Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 15-16

Sponsored Links

15-16*

★★★~~~★★★~~~★★★

Yana faɗin haka ya saki hannunta ya miƙe yana cewa “ki kula da kanki” ajiyar zuciya ta sauke tabisa da kallo hakanan zuciyarta tayi mata babu daɗi ta tsinci kanta da kewarsa da tunanin makomarta idan bayanan da wannan ta koma ta kwanta a gadon zuciyarta nayi mata babu daɗi hawaye na bin gefen idanunta tana sharewa taji an buɗe ƙofar an shigo bata ɗago ba Khalisa ta zauna a gefenta tace “Beebah faɗa wannan masifaffen yayi Miki ko?” Numfashi ta sauke ta tashi zaune tana gyara rigarta tace “Wa kenan?” Tana binta da kallo tace “Bro mana naga ya fita a dakin nan yanzun kuma nasan idan ba masifarsa ce ta ciyoshi ba baya shiga ɗakin mu bare kuma naki” ƙasa tayi da kanta tace “to Meye laifi Inma faɗan yayimin ai ya isane bakiji abinda manya suke cewa ba “yaro yi kuka in ka rasa me maka faɗa” saboda haka Ni daɗi ma naji da yasan da zamana har yaji a ransa na cancanci yayimin tsawa akan rayuwata”
Jinjina kai Khalisa tayi tace “hakane Allah yasa mu dace amma nikam haushi nakeji idan anamin faɗa saboda wani abin ma bai kai laifi ba yanzu ranar nan da akasa babban Yaya ya zane Amna da Khaulat laifin baifa kai ba wai kawai don sunyi video sun ɗora a TikTok shine akayi kamar za’a kashesu wlh yaran Saida suka bani tausayi”
Sauya akalar mgnr tayi da cewa “yaushe zaki fara yimin lesson na turancin” don batamasan Meye TikTok ɗin ba.

Related Articles

 

Murmushi Khaly tayi tace “toni yanzu Beebah ta ina zan fara a koya Miki turanci Ni abinda naga yafi kuma zan shawarci Kilishi a nema Miki makaranta ki shiga sai a rinƙa yi Miki lesson a gda tunda da alama ƙwanyarki tana ja zaki gane komai a hankali” kallonta tayi tace “Khaly nayi fah karatu a ƙauyenmu nida Yaya Tani ne kawai mukayi makarantar primary da secondary aji uku daga wasu ƙauyukan ma idan aka rubuto sako aka aiko kiranmu akeyi mu karanta mutuwar yaya Tani ne tasa aka dakatar da karatuna” daɗi ne ya cika Khaly tace “kay alhmdllh amma naji daɗi yanzu muje gurin Kilishi ai ba wani girma kikayi ba kawai a sama Miki Form ki juya senior secondary inyaso ma a saki a tamu tunda muma bamu gama ba sauranmu 1 years tashi muje hakama za’ayi”
Hakan kuwa akayi suna zuwa suka sanarwa Kilishi tayi murna da hakan tace “Zan kira Mas’ud zaiyi mata Screening indai takai za asan yanda za’ayi” Beebah tayi gdy sukaje suka kwanta sunata murna tama manta da lissafin tafiyar Habeeb.

 

Washegari kuma da safe Hajiya Kilishi tasa aka ɗebe su a mota aka kaisu gyaran gashi wannan tasa basuyi sallama ba hakan baiyi masa daɗi ba yaso yaganta suyi sallama amma hakan ya faskara da zai tafi ne ya shiga ɗakinta ya ajiye mata wani tsadadden card a gefen kayanta sai wani ƙaramin akwatu da ATM card da wasu takardu.
Sai yamma liƙis suka dawo sun kuwa yi muguwar gajiya suka zube a parlourn suna mayar da numfashi kowacce ta jefar da mayafin itakam Beebah kwanciya tayi saboda sosai tafi kowa gajiya Gara su sun saba da komai da akayi musu ita kuwa komai sabo ne a gurinta hakance tasa jikinta ya gaji zuciyarta ta gaji brain nata shima ya gaji ta baje a parlourn tana juyi gashin nan yasha gyara sai kyalli yake abin ba’a cewa komai gashi an gyara musu farcensu harda jan lalle ya zauna das a fatarta tayi wani sihirtaccen kyau na ban mamaki Kilishi da kanta satar kallon surukar tata takeyi duk da yammatan nata ma ba baya ba amma sun samu uwarsu a fannin kyau hasken fata kawai zasu faɗa mata sai murjewa itama kuma fatar tata me karɓar sauyi ce cikin sati biyun har wani glowing takeyi.
Gyaran murya Kilishi tayi tace “nayi magana da Dr Mas’ud da dare zai zo Habeebah ki zama ready” cikin ɗoki tace “Ok Hajiya”

 

Miƙewa tayi ta nufi ɗakinta ta cire kayanta ta ɗaura towel ta faɗa wanka dake tana fashin sallah alwala kawai ta ɗaura kamar yanda Kilishi ta koyar da ita zama da alwala a kowanne lokaci ta dawo ta zauna saman dressing stool ta gyara gashinta ta ɗaure da ribbon a tsakiya ya sauka har tsakiyar bayanta ta shafa powder ita kanta tasan tayi kyau na mamaki ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo taji an buɗe ƙofar ta madubi taga yanda suke kallonta Hudah tace “Barakallahu ahsanal kaliƙin Beebah wlh koni mace ban gajiya da kallonki saima boko ta ratsaki tukunna” murmushi tayi ta zauna tace.
“Yunwa nakeji Wlh” dariya sukayi sukace “waima kekam wanne irin cikine dake zakuwa ki iya azumin Ramadan gashinan yana tahowa saura wata biyu?” Harararsu tayi ta miƙe tana cewa “in kukayi wasa ma saina fiku yi” tana mgnr tana rankwashinsu suka kuwa zuba a guje ta zille musu ta nufi ɗakin hutawar Kilishi ta shige bayanta ta ƙanƙameta tana dariya itama sun bata dariya tace.
“Dama haka kukeso mala’ikin naku ya tafi zaku addabeni zakuyi bayani rubuta duk kalar rashin jinku zankeyi a littafi in yazo na bashi” zaro ido Beebah tayi tace “na shiga uku an fasa aurena Kilishi Wlh idan kika haɗamu da Bro kisa ne kawai nikam na nutsu na daina kai taking care Wlh Bro zai hukunta ku babu ruwana”

 

Hudah ce tace “ai kafin ya dawo ta manta yauwa Kilishi wannan karon wacce ƙasa zamuje siyan kayan sallah?” Harararsu tayi tace “Aifa nice marainiyar wayon ku to kuje ku tambayi Mai martaba mana ko kuma ku kira Babban Yaya ku tambayeshi” langwabar dakai Khaly tayi tace “Ai ko Ya Naseer bamu isa mu tambaya ba yanzu asamu gwale² Hajiya kece dai zaki faɗa mana inda zamu Ni dama zaki yarda Allah banson azumi a kasar nan Dubai nakeson muje muyi azumi ko Saudi” Hajiya Kilishi akwai son farantawa yaranta hakanan tace “Shikenan zansa ayima Habeebah passport saiku tafi Saudiyya tunda ita bata taɓayin Umrah ba in yaso dagacan in kunyi sati biyu saiku wucce Dubai ɗin” wani tsalle sukayi suka rungumeta itakam Beebah jikinta ne ya mutu komai ya kwace mata zuciyarta tayi rauni “to wannan wanne irin family ne Habeeb ya koka mata matsaloli haka Hajiya Kilishi ranar da aka kawota amma ita har yanzu bata fara ganin matsalar ba ya kawota matsayin ƴar aiki amma mahaifiyarsa ta ɗaga darajar ta ta mayar da ita ƴa a gurinta Bama ta jinginata da aikin in har ba’a gaban sauran mutanen gidan bane, su kansu mutanen gidan cewa suke Hajiya wannan yarinyar tamafi Sakina samun fada a gurinki” saidai tayi murmushi tace “to ai kowa da kalar baiwarsa wai yau ita Habiba bamagujiya ita ce zata tafi ƙasa me tsarki ta gana da ubangijinta data sanshi ta fahimceshi kwanan nan?”
Saurin share hawayenta tayi saboda tasan sarai Kilishi batason kuka ta miƙe zata fita ta riƙota tace “Akwai damuwa ne Habeebatullah?” Girgiza kai tayi ta rusuna ta kama hannun Kilishi tace “a duk lkcn da kukayimin wani abin alkhairi nakanji bankai nan ba yaushe matsayina yakai aimin haka sannan shine sila kuma tunanin mahaifiyata da Babana yakan bijiromin irin rabuwar da mukayi dasu dutsi a hannun riga dominsa…..”

 

Rufe mata baki tayi lkcn da Hajiyan soro take shigowa tace “Shikenan Habeebah Sarkin rigima bazaa kuma ba ku tashi kuje” miƙewa sukayi dukkansu Hajiyan soro tabi Habeeba da harara bata daina harararta ba Saida suka fice ita kanta Beebah ta fahimci Hajiyan soro da Hajiyan ƙofa basa sonta saboda kullum cikin harararta suke wannan tasa bata fiye shiga sharafinsu da ƴaƴansu ba komanta tafi yinsa a inda aka ajeta wai a haka ma gara Hajiyan soro ita Hajiyan ƙofa yaranta ma ta hanasu mu’amala da Habeebah a cewar ta ita kawai yarinyar batayi mata ba har tana cewa garin yakabe²n Kilishi saita ɗauko musu ajalinsu sauƙin ma da take samu dake ana shayin Kilishi da ƴaƴanta tunda sune manya kuma sune masu faɗa aji a gidan shine kawai yasa take shanyarta a inda takeso.
Kilishi ce ta katse shirun da cewa “Soro ya akayi ne?” Hankalinta ta dawo dashi ga Kilishi tace “Gulma ajali Hausawa sunce in baayi ba a mutu yanzu na fito daga gurin Mai martaba ina turakarsa yana Parlour naji Wannan makirin Lukman ya shigo yana cewa wai akwai wani abu da aka rufe a gdannan da ya kasa gane menene amma tabbas bincike yana nuna masa akwai wata rufaffiyar ƙura da take shirin tashi a gdannan, to kinsan Mai martaba bai fiye sauraron shirme nan ya dagansa tsawa yace baison shiririta, shine suka koma mgnr ƴaƴan nan shine Alh Lukman ɗin yake cewa tunda an samu Habeeb ɗin ya tafi yanzu ayi maganar aurensa da Khausar shi kuma Naseer za’a haɗashi da Mufeedah Yassir da Hanifah su kuma matan Khaulatu da Aliyu Amna da Bashir Khalisa da Ibrahim Hudah da Isma’il kuma Mai martaba yace dukkan auren za’ayi su ne nanda shekara ɗaya….”

 

Gumi ne ya karyowa Kilishi tayi saurin tashi zaune tace “Habibu da Khausar Mai martaba ya manta yanada wadda yakeso bayan nan ma ya manta cewa kaf wannan family ɗin babu yarinyar da Habeeb ya tsana irin Khausar kayy ina gsky a sake lale nikam inajin tsoron lamarin Habeeb irin kafiyar mahaifinsa gareshi” taɓe baki Hajiyan soro tayi tace “Yo tunda bashi ya haifi kansa ba haihuwarsa akayi ai dole ya haƙura kamar yanda kowa ya hkr Ni Wlh nama ɗauka ya hƙr da yarinyar nan daya sheƙa yaga babu ƙwayar”
Miƙewa Kilishi tayi tace “Shi Allah Sarkin daidai ne amma Wlh nima ban karɓi Khausar matsayin suruka ba haba koda dai naka sai naka amma ai kowacce ƙwarya tanada abokin burmi Meye Habeebu zaiyi da Khausar kawai saboda yaro bashi da ƴanci shine za’a koramin shi Japan sannan ayi masa tukuici da wannan fitsararriyar yarinyar da iyayenta suka jiƙa suka lalata to wallahi da sake dadai abawa me kaza kai gara a bashi romon koda bread ya lasa”

 

Riƙe haɓa Hajiyan soro tayi tace “Ni Zulaihatu to banda abinki Ummusalma wannan hukunci ai kinsan kamar da ƙasa tabbatuwarsa inji me ciwon ido tunda suka shiga suka kulle da wannan makirin ƙanin nasa bare dama ku ya daɗe yana haƙonku kada ki manta tun akan Hisham babban Yaya yaso haɗashi da kanwar Hajiya Indo Safiyya kuka zille dole aka barta to yanzu kuma kema kinsan ba ƙaramin shiri zakiyi na rusa wannan shiri ba domin kuwa Khausar ƴarsa ce ta cikinsa daga ita sai Aliyu ya haifa kinsan kuwa ko duniya zata tashi saidai ta watse don kuwa me hana auren nan sai ƙudurar Allah babba”
Sosuwar da zuciyar Hajiya Kilishi tayi ta sanyata barin dakin hutun ta nufi ɗakinta tana kaiwa da kawowa saboda ba Habeeb ba ita kanta Allah ya sani bata kaunar jinin Hajiya Indo ganin shaiɗan yanata yimata ayyane ayyane yasata dauro alwala ta tayar da sallah tana roƙon Allah ya bawa Habeeb mafita cikin wannan cukurkuɗaɗɗen lamari na rayuwarsa gabaɗaya sai taji tana tausayinsu dagashi har Habeebah ta shaida ta haƙiƙance Habeebah nason mijinta so na gaske shima kuma son kyautar rai yakeyiwa matarsa batajin akwai wani dalili da zaisa Habeeb ya iya hƙr da Habeebatullah matuƙar ba mutuwa ba.

 

_IDAN KIKA KARANTAR LITTAFI BAKI BIYANI BA BAN YAFE BA._
[4/18, 1:30 PM] AM OUM HAIRAN: BMGJY

 

KIYIWA GIRMAN ALLAH KI BIYANI HAƘƘINA KAFIN KI KARANTA NORMAL 300 PC 600, KI BIYA TA WANNAN HANYOYIN ACCT DETAILS 0255526235 FAUZIYYA TASIU GTBANK KO KATIN WAYA MTN TA WHATSAPP NUMBER NA 09013718242 ƳAN NIGER ZAKU TURA KATIN AIRTEL 400CF TA WANNAN NUMBER +227 95 04 58 22 SAIKU TUROMIN SCREENSHOT NA SHAIDAR KUN TURA MATA NIKUMA NASAKU A GROUP.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button