Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 23

Sponsored Links

Saida takai bakin gate sanan ta juyo ta kallai cikeda masifa tace “wai wat is ur problem with me ne eh? Dan Allah ka rabu dani” “I can’t” yafada tareda folding hanunshi a kirji yana kallonta, kwafa tayi tace “okay shikenan duk randa nama kara saka ka a idona sainai reporting dinka to police station” dan murmushi yayi dan baiso tadena magana ba, ta gefenshi tazo zata wuce yariko bakin hijab dinta da sauri ta dawo tana waige waige ko akwai wani a tsakar gidan ta kalleshi tace “na shiga uku wanan wai kai dan Allah wani irin mutum ne, wlh wlh kaga na rantse sau biyu niba nice wacce kake nemaba, Allah zan hadaka da Abba nafa this is not norm…al” hanunshi dayasa akan bakinshi yamata alamun tai shiru yasa takasa karasa maganan da kyau kirjinta nawani irin mugun bugawa gashi yaki sakin bakin hijab din nata balle ta gudu, ahankali yadan zo kusa da ita kadan, sosai taji kirjinta ya cigaba dawani irin mugun racing gashi takasa magana kaman yay mata magic dawani irin murya yace “will you marry me plz?” jin maganan tai daga sama da sauri ta kalleshi danta tabbatar shiya fada inko dai shiya fada to mutumin nan baida lpy, dawani irin murya yace “plzzzzz” wani karfi taji yazo mata ta fizge hijabin ta tana wani irin hararan shi da manyan idanunta, batare datace komiba tazo zata wuce ajiyar zuciya yadan sauke yace “at least kifada min sunan ki to kafin kitafi” juyowa tai ta kalleshi taja tsaki ta wuce fuuuuu, yafi minti uku a wajen da kyar yadaga kafan shi ya bude gate yafita kanshi nawani irin ciwo, shi kadai yasan me yakeji.
Ahankali ta bude kofa ganin Anty Hindu bata falo yasa da gudu tai sama ta shiga dakinsu, Farida tagani zaune tanacin abinci tace “waye yazo wajen ki Fahad ne?” tsaki tadanyi tacire hijabin Maman Miemie ta ijiye tace “wani unwanted guest ne” tai tsaki tawuce bathroom dan tadan wanke fuska jin har yanzu kirjinta na bugawa.

Yau dasafe takeda lectures while Farida Kuma sai 11, da wuri ta shirya cikin atampa ta daura Maroon hijab akai dayay mata kyau Bala ya dauketa a mota aka bude musu gate suka fito, hada ido sukayi da Khaleel dake sanye cikin sport wears kafarshi cikin Nike sport shoes yana jogging agaban gidan su, gadan towel dinshi akafada yana goge zufa idan yayi, wani heart melting murmushi ya sakar mata daya fito dayar wushiryar shi, ya daga mata hannu alamun Hi, sanan ya cigaba da jogging abinshi kaman da gaske, dauke kai tayi daga kallonshi ta turo baki tacema “Bala mutafi” samun kanta tayi da kallonshi ta mirror mota taga ya daga mata hannu da sauri ta dauke kai.

Around 3 tadawo kaman jiya Fahad ne ya sauke ta abakin layinsu ta dandaro da kafa, a kusa da gidan su ta ganshi tsaye ya rike wani katoton balloon da aka hura an rubuta I love you ajiki murmushi kwance akan fuskar shi yana kallonta, dauke kai da sauri tayi ta cigaba da tafiya. Biyota yay da sauri yasha gabanta wani dan Kati mai kyau pink yaciro daga aljihun shi ya bude an rubuta “please tell me your name” . Fizge katin tayi tayar ta kalleshi masifa tai niyyar mai amma saitakasa ahankali tace “please leave me alone” da sauri ta wuce shi ta shiga gida tabarshi nan tsaye.
Wuraren Magrib Farida tashigo gidan dakinsu ta shigo ta zauna akan gado batare datacema Islam dake rubutu komi ba, kallo Islam tabita dashi sanan tace “Faree wah happen a school why are you like this?” hawaye ne yazubo sharr daga idonta, ajiye biron dake hannunta tayi tadawo kusa da Faridan ta dafata tace “meya faru me aka miki” fadawa tayi jikin Farida tafashe da kuka da kyar tai shiru duk hankalin Islam yatashi tace “baki da lpy ne?” girgiza mata kai tayi sanan tace “tun jiya bayan mun rabu nake kiran my superman yaki dauka, wlh har Gym dinan saida naje yau amma bayanan ban ganshi ba, nakasa komi ko lectures ma babu wanda nagane, I don’t know why he is not picking my calls” tafashe dawani kukan, ba karamin tausayinta Islam tajiba hannu tasa ta share mata hawayen tace “stop crying hala baya kusa da wayan ne kokuma ansace mai wayan, please stop crying in sha Allah zai kiraki kokuma kuhadu” gyada mata kai Farida tayi, murmushi Islam tayi tace “oya cire kayanki bari naje nakawo miki abinci ta superman”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button