Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 12

Sponsored Links

12….

Tashi Abie yayi yadauko maganin shi da yawancin inya fara surutai haka shi ake bashi ya dauko da sauri yadawo kan gadon ya dagoshi yana mikama Mami maganin yace “tashi kasha to saimuje wajen She” gyadama Abie kai yayi yana kuka ahankali yana yatsine fuska, zuba maganin Mami tayi ta mikamai ahankali yabude baki ya shanye maganin da kyar kullum yake yarda yasha amma yau yasha da kanshi, yanasha ko two minutes baiyiba bacci yay gaba dashi, gyaramai kwanciya Abie yay da kyar yaja bargo ya lullubeshi ya tofamai addu’a yajuyo ya kalli Mami dake share kwallan dake xubo mata, tasowa yayi ahankali yadawo bakin gadon kusada ita hanunshi yasa ya rungumota batare dayay magana ba, ahankali ta saukar da kanta kan kafadarshi wasu sababbin hawayen na gangaro mata kumatu tace “Abie why this? Why we? Why our Son? Shekaru talatin da biyu kenan muke fama, Abie please kafadamin what else dazanyi da yaronmu zai sami lafiya, banda burin daya wuce nabude idanuna naga Aadil kaman kowani namiji aduniyan nan, kaman dan uwanshi, Abieee” taja sunanshi cikin kuka, kiss yama forehead dinta yanadan shafa bayanta shima idanunshi sunyi ja, zaiyi magana wayarshi dake aljihun jallabiyar shi ta shiga ringing, riketa yay da hannu daya yasa hannunshi a aljihu ya ciro wayar yana kallon screen din, dan juyowa yayi ya kalleta yace “Baba ne” da sauri ta share hawayen datake yi tana mishi alamu daya dauka, daukan wayar yayi cikeda girmamawa harda dan dukar dakai yace “barka da safiya Baba” daga tachan bangaren tsohon da akalla xaikai shekara 80 yace “da Abdullahi nake magana ko?” yay maganan a natse kuma dadaddaya kaman yanda tsofaffi ke magana, cikeda girmamawa yace “eh Baba nine” a natse yace “to, to, to Masha Allah, ya kuke? Ya sana’ar taka tachan?” murmushi yayi yace “Alhamdulillah Baba, sana’ar munakan yi kuma ana samun riba daidai gwargwado” ahankali yace “masha Allah, Allah ya taimaka, Maryama fa?” murmushi yayi yace “gatanan Baba bari nabata wayan” ahankali yace “tsaya tukunna” cikeda girmamawa yace “to Baba” dan shiru yayi kafin ahankali yace “ina Hassan da Hussain?” kallon Mami yayi suka hada ido sanan ya maida hankalinshi kan wayan yace “Alhamdulillah suna lpy, Hussain na Nigeria yanzu haka yana Lagos ya….” cike da fada yace “Hussain na Nigeria shine baizo gidaba? Abdullahi dagakai har Maryama inda kusan bazaku iya bama jikokina yan biyuna tarbiya mai kyau ba dakun banisu na rainesu sun girma sun taso anan wurina, amma yaro ace yana kasar iyayenshi munan bamamu da labari yana gari, kenan inda ban kirakaba da bazaka fadi mini ba” cikin kwantar da murya yace “kayakuri Bab…” da sauri yace “bannemi wanan daga gareku ba, yau kwanan shi nawa?” ahankali yace “kwanan shi tara Baba, wani assignment yajeyi a Lagos amma dama…” katseshi yayi ta hanyar kiran sunanshi. “Abdullahi” da sauri cikeda girmamawa yace “na’am Babana” ahankali yace “kafadama Hussain yakamo hanya yazo kano yauyau dinan gidan kakanin shi banason naji wata magana, sai magana nabiyu dayasa na kira” yadanyi shiru yana hutawa, a natse yace “ina Hassan, yaya jikin nashi?” dan juyawa yayi ya kalli Aadil dake bacci har lokacin yace “Alhamdulillah Baba, jikin nashi da sauki” cikin dan kakkausar murya tsohon yakira sunanshi. “Abdullahi” ahankali yace “na’am Baba” shiru yayi nawurin minti biyu kafin yace “kaima kasan nabaku lokaci mai tsawo, na tsaya sanan na zuba muku ido ina kallon ku dakai da Maryama, nasan ku nasan halinku na yaran zamani, sanan bankuma tauye muku hakkin ku ba a matsayin ku na iyayen yaraba, na barku babu kasashen duniyan nan dabaku zaga da Hassan ba tun yana dan mininin shi neman mishi magani, to kanajina?” da sauri yace” eh Baba ina jinka” cikin yar shakakkiyar muryanshi ta tsofaffi yace “masha Allah, abinda nakeso daku shine, ka tattaro yinaku yinaku ka kawomin jikana nan kano, ku kawomin shi nan kano afara mishi maganin gargajiya, zamu jaraba mugani abinda Allah zaiyi, bazan zuba muku ido ku karar min da rayuwan jikana a hanyar asibiti ba, burina shine ya warke namai aure naga tattaba kunnena kafin mai afkuwa ta afku wato mutuwa, ku kawomin jikokina Kano zan nema mishi magani da kaina, ku kawomin su, ku zaku iya komawa indanta Hassan ne zan daukomai babban nurse ko Nani dazai dinga kulanmin dashi” yay dan shiru yana Tari da sauri yace “sannu Baba” saida tarin ya lafa sanan yace “kuyi shirye shiryen dazakuyi, ku kwasan mai duk wani abu dayake so gudun karya muku kuka a jirgi inya gaji da zama, ku hada komi kutaho Nigeria gobe, kufadima Hussain ina jiranshi shikuma yauyau dinan” ahankali yace “to Baba” “yauwa ka gaidamin da Maryama” “to Baba zataji” ahankali yace “Allah yamuku albarka dukan ku, Allah yabama Hassan lafiya, Allah ya kiyaye hanya yakawoku lafiya” da sauri yace “Ameen Baba” “yauwa to, nabarku lafiya” ya katse wayan. Ahankali ya zare wayan daga kunenshi ya juyo ya kalli Mami data gamajin komi, ahankali yace “anjima kihada mai kayanshi komi da komi, I will sort out d booking” gyadamai kai tayi tace “to Alhaji Allah yabada sa’a” juyowa sukayi dukansu suna kallon Aadil din dake bacci ahankali Mum tasa hannu tana shafamai kai kafin tadan kwanta a gefenshi tana shafamai kai tana kallon fuskarshi, Allah kadai yasan yanda takeson Aadil dinan, zata iya bada duka abinda ta mallaka a duniya inhar zai warke, shafa fuskarshi tayi tana kallonshi hawaye ya gangaro mata daga ido ahaka bacci yay gaba da ita hanunta akan fuskarshi, kafesu da ido Abie yayi feeling guilty, babu irin tunane tunanen da baiyi ba, blanket din gadon yaja ya lullubesu dashi yatashi yafita daga dakin yarufo musu kofa yafita, dakinshi ya shiga ya zauna gaban study dinshi ya kunna laptop dinshi yaje sight din emirate airlines, booking yamusu yay making payment aka turamai booking reference din ta email dinshi sanan ya rufe laptop din yay shiru yana kallon wani babban zoben dake kan yatsarshi yakai kusan 10min yana kallon zoben sanan yasake daukan wayarshi, dailing number Aadil yayi amma baishiga ba hakan yasa yatashi ya kwanta akan gado.

 

***
Shafashi dayaji anayi yasa yabude ido daga wani irin nauyayyan bacci daya samu ya kwasheshi around 4 nadare tunda jiya dayadawo daga asibitin da aka kwantar da Hamida yakejin wani irin kunci, sosai zazzabi yarufe shi jiyan nan, ahankali ya daura idanun akan fuskar Vanessa dataci gayu sosai tai makeup a fuskar tana daure dadan white towel, kwanciya tayi akan kirjinshi tanama kirjinshi kiss murya chan kasa tace “handsome baccin ya isa haka okay, your temperature is normal yanzu, am so lonely Aabid how are you feeling now?” lumshe ido yayi yanadan cije lips yakira sunanta achan kasan makoshi yace “Vanes…sa” dago kanta tayi tace “yes Handsome menene? something seems off about you tun jiya dakadawo, kodai yarinyar nan is a witch ne dama she’s too fine” bude idanunshi yayi duka yadaura akanta yana mata wani irin kallo da idanunshi dasuke cike da bacci a gajiye yace “watch your tongue” yay maganan yana kara lumshe idonshi danko kadan baison hayaniya ko motsi zaiyi sai Hamida tafado mai arai, anytime daya kulle idanunshi ita yake gani, ta tsayamai arai, ta tsayamai a thought, ta tsayamai akomi ma, baitabajin yanda yakejin nanba akan any girl, pink lips dinshi Vanessa takafe da ido kafin ahankali ta daura fuskarta kan nashi tana kallon lips din tana breathing heavenly takira sunanshi dawani irin low sweet voice. “Aabid, talk to me handsome, what’s the matter uhm?” tai shiru tana kallon fuskarshi amma baiyi magana ba, kiss tamai akan fine soft lips dinshi light one, bude ido yayi kadan ya kalleta batare daya cemata komiba, murmushi tayi tai cupping face dinshi tace “lemme make you feel better” zaiyi magana ta daura yatsar ta akan lips dinshi tana wani irin mai sexy kallo tasanya dayan hanunta ta warware towel din jikinta tai flinging dinshi, lumshe ido yayi da sauri dan she’s so tempting, yasan dayana school he and Vanessa dated for a very long time, but yanzu ya girma he really wants to change, baya sonta but she’s just a girl a d tun yana school ta makale mai dudda ba same course suka karantawa ba, kuma ba same school sukayi ba, lokacin dasuka haduma masters yakeyi ita tana degree dinta a New York film academy, another thing dayasa yake kara kulata is because bata kula any guy bandashi dan yanada mugun kishi, yarinyar na sonshi sosai bana wasaba, they had sex couple of time dan akwai wasu abubuwa datake mai da koyaya yaso karyayi saiyayi but yanzu he really wants to change, yasan a Islam abin is a sin haramun ne saisa yaketa son yay aure but baitaba ganin wacce yakeso ba, wacce tamai ta kwantamai arai baitaba ganiba, yaje kano sau da dama all his cousins, duk yanmatan garin dayake gani ko sha’awa basu bashi balle yamaji yana sonsu, sai akan Hamida dayaji he loves every single thing akan yarinyar, yaji his whole world is revolving akanta.

Grabbing dinshi dayaji tayi down there yasa ya saukar dawani irin ajiyan zuciya ya ware Ido ya kalleta, da kyar ya iya yay fighting yanda yakeji dan he so want it shima bana wasaba, hanunta yarike cikin rashin karfi ya girgiza mata kai yace “stop it” fashemai tai da kuka ahankali tace “please Aabid, I want you badly handsome, nakasa saurayi Aabid, nobody can f*ck as good as you, please my love, okay I understand you said having sex without marriage in your religion is a sin right” tai maganan tana share fuskarta da bayan hannu ta kalleshi, gyadamata kai yayi yana mika mata bargo danta rufe kirjinta dake dancing a face dinshi, karban bargon tayi tarike tareda hanunshi tace “okay let’s get married handsome” lumshe ido yayi ya girgiza mata kai yace “I cannot get married to you” da sauri tace “why?” bude idanunshi yayi ya kalleta ahankali yace “because I don’t have feelings for you” fashemai tayi da kuka tafada jikinshi tana girgiza mai kai tace “please love dont say that kaji My Aabid, am begging you” zaiyi magana wayarshi tai kara alamun shigowan message ahankali yamika hannu yadau wayar da sauri yabude sakon ganin daga Abie ne, yana gama karantawa ya ijiye wayan wani irin murmushi yayi yace “Kano!” tashi yayi daga kan gadon, drawer gefen gadon yajawo, bundle din kudi yaciro nayan dubu daidai guda biyar ya ijiye mata yana kallon yanda take goge idanunta da hannu yace “get ready and leave, am going to my grandparents house, my parents are coming to Nigeria tomorrow, take care okay will call you” juyawa yayi ya shiga bayi tabi bayanshi da kallo kafin ta kalli kudin daya ajiyemata tafashe da wani kukan sanan ta tashi ta kwashi kudin ta wuce tafita ta shiga next room ta shirya tsaf tsabagen yanda takeji haushin shi ko jiranshi tamai bye batayiba tadau jakanta tafita tana kumbura kumbure.

Yana fitowa shafe shafenshi yayi yana murmushi, yasan halin kakan shi hakan yasa ya shirya cikin wani white soft yard da akamai dinki jumper, bakaramin kyau kayan sukamai ba, kallon wardrobe din yayi yana kallon kayanshi he’s so lazy, baida karfin dazai wani hada kayanshi a akwati banda hakama yanada kaya achan kano, hakan yasa yaje gaban madubi turaruruka ya fesa yana kallon kanshi a gaban mirror yanda farin kayan yawani irin haska shi ya shiga kayan dam yay wani irin shegen kyau, ahankali yana murmushi yace “am coming Jewel saina nemoki koma a ina kike agarin kano, ur husband is coming Mrs Aabid” murmushi yasakeyi ya zira takalmin shi na Gucci yadau wrist watch dinshi ya daura, wayarshi ya dauka yafita daga dakin yafara sauka kasa yana danna waya yana order Uber, ya sauka kasa yana wani irin kamshi dukya cika gidan da kamshin turaren shi, kitchen ya shiga yahada coffee a mug yafito zama yayi kan kujera yanashan coffee kafin Uber yazo yana cikin sha mai Uber yazo, tashi yayi yaje ya ijiye mug din a kitchen yafito ya kulle gidan, mai gadin yabama key yamai sallama tareda mai kyauta sanan yawuce yafita gate ya shiga motar Uber yajashi har airport yana zuwa yay komi Azman airline zaibi to Kano, ya karbi boarding pass dinshi yawuce upstairs ya shiga departure lounge bai wani dadeba akai announcing boarding dinsu, tashi yayi yawuce yaje yay boarding jirginsu yadaga, 1: 25 jirgin su ya sauka a Airport din kano, wani irin murmushi yayi yafito yana kallon ko ina rabonshi da kano almost a year kenan, yasan inda yafadama grandpa yana hanya da yanzu airport dinan yacika da motoci anzo daukan shi, he’s so eager yaga Aadil gobe, karasawa yayi yashiga taxi yacema mai taxi din “New GRA zaka kaini”.
_🌹IN BANI 🌹_

Maman Abd Shakur

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button