Hausa NovelsNi da Almajirina Hausa Novel

Ni da Almajirina 17

Sponsored Links

NI DA ALMAJIRINA
(Our Incomplete Story)

Episode 17

Nasan burin ki be wuce ace na fadi na mutu ba, murmushi me wiyan fassara yayi kafin yace ko na mutu bazan taba rabuwa dake ba coz na bar part of me in here yayi maganar yana dauran a hannun sa samar cikina.

Related Articles

Lalle ashe gaskiyar Hajjahkaka ce, Baana Dodi ne sai yau na yarda,wai shi a tunanin sa yayi ajiya aiko ze ga ajiya, nayi maganar cikin raina.

Tashi kiyi wanka sai na kaiki gun Hajjahkaka.

Bata rai nayi kafin nace haka zanje base nayi wani wanka ba.

Dariya yayi kafin yace yanzu haka zaki je mata da warin gawasa ?

Rai bace na mike na fara takawa zuwa kofa, yayi saurin jawo hanuna na, kallon sa na keyi ina yamutse fuska kamar zanyi amai.

Hadani da bango yayi fuskar sa dab da nawa, yau ko amai za kiyi,kiyi shi a bakina but naga dazun ba kiyi ba does that mean…

Ban bari ya karasa maganar nace kai dan kazanta sai… Ewe disgusting !

Murmushi ya dinga yi yana kallona kafin yace eh, indai daga jikin ya fito zan iya…

Rai bace nace kabar wannan maganar karka sa nayi amai ewe ! Kuma ka matsa kusa dani na samu na futar kuma nashaqa numfashi da kyau.

Kara zuwa daf dani yayi kamar za mu shige bango, idan na tuna NI DA ALMAJIRANA a wannan yanayi sai naji kamar na mutu tsabar bakin ciki. Na tsane sa amma shi sam be damu ba.

Ouch nayi maganar kokarin sulalewa kasa, amma be bani damar kai wa kasa ba, cikina na murdawa don Allah ka matsa zan iya suma.

Dariya ta bashi, yace matsoraciya bazan miki kome ba, zo muje amma inda ta koroki nide ba ruwana yayi maganar yana ja da baya,
Sauke ajuyan zuciya nayi kafin nabi bayan sa.

Hajjahkaka dake zaune wheelchair ta na shan tea tayi kamar bata gamu ba.

Na karaso gunta da sauri nace barka da dare Hajjahkaka.

Nasha gaya maki ki dena zuwa min da warin gawasa amma qinki, to walh ba zaki hallaka ni da warin gawasa ba,
kai dauke ta ku koma idan kuka fito. Hajjahkaka tayi maganar ba alamar wasa.

Rai bace nace ke kulum sai kinyi maganar gawasar ? Ni bana wari saide shi.

Baana dake tsaye yana kallon su yana murmushi , Hajjahkaka ta bishi da mugun kallo , can tace zufan namiji ya hadu da na mace ba dole kuwa warin gawasa ba ? Yanzu de Baanaliye sai da ka taba ta kenan ?

Takowa Baana yayi zuwa inda suke , Hajjahkaka zamu yi tafiya kila nadan jima, don Allah king kulamin dasu

Ayo me matsetsan duwaiwai kamar hura biki yayi kira kenan ? Za aje ai ta ‘asa to Allah ya kyauta yasa ku gane gaskiya. Hajjahkaka tayi maganar tana kallon sa da kyau.

Amin Hajjahkaka sai na dawo. Yana fadin haka ya juya zai tafi , Hajjahkaka tace to ya za ayi da kayan kwallama?kasan masu ciki da kwadayi .

Yabawa tana nan duk abin da kuke so zata baku. Nabar ku lafiya

Yana fita nace Allah yasa ya tafi kenan ba dawowa, HajjahKaka ta buge min baki harda saurin cewa ba amin ba.

Falmata yaushe zaki samun spiriyens ne? Bacin Baanaliye da Allah kade yasan a wani hali muke a yanzu? Da yanzu killa ma an kashe ki ko kuma ai ta maki abu manya. Dan kinsa ba imani ne dasu ba, ki godewa Allah da ya daura masa son ki.

To ba gara ma ankashe ni ba, da ina wannan hali da muke ciki? A gabana aka kashe Bestie na sannan wannan azulumin baqi kazamin Almajirina yayi min fyade na karasa maganar ina me fashewa da kuka

Dallah can rufemin wannan burmamen bakin naki, to ina sha an danka mana sadaki kuma mun amsa?
Da kika je kika bude kanti patari ni na aike ki? Bacewa nayi ki jawo hankalin sa ba yadda zamu fita daga nan? HajjahKaka tayi maganar tana bina da mugun kallo.

HajjahKaka nifa ban gane maki ba kwana biyu nan? Naga kamar kina shigewa wannan kazamin?

An shige din yo ba dole na shige ba tudan naga har yanzu ke Dodi minal Dodi ce, ina nuna maki hanya yadda zamu bar nan amma ke kamar so kike mu dawwama annan
Idan zaki sauke girma kan nan ki amshe shi a matsayin mijinki na dan wani lokaci Walhy ko me matsatsen duwawai nan kamar huran biki Ya Amir yake kowa to ko shi juya me baya Baanaliye ya dawo da ga rakiyar sa amma kin daukar spiriyens.

Shiru nayi ina kallon ta cike da mamaki, wai na amsa ALMAJIRINA a matsayin mijina? Wai miji?

HajjahKaka tace to miye? Ke maganar gaskiya ayi ta domin Allah bacin farin fata da hanci karot ba abinda zaki nuna wa Baanaliye, Baanaliye Namiji ne har iya Namiji Walhi.

Shiru nayi kamar wata me lisafi ina kallon HajjahKaka, shin zan iya playing insa kamar yadda HajjahKaka tace kuwa? I don’t think zan iya nayi maganar cikin raina

HajjahKaka tace to wai na tambaye ki man? Wanda yasan ciki da bai dinki har akwai wani jin kai da zaki masa ne? Ya riga da yasan ki ya mace to miye rage kuma? Idan zaki spiriyens kiyi mu samu mubar nan dan na gaji da hazo hazo na gafi da warin gawasa, kowa ya zo sai kaji dummm ya dumeka da warin gawasa

HajjahKaka I need time to think about this issue and i pray it works kar na sake fadawa wani tarkon sa

Ahab sai kiyi kuma,ke kika san abinda kike cewa, Falmata na dafa ki da alheri HajjahKaka tayi maganar tana dafa ni, jiya basai ga wannan me tsiyayyen duwawai ba ta dau wanka tayo shadaudau abinta.

Mikewa nayi na nufa toilet trying to divert from the topic…

BAYAN SATI DAYA

Gaba daya kasar ta dauka,kuma tasan da zaman su, Ya Amir wayan kan waya yake amasawa, a sati daya sun zauna da manya mutane daga kasashe akala kusan goma, yanzu haka ma wata kasar zasu nufa.

Cike da damuwa Baana yace Ya Amir why not na koma can,tudan duk mun zauna da mutanen da yakamata ace mun zauna dasu ?

Kallon Baana Ya Amir yayi can yace Baana ina tunanin yarinyar nan zata ja mana matsala,idan har naga kana kokarin fifita akai na to zan kashe ta.

Cike da mamakin furucin Ya Amir, Baana ya tsaya kallon sa, cikin taushin mirya Baana yace haba Ya Amir duk duniya bani da tamkar sannan duk duniya ba abinda nake so kamar Falmata, idan ko narasta to nima ka rasa ni har abada .

Cike da mamaki Ya Amir ke kallon Baana , wai shi suke musanyar yawu? Murmushi manya yayi kafin yace My son farinciki ka shine nawa amma for now focus on your goal. Ka tuna our motto?

A tare suka hada baki da cewa “WE’RE BORN TO RULE THE WORLD”
Sauke ajiyan zuciya Ya Amir yayi yace son wanna country da zamu there are one of the intelligent country in the world, and we need you there .

Shiru Baana yayi kafin yace still akan Net marketing?

Ya Amir ya amsa da eh. Yanzu karfin ya fi karfin Maiduguri yanzu so nake afara rating mu cikin top ten terrorist duk da de musan mu ba terrorist bane aikin Allah mu keyi.

Sauke ajiyan zuciya Baana yayi kafin yace tam.

A kala sai da suka kwashi wata daya suna tafiye tafiye,.kuma ko ina suka je hannu bibiyu ake amsar su, kamar wasu masu fada aji a duniyar.

Baana murna yake yau zai ga matar sa, jin kansa yake kamar wani sabon ango sabida zumudi, har Gambo zolayar sa ya dinga yi wai ango yasha kamshi.

Karfe biyun dare ya iso bai sauka ko ina ba sai dakin su Hajjahkaka, murmushi yayi ganin how peaceful she’s sounding, an hankali ya tako zuwa side din da take..

Kamar a mafarki naji ana shafa min lebe, cikin hanzari na bude ido, ina ganin sa na bude baki zan saka ihu ya tare bakina, shhhhh yayi min alama da hannun….

Whispering abu yayi min cikin kunne nayi saurin mikewa,.nabi bayan sa zamu bar dakin kawai…..

Pharteema(DMK)
THANKS

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button