Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 41-42

Sponsored Links

_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba_

Assalamu alaikum My Fan’s shin ko kunsan cewa bigi sai bigi babban goro sai magogin ƙarfe, tabbas ramin kura sai ƴaƴanta,
Nasan zakuce yau dame kuma Oum Hairan tazo mana? To ku daina tambayar kanku sabbi kuma shahararrun kayan mata ne masu ban mamaki daga taskar Siyat yar mutan Katsinawan dukko da Oum Hairan.
Muna da kayayyaki kamar haka👇🏼
Maganin gyaran Nono, maganin ƙarin hips, Sirrin matsi na musamman, gumbar dagake babu wata, humra mai taken madarar ƙauna, muna dafa kazar amarya da haɗin jijjiɓi musamman don masu jego tare da aikawa ko ina kuke a fadin Nigeria, munada maganin sanyi wanda duk shaharar sanyi muddin kikayi amfani dashi yanda ya dace to kin rabu dashi kenan.
Sannan munada kaloli na kayan Malama A’isha Mai Da’ira musamman turaruka wanda ke da kanki saikin dawo idan kikayi amfani dasu domin zasu janyo Miki hankalin mijinki zasu sanya nutsuwa da fahimtar juna tsakaninku zaki zama tauraruwarsa domin an haɗasu ne da wasu keɓantattun ayoyin Alkur’ani mai girma domin sharewa mata hawayensu babu boka babu Mallam, karki manta cikin kalolin turarukan mu akwai wanda Bama taɓa siyarwa me kishiya saboda haka kiji tsoron Allah in kinsan kina da kishiya karki siyeshi domin gudun shiga haƙƙinta.
Mai buƙata DM me 09013718241.

★★★~~~★★★~~~★★★

Miƙewa Najeeb yayi yana cewa “Kada kayi mata hukunci da baccinta waina watanka nawa da dawowa ne?” Baisan meye halaƙar tambayarsa da tambayar da Najeeb keyi masa ba amma haka yace masa biyu na shika na uku ina tunanin ma sati me zuwa zan koma” murmushi Najeeb yayi yace.
“Kuma sau nawa ka kusanceta daga dawowarka zuwa yanzun?” Kafe Najeeb yayi da ido Najeeb ya numfasa yace “Ta iya yiwuwa kaine matsalar ko lkcn da kana London kullum maganarka kayi missing Beebah kayi missing Beebah ta yuwu ka sake jefa ƙwallo a raga ne tunda naga Khalisa tunda ta samu ciki batada aiki sai bacci ƙila itama nata ne yazo da haka….”
Dariya Habeeb yayi yace “Da gaske zai iya zama hakan ko?” Ɗagansa kai yayi yace “Don tabbatarwa kana zuwa gida ka ɗauketa kuje a dubata hakan zai cire maka kokwanto”

 

Numfasawa yayi sukayi musabaha tare da sallama kowa ya kama gabansa zuciyar Habeeb ta kasa gasƙata masa abubuwan daya gani amma shaiɗan yanata taka rawarsa na son sai ya tabbatar masa.
Koda ya shiga gdan baiyi ƙasa a gwiwa ba ya nufi part ɗinta Khausar na ƙoƙarin ɗauke masa hankali da salon kirsarta ya watsa mata wani mugun kallo ya buɗe ƙofar ya fice ya nufi sashin Beebah tana zaune saman sallaya da alamun sallah ta idar Hudais na zaune a gabanta da kayan wasa yanata yan kararrakinsa kamar gyare inda ita kuma ta kifa kanta a cinyarta bacci na fusgatta taji an buɗe ƙofar ta ɗago idanunta cike da mayen bacci ta saukesu cikin nasa, shi ɗin ma itan yake kallo fuskarsa babu wani yanayi da zaka tantance walwala ko akasinta.
Haka ya tako ya zauna yana ɗaukar Hudais da ganin uban nasa yasashi sakin wasan da yakeyi ya fara miƙa masa hannu, lakacewa yaron kumatu yayi yana maida dubansa gareta yace “Meye yake damunki?” Yanayin yanda yayi tambayar yasa ta kasa gane me yake nufi sai kawai tayi ƙasa da kanta tace “Wallahi tallahi Hero ko maganin mura bantaɓa sha ba da niyyar ya fitar dani daga hayyaci na Please kada ka fara dasawa rayuwata kokwanto bayan Allah banda wani gata bayan….”

 

Rufe mata baki yayi yace “Ya isa nasani ina nufin game da lafiyarki kamar akwai wani abu dake damun jikinki ina ganinki saɓanin yanda nasanki” numfashi ta sauke tace “Ni babu abinda yake damuna yanzu ɗazun ne ma kafin shigowarka ta farko kaina yayi ciwo shine naje na kwanta bacci ya ɗaukeni” Jinjina kai yayi yace “tashi ki rakani unguwa” da sauri ta dubesa ya ɗaganta gira ta sani yanda ya haɗe yaci ganye ta tabbata babu kalmar data isa ta furta masa da zai saurareta hakanne yasata miƙewa ya ɗauki Hudais suka fita.
A babban parlourn suka wucce Khausar itace tayi mata sannu bata samu damar amsawa ba saboda wani malolon baƙin kishi da takaici dayake neman kassara mata zuciya, har suka shiga Mota suka tayar tanata takaicinta.

 

Jifa tayi da glass na cup na hannunta ta cire ɗankwalinta ta jefar ta nufi ɗakinta kamar sabon kamun hauka ta ɗauki wayarta ta kira lambar Deedah tana ɗagawa tace “Saida nace Miki mu canza salo wannan bazai yiwu ba kikace zai yuwu to yanzu me gari ya waya mun haɗa makircin ƙarshe gashi can ya ɗauke ta da ɗanta sun fice nikam hƙr na ya ƙare a gdannan babban burina ko zan rasa inga na rabashi da wannan ƴar Iskar Yarinyar wlh indai tana rayuwa a da’irarsa bazai taɓa kallon wata mace ba”
Tsaki Deedah tayi tace “Nifa wlh da kinbi shawarata ta da tuni tabar mana gdannan amma kika tsaya kina cewa wai kinfiso kibi komai a sannu to ai ga sannun nan kina gani mijinki kusan shekara da watanni ya gagareki saidai kiji dariyarsa a makotan….”

 

 

Cigaba sukayi da tattaunawa can sukayi sallama Deedah tace zasusan yanda zasuyi, itakam Khausar bata yarda da shawarar Deedah ba ta kira Hajiyan ƙofa bugu ɗaya ta ɗaga tace “Hajiya nifa lamarin nan ya fara isata wlh idan bata barshi ba ni zan barshi Mama tace mu shigar da boka na bakin kogi maganar ke kince a’a kuma alamu sun nuna itama hanyar da kikace kar mubi ita yakebi.
Yanzu ace duk kyauna da ƙirata bantaɓa burge Prince ba indai ba aikin asiri ba, haba Hajiya a duba wannan lamarin fah mazan titi ma haɗiyar yawu sukeyi idan sun ganni sai mijina ne zaice banyi masa ba nikam na gaji wlh na gaji sha’awar Habeeb na neman kasheni”

 

Murmushi Hajiyan ƙofa tayi tace “Yaro yaro ne to ke banda abinki kina tunanin akwai asirin dayake cin waɗannan kafaffun mutanen ne? Haba Khausar kamar baa wannan ahlin aka tsirar dake ba ai in faɗa Miki indai jinin Khalil ne to ba asiri ba ko tsafi ne asarar kuɗinki kawai zakiyi basajin bayaƙi da kiranye, Khausar mantawa ma kikayi shekara nawa kikayi keda uwarki kuna badda kuɗi wajen ganin kun samu Habeebun amma yaƙi samuwa? To ki nutsu wannan aikin bana gaggawa bane akwai shirin da nakeyi duk zakujishi amma sai bayan Habeeb ya koma shine aikin zaifi tafiya yanda akeso ke nifa Khausar na daɗe da ƙayyadewa wannan bamagujiyar adadin kwanakinta a wannan gidan kedai kiyi duk me yuwuwa kiga kin cusa kokwanto a zuciyarsa kafin yabar ƙasar nan”

 

Kwantar da murya Khausar tayi tace “Kina gani fah nasa mata kaskon shisher da kwalin sigarin da kwalbar maganin mura har uku har buɗewa nayi na zubar a kan carpet ɗin Hajiya sigarin fah har kunnata nayi Saida ta ƙare na kashe kuma na zubar da tokar a Carpet ɗin amma hakan baisa yaji wani ɗar ba yanzu haka ma ya ɗauketa da ɗan su sun fice sun barni da gadin gida”
Murmushi Hajiyan ƙofa tayi tayi ƙasa da muryarta tace “zan rubuto miki mataki na gaba” saurin katse wayar tayi lokacin da taji an turo ƙofar, daga bakin kofar ya tsaya fuskarsa a washe kai bazakace ya taɓa shiga damuwa ba ya tsaya yana kallon Khausar taja numfashi tare da ƙoƙarin saita nutsuwarta don tasani karamin abu baya kawosa ɗakinta tace “Ina farin ciki da farin cikin me sani farin ciki halan anyi maka albishir da sarautar Dutse ne?”

 

Murmushi yayi ya kwantar da kansa jikin ƙofa yace “zan iya samu taimako daga gareki Wyf ce takeson wainar fulawa ta manja” murmushi tayi tace “to ai akwai komai a kitchen ɗin parlour tayi mana” murmushi yayi yace “batada lfy ashe duk wannan kasalar shigar ciki ke gareta….”
Da wani mugun sauri ta ɗago tace “Ciki kuma?” Annurin fuskarsa ne ya ɗauke ya zubanta manyan lulu eyes ɗinsa nandanan ta daburce tace “Nothing karka kawo komai a ranka kawai naga Hudais baifi five months ba.

 

Naji tsoffi suna cewa idan yaro yasha ciki lalacewa yakeyi….” Juyawa yayi ya fice yana cewa babu abinda zai sameshi zan tafi dasu London a kula dasu acan ina jira ki kawo min wainar” da wannan ya fice ta zube a ƙasa ta ɗora hannu aka tana shirin rusa ihu tayi saurin toshe bakinta ta miƙe jiri na ɗibanta ta nufi kitchen ɗin parlour harta haɗa kayan wainar wata zuciyar ta hanata kawai tayi komawarta ɗaki.
Shima yana can yanata lelen matarsa ya manta da batun wata waina bai fito a ɗakin ba sai sha biyu da rabi sukayi sallama ya tafi ya kwanta.
Kacokan ya ɗauki kulawarsa da tattalinsa ya ɗorawa kanta ita da cikinta da ɗan su gefe kuma kullum sabbin abubuwa ɓullowa sukeyi zaman kullum ƙara rikicewa yakeyi Khausar ta dage kuma tana samun nasara donma ubangiji yana tare da me gaskiya a duk inda yake baya sanya makircinta yin dogon zango.
To yauma tun safe yayi asubancin tafiya Lagos zai karɓo saƙo dake tafiyarsa saura kwanaki uku, Beebah ke kwance a ɗaki ko parlourn ta kasa fitowa saboda zazzaɓi batasan wainar da ake toyawa a wajen ba sai yamma liƙis taji hargowar mutane a babban parlourn, zuciyarta bata bata taje taga su waye ba tunaninta mutanen Khausar ne.
A hankali taji hayaniyar na matsota ta tashi da sauri dake kwance take daga ita sai under sikert ta ɗauki hijjab batakai da sawa ba aka buɗe ƙofar aka shigo babu zato babu tsammani taji wani ƙato da aka cukuikuyo yana cewa “Hajiya ki taimakeni kice su sakeni wlh ba halina bane kece kika takura sai na zo Hajiya idan suka kasheni ya Iyata zatayi Ni kaɗai ta haifa saboda lafiyarta na yarda da sharaɗin da kika gindaya min na zuwa yau mijinki bayanan……”

 

 

Bata gane komai cikin maganganun da Saurayin yakeyi ba saidai bin waɗanda suke zagaye dashi da kallo da takeyi Mai Martaba Alh Lukman Mahaifin Khausar Hajiyan ƙofa Hajiyan soro da Jakadiya sai Baba Larai da keta sharar hawaye da Hudais a bayanta sai Hajiya mandiya Khausar da keta taunar cingam.
Cikin rawar murya Beebah tace “Wai meke faruwa ne? Waye kai?” Wata shaƙa Mai Martaba yayi mata data sanya numfashinta ɗauke wa yayi watsi da ita a gefe cikin ƙunar zuciya yace “Shiyasa tun farko naki amincewa Habeeb auren wannan bamagujiyar yarinyar saboda duk yanda kakai ga son kaga sunyi daidai bazasuyi maka daidai ba domin basu gaji daidai ɗin ba mutanen da suke bautar gumaka da duwatsu ace sune zaka zaɓawa ƴaƴanka matsayin uwa? Tur da wannan zaɓin wannan zaɓen tumun dare ne…..”
Hajiyan soro ce tace “Allah ya taimake ka duk da ance ba’a shaidar mutum amma fah komai yakan nuna alama Habeebatullah batayi kama da wacce zata aika…..”

 

Tsawa ya buga mata ya nuna ta da yatsa yace “Dake da Ummusalma bakinku ɗaya kuna goyan bayan rashin gaskiya to bari kiji Wlh tallahi na rantse da girman Allah yau yarinyar nan sai tabar cikin ahlina Ni a matsayina na uban daya haifi Habeeb na sawwake mata aurensa kuma mun karɓi Ibrahim ta fito ta fice min daga gidan ɗana kafin nasa a fitar da ita………

 

_Ku ƙara yimin uzuri my lovely Fan’s aradun Allah duk inda nayi kuna raina koda yake nasani soyayyarku da wannan labari me farin jini ke gajarce uzurinku gareni, wlh tun jiya nayi muku typing kamar yanda na alƙawarta wani uzurin yazo yasha kaina.🤗_

_Wannan Page Bonus ne bayanshi duk wani page da zaku gani paid ne kiji tsoron Allah ki biyani haƙƙina ki karanta cikin salama_
[5/18, 8:31 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button