‘yar uwa gayamin”
“Wai aure zanyi,aure na ya kusa”
“Kaman yaya?,how comes?…labarin daya cancanci ace ni zan bada shi ni ake baiwa….aysha ban fahimceki ba….wanne irin aure?ina fatan babu cutarwa a ciki” dan qaramin murmushi daya fidda sauti ta saki,duk da cewa tsoro fargaba da alhini ne danqare a qasan zuciyarta
“Maganar tafi qarfin waya Aliya…..idan kin samu lokaci kyazo”
“Wanne lokaci ne zan samu?…ki jirayeni gobe da sassafe in sha Allahu”
“Allah ya nuna mana….ki gaida mama”
“Zata ji” da haka sukai sallama,aysha ta jima zaune riqe da wayar tana kallonta,jifa jifa tana sauke ajiyar zuciya,haka kawai take jin nauyin da take ji a qirjinta ya dan ragu duk da bata ce komai ba,lallai ba shakka rashin abokin shawara(aboki na gari mai addini) ba qaramin nakasu bane a rayuwar mutum.

 

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 9:01 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*KO KUMA*

07067124863

*DB*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button