Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 47

Sponsored Links

Yakamo hanunta yarike gam yana yar dariya, turo baki tace “kasaken” make mata kafada yayi yaja hanunta har gaban wardrobe, wani madaidaicin black hijab yaciro ya warware yasaka mata sanan yarike mata hannu ya kalleta yace “banason ana kallon mu goody bag dina muje naraka ki” akunyace ta dauke kai, tare suka fita daga dakin suna zuwa dining tafara kokarin kwace hanunta sabida mutanen datagani su kusan five ga manyan kuloli kusan 5 dasuka ajiye a tsakar falon, kin sakinta yay ahaka suka shigo falon, kasa daina kallonta su Ihsan sukayi, tana tsaye agefenshi tadan kallesu tace “ina kwanan ku” manyan matan guda biyune suka amsa da lpy lau, harara ya watsama su Ihsan yace “ku baku iya gaisuwa bane” atare suka taso sukazo inda take tsaye Ihsan ta mika mata hannu tace “ni sunana Ihsan his sister, welcome to our family” ahankali tai murmushi ta bata hannu, Ilham ma tace “sunana Ilham welcome to the family” murmushi tamata tace “thank you” Fa’iza ma tace “nice Fa’iza welcome and u are very very cute wlh” murmushi tai tace “thank you” hanunta Ihsan tarike tace “ga masu lalle nan mum tace amiki idan angama za’a kaiki chan family house ne, muje afara yimiki sai muyi dishing abinci kiyi breakfast ko” gyada musu kai tayi sukaja hanunta hakan yasa yasaketa, dan juyowa tai ta kallai tai raurau da ido, girgiza mata kai yayi alamun no, ya kalli Ihsan yace “ku kullan min da ita kuma, ko kuda karku bari ya tabata, bari naje” hanun yadaga mata alamun bye kunya taji yakamata ta dauke kai da sauri su Ihsan sunata mata dariya. Harara ya balla musu sanan ya juya yafita daga dakin yana kallon fuskar ta.
Lalle aka fara zizara mata, daya nayin na hannuwa dayar kuma na kafafu, Ihsan ta debo abinci tana bata abaki, Ilham kuma da Fa’iza sun kwanta akasa suna bata labarin Khaleel suna tafawa suna ihu, bakaramin tunamata da Farida sukayi ba, sosai taji tana kewan yar uwan nata da kyar ta iya tahana kanta yin kukan. In less than awa daya lallen ya bushe da aka mata sabida sanyin ac dakuma fanka dasuka kunna, wankewa akayi ba karamin kyau lallen amaryan yamata ba, sanan aka wanke mata gashi akai using handryer aka busar dakan sanan aka fara yaryada mata kitso yan mini mini. Sai Wuraren azahar suka gama sanan suka tafi yarage daga ita saisu Ihsan sosai tasaki jiki dasu sabida yanda suketa janta jiki kaman sun santa, sata tai wanka sukayi suka shiryata cikin wani ubansu lapaya, Fancy glamour suka dauko ta chanchara mata makeup din amare idan kun ganta bazakuce itabane, sanan suka kira Umma cewa sun gama, Umma tace “to, yanzu za’a zo ataho da ita”. Anty Hindu ne dawasu mata duk sunci gayu sukazo gidan, rungume Anty Hindu Islam tayi zatai kuka ta girgiza mata kai, sanan ta lullubeta mata fuska aka dauketa suna wakoki aka tafi da ita gida fuskarta a rufe, ta lapayan ta take hango yanda gidan ya cika da mutane sai taga gidan su kaman ba biki akeyi ba, wani babban falo taga an shiga da ita an zaunar da ita akan kujera Anty Hindu ta zauna a gefenta tana gaggaisawa da mutane anata guda, wata matace dataga suna kama da Khaleel taci gayu sosai tazo gaban su, Anty Hindu tace “ga maman mijinki nan” yaye lullubin fuskarta Ammi tayi, ahankali tasa hannu ta daga habarta kasa dago ido tayi sabida kunya hawaye taji ya gangaro, murmushi Ammi tayi tace “masha Allah daughter” sababbin kudi taciro ajaka yan 500 tadinga mata manni ana guda har saida kudin yakare sanan takoma ta zauna, haka ma Umma tazo ta wanketa da liki, duk wanda yazo Anty Hindu tana fadamata waye, sosai aka dinga ihu ana guda sanan aka tafi da ita bangaren Goggo, Goggo Kam harda rawa sabida murna tai manni tai manni har saida duka kudinta ya kare, wata malama tagani ta tashi tai musu wa’azi da addu’a sanan Goggo tace “to kowa yatafi abarmata amaryan ta tahuta” haka duk aka watse ya rage Anty Hindu da Ammi da Umma, tashi sukayi suka shiga uwar daka Goggo sunata magana, muryan Goggo taji tana cewa gaskiya anan zata zauna. Fitowa sukayi Ammi tazo ta dafata tace “kinajin yunwa insa akawo miki abinci daughter?” akunyace ta girgiza kai, murmushi Ammi tai ta kalli Anty Hindu tace “daughter na badai kunya ba” dariya Anty Hindu tayi daga nan duk suka fita suka basu wuri, sosai Anty Hindu tamata wa’azi da fada akan tabi mijinta, sanan tacemata Khaleel yamata sabon akwati set daban daban har 6, Abban ta duk yahada an wuce mata dasu gidanta na Abuja. Sai bayan sallan Isha Anty Hindu ta tafi ba karamin kuka tasha ba hakanan ta hakura tai shiru gyangyadi tafara yi akan kujeran Goggo sabida yanda tagaji gakuma kukan datayi hakan yasa Goggo tace “tashi ki shiga ciki ki kwanta abinki ki huta kinji, sannu yarnan yan iskan yaran nan duk sun wahalar dake” murmushi tai dan hakanan taji Goggo ta shiga ranta gatadai tsohuwa amma akwaita da tsafta, “au bazaki tasoba” Goggo tai maganar tana kokarin tashi daga kan tabarmar data shimfida a tsakar dakin, kamo hanunta tayi tace “muje ki kwanta bakisan bacci nada amfani ga lafiyar dan Adam ba” kofar uwar dakanta ta bude da gadon ke agyare tsaf tace “jeki kwanta abinki zanga dan kan uban dazaizo yafita dake, jekiyi baccin ki saida safe kinji yar albarka” gyada kai tayi sanan tace “saida safe Goggo” kwanciya tayi akan gadon da aka gyara tsaf dakin sai kamshin turaren wuta yake within 2 min bacci yay gaba da ita, Goggo dake kishingide akan tabarma taji ana kokarin bude kofar ta tashi tayi ta zauna da kyau tana wawware ido, Khaleel ne ya shigo sanye da doguwar jallabiya sai kamshi yake yawani daure fuska yace “ina matata? Daga barinta tazo gidan naku shikenan kuma bakusan ku komar da ita inda kuka daukotaba?” ko kallonshi Goggo bataiba taja filo abinta takara kwanciya sanan tace “jeka tambayi uwarka, bata fadama daga yanzu anan gida zata zama ba, to saikun koma Abuja ne zata tare a gidanka” karaso wa ciki yay yace “nida matar tawa lallai nema” yazo zai wuce yay bedroom Goggo ta mike tsaye da sauri tasha gabanshi ta rike kugu hakan yasa yaci birki yana kallonta cike da bacin rai, dariya tayi tarike haba tace “mara kunyar banza, fitarmin daga daki tunda bakai ka ginamin ba wlh kona hadaka da ubanka” ganin Goggo ta daure babu alamun wasa tawani rike kugu yasa yajuya yafita daga dakin rai abace, Goggo tarakashi da dariya sanan ta maida kofa ta rufe harda saka Sakata tace “fitinannun yara” kwanciya tayi abinta rai fes tace “dan kanuba to yarinya sai tasha gyara sanan za’abaka, idanma nabari ka kara sata a ido ba sunana Lami ba” lumshe ido tayi tana sauke ajiyar zuciya. Direct part din Ammi yawuce duk ranshi a dagule Yusuf yagani zaune afalo yana jiran Ihsan tagama dafamai Indomie dayace tadafamai, yana ganinshi ya gimtse dariyar datazomai, ko kallonshi baiyi ba ya shiga bedroom din Ammi wata kawarta ya tarar tana magana da ita hakan yasa yaje kusa da ita ya zauna, sallamar matan tayi sanan ta juyo ta kalleshi tace “Ya akayi Son?” da kyar ya iya cewa “Ammi wai kekika cema Goggo karta bari Islam tabini anan zata dinga kwana” Ammi taso tai dariya da kyar ta saita kanta sanan ta kallai tace “eh nafiso kawai ran Sunday idan duk mun tafi Abujan basai ta tare wajenkaba, yanzu ga duka family anan mezataje tai ita kadai achan gidan kadaici zai isheta mana” zaiyi magana tace “ka bacemin daga nan I have alot of things to do” tashi yay yafita daga dakin duk ranshi acinkushe ta gefen ido yaga Yusuf ya ijiye Indomie hanunshi yanamai dariya ciki ciki haka yay kaman bai ganshi ba yana zuwa dai dai inda yake yadau plate din Indomie yace “wlh bazaka ci shiba” Yusuf ya kwalama Ammi kira yace “Ammi kinga wai akaina zai huce takaicin shi” da sauri Khaleel yafita yay part dinsu ya kulle kofa ya ijiye Indomie anan kan kujera yawuce bedroom yafada kan gado kasa bacci yayi sai juye juye yake daga baya yatashi ya shiga bayi kawai ya dauro alwala yazo ya kabbarta salla.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button