Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 27

Sponsored Links

28 – 29

_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta keda Allah_

_in kinason this book zaki turo 300 ta 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_

Related Articles

_you can also send MTN card 300 ta watsapp number na 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_

_masu fitar min da novel waje kuda Allah, kunma kanku_

 

Sosai Aadil yake clapping hands dinshi yana murmushi yana dariya kaman bashine yagama kuka yanzun nan ba, wani irin murmushi Hamidan tayi tana kallonshi dan jitayi dariyan dayake mata means everything to her, looking at the way he’s doing yanzu yana smiling da swollen eyes dinshi yasa taji ta manta da duk wani bakin ciki da tsoron datake ciki all she sees is Aadil yana mata murmushin dake sanyaya mata rai tama manta dasu Mami da Abie dake wurin, hanunta ya karba da sauri yana kallo, zaro ido tayi tana kallonshi asanyaye, yatsun ta yafara kirgawa yana murmushi sosai yace “your fingers are fine, and they’re so fair” dan murmushi tayi tanajin wani irin tausayinshi ta mikomai dayan hanun ahankali, da sauri yahadasu yana kirgawa yana dariya sosai, shiru Mami tayi takama habanta tana kallon Aadil din da kyaykyawan yarinyan dayake wasa da yatsunta suna magana kasa kasa dan kosu basujin mesuke fada Aadil sai dariya yake kyalkyacewa kaman ba gobe. Dan lumshe ido yafara yakai hanunshi yana sosa saman idanunshi hakan yasa tace “you are sleepy” gyadamata kai yayi ahankali yanajin wani iri sanyi da sauri ta nunamai kan gadon tace “zoka kwanta” make mata kafada yyi yace “you will run away” da sauri ta girgiza mai kai tanajin wani iri kaman tamai kuka tace “bazan gudu ba i will be here, zoka kwanta” tashi yayi ahankali kanshi narawa jikinshi namai mugun ciwo ya kwanta akan gadon yasaka kanshi ta wajen saitin kanta yana kallonta, ahankali yamiko mata hannu yace “promise u will not go away” yatsarshi dayake miko mata ta kalla tace “yes” murmushi yayi dayama fuskarshi wani irin kyau dawata irin murya kaman na dan karamin yaro yace “thank you Hamida my wife” yay maganan yana kamo hanunta yarike gam ya lumshe ido yana hamma wani irin wahalallen bacci yay gaba dashi, Sai alokacin ta sauke wani irin ajiyan zuciya, “sannu da fama” Mami tafada ahankali, da sauri ta dagokai ta kalli Mami wani irin kunyan matan taji tanaji hakan yasa ta sunnar da kanta kasa da sauri tanajin wani irin kunya dakuma nauyinta, ahankali tace “ina yini” murmushi Mami tayi tace “lpy lau, mungode sosai kinji Allah yabaki lada a ina kika ganshi?” kanta akasa batare data dago ba tace “awanan anguwan na ganshi yanata bina na tambaye shi inane gidan su baifadamin ba tun jiya nasoma yadawo gida” ahankali Abie yace “angode yakamata kizo kitafi gida kar’a nemeki” dan kallonshi Mami tayi gyadamata kai yayi yatashi Mami ma ta tashi tana kallonta tace “zauna bari na kawo miki abinci da mayafi idan kikaci saimu tafiko” gyadamata kai tayi ahankali a kunyace, Mami tajuya tareda Abie suka wuce suka fita daga dakin.

 

Ahankali ta waigo ta kalli fuskarshi bacci yake sosai yana sauke ajiyan zuciyan kuka dake wani irin taba ranta yay wani irin kyau gashin idonshi dogaye bakake sosai sunyi lub lub dasu, hancinshi dogo dan siriri ya tsaya a fuskanshi das, sai lips dinshi pink sosai gasu sunyi moist, shiru tayi tana kallonshi kirjinta nawani irin bugawa, ahaka idan ka ganshi bazaka taba cewa baida lafiya ba, yanada wani irin kwarjini a fuska bana wasaba dabaka iya jure kallonshi for long unless idan yana haukanshi, janye idanunta tayi daga kan fuskarshi jin yanda gabanta kefadi tajuya tana kallon dakin, dakin hadadde ne bana wasaba gadon makeke ne sosai guda daya an shimfida white bedsheet ajiki, juyawa tayi tana kallon bangon dakin ta saukar da idanunta kan katoton hoton bangon dake makale a bangon dakin, inda Aadil din da Aabid suke a tsaye sunsa fararen shadda iri daya kaman ma ranan salla ne dan Aabid na rike da dadduma, shiru tayi tana kallonsu ta iya gane bambamcin sune sabida chocolate da Aadil yake rike dashi a hannu kafe Aabid tayi da ido wanda ke rike da dadduma tana tuna ranan dasuka hadu dashi a lagos, ahankali ta lumshe ido kafin ta bude tasake kallon fuskar Aadil ajikin hoton tana jin wani irin sanyi na shiganta. “baki taba sanin yan biyu bane bako?” taji magana akanta da sauri ta dagokai Mami ce ta shigo dakin wayansu masu aikin gidan biye da ita guda biyu suna dauke da tray a hannu, nuna masu gabanta Mami tayi tace “ku ajiye anan” ajiyewa sukayi suka wuce suka fita daga dakin sukamaida kofa suka rufe, ahankali Mami ta zauna a gefenta taidan murmushi ta kalli fuskar nata tace “twins ne wanan ne babba shine Hassan” ta nuna Aadil dake bacci tadan shafa kanshi tai shiru jin jikinshi da zafi, ahankali ta janye hanun tace “dayan kuma shine Aabid, dukansu haka sukeda zuciya barin ma wanan” ta nuna Aadil tace “yauma bansan meya faruba, dan Aabid dawuya kiga fushin shi, inata miki surutu ko baki fadamin ba ya sunanki?” ahankali kanta akasa tana wasa da yatsun ta dan hakanan taji tanajin kunyan matan tace “Hamida” ahankali Mami tace “suna mai dadi amma asalin sunanki kenan?” girgiza mata kai tayi tace “sunana Amatullah” “masha Allah wat a nice name, wani mataki kike a karatu?” wasa ta shigayi da yatsunta tace “100 level Islamic studies” “masha Allah, oya ci abinci karya huce kinji daughter na” gyada mata kai tayi ta kalli uban tilin abincin tarasa mema zataci da kyar ta mika hannu tadau spoon ta dau plate hanunta na rawa takasa diba, ganin haka yasa Mami ta karba tace “kawo nai serving dinki tunda kunyana kikeji” zuba mata white rice din Mami tayi a plate tazuba pepper soup din asama ta mika mata ahankali ta karba tace “Allah amfana” murmushi Mami tayi dan taji dadin addu’an tace “Ameen Amatullahi” diban abincin tayi tai Bismillah takai baki duk Mami na kallonta tana yaba natsuwan yarinyar da kyar ta iya tai 5 spoon sanan ta ijiye ta dau ruwa tasha batare data taba juice din wurinba tace “nakoshi nagode zan tafi” “kai dan Allah daughter bakici dayawa ba” girgiza mata kai tayi tace “nakoshi” gyadamata kai Mami tayi tace “Tom ina zuwa bari nazo saimuje mu saukeki daganan mayima iyaynki godiya” gyadamata kai tayi gabanta na faduwa, fita Mami tayi daga dakin ba jimawa yan aiki suka shigo suka kwashe kayan abincin, juyawa tayi tasake kallon Aadil dake bacci hakanan taji bataso ta tafi ta barshi tasan idan yatashi saiya nemeta, kafeshi tayi da ido tana kallonshi daidai lokacin Mami tabude dakin da sallama ta shigo kallon Mami tayi, Mami takarso ta mika mata wani hadadden black gyale tace “gashi ki yafa” karba tayi kanta akasa tace “nagode Mum” murmushi Mami tayi batare datace komiba, ahankali tamike tsaye ta yafa gyalen kaman yanda taga su Zainab nayi sosai gyalen yamata kyau Mami tace “masha Allah yako miki kyau, muje” gyadama Mami kai tayi Mami tai gaba tana binta abaya harsunkai bakin kofa takasa daurewa saida tajuyo ta kalli Aadil din dake bacci sosai da sauri ta goge hawayen dake neman zubo mata tasakai tafice tarufo kofan ahankali suka fito tsakar gida sai sunnar dakai take Mami ta bude mata bayan mota ta shiga ta zauna Mami ta zauna agaba Abie yatada motar yaja sukabar gidan, sosai gabanta ke faduwa itato ina zata kaisu yanke shawara tayi gidan Anty Lami haka tadinga nuna musu hanya har zuwa gidan Anty Lami dake ta wuraren gwamna road har zuwa kofar gidansu suka sauko daidai lokacin ana kiran sallan magrib fitowa sukayi daga motan Abie yarufe motan ya kalli Mami yace “ku shiga ciki bari in shiga masallaci” ya mikama Mami key dan akwai abubuwa acikin boot din, yanda ta tsaya gefen Mami kanta akasa tana wasa da yatsunta yasa Mami tace “muje daughter” gyada mata kai tayi tabude kofar gate din ahankali ta shiga Mami biye da ita.

 

 

Babu kowa a hadadden tsakar gidan sai tulin textbooks dake kan wani table da alamu yaran homework suke sun tafi masallaci, sallama tayi ahankali tabude falon ta shiga babu kowa ciki ta kalli Mami dake tsaye tana kallonta tace “ki shigo Mum” gyadamata kai Mum tayi tai sallama ta shiga ta zauna akan kujera hakan yasa tai ciki da sauri sallama tayi agaban dakin Anty Lami daidai lokacin anty Lami na sallame salla ta juyo da sauri ta ware ido tana kallonta daga sama har kasa takama haba cikeda mamaki tace “Hamida!” kasa amsawa Hamida tayi saima kasa datai da kanta tana wasa da yatsunta, cikin mugun takaici Anty Lami ta tashi daga kan dadduman tana gyara daurin zanin jikinta tace “ba magana nake mikiba kinyi shiru tun safe mahaifiyar ki ke kirana taji kokinzo nan bakizo ba Hamida, ina kikaje kodai mazan kika farabi da gaske? Ina kikaje Hamida” girgiza matakai tayi ahankali tasa bakin gyalenta ta share hawayen dasuka zubomata, tsayawa kallonta Anty Lami tayi ta rungume hanunta akan ciki cike da mamakinta tace “hala namiki wani abune dakike min kuka?” girgiza mata kai tayi ahankali. “to menene?” cikin muryan kuka tana goge ido tace “ana nemanki a falo” zaro ido Anty Lami tayi tace “wakika kawomin gida?” tai maganan tana zuwa hanyar falo da sauri ta yaye curtain ganin kamilalliyar mace cikin shiga ta alfarma zaune akan kujera tana fira da yaranta maza guda uku su Ra’is dasuka dawo daga masallaci tana murmushi yasa tasaki labule da sauri ta kalli Hamidan dake gefen ta tace “ke wacece wanan ni yatsu? A ina kika samo wanan hajiyan Hamida?” ahankali tace “nima bansan suba, maman yaron ne” da sauri Anty Lami tace “yaro? Au wai wanda aka ganku tare?” gyadamata mata kai tayi ahankali da sauri Anty Lami ta yaye curtain tafita fuskarta cikeda murmushi tace “barka da zuwa” dagokai Mami tayi da sauri ta mike tsaye, da sauri Anty Lami ta nuna mata kujeran tace “please sit, ki zauna dan Allah” zama Mami tayi ahankali tace “ina yini ina gajiya” cikeda fara’a Anty Lami tace “Alhamdulillah, maraba, sannu dazuwa, Hamida” ta kwalama Hamida kira ta kalli yaran nata dake kallon cartoon tace “kutashi kutafi dakinku, ku kiramin Hamida daga nan” tashi sukayi sukai ciki ba’a jimaba Hamida tafito kanta akasa Anty Lami tace “je kawo drinks da snacks mubama bakuwar mu ko” da sauri Mami tace “haba haba wlh bakomi dama har gida nazo namuku godiya akan karamcin da Amatullah daku kukama d’ana mara lafiya nagode, nagode, ubangiji Allah saka da alkhairi” daidai lokacin mijin Anty Lami ya shigo tareda Abie aka zazzauna ana gaggaisawa Hamida da kanta ke kasa ta kawo drinks ta ijiye da snack takoma ciki, ruwa kawai Mami tasha Abie kuma sai hira yake da mijin Anty Lami kaman sunsan juna nan Mami tabama Anty Lami labarin yanda Aadil din yafita daga mota haryasa tai hatsari, sosai Anty Lami ta tausayama yaron dudda bata ganshi ba sai bayan sallan Isha sanan sukai sallama Anty Lami ta kwalama Hamida kira. “Hamida” fitowa tayi kanta akasa Anty Lami tace “zasu tafi” dan dagokai Hamidan tayi ta kalli Mami a kunyace tace “Allah ya kiyaye hanya Mum” murmushi daga Mami har Abie sukayi sukace “mungode Hamida” suka wuce suka tafi har gate suka rakasu sanan suka dawo ciki ko minti daya basuyi da zama afalo ba wasu yara suka fara shigo da kaya niki niki wasu manyan ledoji ne guda uku na hadaddun turare da gyaluluwa, saikuma na atampopi guda uku da lace guda uku, dayan kuma na su chocolate da lot of cookies da sauri Anty Lami tace “inaa gaskiya bazamu karbaba haka akeyi” binsu akayi da kayan amma har sun tafi haka aka dawo da kayan.

Wanka tayi adakin Anty Lami takawo mata wani free doguwan riga blue tace “gashi nan kisa inkin gama kizo dakin Abban su yana nemanki” tajuya tafita, ahankali takarasa gaban madubin dakin tadau man Anty Lami ta lakato da hannu ta kalli Madubin zata shafa fuskar Aadil tagani ajiki yana turo mata baki yace “why did you leave me?” da sauri ta juyo ganin babu kowa a wurin yasa taji wani irin sanyi ajikin ta, jikinta yay wani irin sanyi taji jikinta dukya mutu, ahankali ta juyar da kanta tafara shafa man ajikinta kaman ance ta kalli madubin, Aadil tagani ta madubin yana mata kuka ahankali yana mata alamu da hannu datazo cikin kuka sosai yace “please come back Hamida my wife, I need you in my life, u promise you will not leave me” da sauri tasake waigawa ta kalli bayanta babu kowa a wurin wani irin fadawa kan kujeran gaban madubin tayi ta kifa kanta akan slap din madubin jikinta yay wani irin sanyi, kwala mata kira da akayi yasa ta dago kanta da sauri tace “gani nan zuwa” man dabata shafa ba kenan ta tashi ta dau doguwar rigan ta zira tafita.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button