Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 32

Sponsored Links

Kaman mai rada yace “I love you so much, zuciya ta bazata iya jure rashin kiba, nasan baki sanni ba but please give me a chance, ina sonki sosai” dan hawaye taji ya gangaro mata, girgiza mata kai yayi ahankali yace “will u marry me please” dan lumshe ido tayi tareda dagamai kai maganar Anty Hindu dataji tawaje ya mai do da ita hankalin ta da sauri ta tashi ta zauna ta kawad dakai kirjinta na bugawa sosai tashi tsaye yayi shima yana kallon fuskarta, bude kofa Anty Hindu tayi ta shigo ita da Dr, dubata Dr yayi sanan yace “Hajiya babu wata matsala, nan da yan kwana biyu yan ciwukan nan zasu warke zaku iya tafiya” Anty Hindu tace “to nagode Dr, bari nakira Bala yazo ya dauke mu” da sauri Khaleel yace “basaikin kirashi ba nina kaiku Hajiya” yay maganar yana kallon fuskar Islam da har yanzu taki kallonshi, “to shikenan, ke tashi mutafi” ahankali ta mike tsaye tadau Hijabin ta tasaka shiya fara fita sai ita da Anty Hindu dasuka fito suna biye dashi abaya kofar baya ya bude musu suka shiga sanan yarufe sanan yakoma gaba yabude motar ya shiga ya kunna yafara driving har suka fita daga hospital din, ta mirror gaban mota yaketa kallonta amma taki dago kai saima wasa da yatsun ta da taketayi, har cikin compound ya shiga dasu suka fiffito da sauri tai cikin gida dan bataso su sake hada ido, Anty Hindu ce tamai godiya cike da fara’a da addu’a sanan ya kunna mota yafita daga gidan.
Afalo taga Farida ta zauna taci uban tagumi tsakanin jiya da yau duk tai zuru zuru tana ganin ta ta taso da gudu ta rungumeta tsam tsam sakinta tayi ta kalli fuskarta tace “sannu Islam ya jikin?” dariya ma tabama Islam hakan yasa tai dan dariya tace “ke dalla am fine ciwo fa kawai naji, Ina Mum?” jiki a sake tace “tana daki” tace “bari naje na gaishe ta” sama tayi saida ta gaida Mum tamata ya jiki sanan ta wuce dakinsu bayi ta shiga tai wanka da ruwa mai dumi sanan ta fito, light kaya tasa tazo ta kwanta akan gado dan bacci takeso tayi ta lumshe ido, fuskar Khaleel tagani yana mata murmushi da sauri ta bude ido tajuya dayan gefen tasake lumshe ido tuna sanda ta daura fuskar ta akan hanunshi tayi, bude ido tayi da sauri ta tashi ta zauna tareda jan uban tsaki dan mugun haushin kanta takeji tayaya ma tai hakan wat was wrong with her, waya ta dauka tasake dailing number Fahad bai dauka ba, message ne ya shigo wayar ta bude bakuwar number ce hakan yasa ta bude “I love you so much. Khaleel” wirgi tai da Wayan akan gado tareda yin tsaki “mutum sai shegen naci anaci”
Misalin 9 na dare Yusuf ya shigo part dinsu ya sameshi yana zaune yana daddana waya gefenshi kuma tea ne daketa kamshin su citta, zama Yusuf yay kusa dashi yadau tea ya kurbe hakan yasa ya kalleshi batare dayace komiba, murmushi Yusuf yayi yay gyatsa sanan yace “idan ma masifa zakamin naji amma kafara zuwa Abba na kiranka” filon dake kan kujeran yadau ka ya naka mishi akai sanan yabar dakin. Sallama yayi ya shiga dakin Abban, shi kadai ne sanye da farar jallabiya idanunshi acikin medicated glass yana karanta littafin addu’oi samin waje yay ya zauna akasa. Saida Abba yagama sanan yarufe ya ijiye gefe ya kalleshi yace “Son” “Na’am Abba” Abba ya gyara murya yace “ahh dama magana nakeso nai dakai kan yar abokina, nafison naji daga gareka ne dan mahaifinta yacemin yayarshi tace kun dan dade da sanin juna dan har gidan su kajema” shiru yadanyi yana nazarin fuskar Khaleel din sanan yace “kana sonta ne?” sosai yaji kunyar maganan Abba hakan yasa yadanyi murmushi yana sosa keya, dan dariya Abba yayi yace “a’a to to to, wanan murmushi haka Khaleel ta eh ce ko” dan gyada kai yayi kanshi akasa Abba yace “to masha Allah dama nariga nai magana da mahaifinka ran sati zaizo sai muje nema maka auran ta, banason awani nisanta bikin sabida dazaran anyi auren kukadan yimana kwana biyu anan saika koma bakin aikin ka ko” gyada ma Abba kai yayi Abba yay murmushi yace “saura dan uwanka yanzun nan nagama dashi nabashi wata daya idan Bai fito da mataba nizan nema mai” dariya Khaleel yayi wanan karan, Abba yace “tashi katafi Allah muku albarka”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button