Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 37

Sponsored Links

Bude idanunta dasukai wani kala sabida kankamesun datayi cikin tsoro tayi ta kalleshi jin maganan dayayi tana kokarin fizge kanta daga jikinshi, make mata kafada yayi danko kadan bayason ta tashi daga jikinshi wani irin dadi yakeji da shauki dawasu abubuwa dayake sashi yakejin he wants the moment to go on batare daya yankeba, yanda yake kallonta yana mamatse kafa sosai dan he could feel yanda yake dripping down there, sosai taji wani tsoro dudda bata lura da wat he’s having ba dan hijabin ta yarufe mai cinya, ahankali tace “tokasakeni na zauna kaji” make mata kafada yayi hawaye suka zubo daga idanunshi a shagwabe yana karakai bakinshi kan kumatun ta da sauri ta runtse ido gam sabida yanda tsigan jikinta kewani irin tashi, ahankali yadaura bakinshi akan kumatun wani irin nishi tayi tasaki kara ahankali. “wayyo” tarike wuyan riganshi da kyau sabida yanda tafin hanunta kemata wani irin shocking, da sauri da sauri yake lasan soft kumatunta kafin ya birkito da fuskarta ahankali yana kallon fuskarta yanaji kaman kanshi zai tarwatse, lips dinta dake shining din man bakin data shafa ya kafe da ido baisan lokacin daya wani irin daura bakinshi akan bakin ba ya shiga kissing dinta da sauri har wani nishi yake yana sauke ajiyan zuciya shi kanshi baisan meyake yiba kanshi kawai ke directing dinshi yake abinda yakeyi, da duka karfinta tasa hannu ta ture kirjinshi ganin kaman zai cire mata baki hakan yasa yasake a tsorace, cikin fushi ta waska mai mari da karfi tana hararanshi sabida bakin cikin abinda yamata da sauri yadafa wajen yana kallonta, goge bakinta tayi tanaji kaman tai ihu hawaye na zuba daga idanunta kafin ta kalleshi shima ita yake kallo hanunshi dafe da kucinshi, harara tasake ballamai tama rasa mezatace mai tajuya da sauri zata fita daga dakin dan ko ina na jikinta rawa yakeyi, wani irin fashewa yayi da kuka yana girgiza mata kai cikin kuka sosai yace “don’t go please” tsayawa tayi chak tajuyo ta kalleshi batare datama san meya hanata tafiyan ba, sakin mata wani irin kuka sosai yayi daya wani irin narkan da zuciyanta yana girgiza mata kai cikin kukan yace “please don’t leave me again” karasawa ciki tayi asanyaye batare data sake kallon fuskarshi ba taja plastic chair ta zauna tareda daukan furan ta rufe ta ijiyemai akan saman drawer sai kallonta yake soyake ya shige jikinta kozaiji dadi but he’s scared bayaso tamai fada kota sake marinshi, baiso yaga tana fushi, dan kallonshi tayi ganin yanda yay wani irin zuru zuru sai goge kwalla yake yasa tadan sakin mai murmushi da sauri ya sakin mata murmushi yana clapping hands da sauri hawaye na zuba daga idanunshi yace “Hamida my wife is smiling” murmushi tasake mai tai shiru tana kallonshi dan wani irin mugun tausayi yake bata zataso taji yanda yafara ciwon nan, zataso taji labarinshi, zataso taji ya akayi shi baida lafiya and dan uwanshi is fine, hakanan takeji zata iya komi dan kawai taga yadawo kaman kowani babban namiji, sosai takejin Aadil aranta kuma tarasa mesa hakan, bude kofan da akayi yasa duk suka dago kai, Baffa ne ya shigo tareda Kaka sai Mami da Abie da Aabid dake tareda Mami dan sun shirya yanzu duk yay wani iri, ahankali ta saukar da kanta kasa tana wasa da yatsun ta, Kaka ta kalli Aadil din dake kallon Mami yana mata alamu datazo tace “sannu da jiki, Allah sarki ya rame sosai, idanunshi sun kode alamun ciwo, ya jikin?” kallonta yayi saikuma yaturo mata baki tareda mata fari da ido yace “fine” sanan ya kalli Mami batare daya kalli Aabid daketa kallonshi ba cikin tsananin farin ciki yamata alamu datazo yana mata pointing Hamida yace “Mami come and see My Hamida, tazo” ya kalli Baffa daketa murmushi yana kallonshi ganin yanda yay kaman bashiba yace “come and see her grandfather” Mami ce takaraso kusa dashi yawani irin fada jikin Mami cikin tsananin murna yana nuna mata Hamidan da hannu yana wani irin cute smile dake karamai wani irin mugun kyau, murmushi Mami tayi tace “naganta amma yanzu Hamida zata tafi itada grandma dinta she will come tomorrow okay kaga yamma tayi” kallon Mami yayi da sauri kafin ya make mata kafada yace “no i don’t want her to leave me again” ahankali Mami tace “please Aadil zata dawo kaga magrib tayi ko” make mata kafada yayi kafin yasaki kuka ahankali, Mami ta kalli Hamidan data kasa dago kanta tace “tashi kutafi daughter kinji” sakin Mami yayi yarikema Hamidan hannu da gudu yana kuka yana bubbuga kafa da sauri Kaka ta share hawayen dake neman zubo mata ta girgiza kai, kai wanan yaro na bata tausayi bana wasaba wlh, hakan yasa ta matso kusada Mami tace “kinga maman yan biyu barshi kinga sai kuka yake kar zazzabin yarufe shi kuma, anjima inyay bacci matafi” da sauri Baffa yace “a’a baza ai hakaba, magrib tayi Hajiya in aka biye tashi ba yanzu zaiyi baccin nan ba” yay maganan yana dogara sanda yana kallon fuskan Aadil din daya rirrike hanun Hamida yana kuka sosai yana bubbuga kafa, wani irin jin kukan nashi Hamida take har akasan ranta amma takasa dago kai balle ta lallashe shi sabida kunyan su Mami gashi saijan hanun nata yake yana kuka, ahankali Baffa ya dafa kafadarshi yace “zokaji” magana yamai a kunne da sauri ya kalli Baffan cikin kuka sosai yace “are you sure?” gyadamai kai Baffa yayi cikin lallashi yana sharemai hawayen, ture hanunshi yayi ya tsugunna agaban Hamidan ya daura hannayenshi akan cinyarta ya leka fuskarta hawaye nafito daga idanunshi jiyake kaman zaiyi hauka, hada ido sukayi da Hamidan, ahankali cikin kuka yace “is it true zamuyi video call?” gyadamai kai tayi dudda bamata da waya, girgiza mata kai yayi yace “please don’t go and leave me zan mutu” yanda yay maganan yana kuka saida yataba zuciyar kowa adakin da sauri Abie yafita daga dakin ya shiga restroom dayake hanyar dakin, ya shiga wani bayi da sauri yarufo kofa yaciro handkerchief daga aljihun shi ya daura akan idanunshi yahau kuka, kuka sosai bana wasaba. “wani irin kwadayin duniya yakaini na jefa d’ana wanan halin dayake ciki yau? Banrasa ci ba, ban rasa shaba, ban rasa sutura ba, inada su Suleman dasuka daukeni a matsayin dan uwan su, inada mahaifin su daya daukeni a matsayin danshi, ina da aiki na, ana biyana daidai na level din karatuna a kamfanin Baffa what push me? Wani irin greed yakaini nafada wanan halakan? Aadil na cuceka, na cuce ka bana wasaba, nacuce ka my son, i can’t forgive myself, i can’t forgive my self, my son has been suffering yanzu for more than 30yrs all because of me ya zanyi? Tayaya zan bulloma wanan tsaka mai wuyan danake? Tayaya zan hana Aadil auren nan? Tayaya zan ciremai son yarinyar nan? Tayaya zan rabashi da yarinyar nan” yabata kusan rabin awa abayin yana kuka sanan ya wanke fuskarshi ya share tass sanan yafito.

Fitowa yayi daga bayin daidai lokacin Mami tafito daga dakin hada ido sukayi da sauri ya saukar da idanunshi kasa dan bayason tagane yay kuka, hakanan kawai yaji yana wani irin jin nauyin ta dan ya mugun yaudaranta, ya cuceta itada yayan su, hanunshi dayaji an kama yasa yadago kai suka hada ido da ita, tattausan murmushi ta sakin mai tasa hannu ta shafa sajenshi cikin muryan kwantar da hankalin miji down tace “kadena damuwa Abie, Aadil dinmu zai warke da izinin Allah, watarana duk wanan abin labari zai zama kaji” gyadamata kai yayi asanyaye hakan yasa tai murmushi tace “zomuje office din Dr, kaina fito na nema dama Aadil yay bacci, Dr yace muganshi, ni inaso a sallameshi ma gobe kawai dasafe mukoma gida mai maganin da Baffa yakiramai yazo afara gwada maganin gargajiyan kafin bikin nashi ko, let’s see what Allah has install for us and banda hakama aure rahama ne let’s just team up and be praying for our children ko Abie” gyadamata kai yayi yama kasa mata magana sabida yanda jikinshi yay mugun sanyi, yasha attempting yafadi mata gaskiya but bayataba iyawa he loves Mami so much da he’s afraid of losing her, bayaso yafadi mata gaskiyan wayeshi ta tsaneshi taki zama dashi, his heart cannot bear that, ahaka suka bude office din Dr suka shiga shiga sai tunane tunane yake.

**
Gari yafara dan duhuma dan gab da isha’i suka isa gida, Mama kadaice a tsakar gidan tana nannade tabarma zata shiga daki, da sauri Hamida tai wurinta tafada jikinta tana murmushi tace “Mama mun dawo” dan murmushi Mama tayi dan sosai take fushi ta kalli Kaka data karaso wajen tace “sannu da zuwa Umma, ina yini” “yauwa Haleematu, lpy lau ina sauran yaran?” Kaka tafada tana daure fuska ta kalli Hamidan tace “ke wuce mutafi akwai gyaran dare dazan miki” tai maganan tanajan hanunta tai gaba da ita Hamida tajuyo da sauri tana kallon fuskar Mama data shige daki abinta, Kaka tawuce sasan ta da ita, akwatin falon ta nuna mata tace “ga akwatunan kayan sa ranan ki nan keda Aadil sati hudu baban ki yasaka, shi suka kawo dazu da safe shine ubanki yace na dauke ki nakaiki ki gaida yaron, ashe haka yaron ke sonki yarnan? Jibi yanda yadinga babbaka kuka dazaki tafi, Allah dai yakaimu bikin mu auramai ke yahuta da wahala wlh yaron na masifan bani tausayi” da sauri Hamidan ta kalleta dan bakaramin faduwa gabanta yayi da maganan ba ahankali bakinta har rawa yake tace “ni Kaka? Nace muku ina sonshi ne? Ninace zanyi aurene? Ba Anty Zainab za’a aurar ba kafin niba” mugun harara Kaka ta watsa mata tace “kisami ubanki kimai maganan ja’ira rasakunyan beran tanka, ai bani nabada auran nakiba, wuce kije kiyo alwala kiyi salla akwai abinda zan hadamiki kici, kuma wlh aure bafashi saisa daga yanzu andena ganin murmushi na balle wani shege ko shegiya takawomin maganan banza a gidan nan, bazan bude ido inaji ina gani kumin bukulun gidan hutuba, arziki inaji ina gani kumin bakin cikin samuba” taja tsaki tawuce tabude dakinta ta shige tana ihu tace “kuma wlh nabaki minti goma kiyi salla kizo nan wurin, gobe yar buzu zata zo tafara miki gyaran jiki” da gudu Hamida ta shige dakinta tafada kan gado wani irin kuka neyazo mata sai maimaita kalman aure take abakinta tama kasa yarda wai ita za’ama auren, to wani irin aure ma, Aadil, ita ta shirya aure ne yanzu? Tayaya zata auri Aadil ma? Haka taci kukanta takoshi saida Kaka ta kwala mata kira sanan ta tashi ta shiga bayi ta daura alwala tafito tahau kan dadduma tai salla sanan tawuce dakin Kakan tana goge kwalla.

Related Articles

Misalin 10 nadare Abba ya shigo gidan, abinci Mama takaimai, sai bayan yagama ci yay wanka sunyi shirin bacci sanan Mama ta gyara zama ta fuskance shi fuskanta adaure, ahankali tace “tundazu kadawo kai shiru ina kallonka nazuba ido inji kozakamin maganan amma kai shiru ko kala bakace min bako, ka dauki y’ata kabama mahaukaci baka fadanmin ba baka shawarceni ba saidai naji abakin wasu sabida kaganni shiru shiru kome kakeso shinakeyi ina binka sau da kafa saika nemi ka takemin hakkina a matsayina na mahaifiyar Hamida gas….” da sauri Abba yatareta ta hahanyar cewa “Hamida ba yarki bace kadai ba nima y’ata ce, sanan yanda abin nan kemiki ciwo haka nima yakemin ciwo, yakike so nayi eh Haleematu? Umma ita taje tahado komi kawai nima ganin mutane nayi yau da kayan saka rana sun taho, so kike na nabada Umma agaban su? So kike amana kallon kananun mutane da basusan mesuke yiba? Yayama zanyi eh” da sauri Mama tace “gaskiya bazan yardaba, nibazan bari Hamida na ta auri mahaukaci ba nafadama bazan bari ba kacema Kaka anfasa, nibazan bama y’ata mara lafiya ba” shima Abba cikin tsananin bacin rai kyace “sokike ta tsinemini? Ke bakiga Umman bane? Yaya zanyi da ita mahaifiyata ce dole kome tace namata biyayya, yaya zanyi Haleematu fadamin” fashewa da kuka sosai Mama tayi takasa cewa komi hakan yasa ya dafe kanshi yay shiru yasan Mama da mugun hakuri kuma yasan da gaskiyan ta amma yaya zaiyi? Shi kanshi abin yafi karfinshi, ahankali ya janye hanunshi daga kan
goshinshi ya matsa kusa da Mama ya rungumota jikinshi yana shafa bayanta yana jijjigata harta rage kukan ahankali yace “kiyakuri Haleematu, i need your support more than anything ayanzu, kece karfi na, idan kika karaya haka ninai yaya eh? Nasan Umma bata kyautaba amma kiyakuri, bamu miki adalci ba amma kiyakuri uwata ce dole nabi abinda tace, addu’a zamubi yarmu dashi, babu wanda ya isa yahana kaddara faruwa, kuma rabo na kisa bamusan me Allah yagani yahada suba, kawai mubisu da addu’a kinsan Allah na karban addu’an uwa akan yaranta, mumata addu’a kinji muga me Allah zaiyi, am sorry for hurting you kinji best wife, stop crying” gyadamai kai Mama tayi ahankali hakan yasa ya sumbaci gaban goshinta yasake rungumeta da kyau yace “akwai wasu kudi danake expecting once anbiyani zan baki kije ki siyo mata duk abinda yadace kinji” gyadamai kai tayi nan yadinga bata kalamai masu ddi da sanyaya rai harta sauko sosai ta share ta barma Allah komi kawai ta tasa addu’a agaba.

 

***
Kwanaki nataja sosai gidaje biyun aketa shirye shiryen biki, gabaki daya Aadil baida lafiya magungunan hausan da Baffa yasa akemai da in yasha ma amai yakeyi gashinan gashinan ne kawai mugun so yake yaga Hamida bana wasaba, gashi kullum yana dakin Mami inyaga Aabid wani irin tsoranshi yakeji yayta tuna yanda yamai mugun duka yay lamo koya kulle ido, Aabid gabaki daya yadawo wani iri shima saiyahau ciwon abun yama Mami yawa ga Aadil ga Aabid Abba yay wani irin ramewa shima haka dai suka dinga lallabawa Dr na zuwa treating nasu a gida, Aadil harda drip yasha kusan hudu.

Kaka takawo yar buzuwa anata ma Hamida gyaran amare bana wasaba, gabaki daya Hamida duktai zuru zuru kullum saitaci kuka, ko kadan batason auren nan dudda kullum tunanin Aadil take bana wasaba takuma rasa mesa take tunanin shi, tasan yana chan yana nemanta yanzu yana kuka rabonta dashi tun yana asibiti.

Kuka, kukane aikinta gashi tai wani irin kyau tai haske bana wasaba, fatarta dama yanada taushi saiya kara wani extra ordinary taushi, ga sheki ga kamshi datake yi, ana saura sati daya biki family Aadil suka kawo akwati nagani nafada guda 12, Kaka harda rawa tama manta da Faruk da rabonta dashi yafi sati, dasuka tashi tafiya aka hadamusu shatara na arziki, Hamida kin duba kayan tayi Zainab da Ihsan sai rawa suke sunata murna Hamida zatai aure, Mami dai kullum bayan magrib takan koya mata yan dabaru na zaman gidan miji, ko kadan tarasa sukuni bama ta iyacin abinci hakan yasa wani irin ciwo yakamata tafara zazzabi bana wasaba, har aka fara sha’anin biki yayyinta duka harda su Ayush duk sunzo sai mamakin aurenta suke yaushe Hamida tai miji, yaushe tai saurayi kawai sunji bikin ne, ranan walima saida Abba yakira wata likita sabida yanda ta dinga kwara amai hankalin Mama duk yabi yatashi sai sannu kowa yake mata.

Ana gobe daurin auren Abie yakusa karamin hauka adakinshi, baisan me Ozo zaimai ko Aadil gobe idan an daura auren ba, baisan wani hukunci Ozo zai yankemai ba, dudda dai har yau baisan meye dalilin dayasa Ozo yace kar Aadil yasake yay aure ba amma yadamu, abinda haryau yake bashi mamaki shine Ozo yariga ya maidashi yaro ababba to menene dalilin shi nacewa karya sake yabari yay aure, kodai aure zaisa Aadil yadawo normal ne? Ajiyan zuciya ya fuzar yana fifita kanshi da hulan daya zare daga kanshi yacigaba da tunani, gashi yanzu Ozo bai bayyanar mishi ba koda warning ne yabashi ba, kawai yay shiru yasakamai ido kome yake planning oho.

********
Hausawa sunce rana bata karya!
Yau asabar misalin karfe biyu na rana dubbanin jama’an dake cikin babban masallacin janbulo suka shaida dauren auren Hassan Abdullahi Aadil da Amatullah Isma’il akan sadaki dubu dari inda jama’a da dama suka hallarci auren suka shaida, Aadil dayaci gayu sosai ya rame kaman bashiba yana tareda su Baffa da Suleman dan tun safe yau ba’aga Aabid ba sai murna yake yana tsalle, yau yay wani irin kyau na musamman yawani irin cika yafito sak cikakken namiji dashi kodan yau auren shine oho amma dai yau akwai wata irin haiba da kwarjini daya kara na musamman dahar abin saida yabama Baffa mamaki yadai share yacigaba da attending to jama’a, Abba ma sai neman Faruk yake bai ganshi ba dan rabon shi da Faruk tun sati daya daya wuce.

Misalin karfe nine nadare akazo tafiya da amarya Hamida kuka kaman zata shide harsaida tasa Mami kuka da kyar yayyinta da yan uwanta suka rakata gidan mijinta daya mugun hadu.
[11/28, 9:58 AM] +234 701 218 1461:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button