Hausa NovelsWata karuwa Hausa Novel

Wata karuwa 22

Sponsored Links

Wannan kuma meye” bata samu amsa ba wata doguwar tankasheshiyar mata fara sol ta shigo ta zauna a gefen gadon da Hausarta da bata fita sosai tace mata “sannu ammarya” sunkuyar da kanta tayi matar tayi murmushi tace “yau za’ayi bikin kirɓa Sakwara Mother tace bazaki iyaba saboda haka akaiki part nata idan anyi dare ki ɓuya acan”
Zubawa matar idanu tayi tace “Wace Mother?” Da sauri matar ta ɗago tace “Mama na mijinki itane Mother ki tashi muje kada yan bugun Sakwara suzo” suna haka wasu mata suka sawo kai ɗakin matar tayi saurin rufeta ashe idon wata ya faɗa kanta da yarensu tace “Gatacan” kafin matar nan tayi wani yunƙuri sunyi kanta sun cafketa sun ɗagata cak sun fice da ita daga ɗakin suna cillata sama suna cafewa suna tafi suna rawa da manyan ɗuwaiwakansu.
Tsakiyar wani babban fili suka direta ta buɗe idanunta ƙirjinta ya doka da ƙarfi ganin wasu kankama²n turame da wasu jibga²n taɓare sai wasu tukwane manya guda kusan goma an cika su da doya sai zaɓalɓala sukeyi.

 

Bin kowa ta rinƙayi da kallo cikin abinda bai wucce second ba wasu hawaye masu ɗumi suka shiga zarya a idanunta ga wani sanyi da yake ratsata kasancewarta cikin sabuwar al’ada da bata saba da itaba itakam wannan lamari yayi mata nauyi gansamemiyar mace ta rinƙa yawo tinƙi tinƙi a ranta take tambayar anya ma waɗannan mutanen musulmi ne?
Tana cikin wannan tunanin taji an taɓa ta dawo hayyacinta ta zuba musu ido yanda suketa tsamo doyar daga ruwan suna zubawa a turmi wani turmi ne da yasha kwalliya gabaɗaya cikin turmin an naɗeshi da zani irin na jikinta hatta taɓaryar itama haka take aka miƙo mata taɓaryar ta tsaya tana kallonsu ba su take kallo ba tunanin ta yanda zata fara dukan sakwarar kawai takeyi taji wata tace “Kiyi zaki iya idan kikaji a ranki saboda mijinki zakiyi Allah zai haɗa miki ƙarfinsa dana danginsa gabaɗaya ki daka masa Sakwara kibashi a baki yaci wannan shine tabbacin zaki iya kula dashi kinsan mu culture namu duk amaryar data kasa dakawa angonta Sakwara to batada kwarjini kuma bata samun albarkar dodo”

Related Articles

 

Kuka ta saka ta riƙe hannun matar tace “Na shiga uku Ni Aneesah Mama ki taimakamin bazan iyaba banida lfyr ƙirji inada athmer idan ta tashi inashan wahala” duk matan gurin kallonta sukeyi cike da tausayi su kansu sunsan ba kowacce ƙabila ce zata iya da wannan al’adar tasu ba balle ita da yanayinta ma bai nuna tanada wani wadataccen karfi a jikinta ba” wannan matar ce ta dafata tace “Sorry Mother haka zaki gwada zaki iya” ganin taja suma sunja yasata shahadar karɓar taɓaryar tayi bismilla ta ɗagata ta buga aikuwa gabaɗaya doyar ta tarwatse suka hau ihu suna mata dariya itakuma banda kuka babu abinda takeyi tayi tunanin da doyar ta zube zasu ƙyaleta ashe wasa ma farin girki kawai sai taga sun kuma zuma mata wata.
Dakiya ta sanyawa zuciyarta ta fara dukan sakwarar tanayi suna tafi suna waƙoƙinsu na al’ada gabaɗaya ta jigata gashi bataga alamun sakwarar zata daku a gurinta ba kuka takeyi sosai tana jefa taɓaryar sama tana cafewa taji gurin yayi tsit hakan yabata damar dakatawa ta ɗora kanta saman taɓaryar tana haki, ƙamshin turarensa ne yasata juyowa suka zubawa juna ido yana takowa gareta da wani taku na izza yana fuskarsa a ɗaure babu alamun wasa.

 

Mutanen dake take masa baya duk suka juya musu baya sukayi ƙasa da kansu, tsayawa yayi a gabanta duk da kasancewarsa ba dogo ba sosai amma yafita tsayi wannan tasa taganta iyakar ƙirjinsa tayi ƙasa da idanunta ko a baya bata iya jurar haɗa idanu da Abdul-Ahad balle yanzu da ya ƙara mata matuƙar kwarjini.
Hannunsa ya ɗora a kafaɗarta yaja numfashi ya sunkuya yayi kissing nata yace “Aneey bakya nemana ko?” Shiru tayi masa yayi murmushi yace “kinga sabuwar rayuwa daban da ta garinku ko?” Nanma batace masa komai ba yaja numfashi yace “halan kina fasting na magana ne ko Aneey?” Nanma batace komai ba ya ɗago fuskarta ga mamakinsa yaga kuka takeyi sosai harda majina kafin yayi magana ta durƙushe ta riƙe ƙafarsa tace “Meyasa dole saini Abdu wlh ban shirya rayuwa dakai ba bazan iya rayuwa a wannan garin naku ba ni al’adunku da yanayin mutanenku sunamin kama da bana cikin jinsina na mutane Abdu komanku yafimin kama da wanda nake gani a Nigerian film nikam Abdu ka tausaya min ka barni Allah banason haɗa rayuwata da taka inajin tsoron abinda zai iya biyo baya Please Abdu ka tabbatar min da soyayyar nan Indai ta gaske ce ta hanyar fita daga rayuwa…..”

 

Rufe mata baki yayi da ƙirjinsa lkcn daya ɗagota ya matseta sosai kowa dake gurin ya rinƙa zame jikinsa suna sulalewa saida gurin ya rage iyakar excourt ɗinsa ne matseta yayi sosai yana jan numfashi me kashe jiki ya ɗora haɓarsa a kanta ƙamshin turaren gashinta yana bugarsa yanajin wani yanayi me narkar da zuciya baisan meye yasa Allah ya jarabceshi da tsananin ƙaunar Aneey ba ya fahimci bayan son faranta zuciyar ƴar uwarta harma da ƙiyayyarsa a zuciyarta data kasa bata damar sakin jiki dashi.
Fasali yaja ya janyeta saboda spark ɗin da jijiyoyinsa suka fara bayarwa idan yaci gaba da mannata da jikinsa tsaf komai zai iya faruwa cikin murya me nuna gajiya ya dubi wata hadima yace “ki kaita gurin Mother banason aci gaba da wahalar da ita” rusunawa tayi tace “gdy nake ranka shi daɗe” kama hannun Aneey matar tayi suka nufi sashin Mother yabita da kallo yana haɗiyar yawu tun jiya yakeson yaji ɗumin matarsa ya kasa samun ko ganinta sosai feeling ke damunsa baya sha’awar zuba ruwansa a waje kamar yanda ya saba burinsa da fatansa tunda yayi aure ya daina aikata zina shi yasa yaketa daurewa gashi bikin al’adar tasu bana gamawar wuri ba a ƙalla sai an shafe wata guda anayi kuma bai isa yaganta ba saidai satar hanya yauma Jimba ce taje ta sanar dashi abinda ke faruwa shiyasa ma Mother ta bashi damar ganin Aneesan badon haka ba da sai ancishi tara ya karya doka girgiza kai yayi ya juya suka bar gurin.

 

Part ɗinsa ya nufa ya sallami excourt ɗin nasa ya kulle kofa ya shiga katafaren ɗakin nasa da aka ƙawatashi da duk wani nau’i na jin daɗi ya cire rigar ƴar sharar dake jikinsa ya cire T-shert ɗin da dogon wandon ya rage dagashi sai boxes da vest ya zauna a ƙasa yaja tumtim ya tada kansa dashi ya kishingiɗa ya lumshe idonsa a yanayin da yake ciki gindi kawai yakeson ci shikam koma wanne irin ne bazai iya sake kwana batare da yaci ba, wayarsa ya ɗauka ya kira layin Mother ta daɗe tana ring sannan ta ɗaga ya gaisheta ta amsa tare da cewa little meye take faruwa matarka tayi bacci” ƙasa yayi da muryarsa yace “Please Mom Ina buƙatar kulawa banida lfy fah” nandanan hankalinta ya tashi tace “Ina keyi maka ciwo” shiru yayi mata tace “kayi mgn mana little” Numfashi yaja ya sauke yace “Mom kibani Matana Please inason najita a jikina” shiru Mom tayi can tace “Kasan ba’a haka ko?” Katseta yayi da cewa Mom please wlh zan jigata idan kikaƙi little ɗinki ne fah”
Murmushi tayi tace “ka koyi juriya zan baka matarka amma sai an gama bikin al’ada little yarinyar nan ma ba daidai takeba da mukace kaje ka taho da ita saida ka kusanceta dakai da little father baku da hƙr akan mata so nikam bazan saɓawa umarnin dodo ba kai ka gde ma iya wata ɗaya aka baka su yayyanka daka masu wata uku sai masu wata shidda suna kallon matan basuda amfani a gurinsu su ya sukayi” kashe wayarta tayi yayi saurin miƙewa yana kiran Mom bafa addini bane don Allah kibani Wyf nayi miki alƙawarin babu wanda zai san a gurina ta kwana……”

 

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•
_*WATA KARUWAA* Na kuɗine ,Zafafa ne🔥 Cikin jerin gwanon *TAURARI UKU🔥🔥🔥✨ MASU HASKAWA💡* Da suke zuwa maku daga alƙalumman gwanayen marubutanku,Taurari Uku ✨Masu Tashe ,wanda suka haɗa da:_
_*WATA KARUWA* Daga Alƙalamar OUM HAIRAN_
_*SIYASA TAH* Daga Alƙalamar MAMAN TEDDY_
_*AUREN SHA’AWA* Daga Alƙalamar OUM APHNAN Karku bari a baku labari,zaku samesu cikin sassauƙan farashin da babu kamarsu_
_Regular_
Zaki samu guda *Ɗaya* ₦300
*Biyu* ₦500
*Duka ukun* ₦800

_Manyan mata kuma ƙasaitattu ba’a barku a baya ba,ganaku kaɗan cikin tunjimin aljihunku_
*Ɗaya* ₦1000
*Biyu* ₦1500
*Duka ukun* ₦2000

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

_Zaki biya ta wannan Bank account ɗin_
0255526235
_Fauziyya Tasi’u. GTbank_

Ko katin MTN
_Zaki biya ta wannan number_
08081202932

Ko VTU
_Zaki biya Ta wannan Number_
09065990265

•┈┈┈••✦✿✦••┈┈┈•

*SHAIDAR BIYANKI SAI KI TURA TA NAN*
09065990265

♡♡ “`Sai munjiku Masoyan Amana….Share💃👍Share💃💃👍And Share💃💃💃👍Habibties Allah ka barmu da masu sonmu😍😍😍“`♡♡

 

*OUM HAIRAN*
[12/16, 2:34 PM] Oum Hairan&Affan: *Ki tausaya karki fitar mana dashi in kin siya ,Inkin san siya zakiyi don kiyi sharing don Allah karki siya mun hutashsheki,Haƙƙin mallakar marubutanne su kaɗai,Ki tausaya masu plz ,Inkinga wani pages na yawo to na sata ne ki runtse idonki karki karanta ki biyo ki siya ,Mungode*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button