Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 53

Sponsored Links

Ahankali take bude idanunta dasuka mata nauyi sosai jikinta ko kadan ba karfi gabobin jikinta sun mata tsami sosai, bude idanun tayi gabaki daya ta daura shanyayyun idanunta akan makeken agogon bangon, tana fitar da numfashi ahankali ahankali da baki bata feeling jikinta ko kadan, motsin da kunnuwanta sukaji yasa tajuyo da kanta ahankali, sauka idanunta sukayi akan fuskar Aadil dake kwance agadon dake dayan bangaren dakin akwai dan gab a tsakanin su, motsi yake sosai batare daya bude idoba sai motsi dayakeyi idanunshi na rawa suna shirin su bude, lumshe idanunta tayi asanyaye takara budesu ahankali tasauke su akan fuskarshi, wani irin sanyi taji ajikinta bana wasaba, ahankali ta matsar da hanunta da kyar zuwa baki bakin gadon datake kai tai pointing Aadil din da hanunta tana lumshe ido batare datai koda kwakkwaran motsi ba, bude ido Aadil yayi gabaki daya yana kallon dakin yanabin ko ina da kallo, yakai kusan minti biyar ahaka kaman mai nazarin wani abu kafin ahankali yatashi ya zauna yana kallon drip din da ake karamai yadan yatsine fuska sabida ciwo da jikinshi kemai sosai yana shafa hanun nashi dan wurin karin ruwan namai zafi sosai, lumshe ido tasakeyi ahankali tanajin wani irin murna har cikin ranta ganinshi atare da ita dat means he’s fine bai mutu ya barta ba, bude bakinta dayamata nauyi sosai tayi zatai magana wani atishawa mai karfi yazo mata tayi, da sauri ya waigo ya kalli bayanshi jin karan atishawa tsayawa yayi chak batare dayace komiba yakafeta da ido, wata yarinya yagani fara sosai kan gadon, tana sanye da wani pink rigan asibitin akwai bandeji biyu a jaws dinta tana kwance gashin kanta ya barbarzu kaman na yar buzuwa ta kafeshi da ido kaman mayyar dataga yaron dazata lashe, murmushi tasankin mai daya bayyanar da cute dimples dinta ganin ya ganta yajuyo yana kallonta, yatsine fuska yayi akasalance ya dauke kai ganin yarinyar tanamai murmushi tana wani irin kallonshi kaman zata hadiyeshi daidai lokacin aka bude kofar dakin za’a shigo, atare dukansu sukabi kofar da kallo, Big Mum ce ta shigo dakin tareda Baba Suleman suna hira batare da sunma lura dasuba. “eh saida na tabbatar tasha maganin Yaya sanan nafito, saida nahada da yimata alkawari zan kirata a video call taga fuskokin su sanan ta yard….” shiru tayi batare data karasa maganan ba ganin Aadil zaune abakin gado ya kafesu da ido yana kallonsu, dukansu kamewa sukayi tsaye suna kallon Aadil din daya kafesu da ido bayako kyaftawa, da wani irin sauri Big Mum tai wurin gadon ta zauna kusa dashi cikin murna tadaura hanunta akan fuskarshi tana shafawa tace “Aadil, Boy katashi, yaushe katashi ya jikin?” hanunshi ya daura akan nata dake kan fuskarshi yadan lumshe ido ya bude ahankali kafin cikin wani cool calm voice yace “Big Mum ina Mami na? Ina Bid?” chak daga Big Mum har Baba Suleman suka tsaya suna kallonshi ganin for the first time in life sunga Aadil yay magana batareda kanshi yay rawa ba batare da miyau ya zuba daga bakinshi ba and magana ba childish magana daya sabayi ba yana turo baki a shagwabe yana fari da ido yana lankwasa kai yana make kafada, tashi Big Mum tayi tafada kasa cikin so much happiness tai sujjada kafin ta tashi tafashe da kuka sosai tana kallon Aadil din dake binta da kallo, kawai takasa holding tears nata back ne, sake zama tayi ta matso kusada Aadil din sosai taima fuskarshi kyakkyawar cupping tace “Aadil, Aadil am I dreaming kaine Aadil, Aadil u are fine kaji sauki wayyo Allah na Yaya am so happy today, kalli Aadil dinmu fa, Alhamdulillah, ya rabb i can’t wait to tell kanwata this good news dasu Baffa” tai maganan tana wani irin rungume Aadil dayay shiru yana kallonta kaman mai tunani yanason gano wani abu, karasowa cikin dakin Baba Suleman yayi ya zauna adayan gefen side din Aadil din yana kallon Aadil din today is such a good day hanun Aadil din yakama yarike, hakan yasa Big Mum tace “kagane shi Aadil?” juyodakai yayi ya saukar da manyan eyes dinshi akan fuskar Baba Suleman din ya kafeshi da manyan milky eyes dinshi yana kallo ahankali yace “Uncle” wani irin ihun dadi Big Mum tasakeyi tana goge hawayen datakeyi nonstop tana kokarin ciro wayarta daga jaka da sauri Baba Suleman ya fizge wayan yace “babu wanda zaki fadamawa saidai su ganmu mun da Aadil din kawai, lemme go an call Dr yazo yaduba shi” tashi yayi daga kan gadon daidai zai juya yay wurin kofa idanunshi suka sauka akan Hamida dayagani idanunta biyu tana kallonsu hawaye nafita daga gefen idanunta tana kallonsu da sauri Baba Suleman yace “H…Hamida” yay maganan yana karasawa wurin gadon cikin tsananin farin ciki da sauri Big Mum ta mike tsaye jin sunan da Baba Suleman yakira, karawasa gaban gadon Baba Suleman yayi ya tsaya yana kallon Hamidan ahankali yace “Hamida kin farka?” kafin ma tabada amsa big mum takaraso wajen tana Share kwalla tace “daughter na, Hamida na kintashi” da kyar Hamida ta iya ta gyadamata kai sabida bones dinta dake mata ciwo sosai daidai lokacin Aadil yamike tsaye ahankali yana yatsine fuska ya cizge karin ruwan dake hanunshi ya yar, singlet da 3quater dayagani kan gadon ya dauka yadaga kafa ahankali yay hanyar kofar dakin dayagani wanda ya kyautata zaton na bathroom ne, yanda Hamida tabishi da kallo batare databa Big Mum amsar tambayanta ba yasa Big Mum da Baba Suleman suka juya atare dan suga metake kallo haka, ganin Aadil ne yatashi yana tafiya yabude bathroom ya shiga yasa big Mum tace “Yaya akira mana Dr yakamata yasan sun farka beside Hamida doesn’t look good, meke miki ciwo daughter?” fita Baba Suleman yayi dan zuwa kiran Dr, ahankali batare datai magana ba Hamida ta nuna mata fuskarta da jaws dinta alamun su kemata ciwo, a forehead big Mum tamata peck cikin tsananin son yarinyar tace “don’t worry zakiji sauki kinji, Maman ki kullum saita kira taji yaya jikin ki, i know she will be very happy idan taji kin farka” shigowa Baba Suleman yayi tareda Dr da nurses guda biyu, kana ganin su kaga larabawa, da farin ciki gabaki dayansu suka shigo suna tambayan ina Aadil Baba Suleman yace “ya shiga bathroom wanka” Dr ya shiga duba Hamida daidai lokacin Aadil yafito daga bathroom din sanye da white single da 3quater ajikinshi yana tafiya ahankali, tafi duka Dr da nurses din suka fara suna kallonshi suna murna ganin patient dinsu yatashi strong and healthy, dan kallonsu yayi kafin ya dauke kai yakarasa yazauna akan wani plastic chair dan yagaji da kwanciya Hamida tabishi da kallo, so kawai take yamata magana koma ya kalleta amma yaki, saida aka gama dubata sanan Dr yaduba shi, babu wata matsala tattare da shi sai rashin kuzari wanda dazaran yaci abinci zai dawo normal, har Dr zai fita Baba Suleman yace “yaushe za’a sallame mu Dr? Munkosa mutafi gida dasu” dariya Dr yayi yace “i just want to run two scans for Amatullah once d result is clear and fine zanyi discharging naku yau, but before then amata wanka zan turo dietitian yazo yaduba su yafadi abinda zasu iyaci” murmushi Baba Suleman yayi looking satisfy da service dinsu yace “angode Dr” fita Dr yayi nurses biyedashi hakan yasa Big Mum yaye lullubin jikinta ta ijiye akan gadon da jakar hanunta tace “bari naje nahada miki ruwa mai zafi sosai ko kyaji dadin jikinki nazo muje muyi wankan, dan bude ido Aadil yayi kadan ya kallesu kafin yasake lumshe ido abinshi ya kishingida, shiga bathroom Big Mum tayi tahada ruwa sanan ta dawo dakin takama hanun Hamidan tace “yauwa tashi muje daughter na” ahankali Hamidan ta tashi tana yatsine fuska gashin kanta yakara barbajewa ta sauko da fararen kafafunta kasa ta zauna tana runtse ido sabida yanda jikinta ke ciwo bana wasaba kaman Big mum zatai kuka tace “sorry kinji” huta saimu tashi, kai ta gyadama Big Mum tadan saci kallon Aadil dahar lokacin idanushi ke lumshe kaman wanda yay bacci, hanunta da kafadarta bigmum takama tace “yauwa muje” saukowa tayi daga kan gadon ta mike tsaye da kyar jikinta na rawa kaman zata fadi hawaye ya gangaro daga idanunta sai sannu Big Mum take mata takaita gaban bathroom din tabude bathroom din suka shiga, yatsine fuska Aadil yayi dan surutun Mami na damun brain dinshi yabude ido kadan yana kallon kan gadon data tashi daga kai kafin yasake lumshe idon, basu jima da shiga bayin ba Big Mum tafito tabude wardrobe din dakin taciro free plain gown na cotton black mai kama da rigan da sauran abubuwan dasuke bukata da ribbon takoma bayin, sunbata almost 20min sanan suka fito yanzu tafiyarta yadanfi nada dan tanayi ahankali rigan jikinta yamata kyau yakara haskata, big Mum ta zaunar da ita akan gado zama tayi ahankali, daidai lokacin dietitian din ya shigo da abubuwan da zasuci bigmum ta karbi na Hamida Baba Suleman yakarbi na Aadil, sanan Dr yace “Hamida tagama da wuri za’a mata scanning” to Big Mum tace “ta shiga bama Hamida abincin” da kyar ta iya ta karbi abincin tanaci ko kadan batajin dadin komi ganin yanda ko kallonta Aadil bayayi bama ya magana ya lumshe ido kaman mai bacci, tana gamawa nurses suka shigo suka fita da ita dan zuwa scanning big Mum tabisu.

 

Sai wajen la’asar aka dawo d ita komi is fine babu wani complication, bakaramin dadi su big Mum sukaji ba nan aka basu sallama bayan Baba Suleman yagama clearing komi na bill, big Mum kuma ta shiga hada kayayyakin su she can’t wait to see Mami’s face dana Aabid idan sukaga new Aadil not baby Aadil.

Related Articles

 

Wuraren biyar da rabi suka gama komi tsaf suka fiffito har haraban asibitin Aadil da Baba Suleman suka shiga gaban mota itakuma da big Mum suna baya, Baba Suleman ya kunna motar yaja suka shiga hanya yace “i can’t wait to see yanda su Mami da Aabid zasuyi idan suka ganmu” dan dagokai Hamida tayi ta side glass ta kalli fuskar Aadil taga idanunshi a lumshe suke kaman mai bacci, kuka ne sosai taji yazo mata, she’s so longing for his talk, so kawai take yamata magana amma ya share ta, da kyar ta daure ta hana kanta kukan dan bamata da karfin yin kukan tanata kallon garin dasuke dan daga gani tasan ba Nigeria bane dan larabawa take ta gani tako ina, tafiyan kusan 20min sukayi taga Baba Suleman yay parking agaban wani babban gida yace “muna shiga da mota zasu gane kuzo muje” fitowa yayi hakan yasa Aadil yabude kofa shima yafito yakosa yaga Mami da dan uwanshi, big Mum ma tafito ta taimakama Hamida itama tafito, Baba Suleman yabude gate suka shiga har gaban babban flat dinsu Baba, Suleman ne yajuyo yana zare ido hadaura yatsarahi akan lips dinshi ya kallesu, hanun Aadil yakama ya daura akan na Hamida da sauri Aadil ya yatsine fuska tareda janye hanunshi da sauri yana kallon Baba Suleman irin me haka, ahankali Hamida ta kallai yanda yake yatsine fuska, cikin rage murya batare da yalura damai yafaru ba Baba Suleman yace “kariketa karta fadi kaga batada karfi nida Aisha ne zamu fara shiga ciki kafin ku kubiyomu abaya” yay maganan yana kara daura hanun Aadil akan na Hamida ahankali Hamida ta saukar da kanta kasa dan tana gabda sakin kuka, Baba Suleman da Big Mum suka juya suka bude kofa suka shiga ciki atare, wani irin gajeren wahalallen tsaki Aadil yaja ya saki hanunta da sauri hakan yasa tai baya zata fadi atsorace taidan kara tadafe bango ahankali tana maida ajiyan zuciya, ko kallonta baiyiba yasa hannu yabude kofa ya shiga dakin idanunshi suka hadu dana Mami da Aabid yadebo rice a spoon yana kokarin kaimata baki danko kadan bata iyacin abinci sai an tursasata tarame sosai bana wasaba, Baba Suleman da Big
Mum tsaye agefe suna murmushi sosai suna kallonsu sunyi folding hand akirji, atare Mami da Aabid suka mike tsaye suna kallon Aadil din, wani irin cute adorable smile Aadil yayi yace “Mami na” ya kalli Aabid yace “rascal” sakin plate din abincin Aabid yayi akasa jikinshi yadau wani irin rawa bakinshi har rawa yake yana kallon Aadil din yace “d…Dil”
..

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button