Hausa NovelsMunayamaleek Hausa Novel

Munayamaleek 20

Sponsored Links

XX….
(20)

MunayaMaleek is 500 via 3200689860 Haruna Rukayya first bank, shaidar biya ta Whatsapp number dina 07082281566.

A farfajiyar gidan doctor Aaban Shakur
yayi parking kasancewar a motar sa suka taho.
Ya bude wayar sa ya kira number’n barrister Abrar bayan ta daga ya shaida mata yana waje tare da bako, ta bashi izinin shigowa.
ita kadai ke zaune a falon tana duba littafin Bulugh al-Maram ta amsa sallamar su tana rufe littafin.
Bayan sun zauna, suka gaisa da barrister sannan ta mike ta kawo musu small Chops da drinks, suka mata godiya, bayan ta zauna doctor Abbas yace “barrister Abrar wanna sunan sa Abdulshakur, kanin wanda yayi wa Munaya….” Sai ya tsaya domin ya rasa yanda zai karasa maganar saboda nauyin Shakur ɗin.
Barrister Abrar tayi murmushi tace “oh i understand, sannu da zuwa”
Cikin jin nauyi Shakur ya amsa mata.
DOCTOR ABBAS ƴace “Ina yaran ne ban ji motsin su ba”
“Sun tafi islamiyya har junior, pure heart yace ya fara zuwa ko bakin sa ya bude, da kyar aka raba sa da mutuniyar sa, har mamakin wanna Shakuwar tasu nake da Munaya, bari na kira ta” da fada tana mikewa, tun kafin Shakur ya kasa hakuri ya tambaya domin ta lura da take-taken sa.
Shima doctor Abbas yana mamakin wanna Shakuwar tasu, saboda junior ya kasance yaro mai kin mutane.
Mami na shiga ta tarar dashi Munaya zaune kan sallaya, ko cikin hijab ne ramar ta bata buya ba, sai Cikin ta dake neman rinjayar ta saboda nauyi, a nutse ta dago kanta tana sakarwa barrister Abrar murmushi jin tana tsokanar ta da cewa dan junior ya tafi islamiyya shine ta kulle kanta a daki

Related Articles

“TOH taso doctor Abbas yazo tare da bako” ta fada tana fita Daga dakin, ta koma wajen su tace “tana zuwa barin hau sama”
“Toh Nagode” doctor Abbas ya fada yana tunanin irin reaction din da Munaya zata nuna idan ta gan Shakur.
Munaya kuwa ta lallaba da kyar ta mike tsaye, sam bata kawo komai a ranta ba, a tunanin ta abokin doctor Abbas ne suka zo tare, hijab data yi sallah ta fita da shi, wands milk color ne ya saukar mata har kasa, kanta a kasa ta fito tana tafiya a hankali, da ba dan girman cikin ta ba sai mutum ya dauka bata son taka kasa saboda yanda take daukan every step slowly.
Tun kafin ta ƙaraso Shakur ya zuba mata ido, wato wani mugun tausayin Munaya ya kara mamaye zuciyar sa, sam bai yi tunanin Abin ya kai haka ba sai yanzu daya ganta a zahiri, lallai dan’uwan sa bai kyauta ba, amma ya zai yi, kaddara ta riga fata, he can’t changed anything, burin sa daya a yanzu Munaya ta kasance cikin farin ciki, but he can’t do it alone, Maleek kuma baya kaunar jin ko sunan ta, tunanin sa ya katse ne a lokacin daya ji sanyayyar sallamar ta, dole ya dawo Cikin tunanin sa.
Cikin sauri Munaya ta dago kanta jin muryoyi biyu sun amsa sallamar ta, murya ta biyu ce ta ja hankalin ta, kamar ta san mamallakin ta, idanun ta suka fara sauka kan fuskar Shakur, ta daskare a tsaye because she wasn’t expecting him, ta tsakankanin lips din ta ta furta “ya Shakur!” hawaye suka zuwa mata masu dumin gaske, ta tuno ranar da duk wani farin cikin ta ya kau, ranar data rasa kanwar ta da kuma budurcin ta, ta tuna da niyyar neman taimakon Shakur ta fita, amma sai ta hadu da azzalumi Maleek daya tarwatsa mata rayuwa, ta san da a ce da Shakur ta hadu a ranar zai taimaka mata, ko da Amnah bata rayu ba, amma data tsira da budurcin ta, amma ta yi zero, zeron ma behind the decimal point, ta kasa rike hawayen ta, ta ɗora hannun ta kan fuskar ta ta saki kuka.
Cikin damuwa Shakur ya mike zuwa gare ta, fuskar sa na fidda zallan damuwa yace “karki yi kuka, kiyi hakuri Munaya, i understand have you feel kiyi hakuri kinji”
Hakurin da yake bata sai ya kara karya mata zuciya, kukan ta na karuwa ta samu kujera ta zauna saboda yanzu bata iya jimawa a tsaye.
Hannu doctor Abbas yayi wa Shakur kan ya barta, suka yi shiru suna jin yanda take kuka wanda duka ya sosa zuciyoyin su, amma gwara su barta din, sometimes yin kuka na rage wa mutum damuwa dake dankare a ransa, Munaya ta kwashe mintuna bakwai tana kuka kana tayi shiru ta shiga sauke ajiyar zuciya.
Mazan biyu suma suka saki ajiyar zuciƴa, ganin tayi shiru, Shakur yace “I’m sorry Munaya kin ji, naji dukkanin abinda Ya faru, on behalf of me and my brother ina Miki taaziya Allah ya jikan ta, ina kuma kara baki hakuri kan abinda MALEEK ya Miki, da a ce akwai kalmar data fi hakuri daraja da da ita zan yi amfani, kiyi hakuri, dan Allah, ki yafe masa, Allah ya sauke ki lafiya”
Murmushi mai ciwo tayi, Shakur na da wata zuciyar zinari, bai mata komai ba yana bata hakuri, lallai ta kara jinjina wanna kaunar da yake wa dan’uwan sa, maganar yafiya kam babu shi tsakanin ta da Maleek, she so
Much hate him with passion, hakan kuma ya shafi abinda ke cikin ta.
Cikin raunin murya tace “ya Shakur baka min komai ba, dan Allah ka daina min maganar sa, Nagode” ta fada wani kukan na kokarin zuwar mata.C
Cikin sauri ya ce “i understand, bazan kara ba”
Doctor Abbas dake kallon su tun dazu yace “Toh mai arahar hawaye babu gaisuwa?”
Cikin jin kunya tace “ya Abbas ina wuni”
A takaice dai hira suka dinga yi, musamman Shakur Burin sa ya sata farinciki, ba laifi kuma ta saki jikin ta, sun ɗauki a ƙalla awa ɗaya a gidan kana suka mike domin tafiya, Shakur ya yi wa Munaya alkawarin zuwa bayan an kwana biyu ya duba ta tunda ya gane gidan.
Bayan kamar mintuna biyar da fitar su, Munaya ta bi barrister Abrar, tana ganin ta tace “zauna, babu aikin da zaki taya Ni na yafe wallahi” kasancewar tana gyara wardrobe ne.
Murmushi Munaya tayi ganin yanda mami tayi maganar, ba musu kuwa ta Zauna.
Suka yi shiru zuwa wani lokaci kana barrister ta yi breaking silence din da fadin “wanna Shakur din is Nice from all indications, unlike dan’uwan sa”
“Hakane Mami, ya Shakur yana da kirki sosai, shi naje samu a ranar da Amnah zata rasu amma….” Sai ta kasa karasawa, ta hadiye wani abu mai tauri ɗaya tsaya a makoshin ta.
“I understand Munaya, har da kuruciya ya sa kika amince masa, komai ya riga ya faru sai dai Allah ya tsare gaba” barrister Abrar ta riga ta fahimci abinda Munaya zata fada, domin Allah ya bata baiwar da ko mutum bai gama magana ba zata san meye azuciyar shi.
“Abu na biyu da zan faɗa miki shine, kiyi kokari ki rage kiyayyar da kike wa abinda ke cikin ki, na san bakya kaunar sa, amma ki san wani abu ɗaya, that child is innocent, ba shi da laifin komai, kada ki Bari laifin baban sa ya shafe shi, kice gatan sa, ke zaki bashi soyayya irin ta uwa, idan kiyayyar da kike masa ta sa tasa kika gaza bashi soyyaaya, ki sani hakan zai yi affecting rayuwar sa ko rayuwar ta, kin san lalacewar da rashin kulawa da nuna soyayyar uwa ke janyo wa d’a kuwa? my dear i know kin yi kankanta da duk wanna abun, amma girma ne zai hau Kanki yanzu,nuna kiyayya ga wanna d’a bazai Sanja komai ba, ki sani cewa jarirai na jin magana, bar ganin yana ciki, duk abinda aƙe yana ji, wanna kalma ta tsana da kike fada yana ji, yana kuma zaune a kwakwalwar sa, idan yazo duniya kika cigaba da fadin hakan, har ya girma me kike tunanin zai faru? Shawara ta a gare ki shine ki daina wanna kiyayyar da kike masa kin ji ko?”

“TOH Mami” Munaya ta fada a hankali kanta a kasa, tana ƙoƙarin danne zuciyar ta kar tayi kuka, suna a haka yaran suka shigo dakin da gudu, Kowa na kokarin fara biya mata karatun da aka musu, mutumin ta junior kuwa manne mata yayi, zuwan yaran ya rage mata damuwa.
***
Kwance take flat fuskar ta na kallon sama, sai faman murkususu take, tun daga lokacin da cikin ta ya shiga wata na bakwai da yan kwanaki yake takura ta, bata iya Bacci, mikewa tayi zaune a kan gadon ta saki wani Marayan kuka, ji take tamkar ta cire cikin ta huta, har wani seizing numfashin ta yake, iskar da take shaka taji Kamar ya mata kadan, ta mike tsaye domin zaman ma babu dad’i, hannun ta kan kugun ta da take jin kamar zai balle ta shiga zagaye dakin hawaye Masu zafi na cigaba da zuba a idanun ta, ta koma bakin window ta tsaya tana kallo farfajiyar gidan, kanta ta ɗora a kan glass ɗin window, tunani kala-kala na zuwar Mata, daga baya ta dawo bakin gadon ta zauna, ta tuna year’s back bata da damuwar komai, bata san wata kalma wai ita damuwa ba, ta lumshe idanun ta tace “i hate you Maleek, bazan taba yafe maka ba” sai ta saki wani kukan mai haɗe da shesheka… A hankali ta fara gyangyadi a zaune, idan cikin ya sake wata irin motsawa sai ta farka, haka ta kasance har asuba, ta lallaba da kyar tayi alwala ta yi sallar ta a zaune bayan ta iddar, ta jingina bayan ta da gado, wani baccin ya sake daukar ta gwanin tausayi.
Har ƙarfe takwas Munaya shiru hakan yasa Mami lekowa ta kuwa hango ta ta sulale tana bacci, cikin tausayin ta ta karaso zata gyara mata wuya sai Munaya ta farka, Mami ta ɗan ja da baya kadan tace “sannu kin tashi?”
“Eh na tashi Mami, good morning”
“Morning dear, sannu ya jikin?”
“Bana iya Bacci Mami, ko ina na min ciwo, ga cikin sai yawaita motsi yake” ta fada idanun ta na yin raurau alamun tana daf da sakin wani kukan.
“Sorry, Dole zaki fuskanci hakan tunda cikin ya fara tsufa, ko ina cin dabino ne?”
“A’a” ta furta a sanyaye.
“Yawwa karki ci yanxu, kin san babyn shima ya kagu ya shaki iskar duniya, dabino kuma na karawa mahaifa zafi, sai Wajen ya musu zafi sosai su shiga neman hanyar da zasu fito, shiyasa ba a son mai ciki da bata kusa haihuwa ba ta ci dabino saboda zai saka mutum yin labour bai shirya ba sai ki ga mace ta haifi premature baby, Amma idan ciki ya tsufa sosai ana son mace ta yawaita ci domin yana saka nakuda yazo da sauki, sannu ki tashi ki yi wanka ki zo muyi breakfast”
“TOH Nagode mami” Bayan fitar mami ta mike tsaye ta shiga toilet, tayi wankan ta, cikin wani maternity gown Cotton mara nauyi ta shirya, wanda Mami ce ta siyo mata, Sam bata da karfin taje gashin ta hakan yasa ta dauki hijab fari ta saka.
Tana fitowa falon shiru, kasancewar yaran sun tafi Makaranta, ta hango barrister da doctor a zaune, yana bata chips a baki, sai ta ji kunya ta lallaba zata koma ta ji Muryar doctor Aaban yace “ƙaraso mana” dole ta dawo, ta tsaye daga dan nesa ta gaishe shi, cikin kulawa ya amsa mata.
Barrister Abrar tace ” ƙaraso Munaya ga breakfast din ki nan”
Kanta a kasa ta ƙaraso ta zauna, ba tare ds kalli mami ba tace “su miemie sun tafi makaranta kenan”
“Eh sun tafi, sun so zuwa wajen ki nace kar su dame ki”
Munaya tayi murmushi tana tsakuran abincin kadan kadan, doctor Aaban ya mike zai tafi hospital din sa, Munaya ta masa a dawo Lafiya, barrister Abrar ta raka mijin ta ta dawo ta zauna a dining din tana korafin Munaya bata cin abincin, Munaya tayi murmushi kawai, barrister Abrar ta mika mata kwalin waya tace “gashi in ji pure heart, Yace a baki, ko da wani abun zai taso Bama gida sai ki kira”.
Munaya ta rasa bakin magana, karamcin mutanen nan gareta bazai lissafu ba, ita kam me zata yi da waya yanzu, amma zata karba kada su ji ba dad’i, a fili ta furta “mami shine baki gaya min na masa godiya ba ”
“Ai godiyar ce baya so shiyasa yace na baki idan ya tafi ”
“Nagode sosai, Allah ya saka muku da alkhairi Mami” Munaya ta fada tana kokarin russunawa duk da girman cikin ta, barrister ta hana ta, tana fadin “Ameen Ameen, zan saka miki chargi anjima Sai na tura miki wasu apps masu muhimmanci wandanda zaki karu da su, sannan zaki dawo dakina da kwana yanzu har ki haihu saboda ko a cikin dare zaki bukaci wani abun”
“A’a Mami, zan iya kwanciya ni ɗaya kada na takura ki, tunda ma ga waya”
“A’a ba zai yu ba Munaya, kina bukatar wani a kusa dake”
Shiru Munaya tayi ita sam bata son shiga hakkin mutum. Sai tace “TOH Mami ki bani miemie tana taya ni kwanciya idan yaso ko wani abun ne sai ta kira ki”
“Toh shikenan” Mamin ta fada tana ƙoƙarin buɗe kwalin wayar domin ta sa mata a chargi.
*BAYAN SATI DAYA*
A duk zaman da barrister da Munaya zasu yi sai tayi ƙoƙari wurin cusa wa Munaya son babyn cikin ta, domin ta lura a matsayin ta na wacce ta girmewa Munaya ba karamin tsana ta ɗora wa babyn da ko duniya bai fito ba, kuma ba laifi maganganun na shigar ta a hankali ba tare da ita kanta ta san da hakan ba, Sai dai abu daya ne bata jin zata manta ko yafewa har abada ba, MALEEK!!!
Kiyayya mai yawa take masa.
Kamar yanzu zaune take a kan sallaya ta tuna wata hira da suke da barrister Abrar jiya, “na ji dadi da baki kulla ce ko jin haushin dan’uwan sa AbdulShakur ba, hakan abu ne mai kyau, kuma in next week za’a aika masa sammaci, ina so mu gama da shari’ar da nake yi yanzu ne, jibi za’a yi zaman karshe a kotun”
Wani murmushi mai ciwo Munaya tayi tace “mami bazan taba jin haushin sa ba, saboda bai min komai ba, ya Shakur na da kirki sosai da tausayi”
Dawowa hayyacin ta tayi ganin kuka na neman kufce mata, doctor Abbas ya zo jiya ya gwada bp din ta, yayi mata fada sosai ganin baya wani sauka, ya kuma yi gaya mata illolin dake tare da hakan idan ta zo haihuwa matukar bata daina tunani ba.
Tunani kam Bata san ranar dainawar sa ba, kana bakin tabon dake manne a zuciyar ta bata san ranar goguwar sa ba, sai dai zata yi kokari matuka wurin rage damuwa da mika dukkanin al’amuran ta ga rabbil alameen.
Hannun ta ta daga sama tayi addu’o’in ta ta shafa daidai lokacin aka Turo kofar dakin ta.
Miemie ce, ta sakar wa Munaya murmushi, Munaya ta mayar mata da martani cikin Muryar ta mai kama dana Mami tace “Mami tace ki zo”
“TOH” Munaya ta fada tana ƙoƙarin mikewa da kyar saboda girman cikin ta har yamutsa fuska tayi saboda yanda kasan marar ta ya amsa, barrister na zaune a falo tana danna system da alama wani Muhimmin aiki take wanda ya shafi shari’ar da za a ƙarƙare ta a gobe, ta dago tana fadin “Munaya, Abdulshakur ne yazo yanzu mai gadi ya shigo ya fada min, nace ace ya shigo ya ce sauri yake zuwa yayi ya ga lafiyar ki, zaki iya fita ko?
“Eh mami zan iya”
“Wanna da nawa ko yata na wahalar mana dake, zamu bashi pushiment ranar daya zo duniya” Shakur ya fada a zolaye ganin yanda take tafiya da kyar tamkar mai koyon tafiya.
Murmushin yake tayi, ita fa bata son ana mata maganar cikin nan amma ta lura kamar suna da farinciki da zuwan sa ko zuwan ta duniya.
“Ina wuni ya Shakur?” Ta fada a daidai lokacin data ƙaraso wajen tana jingina da motar sa domin yayi supporting din ta wurin tsayuwa.
“Lafiya Lou Munaya, kina lafiya ya jiki?”
“Alhamdulillah”
“ina son tambayar ki na manta,
menene gender din babyn?”
Yanayin fuskar ta ne ya Sanja a sanyaye tace “ban sani ba” kuma har ranta bata sani din ba, an buga da ita kan zuwa awo taki, ganin kamar damuwa maganar yake sa ta, barrister ta ce a rabu da ta, domin yanda babyn ke yawan motsi zai tabbatar da cewa cikin ta na cikin koshin lafiya.
Shima ya lura da sauyawar ta sai ya sauke ajiyar zuciya yace “Munaya Dukkanin mu ba haka muka zo dan nan ya zo ba, mun so ya zo ta tsaftattaciyar hanya, amma ya zamu yi, mai afkuwa ta riga ta afku, abinda ya faru bazai saka mu ki nuna wa babyn soyyaaya ba, ina son babyn sosai tamkar yanda nake son mahaifin sa, saboda haka kiyi hakuri ba ina faɗin wani abun bane domin ya zame miki damuwa ba”
Jinjina kai kawai tayi yace “yawwa tsaya na miki hoto, hoton tarihi, abinda zan nuna wa babyn kenan idan ya girma ” ya faɗa yana murmushi, da gaske yake son gudan jinin dan’uwan sa, har baya iya boye ta ko da yayi kokarin yin hakan domin farincikin Munaya.
“Kai ya Shakur nayi muni fa”
Munaya ta fada tana kokarin kare fuskar ta sai dai tuni ya dauke ta daya, sosai girman cikin ya sake fitowa ta cikin peach color din hijabin ta. Yayi dariya yace
“Ba wani muni, Akwai Abinda kike bukata?” Ya fada yana mayar da wayar sa aljihu.
“A’a” ta furta.
Ya bude bayan motar sa ya shiga fito da kaya, Munaya ta zuba masa ido ganin kayan jarirai irin daban daban, bayan ya fito da su duka ya kara bata wani leather mai dauke da kayan ciye-ciye yace “wanna kuma naki ne, wanna kayan Maleek yace na kawo, ayyuka ne suka masa yawa amma zai zo” Shakur yayi karya, domin abin ba tsari a ace babu wani labari ko nuna caring and concern kan abinda yayi.
Munaya tayi murmushi mai matukar ciwo hawaye suka ciko idanun ta tayi saurin yin kasa da kanta, ta san cewa wanna kaya ya Shakur ne ya siya ko kaffara bazata yi ba, ya dai ce haka ne domin ya dajarta dan’uwan sa, sai dai bata ganin darajar ba kuma zata taba gani ba, wani irin so Shakur ke wa ya’yan sa, abun har mamaki yake mata, sai da ta shanye hawayen ta yanda ba zai gane ba ta dago kanta, tace “na gode….”

“Karki yi godiya, ai duty din sa ne yin haka” ta kasa magana ta yi shiru.
Yace “toh ni zan tafi, akwai waya hannun ki ne zan dinga tambayar lafiyar ki, in babu sai na siya Miki”
“Akwai, an siya min, yana ciki”
“Toh ga card dina mai dauke da number’n na, ki min ko Flashing ne zan kira, sai anjima ko”
Jinjina masa kai kawai ta iya yi, because she’s totally out of words, ta matsa daga jikin motar tana tsaye har ya fice daga gidan yana daga mata hannu.
Tana nan tsaye har barrister Abrar ta fito tana cewa “na ji fitar mota shiru kuma baki shigo ba lafiya”
“Mami kin gani” Munaya ta fada tana nuna wa Mami uban Kayan dake zube a kasa…

“Allah Sarki” kawai barrister Abrar ta iya faɗa domin ta gane komai, hannun Munaya ta kama, tace wa mai bawa flowers ruwa dake kokarin tashi tace ya shigo mata da kayan falo, cikin ladabi ya amsa mata ta rike hannun Munaya zuwa ciki.
Bayan ya shigo da su, abin ka da namiji da uku hudu haka ya dinga kwasar su zuwa falon cikin kankanin lokaci ya gama, barrister Abrar tayi masa godiya.
Barrister da miemie ne suka dinga kai Kayan a wani empty room dake kasan, mami ta jere komai ba tare da ta cire daga cikin leathers din su ba, tunani kala kala take, ga sanyin da jikin Munayan ya kara ya dame ta, karamar yarinya babu abinda ta sani sai damuwa, tausayin Munayan har kwalla ya sata, wanda ya riski kansa a hali irin na ta kadai zai fahimci irin tsananin kuncin da zuciyar ta ke ciki.

***
Da misalin karfe goma na dare Shakur ya buɗe dakin Maleek ya shiga bakin sa dauke da sallama sai dai Babu walwala a Muryar sa.
Maleek dake kwance rigingine ya mike zaune ganin dan’uwan sa, zai tambaye shi damuwar sa kenan, ya ji Shakur din ya dora masa wayar sa a cinya, bai kalli wayar ba fuskar Shakur din ya kalla, cikin neman karin bayani. Cikin calm voice din sa Shakur yace “check and see for your self, ka Kalli halin da karamar yarinyar nan take ciki wanda kai ne sila, idan baka tausaya mata, amma ta ci darajar gudan jinin ka dake kwance a mahaifar ta, ina tausayin ka ya tafi Maleek? Please change, i have promise my self that bazan kara rigima da kai ba, but Please do the needful” yana fadin haka ya juya ya bar dakin ba tare da ya dauki wayar sa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button