Hausa NovelsZarrah Hausa Novel

Zarrah 21-22

Sponsored Links

21-22*_

 

Sake qoqarin shigar  da ita yakeyi jikinsa ta sunkuya  a hankali tanajin quncin abinda yakeyi mata A ranta tace “don Allah ka kyaleni na tafi jirana akayi….” Sunkuyawa yayi ya dora  hannunsa a bakinta yace “da hakan ma ni  meye yasa da nabaki umarnin kije kikaqi zuwa?” Yana mgnr yana dagota ta sake lumshe idonta yayi murmushi yace “ke jaruma ce  kuma mara  kunya tabbas saurin kuka bai kamaceki ba” Yana fadin haka ya juya ya fice yana cewa dole kibi abinda na gindaya miki  idan kinqi kuma ki sake shigar da kanki  sawarwarin wahala sakarya kawai”
Bayan tafiyarsa ta jima tsugune a gurin kafin ta tashi ta fice daga gdan ta nufi gdan hajar tana zuwa ta kwanta kanta yana juya mata abubuwan da suka faru suna dawo mata nan Hajar tazo ta sameta tana tambayarta meye yake faruwa ta miqe zaune tare da jan fasali tace “wai zai aureni ne matsayin baiwa Aunty Hajar wacce irin bauta ke a cikin aure bayan wacce duk wata mace takeyi a gdanta?” Shiru hajar tayi tana nazarin kalamin kafin tace “to Allah shi dai yasan karatun Kurma kedai kamar yanda Innah taketa fada miki kiyi hqr kuma kiyi biyayya Allah bazai barki banza ba zai kawo miki dauki a dukkannin lamuranki yanzun meye ya kawoshi?”

Related Articles

Goge hawayenta tayi tace “akan banje gyaran jiki bane” harararta hajar tayi tace “ai dama saida aka fada miki baki gaji da zubar da hawaye bane shiyasa kikeqin daukar shawara kije kiyi abinda kikaga ya dace dake namiji ya aureka ma don qauna yaka qare bare wannan da ya aureki don gayya kada ki saita zamanki kije kina raba hali kishiyarki ta fahimci baraka tsakaninki da mijinki kigani in zakikai labari”
Sosai kalaman hajar ya kashe mata jiki tabbas wannan way din data dauka ba mafita bace gareta miqewa tayi ta zari hijjab dinta ta fice ta hau napep ta nufi gurin kwalliyar cikin saa taje angamawa kowa kawai aka hau yimata abinka da fata me kyau itan tafi kowa daukan kyau,  hakanan bayan an gama suka tafi sai zuba qamshi sukeyi suna zuwa suka tarar ankawo kayan Dijangala da Rabi kayan sun gaji da haduwa kowa sai kodawa yakeyi.

Ko kallo basu isheta ba tayi shigewarta ta kwanta washegari aka shiga hidimar biki gadan² kowa yanata warkajami banda ita domin kuwa kowa daina kulawa tayi batada abokin hira sai wayarta itanma da taga zaa dameta take watsarwa tayi kwanciyarta a ranar ma saida sukakai ruwa rana kana ta yarda sukaje lalle da gyaran gashi yamma liss suka dawo juma’ah da safe aka kawo mata kayan dinner a wata qaramar akwati kayan sunyi kyau matuqa da yamma Aunty Aseemah ta turo aka dauketa bayan kwalliyar da sukaje akayi musu ta kuma gyarata tasa akayi mata shiri na musamman domin ita a ranta yanzun takejin qaninta yana aure domin wancan auren zabin mahaifiyarsu ne wannan kam duk da yana iqirarin bayaso tasan zabinsa ne.
Daganan aka daukesu qarfe Shidda sai gurin dinner din ashe shima gurin dinner din uku ya kama nasu shine na musamman tare kuma a lkc daya motansu ya tsaya aka bude masa ya fito itanma aka bude mata ta fito suka hade a tsakiya sauti me dadi yana tashi itadai banda hawaye babu abinda takeyi tasan daga gobe shikenan kashinta ya bushe a hannunsa,  tana tafe tana layi har suka isa mazauni anan akayi kamu da duk wata bidi’a sannan aka fara gabatar da dinner din suna zaune zaman kurame babu me cewa wani qala tsakaninsu wayarsa tayi ring ya zaro a aljihunsa ya kara a kunnensa bataji abinda akace ba tadaiji yace “ok ganinan”

 

Miqewa yayi ya dubeta kamar zaiyi mgn kamar wanda ya tuna wani abu yayi gaba abinsa tabi bayansa da kallo take MC din ya fara babatun “toh amarya ya haka kika bari ango ya fice wasa bai qare ba?” Wasu hawayen baqin ciki suka zubo mata ta miqe itama da sauri ta nufi hanyar fita da sauri Jabir ya riqota yana girgiza mata kai ta watsa masa wani kallo da yasashi sakinta yace.
“Kiyi hqr kiran gaggawa ya samu a asibiti shiyasa” bata saurareshi ba ta hankadeshi ta fice wannan abu yabawa kowa haushi a gurin da mamaki kowa nata fadin albarkacin bakinsa itakam tana fita ta tsari napep ta fada masa inda zai kaita tana zuwa gda ta fada dakin Inna ta zube a jikinta ta rushe da kuka sosai hankalin Innah ya tashi daqyar ta samu tayi shiru ta lallabata ta fada mata meye ya faru, murmushi Inna tayi tace “banda abinki Ma’uh lfy ai tafi komai kada kisa wannan a ranki komai zakiyi kiduba girman Allah ki zauna da mijinki lfy ki fahimceshi kinji” sake kwanciya tayi jikin Inna tana sauke ajiyar zuciya tace “Innah wlh inajin tsoron mutumin nan bashida tausayi kuma ni nasan ba domin allah ya nacewa aurena ba”

 

Ajiyar zuciya Innah tayi taja bakinta ta tsuke tanaci gaba da shafa bayan Asmah, a haka bacci ya dauketa lkcn goma ta wucce daqyar Innah ta gyaranta kwanciya da taimakon Innah Azeezah a daren Jabir yake fada masa abinda ya faru baiji haushin kansa ba sai ita yayita kiran wayarta tasata a silent ya kira yakai sau uku bata dagaba dole ya hqr amma rainin yarinyar yanacin zuciyarsa ranar kwana yayi yana huci Mimee na kallonsa bata kulashi ba don ta fahimci a yan kwanakin bashi da fushin daya wucce Asmah sai wajen biyun dare sannan ya kwanta shima kiran wayar bai daina ba cikin saa kuwa ta daga cikin mayen bacci bai bari tayi mgn ba yace.
“Ke wacce irin mara tarbiyya ce da zaki jizgani a cikin abokaina kinsan su waye a gurin kuma kinsan dalilin da yasa na tashi nabar gurin ne shashasha sakarya mara tarbiyya…..” Qit yaji ta kashe wayar ya miqe zaune da sauri yana kiran wayar yajita a kashe gabadaya yaja wani huci tare da cilli da wayar ya miqe kamar wanda aka tsikara ya zari mukulli sai kuma ya kalli agogo yaga uku saura wata ajiyar zuciya ya sauke ya koma ya zauna yana dafe kai yana mayar da numfashi a fili yace “saura 7 hours zakiyi bayani duk wani iskanci da kike ji dashi zaki saukeshi a gidan matsiyatan iyayenki” Komawa yayi ya kwanta

 

Tunda ta farka taga kiransa ta kasa sake rintsawa wai yar marasa tarbiyya ta jinjina kalmar nan tafi sau hamsin kafin ta sake kwanciya wannan wanne irin miji Allah ya zaba mata da wannan tunanin ta tashi kawai tayo alwala ta tayar da sallah ta jima tana roqon Allah ya cire mata jin ciwon kalaman Aseem a ranta ya sassauta mata zuciyarta ya bata ikon yi masa biyayya koda zata cutu matuqar bata sabawa shari’ah ba
Da safe kuwa kamar yanda suka tsara hakance ta faru qarfe goma masallacin dake kusa da gdan Mal Hussaini ya dinke maqil da dandazon al’ummah saida aka fara daura auren Rabi’ah da angonta Mansur sannan na Dijah da Khamal sai na Asma’uh da Dr Aseem Shaheed nan gurin ya dauki kabbara maroqa suka rinqa zubawa angwaye kirari a cikin gdan kowacce amarya murna takeyi amma banda Asmah da tayi laqwas ta lafe jikin gado idanunta na saman silling hawayenta tun daren jiya yaqi tsayawa dukkan wata kalmarsa babu me dadin da zata tuna tasata farin ciki a daidai wannan lkcn a ranta tanajin yanzu da bai rabata da Sadiq dinta ba da yanzu itama tanajin irin Happy din da yan’uwanta sukeji, itadai haka ta yini bata iya tsinanawa kanta komai ba sai kuka ko kwalliya taqiyi qarfe Hudu kuwa motocin daukanta sukazo lkcn daqyar Mal Hussaini yasata tayi wanka aikuwa tanajin ance ita akazo tafiya da ita ta rushe da kuka me dukan zuciya ta qanqame innarta tana mata magiyar kada ta bari a tafi da ita idan aka tafi da ita waye zaike yiwa Innah aikin gda,

 

Duk rashin tausayin Mudan ranar saida qanwar tasa tasashi kuka daqyar ya bambareta jikin Innah yasata a mota ya rufe tana kuka tana kiran sunansa shima hawaye yake sharewa hakan motocin suka daga suka dauki hanyar Shagari quarters horn sukayi aka bude musu get Aunty Aseemah ta bude musu bangaren amarya Asmah har zuwa lkcn shassheqar kuka takeyi sukuwa yan kawo amarya lalacewa sukayi a kallon wannan katafaren falo basu qarewa duniya kallo ba saida suka haura saman me dauke da madaidaicin falo da dakuna biyu sun bawa ido abinci sosai.
Dake ba yawane dasu ba kasancewar yace kada a wucce mutum biyar haka suka zaunarta a saman carpet din dake tsakiyar dakin jikin gadonta suka farayi mata sallama suka fice hatta Jiddarh ficewa tayi tabisu aka barta ita daya tanata aikin kukanta me ban tausayi, kusan awa uku tana zaune ita kadai tun biyar har tara sannan taji tsaiwar mota a harabar gidan qirjinta ya buga da qarfi ta koma ta sake lafewa dukan qirjinta na qaruwa daidai lkcn da taji an bude qofar an shigo an sake murda ta dakin an shigo qamshin turarensa ya daki hancinta ta sake narkewa inda shikuma ya tsaya akanta yana qare mata kallo, yafi 5 minutes yana kallonta kafin yayi wani murmushi yace “waike nan kin yarda amarya ce ke ko? Hmmm yarinya kinyi kuskure babba da kika yarda kika fado komata tabbas zaki fahimci bambamcin da kika kasa ganewa, am ba bata lkc nazo ba ga wannan ki taba nasan qila rabonki da nama tun sallah sorry karki damu da sai kin biya bana buqata kasancewar qyanqyaminki nakeji, abu daya da zan fadanki shine idan kin tashi kullum da safe kinada aiki a gdannan, ki shiga wancan part din ki gyarashi sosai sannan ki samawa matata abinda zataci am tanada qaramin ciki ne bata aikin komai saboda tanada matsalar mahaifa tana buqatar tausa kuma batason ta inji so duk sanda ta buqaci tausa kiyi mata har sai tace ya isa haka ina fatan kin gane?”……………..

 

 

_*Oum Hairan*_
[20/06 4:32 pm] Oum Hairan: _*Zarrah*_

 

_*Fauziyyah Tasiu Umar*_

 

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button