Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 7

Sponsored Links

Ance kowani rai mamaci ne, mutuwa bata baka notice, once lokaci yayi you just have to go, mu kusanci Allah mu nisanci zunubai, muyawaita istigifari bamusan kozamuga gobe ba.

Babu wanda ya yarda Eesha bata, Mama gani take ya’ta da yanzun nan tazo tacemin zata fita dama ajali ke kiranta?? Khadija kam kasa magana tayi kuka kawai take, su Ihsan dasu Faiza da kanin Eesha bansan wama ke lallasan wani ba, Maman Khaleel da Umma da Mujiba ma duk zuwa gidan su Eesha sukayi.
Ko alwala ma yima Khaleel akayi sosai yafita hayyacin shi hanunshi damke da ledan da Eesha tabashi yana wasu irin surutai, haka aka mata Salla aka kaita, aka dawo shikenan fa duniyan.
Yauce Rana uku da rasuwan Eesha, babu wanda zaiga Khaleel dabazai yi kuka ba, koka zo gaisuwa bakai niyyar kuka ba shiza kagani kai kuka, ko abinci yakici, ruwama saidai abashi wanda ya shiga ya shiga sauran su zube akasa dan baya zukan ruwan da kanshi, ko wanka yakiyi balle ma wani abun, bayama kowa magana saidai yay ta maganganu shi kadai, addu’a ake mai bana wasaba amma har lokacin ba chanji, Maman Eesha duk idan ta kallai saitai mai kuka, Ammin shi kam baa cewa komai.
Misalin 1:25 na dare kowa na dakin shi, karan fashe fashen abubuwa ne yasa kowa ya mike daga kan gado dan dama bawani baccin kirki kowa keyiba, afrigice Yusuf ya farka gefen shi ya duba ganin babu Khaleel dake kusa dashi yasa yay jumping daga kan gado yafito daga dakin, cin Karo yayi da Abban shi da Umma, Abban shi zaiyi magana saiga Daddy da Ammi sun fito, su Ihsan ma haka atare suka dunguma suka sauka kasa kitchen sukayi dan nan sukejin karan. Shiga sukayi da sauri Khaleel suka gani dauke da tabarya a hannu yana faffasa koma me hanunshi yakai yana ihu yana magana “ba Kaine bakin jeep dinba Kaine my Eesha ke karkashin ka, ku ku 5 ne” tawarwatsa kwanuka kawai yakeyi, ko kallon su Abba dake kiranshi baiyiba, Yusuf ne ya fizge tabaryan ya ijiye hakan yasa ya ture Yusuf, da sauri Ammi ta juya ta koma falo danji tayi wani mugun kuka yazo mata, Ihsan ma fita tayi da sauri jikin Ammi tafada sai kuka da kyar Umma ta lallashe su, wani irin murmushi Mujiba tayi mai wuyar fassara kafin ta dawo falon ta zauna. Baban Eesha Abba yakira dan babban likita ne shi, within 2min ya iso, da kyar su hudun suka iya kama Khaleel dubashi baban Eesha yayi kafin yamai alluran bacci, nan bacci yay gaba dashi akan dogon kujera.
Ajiyar zuciya Abban Eesha yayi kafin ya kalli Abba yace “I think Khaleel yay developing mental issues”.
[6/8, 5:37 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button