Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 39

Sponsored Links

39
Tamkar mai neman wani abu yaje wajen,yayi kaman zai juyo ya take qafarta,wata iriyar azaba ta ziyarceta,sai ta saka hannu ta rufe bakinta dashi tana tunanin zata iya jurewa,sake taketa yayi wannan karon kasa daurewa tayi sai data qwalla qara,baya yaja ya dage labulen yana dubanta
“Me kikeyi a nan?” Tsabar azaba ya hanata magana,sai daya maimaita maganarsa cikin tsawa sannan ta iya amsashi
“Babu komai,abu nake nema….” Tsai yayi ya zuba mata rikitattun idanunta dake sake tsumata cikin soyayyarshi koda yaushe,nauyi sukai mata ta gaza daukarsu,saita sadda kai gabanta na faduwa,kunyar abinda tayi na mamayarta,da kanta ta tona kanta ta hanyar cewa
“Kayi haquri don Allah,wallahi bazan sake ba”
“Daga yau duk sanda muke zaune a falon nan mu biyu kacal ko gilmawarki kar na sake gani,bacemin a gun” ba shiri ta wuce tana dingisa qafarta.

Dariya ce sosai ta zowa aysha,ta kifa kanta a saman tebur tana qunsheta,a nutse ya tako wajen,sai yaja ya tsaya yana dubanta,sam batasan ya dawo ba sai dataji yace
“You,me kike ma dariya?” Ya dage girarshi daya,kai ta girgiza tana qoqarin hade fuskarta daga dariyar da take sadai ta gagara hakan,ci gaba yayi da kallonta yadda take son tsuke fuskarta ya taimaka wajen fito da beauty point din dake kumatunta,wanda ko sau daya bai taba kula dashi ba sai yau,qarar wayarshi ita ta dawo dashi daga duniyar kallon daya tafi,saiya fara laluba aljihunsa cikin basarwa,sai daga bisani yaga a saman tebur ya ar wayar,hannunshi ya miqa ya dauko wanda sauran kadan jikinsu ya gogi juna,hanyar waje yayi yana amsa wayar da alama mai muhimmanci ce.

A hankali ya tura qofar falon ya shiga sanyin ac da qamshin nan na musamman da tun zuwanshi yaji sashen nasa nayi ya daki hancinsa,ba wadataccen haske a falon sosai sai daya sanya hannu ya kunna makunnin qwan falon sannan hasken ya gauraye ko ina,daga can bangare daya na falon ya hangota akwance,sanye da kayan bacci ruwan hoda mai turuwa riga mai dogon da wando mai kauri,sai farin hijabi da take sanye da shi wanda bai wuce qugunta ba,gabanta takardu ne a baje da litattafai,sai torch din wayarta dake kunne da alama karatu take baccin ya sureta,sannu a hankali kamar mai sanda ya isa gabanta yana dubanta fuskarta da tayi fes kamar ba bacci take ba,quruciyarta ta fito sosai,baccin ya mata kyau,murmushi ya saki sanda ya tuna abinda ya faru dazu yana zarar daya daga cikin takaddun gabanta wanda take rubutu akai ya soma karanta rubutun dake jiki daya bayan daya

Related Articles

Dauke idanunshi yayi ya maida kanta yana yaba tarin basirar daya gano sanda take gyara kwanciyarta cikin baccin da alama ta gaji da kwanciyar daya bangaren ne,iya yanda take bayanin aikin da aka bata kawai ya isa ya gaya maka cikin sahun daliban da take,jinjina kanshi yayi yana yaba mata kafin ya durqusa ya maida takardar cikin ‘yan uwanta sannan ya tsugunna yana tattare mata takardun waje daya.

Motsin takardun shi ya farkar da ita,zumbur tayi ta miqe ta zauna tana dan matsawa baya,da sauri ya dora yatsanshi akan lebansa yana fadin
“Shshshsh….in kika sake kikamin ihu irin na dazu saina cinye bakin” kunya ce ta kamata daya tuno mata da kuma lafazinsa na yanzu,saita sadda kai tana gyara zamanta a fakaice saboda yadd wandon jikinta ya tattare qaurinta ya fito,maimakon daya gama hada takardun taga ya miqe sai ya koma ya zauna sosai,yana soke yatsunshi cikin na juna idanunshi a kanta
“Uhmmm,bani labarin abinda ya faru da bana nan” yatsunta ta lanqwasa suka bada sauti,cikin muryar wanda ya tashi daga barci wanda ta cakudu da yanayin sanyinta tace
“Ba abinda ya faru” lumshe idonsa yayi saboda yadda tsigar jikinsa ta zuba
“Me yasa baki nemi ni ba tunda na tafi?,haka ake yaya da qanwar?” Idanunta da suka sake haske saboda baccin da tayi ta daga ta zuba mishi su
“Ya salam” ya furta can qasan maqoshinsa ta yadda shi kadai zai iya ji
“Wai me yake damunka khalipha?” Ya tambayi kansa da kansa,baisan me yasa yake jin baqon yanayi tattare da ita ba,komai tayi sai ya bada wani reaction a jikinsa da zuciyarsa

“Kafin nayi serving number din ne ta gudu” sake gyara zama yayi sosai,haka nan yake son hirar tasu tayi tsayi,duk da cewa ya sani shine mai.laifin da bai taba nemanta ba
“Amma me yasa baki amsa ba wajen anni?”
“Hakan na nufin zata fahimci baka kirana kenan” ta sake bashi amsa a taqaice a sanyaye,murmushi yayi yana gyada kai,sai yanzu ya gane dalilin da yasa anni bata taba masa fada ba kan bai taba kiran nata ba,tafin hannayensa ya game waje daya,bashi da sauran abin cewa,gashi kuma baison zaman nasu ya qare da wuri haka,sai ya sake bude takardun daya hada matan ya soma zarosu yana mata tambayoyi kan course din da takeyi,batayi qasa a gwiwa ba ta soma bashi amsa daki daki,saidai abu daya ne da bata so shine ya daga kai ya zuba mata idanunshi,faduwar gaba da daburcewa suke sakata,har ta qare maganarta idanunshi a kanta yana gyada kai
“Ma sha Allah” ya fada sanda ya fuskanci ta gama
“Allah ya taimaka”ya fadi yana miqewa,a gajiye yake sosai don fitarsa dazu ba qaramin yawo sukayi ba
“Ameen,na gode,Allah ya saka da alkhairi ya jiqan magabata”
“Ameen” ya amsa cikin jin dadi ya wuce cikin dakin.

Koda ya fito tuni ta miqe saman doguwar kujera,da alama nufinta nan zata kwana,ita kanta tasan qarfin hali ne kawai takeson nunawa,amma tsoron da takeji Allah kadai ya sani,saboda shi kanshi falon yayi mata girma,batason ne a matsayinsa na baqo kuma muhallinsa ne ace ya kwana a nan
“Ki koma inda kika saba kwanciya ki kwana” kafada ta maqale
“Ka barshi zan kwana anan” bai sake ce mata komai ba ya juya ciki.

Duk yadda jikinsa da idanuwansa suka buqatu da barci amma hakan taqi samuwa,yayi juyi saman gadon yafi sau shurin masaki,tunda ya kwanta take masa yawo cikin idanuwanshi,komai yake dawo masa fes game da ita,yanayin daya ganta dazu zuwa yanzu daya shigo ya sameta tana bacci,tsaki yaja ya miqe ya zauna dirshan saman gadon sanda wayarshi ta soma ruri,

Tunda ya kalli number dake yawo yasan lili ce take kiranshi,hatsabibiyar matashiyar budurwar data takura rayuwarshi da sunan tana sonshi,saidai bayan soyayya da take masa tana da burin suyi soyayya irin ta watsewa wadda ita a wajensu ba wani abun aibu bane,tsaki ya kuma ja yana tuna sanda ta keta parlour dinshi a can ta taddashi har cikin dakin gadonshi,tun daga ranar bai sake yadda yabar gidan a bude ba,kashe wayar yayi baki daya bayan yayi rejecting call dinta,sake juyawa yayi ya kwanta rigingine yana addu’ar Allah yasa bacci ya daukeshi,saidai hakan bata samu ba,dole ya sauko daga gadon wani abu na kaikawo a ranshi,toilet ya shiga da niyyar daura alwala ko Allah zaisa ta sanadin haka baccin yazo.

Gefan gadonshi ya dawo ya zauna yana tsane ruwan alwalar,bayan ya gama ya sauke hannun rigarshin,haka kawai ya kasa sake komawa gadonshi,sai ya zura slippers dinsa ya tako a hankali zuwa bakin qofa ya budeta a hankali.

Idanunshi ya shuga wuwwulgawa cikin falon,can ya hangota lokon kujera a takure waje daya kanta na saman gwiwoyinta,qofar ya saki ya taka zuwa cikin falon
“Hasbunallahu wani’imal wakil” ta fada a zabure tana miqewa sanda taji motsin tsaiwarsa,ta tsorata sosai da sauri ya riqeta yana mamakin tsoro irin nata,ganin taqi nutsuwa waje daya ya sanyashi riqe dukka hannayenta yana fadin
“Calm down nine,khalipha ne” ya qarashe fada da dan qarfi don ya dawo da hankalinta kanshi,ajiyar zuciya ta saki don ta soma bacci ne taji wannan motsin,uwa uba dama a tsorace baccin ya dauketa,bai saki hannunta ba har zuwa dakin sannan ya zame hannayensa,da hannu daya yayi mata nuni na tahau ta kwanta,saita kalleshi sannan ta dubi gadon,ta taka a hankali zuciyarta na bugawa saboda tsoron data ji dazu.

????????????????

A nutse ta tura qofar dakin anni bakinta dauke sa sallama don su gaisa,saboda bata samu zama breakfast tare da su ba ta tsaya gyaran sashen nasu,tadai kammala abun karin da tasan zai ishi kowa a gidan ta gyara dining din ta bar sashen,da fara’a saman fuskar anni take sa sallamar tata
“Maraba da takwara” murmushi aysha ta saki har wushiryarta na fitowa,tana yaba yadda annin ke mata,tana jin cewa inama inama ace ita tahaifeta,inama ace itace mahaifiyarta,kanta a qasa saboda ta fuskanci suna wata magana mai muhimmanci ne ita da khalipha wanda ya nutse cikin kujerar dake falon annin yana satar kallonta can cikin zuciyarsa yana mamakin sauyarwarta,waishin dama matan cikin hijabi akwai wani sirri na musamman da suke boyo ne ko kuwa wani abu ne ya sauyata?,iyaka saninshi da ita ba haka take ba,kunnuwanshi na sauraren muryarta da suke magana da anni,ita dinma yana jin kaman ba tata ba,kodai watannin daya diba ne yasa yake ganin komai ya sauya?,har suka gama gaisawa da annin da ‘yan maganganunsu baice komai ba,furucin anni na qarshe ne ya dawo dashi
“Karki zauna haka na sanki sarai ki nemi abu kici” kanta ta kada sannan taci gaba da takawa don ficewa daga dakin,sai taji tana son ta harde,ba shakka akwai wani dake kallonta,wani nauyi take ji kamar yau ta saba shigowa falon annin
“Khalipha” anni ta kira sunanshi ganin hankalinsa nai tare da ita,cikin dakewa irin ta gigaggun maza ya soma shafa kanshi kafin ya maida idanunshi a kan annin,cike da basarwa yace
“Anni yarinyar nan tana karatun nan kuwa?” Dariya ke cin anni a qasan ranta,amma a zahiri saita dake gami da bata rai
“Me ka gani?” Kai ya girgiza da sauri,don idan ta tirkeshin kan me ya gani dinma baisan me zaya ce mata ba
“Babu komai”
“Aisai ka fadi abinda ka gani” ta sake fadi tana yin kicin kicin da fuska
“Ba komai anni….na lura bakison laifinta”
“Dole kace haka khalipha saboda kaga na qyaleka kan naka laifin ban tuhumeka ba,duk yadda taso ta boyen nasan abinda ke wakana”haquri sosai ya shiga baiwa annin tare da yi mata bayanin abinda ya kawo tsaikon dawowarshi
“ita zaka je kama wannan bayanin bani ba”ta fada tana miqewa,sai ya miqe tare sa annin yana dariya qasa qasa
“Anni yanzu gwamnatina ta rushe kenan?….”dariya yaso bata,sai taqi cewa komai ta amsa shi a taqaice
“Oho to wa yasani?” Murmushi yayi yana biye da ita duk takunta daya sai daya ga shigarta dakin gadonta sannan yaja mata qofar ya fito.

Tana tsaye cikin kitchen din ta hada corn flakes da madara cikin wani qaramin bowl da alama shi take nufin sha,gefe daya ta dora kankana a kan plate tana yankata qananu qananu itama tana zubata a wani bowl din a haka ya sameta.

Bata ji shigowarshi ba sai inuwarsa data gani a gafenta,jan mayafinta tayi dake niyyar sabulewa daga kanta saboda santsin gashinta,gashin nata ya kalla sannan yaci gaba da kallonta ta gefan fuska,duk saita ta kura,batasan wanne jarabar kallo bane haka wanda da can data sanshi bata sanshi da kallo ba,kafin a daura aurensu idan yazo mata tsahon minti talatin din nan yafi ta’allaqa idanunshi kan wayarshi,a nashi gefan kuwa wani abu daya faru bayan barinsa gida shi ya dinga dawo mishi a kai,nazarin ayshan yake gami da dorata a mizanin da zuciyarshi ta shawarceshi a kai,saidai baiga wata qofa dake nuna tana ra’ayinsa ba bare sukai ga bigiren da zuciyarsa ke hasashen masa,ta yaya zai koya mata sonshi?,ta yaya zabi da ita ta karbeshi ta fuskar da yakeso?,ya tabbatar da cewa irin aysha tun a wancan lokacin dai daikune cikin jinsin ‘yammata,faruwar lamarin ya sake tabbatar masa da wannan.

Hannunshi yasa ya dauki cokalin dake cikin madarar yana juya cornflaske din bayan ya dauke idonsa daga kanta wanda take ta faman gutsira kankanar kaman ba zata gama ba
“Wannan shi zakici a matsayin breakfast?” Kai ta gyada ba tare data dubeshi ba,baice mata komai ba saiya dibi cokali daya yakai bakinsa yana taunawa,shi a rayuwarshi har mantawa yake da abin nan,ya manta rabonshi daya cishi,kadan kadan ya dinga diba yana ci sai gashi yana shirin tashi dashi,batasan sanda ta saki baki tana kallonshi ba gaba daya wanda dama shi haka yakeso,aje cokalin yayi sannan ya soka yatsunsa cikin na juna,cikin cool voice dinshi wanda ba hayaniya sam a ciki ya furta
“Am sorry”
“Bayan ka cinyemin abuna?,da kanaso saika fadamin na hada maka wani” murmushi ya saki sai kuma taji kunya da nauyi,kaman gidanmu?,kaman bashi ke aje komai ba?,qasa ta danyi da kanta,kamar ya fuskanci haka saiya jawo locker da suke aje kayayyakin ya dauki wani cup din ya zuba ruwan dumi ya hada mata wani
“Gashinan na biyaki,ke naki ma da ruwan sanyi kika hafa babu dadi,ni kuwa dana dumi nayi miki”
“Na gode” ta fada tana boye murmushin jin kunyar da take
“Kiyi haquri naje na zauna ba tare dana nemeki ba,ni kuma nayi hakanne don na baki damar yin masters dinki cikin nutsuwa,duba da yadda kike qaunar karatunki”
“Babu komai”,dukkansu shuru sukayi saboda jiyo tashin wata murya kamar ta rahama na doso kitchen din.

Katsam babu tsammani taji gaba daya taji ya rungumota ta baya hannuwanshi saman cikinta,faduwar gaba da kaduwa suka sameta lokaci daya
“Karki motsa” ya rada mata akunneta wanda sautin da dumin fitar furucin ya ratsa har bargonta
“Khalipha me kakeyi a kitchen?,kaman wanda baida mata” muryar rahama dake cike da iyayi da kwainane ta cika kitchen din,juyowa yayi gaba daya har yanzu aysha na cikin jikinsa
“Tare da matar muke,kinsan se ana mata dure bata son cin abinci,ban sani ba ko baby na ke wahalar da ita” wani abu taji ya daki tsakiyar kanta,maganarsa da yadda ta ganshi manne a jikinta,duk da qoqarin basarwar da take amma hakan.sai daya bayyana saman fuskarta ya sauya duk wata walwalwa data shigo da ita
“Ohkey….ohkey” ta fada cikin murmushin yaqe tana bude frdge ta dauki ruwa ta fice ba tare data sake cewa komai ba.

Tayi zaton zai saketa ne bayan fitar ta amma saitaga baida niyyar hakan,tana jin saukar boyayyar ajiyar zuciyar daya saki ta qirjinsa da kanta ke saitin wajen,dumin jikinta ya masa dadi,qamshinta kamar bai taba jin turare mai dadin nata ba,saiya miqa hancinsa zuwa wuyanta da zummar shinshinawa,da sauri ta saki gyaran murya cikin rawar murya
“Su baba atika na iya shigowa koda yaushe fa” banza yayi kaman baijita ba cikin salo na waskewa,wayarshi ya ciro bugu uku aka daga,anni ya kira
“Anni,waisai yaushe ne rahama zata bar yawo tsakanin nigeria da nijer?,yanzu me ya kawota fisabilillahi?” Bata ji me anni tace masa ba,sai taji ya sake cewa
“Bana son damuwa ne anni….ohk to” ya katse wayar yana maidata inda ya dauko sannan ya saketa
“Ina fata baki manta maganar dana taba gaya miki ba abaya,wannan karon any mistake kikayi bazan daga miki qafa ba” ya kai qarshe yana daga girarshi cikin nuna da gaske yake mata
“Duk wani abu da kikai ba dai dai ba idan ba haka nakeso ya kasance ba zanyi yadda ya kamata ne koda kuwa a gaban anni ne,ina fata kin gane?” Kai ta daga mishi
“Oya….take ur cornflakes mu wuce tare,banaso ki zauna yau a sashen nan” bowl din ta dauka gaba daya,sai ya dubeta ta dan kauda kai,ya fuskanci me take nufi,amshewa yayi daga hannunta ya aje saman canter din
“Muje kya hada wani a can” babu musu ta bishi a baya suka fice.

Ranar gaba daya a sashensu ta wuni,shima kuma yana study room di shi yana wasu aikace aikace na office daga gida,da yammaci ya fito ya dubeta yana cire glass din idanunshi
“Ki koma ciki zamuyi wani dan aiki” tattara kayan karatunta tayi ta shige kaman yadda ya umarceta,ashe kitchen aka shirya mata da spare din dan madaidaicin dakin dake cikin ainihin dakinsa na motsa jiki.

Qarfe hudu na yammacin washegarin ranar bayan ta kammala abinda take tashiga wanka wanda bata samu yi ba saboda gyaran kayan sawarsu datayi,harda na khalipha wannan karon nata qyake ba dui da batasan ya zai dauki abinda tayin ba,bata gane kurenta ba sai data fara gyaran don batasan haka kayan keda uawa ba,hakana komai nashi a tsare yake a muhallinsa,kamar side sin tie socks boxers da sauransu kowanne daban daban,dole ta maida tsarin yadda ta gashi.

Tana shirin shafa mai wayarta tayi tsuwwa,murmushi ta saki ganin maman hunaifa ke kira
“Mutuniyar nan anya ba wani ne ya riqe mana ke ba?,kin riga mu tahiwa gashi har yau baki dawo ba koni gashi na haqura na dawo duk da baban hunaifa bai koma ba?”
“Kinga barta dawowar tata duk a suna ne,sun maidani abin tausayi ita da mijinta,a gabana take fecewa mijinta kwalliya duk sanda basu da lactures su fice yawo abinsu,yanzun ma kin ganta gaban kayan kwalliya tanayi” cewar hanan wadda ta amshe wayar ba tare data bar mmn hunaifa ta qarasa fadin abinda takeson fada ba,dariya aysha ta saki,duk sai taji tayi missing nasu,batasan me yasa khalipha ya tsaidata daga komawar datayi niyya ba dazun da safe
“Allah aysha saimun rama,Allah yakai damo ga harawa bari muna muyi auren nan saita ri ga rufe idonta”
“Idan ban wa mijina ba nikam duk banga amfanin ma kamfanin sutura da kayan kwalliya ba,kuma idan yazo kanku ban yadda ku saurara ba” mmn hunaifa dake gefe ta fadi,dariya suka sa gaba daya sannan suka soma gaisawa tare da tambayatta lafiya,sa kawai tace musu basu da lacuters ne dalili kenan amma tana kan hanya,hira suka yi sosai sai data ji kiranabban hunaifa na shigiwa alamar ya iso sannan sukayi sallama,aysha na dariya ta aje wayar,a hankali ta dora idonta kan fuskarta data bayyan a gaban mudubi,murmushi taci gaba dayi tana tuna yadda ma’auratan ke bawa junansu kulawa,abun na mtuqar bata sha’awa da burgeta kaman yadda yake burge hanan,sai kawao ta sami kanta da yin kwalliya sosai duk da cewa a yanzun mawuyacine ka ganta ba kwalliya koda lite ce.

Sosai tayi kyau uta kanta ta gani,siririyar sarqa ta saka da dan kunenta tana hade da zobe mai kyau ta feshe jikinta da turare sannan ta yafa yalolon mayafi daya dace da adon nata,gurin anni takeson shiga sai ta dauki litattafanta ta fita dasu tana son ta duba.

Ba kowa a falon sai rahama dake faman waya,wani kallo tabi aysha dashi tun daga sama har qasa,sauyawar yarinyar na bata tsoro,dudud wata nawa amma kaman an maya wankan engine,amal ce ta shigo daga wata qofa wadda zata kaika bayan gidan,itama kallo tabi ayshan dashi,duk ta lura dasu saita rasa na meye kallon?,a baya sam bata taba tsayawa dubawa ba bare ta tantance,saidai zuwa yanzu rashin jituwa tsakanin amal da rahama ke bata mamaki da tambyar kanta meye sila,uwa uba yadda amal din ta sake ja baya da ita ta rasa daliki,koma meye dukansu ba damuwarta bane,tana qoqarin sauke nauyin da musulunci kawai ya dora mata,haka nan taji zaman falon bai gamsheta ba,saboda haka ta jiya kawai ta fuce zuwa can bayan gidan inda ya wadatu da yawan shuke shuke,ta bude takardunta ta soma dubawa daya bayan daya.

Bata nima da zama ba taji shigowar motocinsu haidar,da alama daga office suka dawo,saitaqi tashi zuwa cikin gidan,don karatin ya soma mata dadi,duk da cewa akwai ma’aikatan dake gayafn flowers din wajen dake wucewa jifa jifa,amma da yake ba hayaniya suke ba basu dameta ba.

Sosai ta duquf tana duba wata paper dake hannunta,sai hancinta ya dinga jiyo mata wani qamshin turare nadaban wanda kamar ta sanshi,hat ta basar taji qamshin na sake daduwa cikin hancinta,saita daga kanta,khalipha ke dosowa inda take,bayanshi yaro shi nasir na biye dashi dauke da wasu fikes,juyawa taga yiyi yayi mahana kadan da shi saitaga yadan rusuna cikin girmamawa ya juya yabar wajen,shi kuma yaci gaba da qarasowa inda take,faduwar gaba tasamu wadda ta zame mata jiki aduk sanda ya kalleta ko suka kadaice daga ita saishi
“Sannu da zuwa” ta fada a yangance wanda ita batasan tayi din ba,idnunshi a kanta ya amsa shima cikin nashi salon.

Ticket din dake hannunshi ya miqa mata guda daya tana duban kwalliyar da tayi ta yau wadda tayi masifar burgeshi,buba ce da zani saidai kuma an danne gefe da gefanta dai dai jikin mai ita,sosai qirar jikinta ta fita,dan siririn mayafin data yane kanta bai rufa asirin gashinta ba da yasha gara yake qyalli,hakanan qamshin jikinta bai bar buso mishi ba tare da iska mai sanyi irin ta la’asar din da akayi dace aka samu raguwar yanayin zafin da ake ciki,fararen qwayar idanunta ta saka tana karanta ticket din,legos?,me zasuje yi a legos din?,kamar ya karanci abinda yake kai kawo a zuciyarta yace
“Gobe zamu wuce,kada ki damu da abinda zamuje yi” ya qarashe maganar yana bin yatsunta da kallo da har yanzu jan lallen dake jikimsu yake ci gaba da burgeshi hakanan
“Toh” ta furta a sanyaye tana ninke ticket din,haka kawao jikinta yayi sanyi take jin fargaba,hannunshi cikin aljihun wandonshi ya juya ya fara takawa,sai kuma ya tsaya cak yana duban gilmawar masu ya kan fulawar dake gyara a wajen,haka kawai yaji wani abu ya taba ranshi,saiya dawo da baya a sanda take ci gaba da rubutun assigment dinta
“Ko zaki koma ciki?,nan din maga bake kadai bace” kai ta girgiza tana shakkar hada ido dashi,batasan me yasa sau tari idan yana gab da ita take yawan jin hakan ba
“Duka bamu takura ba babu komai” bai sake tanka mata ba ya duqa ya soma tattare takardun,saita soma binsa da kallo,baiko dubeta ba har ya gama,hannunshi ya sanya ya zare biron dake tsakiyar yatsunta sannan ya juya ya soma tafiya,ta fahimci me yake nufi dole ta sauko daga saman lilon ta zira takalmanta ta biyo bayanshi.

A fakaice take qarewa tafiyarshi kallo,idan baka sanshi ba sai kayi tsammanin yana sane yake irin tafiyar,kamar saraki ko mai jinin sarauta a jikinsa haka yake takawa cike da nutsuwa
“Kinsan idan namiji ya amsa,sunanshi yanayin tafiyarsa ma kawai abun kallo ce” ta tuna kalaman hanan data sakata a agaba tana koya mata yadda zata gane ta fada soyayya da wani,da kuma siffofin qasaitaccen namiji wanda ba lallai sai mai kyau ne yake da su ba,duka shirme take daukan abun,sai gashi a yanzu batasan dalilin da yasa daya bayan daya komai yake dawo mata ba aduk sanda khalipha yayi wani motsi.

 

*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*ko kuma*
07067124863
[3/8, 9:04 AM] Binta Mustapha

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button