Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 20

Sponsored Links

Tun kafin la’asar tazo ta shiga wanka ta dauro alwala tafito, jin ana kiran sallan la’asar yasa ta shimfida dadduma tai salla. Bayan ta idar ne ta zauna agaban mirror ta tsantsara kwalliyar ta very light hoda ta shafa tasaka kwalli daya kara bayyana hasken idanunta, sanan ta gyara giranta da brush haka nan taji tanajin sa jan baki, red janbaki ta dauko tasa hakan yakara fito da kyan fuskarta leben yakara kankancewa kaman na jaririya, body splash da body spray ta dauko ta fesa sanan taje gaban wardrobe ta tsaya tana tunanin kayan dazata saka wani black lace dinta dake dauke da small small design din red flowers ta dauko doguwar riga akama dinkin A-Shape, sanya kayan tayi ba karamin kyau yamata ba yafito da shape dinta sosai, gaban madubi ta koma tadau brush tai brushing dogon gashinta dashi sanan takama da ribon ta nannade ta cusa a tsakiyar ribon din, jan plain gyale ta dauko mara stone ta yafa tadau flat takalmin ta channel mai igiya ta baya shima red ba karamin kyau baki da ja dressing din yamata ba, phone dinta kawai ta dauka da dan karamin coin purse dinta tarike, humuran da xoxo ta hadamata ta tsiyaya ta shafa kadan a hanunta dan badai kamshi ba sanan tawuce tafita daga dakin, sanin Anty Hindu ne kadai agidan yasa tai sallama tabude kofa ta shiga dakinta, dan tsugunnawa tayi kadan tace “sannu da hutawa Anty Hindu” kallonta tayi daga sama har kasa tana hura hancin nan nata as usual tace “ina zaki ba kince anyi canceling lecture ku nayau ba?” gyada mata kai tayi tace “eh, dama zandan je gidan su yar ajinmu na karbo handout dina ne” saida Anty Hindu tagama nazarin ta sanan tanuna mata kan drawer tace “dauko car key dina na aiki Bala, kidaiyi tuki ahankali” murmushi tayi harda juya kai tace “thank you Anty Hindu” key ta dauko tafita daga dakin cike da murna. Gaban wata Toyota camry taje ta shiga kunnawa tayi taja motar cike da kwarewa mai gadi ya bude mata gate tafita abinta, 20 min yakaita quiks cafe parking tayi tafito tana takunnta daidai ta shiga, wani waiter ne yazo yace “are you Miss Islam Maikano?” gyadamai kai tayi yace “Mr Fahad yamuku reserving table please come with me” binshi tayi ya kaita wani hadadde table dake zagaye da kujeru biyu, zama tayi yace “meza akawo miki Hajiya?” girgiza mai kai tayi tace “don’t worry inyazo” juyawa yayi yatafi, wayarta ta dauka tai dailing number Fahad bai daukaba harya katse, text dinshi ne ya shigo ta bude da sauri “princess am sorry please give me 20-30min Abba ne baida lpy muna hospital but yanzu nan zan fito nazo” reply tamai “Allah bashi lpy, take your time”. Kunna data tayi ta shiga watsapp tana duba messages wanda yawanci na groups ne, ganin Khaleesat tai posting Noorul Huda yasa ta gyara zama tana karanatawa ba karamin dadi novel din kemata ba harta gama karanatawa baizo ba, agogo ta kalla taga biyar da rabi saura minti biyu, number shi tafito dashi zatai dailing message dinshi ya shigo tai maza ta bude “am sorry my luv bazan iya zuwaba, jikin Abba yay tsanani an kwantar damuma. Luv u” reply tamai “Allah yaba Abba lpy, please take care of him, Luv u 2” ta senda mai sanan tadau car key da purse tafito ta shiga mota tabar Cafe din, tadanyi tafiya mai nisa kafin ta shiga wani uban traffic dan tsaki tayi tasa hannu ta kunna radio.

Hakanan yau yaji yanason yabuga kwallo hakan yasa ya shirya cikin jersey ya sanya takalmin kwallo yadau key mota yafita, yadanyi tafiya mai nisa dan stadium yakeson yaje yahadu da traffic dukan kujeran motar yay sabida haushi dan bayason afara bugawa bashi, kashe motar yayi ya bude yafito dan yaga maiya kawo traffic haka gashi ko moving motoci basayi, wata mota yagani babba tafadi gashi ankawo wata babbar mota dake daga mota ana kokarin cireta daga hanya sabida motoci su samu su wuce hakan yasa yadawo mota ya zauna, wani mai saida ayaba ne yazo ta bangaren glass din haggu yace “mallam ga ayaba sun nuna sosai gasu da shegen dadi” alamu yamai da hannu cewa bayaso hakan yasa mai ayaban ya wuce tareda barin jikin window hango Islam yayi tadaura waya a kunne tana magana, da sauri ya goge idanunshi sanan yasake kallon wajen, sosai yaji heart dinshi na racing kaman zai fita gani yayi ta ijiye wayar ta kunna motar ta tafi, wani wawan horn ya danna ma motar gabanshi ganin anfara tafiya, dawani irin mugun gudu yabi bayan motar Islam ganin tamai dan nisa, haka yadinga binta abaya hartakai layinsu, horn tayi agaban gate dinsu kusan sau uku gateman bai budeba hakan yasa tai parking ta bude kofa tafito daidai shima yay parking yafito daga motar shi, batama lura da motanba tadan duka ta mika hannu tadauko purse dinta dake kan sit ta maida kofar motar ta rufe ta juyo kadan yarage bata fada jikinshiba sabida yanda ya tsaya akusakusa da ita, atsorace ta jingina da motar tana kallon fuskar shi, wani irin kallonta yake kaman zai cinyeta, idanunshi data kalla yasa ta tuna fuskarshi a rude tace “innalillahi, wayyo Allahna, you again!” atsorace ta bangaje shi ta ruga da gudu ta bude gate din gidansu ta shiga, da gudu shima ya bude gate din yabita ciki.
[6/13, 10:55 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button