Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 3

Sponsored Links

Page 3*

★★★~~~★★★~~~★★★

Tunda ya fara mgnr suke kallonsa yana ida faɗin abinda yake faɗi ya juya yayi tafiyarsa wani kayan takaici wanda akace yana sonta da ƙawancen har yasha kwana yama riga tafintan nasa barin gurin taɓe baki tayi tayi gaba suna tafe babu me cewa wani Saida suka kusa rabuwa Lantai tace.
“Nifa lamarin ƴan birnin nan ya fara bani tsoro musamman akanki Bibo meye kuma ƙawance tsakanin namiji da mace?” Kawar dakai tayi tace “to basai yayi da gyatumarsa ba tunda shi bashi da ɗa’a aiko mahaukaci yasan wannan ba daidai bane”
Shigewa tayi gdansu Lantai ta wucce nasu gdan, tana shiga tayi watsi da komai ta shige dakinsu ta faɗa kan shimfiɗa ta kwanta tare da lumshe idanunta wannan wanne irin mutum ne? Meye yake nufi da ƙawance tsakaninsu? Tambayar data kwana da ita a ranta kenan har wayewar gari tada tashi wanke fuskarta tayi suka gaisa da uwarta ta nufi wajen gyatuminta ta ishe shi zaune yana shan kunu ta zauna suka gaisa tace “inason dama zanje gona ne” dubanta yayi duba irin na tsanaki yace “gona kuma?” Meye zakiyi a gona?” Sunkuyar da kanta tayi ƙasa tace “Sallau jiya yake cewa da Jumme ciyawa ta ɓata yabanyar gonarka idan ba’a cireba zatayi ɓarna wannan tasa naga ya kamata naje nagani koda abinda zan iyayi” jinjina kai yayi yace “shikenan kije Allah ya tsareki”

Related Articles

 

Ƴar ƙaramar dariya tayi ta miƙe ta fita saboda murna ko sallama batayiwa Jumme ba ta bar gidan ta nufi gonar tanata yan waƙoƙinta.
Tsakanin gonar da cikin gari akwai nisa sosai amma sabo yasa basa ganin nisan haka taci gaba da kurɗawa tayi nisa sosai daidai wata itaciya ta rinƙa jiyo ƙamshi me kwantar da zuciya tana dosarta ƙamshin na ƙaruwa harta isa jikinta, gabanta ya faɗi “Wayyoh!” Tana mgnr tana ja da baya ga mamakinta sai taga yayi murmushi ya taso daga gurin yace “kin tsorata ko?” Wata ajiyar zuciya ta saki me ƙarfi jin dirin saukar muryarsa har cikin lakarta.
Sake matsowa yayi yace “Ina zaki?” Yana mgnr yanakai hannunsa ga buhun dake saɓe a kafadarta, batayi Masa gardama ba ta sakar masa ya fara dubawa yana kallonta Saida ya gama dubawa tsaf koda baisan amfanin kayan ba alama ta nuna masa gona zata hakan yasashi ɗagowa yace “gona?”

 

 

Da sauri a ƙoƙarinta na ganin ya barta ta tafi ta ɗagansa kai yaja fasali ya karyar dakai yace “zan iya rakaki inason na iya aikin gona….” Zaro idanu tayi tare da kunshe dariya ya zubanta idanu har Saida ta saita kanta yace “meye ya baki dariya?” Taɓe baki tayi tace “ba haɗi saniya da tallan kilishi” da sauri ya dawo da hankalinsa gareta yace “sabida me?” Gaba tayi taci gaba da tafiyarta tana cewa “ko cikin malalata akwai gwarzo kaikam ko riƙon lauje bazaka iyaba bare noma”
Murmushi yayi yabi bayanta yace “iya magana kamar ƴar mahauta kuma haka zaki koyamin ba”

 

Tsayawa tayi tare da haɗe fuska tace “Idan muka tafi gona tare zakasha wahala kuma mutanen garin mu zasuje su faɗawa Jimo Ciwake harma su ƙara da sherri ka taimakeni ka barni naje nayi abinda ya fito dani”
Fuzge buhun hannunta yayi yayi gaba batare da ya sake cewa da ita komai ba dole tasa ta rinƙa binsa da sauri tana cewa dashi “bakaji ba kagafa akwai nisa jikinka bai saba da wahala ba banaso kasha wahala…..” Tsayawa yayi ta iso gareshi ya kai hannu zai riƙota tayi saurin ja baya tace “Aa haram giya a gdan Mallam kada ka kuma taɓani jiya daka taɓani Saida Jumme ta kusa ganewa da kuwa ta gane da tuni na zama tarihi don jefani za’ayi cikin ruwan wankin zunubi kuma zunubin nan bazai barni na tsira ba”

 

Zubanta idanu yayi yace “wanne zunubi kenan?” Taɓe baki tayi tace “ai babban zunubi ne namiji ya taɓa jikin mace a nan garin idan har hakan ta faru to duk inda tayi za’a rinka jin warin maza a jikinta kuma zaija mata ƙyama da tsangwama wannan dalilin zaisa taƙi auruwa domin babu wanda zai ɗauki karya yakai gidansa a matsayin uwar ƴaƴansa”
Murmushi Habeeb yayi yace “Al’adarku nada kyau da tsafta kamata yayi ace baku kuke da wannan tsarin ba mu musulmi mune zaifi cancanta da mu kasance a haka domin ubangijinmu ya hanemu da kusantar zina” daga wannan basu kuma mgn ba sukaci gaba da tafiya har suka kai gonar Habeeb ya tsaya yana kallon gonar ba wata babba bace amma tayi kyawun yabanya da ta burge shi.

 

Tsinkayo muryarta yayi tana cewa “kaje ka zauna ga bishiyar mangwaro can tunda ka nace Saida ka biyoni” miƙa mata kayan hannunsa yayi batare da yayi furuci ba bai kuma bi umarninta ba, ganin abin nasa na yine yasata wuccewa ta fara aikinta tanayi yana kallon yanda take tafiyar da komai yana gane irin ciyawar da take cirewa da haka shima yakai hannu ya fara tayata.
Ba ƙaramin mamaki ta shiga ba da taga ko ita data saba aikin bata kaishi kwazo ba ta ɗago tasa gefen zaninta ta sharce gumi ta zubansa idanu tana mamakin inda ya iya aikin gona da kuma yabawa kyawun surarsa tabbas yakai kyakkyawa na gaske duk da ba fari bane amma yanada wani sihirtaccen kyawu da hasken fata na tsabar hutu da jin daɗi da yake bayyana kwanciyar hankalinsa.

 

Ɗagowa yayi ya zubanta idanu tayi saurin kawar da kanta tare da basarwa ta sunkuya tana tattare kayan tana cewa “naga abubuwan mamaki a iya yau dana zauna dakai naga kana isa waccan ƙoramar kana wanke jikinka kana dungura goshinka ƙasa meye hakan yake nufi…. ”
Cikin mugun mamaki Prince Habeeb ya Kalli Bibo tare da kafeta da manyan idanunsa, yanzu ita a nufinta batasan sallah ba? Mamakinsa ya kawar da cewa “koda yake a ina zata sani?”
Tayata tattare kayan yayi yace “Kada kiyi gaggawa da sannu kuma a hankali zakisan komai game dani tunda kin yarda da abotarmu” miƙewa tayi da sauri tana girgiza kai tace “Aa Nifa ban yarda da wata ƙawance ba….” Hannu yasa saman bakinta ta ɗago ta dubeshi idanunsa nakan fuskarta yace “kar kija da ƙudurina inason abota dake kuma ta ƙullu daganan har zuwa lkcn da zan bar garin nan naku kiji a ranki a koyaushe kuma a kowanne yanayi zamu kasance a tare Habeeba bana nufin cutarwa gareki saidai ke kin kasance ƙaddarata”

 

“Ƙaddara” ta faɗa tare da ɗagowa da sauri, bai tsaya bata amsa ba saima gaba da yayi dole tasa ta bi bayansa suka nufi cikin gari duk inda suka wucce hankali akansu yake har suka je ƙofar gidansu taja ta tsaya shima ya tsaya sun jima a tsaye ganin bashida niyyar furuci sai kafeta da yayi da manyan lulu eyes nasa yasata juyawa tana cewa “Na gde ka huta gajiya”
Shigewa tayi ciki yabi bayanta da ido abubuwa da yawa na ayyanuwa a ransa waɗanda ya kasa tantance yuwuwarsu ko rashin yuwuwarsu koda yake Hausawa sun ce da tsoro ake cire saa shikam zuciyarsa na rawa akan abubuwa da dama amma dai zai jarabba kalar tashi nasarar yagani idan yanada rabo.
Da wannan tunanin ya isa masaukinsu Najeeb daya gaji da kiran wayarsa har ransa yayi ƙuna ya tareshi da cewa “Ina kaje?” Tambayar ce ta bashi haushi ya zabga masa harara ya nufi cikin gdan gdane me kyau nesa da cikin gari kaɗan ginin zamani dakunansu harda A C ga babban inji da aka sanya musu me bada wuta kowanne lkc sannan duk wata kalar kayan jin dadin rayuwa sun siya sun zuba a gdan a taƙaice dai idan ka shiga gdan bazaka gane a ƙauye kake asalin ƙauye irin Tsaunin gawo ba.

 

“Habeeb tambayarka nakeyi ina kaje….” Juyowa yayi ya kafeshi da idanunsa wanda ba kowa ke jure sanya ƙwayar idonsa cikinsu ba ya tako gabansa yace “Ni kamar ni kake tambaya ta ina naje kamai dani wani ƙaramin yaro ne ko kamai dani mahaukaci da kake gadi na?”
Yayi mgnr yana zare ƙafar wandonsa, harara Najeeb ya watsa masa yace “ka kuwa ɗaukowa kanka abinda zai dameka banga uwar da ta ɗauki hankalinka akan wannan yarinyar mara addini ba da har ka zaɓi zubar da mutumcinka akanta…..”
Tsawa ya daka masa yace “Wlh tallahi ka ƙara faɗar wata kalma mara kyau akan Habibah saina….”
“Sai kayi me? an faɗa mara addini kayi duk abinda zakayi sakarai da idanunsa yake rufewa idan yaso abu kamar babu wani abu bay…..” “Najeeb….” Ya faɗa tare da ɗaga hannu zai daukeshi da mari me kuma ya tuna saiya fasa jikinsa yana tsuma yace “Ficemin daga ɗaki kafin na illataka…”

 

Hayaniyar tasu ce tayi yawan da har ta fito da James daga ɗakinsa koda bayajin Hausa yasan lallai koga yanayin fuskokinsu ran maza ya ɓaci ganin yanda Habeeb ke tsuma yana ruwan bala’i yana nunawa Najeeb hanya yasa James kama hannu Najeeb suka fice yana cewa “Kuma ka rubuta ka ajiye wlh indai ina raye zamu koma Dutse wlh saina rusa duk wani shirinka baka isa ka auro mana Arniya mara addini ka kawo mana cikin zuri’armu ba wawa kawai da baya lissafa rayuwa wannan abinda kake shirin aikatawa ai ya cika abin kunya ace duk matan da muke dasu a Family saika fito waje wajen ma ka rasa wacce zakaso sai BAMAGUJIYA to saika aura mu gani ai….”
A hassale yace “Idan Allah yayi saika hana ai ɗan hana ruwa gudu kawai Ni na taɓa jin wannan jaraba kun dameni na kawo matar aure na kawo wacce nakeso nakasa samowa yanzu kuma lkc yayi kwatsam ta faɗo rayuwata amma kaine na farko da zakayimin hassada to barima kaji Ni kuma naci alwashin ko zan rabu da kowa da komai saina auri Habeeba…..”
[3/31, 7:39 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

 

*Tsokaci*
Labarin BAMAGUJIYA labarine me dauke da manyan darrusa da jigogi masu muhimmanci, zakuji salonsa daban da sauran salo please kuyi hkr kubini a sannu kamar yanda kuka bini a Juhud Gidan Uncle Ruwan jira insha Allahu zan warware muku zare da abawa.

 

*Jan kunne*
Allah daya bazan dauki zagi cin mutumci a wannan karon ba babu wacce nayiwa dole ta karanta littafin nan bana son shisshigi da katsalandan cikin lamura na domin bana shiga lamarin kowa kowa yasan wannan, harkar gabana nakeyi.

 

*Sanarwa*
Kamar yanda kuka sani ne ba wani sabon abu ba littafan OUM HAIRAN na kudine zaifi ki biya ki karanta cikin kwanciyar hankali, bana Miki/maka fatan kaci haƙƙin daba naka ba domin nasan Allah bazai bari ba musamman yanzu da zamu shiga wata me alfarma.
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241. Normal group 300, Special 700.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button