Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 35-36

Sponsored Links

Rayuwa me daɗi suke gudanarwa Beebah na rainon cikinta da yake shan kulawa wajen mamallakinsa itama Khausar salo taci alwashin canzawa na nuna kulawarta ga Beebah, duk da Beebah taƙi sakin jikinta da ita hakan bai hanata shige mata da nuna mata ai duk ɗaya suke ba.
Itakam Beebah taƙi yarda da wannan tsarin wanda hakan ya jawa Khausar samun sassauci daga gogan tunda shi a rayuwarsa indai ka nuna kanason Habeebatullah da abinda ke cikinta to babu yakai a duniyarsa, takai komai Khausar keyi a gdan ko lkcn da yayi nufin dauko musu ƴan aiki cewa tayi basa buƙata a bari sai Beebah ta haihu Inma za’a dauko ɗin don a ganinta ita bataga aikin da za’a ɗaukowa ƴan aikin ba.
Sanyin yanayin data nuna yasa shima ya sassauta mata yake yi mata mu’amala irin wacce zai iya saidai har yanzun babu abinda ya taɓa shiga tsakaninsu na auratayya, duk wata walwala da yakeyi idan ta shigo masa ɗaki yanzu zai rufe ido yaci mutuncinta, to itama dake ba jurai bace wajen ɗaukar wulaƙanci yasata tattarashi ta watsar ta nemawa kanta wata mafitar.

 

Tasani komai nisan gona dole zaaje kunyar ƙarshe musamman data fahimci shi ɗin irin mazan nan ne da basa iya jurewa rashin mace a kusa dasu domin kuwa cikin kwana biyun da yakeyi a part ɗin ta ya rinƙa ƙuncin rai kenan in taga walwalarsa to ya koma gurin gimbiyarsa ne.
Duk da janye masa tallafin da Mai Martaba yayi hakan baisa sun tagayyara ba cikin lkcn ne kuma ya samu aiki da wani babban campanyn jiragen sama dake England sunyi murna sosai da samuwar aikin nasa saidai damuwar ɗaya ce zai rinƙa tafiya ne sai lokaci lokaci zaike dawowa, wannan ce kawai ta sawa nishadinsu birki itakam Khausar murna takeyi da hakan ko babu komai kowa ta rasa tunda yace bazai tafi da Gimbiyar tasa ba sai yaje yaga yanayin gurin, kuma koma ba haka ba cikinta ya soma girma watanni shidda ya tafi bakwai ya kamata ta zauna waje ɗaya.
Ana gobe zai tafi dagashi har Beebah kamar waɗanda akayiwa mutuwa haka suka kasance babu walwala don ma Khausar na amfani da kirsarta da shekaru da tafi Beebah tana ɗauke mata hankali a fakaice tana nuna mata ai cigabansu ne gabaɗaya da wannan Beebah ta ɗan saki jikinta, tare da Khausar suka haɗa masa kayansa suka shirya masa a jakar da zai tafi da ita har cincin da cake da donut suka shirya masa kayan snacks kala-kala harda na banza duk suka haɗa masa dake ranar ba’a ɗakin Beebah zai kwana ba haka ya kwana kamar Maraya Khausar tayi iya yinta taga ya saki jiki da ita amma fir yaƙi kwana yayi yana zagaya ɗakin shikam badon yasan Beebah bazata taɓa bashi hadin kai ba da ya tafi yaje ya samu nutsuwa da ita.

Related Articles

 

Tsarin tafiyarsa ta safe ce tun asuba da sukaci gaba da shirye-shiryensu yakebin Beebah a gindi a gindi duk inda tasa ƙafarta shima sama yakeyi, sarai Khausar ta lura da yanayinsa koda yanayin yanda doguwar rigar jallabiyar jikinsa take a ɗage saitin Sandar majalisar sa.
Itako Beebah dake ba abinda yake gabanta kenan ba kuma hankalin ma sama² ne yasa batama fahimci halin da yake ciki ba sai lokacin da Khausar ta matso saitin kunnenta tace “Ki bawa Hero ɗinki tallafi jin dadin namu zata ɓalle a jikinsa fah…..” Sai lokacin ta lura aikuwa gabanta ya faɗi cikinta bayason sex ko kaɗan indai Habeeb ya kusance ta yini zatayi mararta na ciwo gashi ta fahimci irin kallon da yake binta dashi na jiran damarsa ne kawai.

 

Miƙewa Khausar tayi ta ɗauki ruwa a freegde ta fice musu daga kitchen ɗin, kamar me jira haka ya nufota ta miƙe da sauri har mararta na amsawa ta ɗan ja baya ya riƙo hannunta da sauri yace.
“Please Wyf karkimin haka tafiya zanyi ki bani nutsuwa don Allah” noƙe kafada tayi ta turo baki tace “Ni meye yasa kake damuna ne naga da mace ka kwana Hero kake fahimtar uzurina wlh wahala….” Rufe mata baki yayi ya matso da bakinsa saitin fuskarta yace “nasani a hankali zan biki Please…..” Yanayinsa ne ya kashenta jiki tasani kome zatace masa ba sauraronta zaiyi ba don tabbatar shiɗin daban ne a kitchen ya rareta tas taso hanawa taga ya jima da nisawa hakanan tayi masa doggie yayi abinda zai yi ya samu gamsasshiyar nutsuwa ya kwantar da ƙirjinsa a bayanta ta zame tayi ƙasa tana dafe cikinta daya dunƙule mata waje ɗaya.
Hannunsa yasa ya shafo cikinta yayi murmushi yace “Very soon zan dawo bby kayi hkr nasan zakayi missing Dad ɗinka” janyewa tayi ta sanya kayanta ta nufi ƙofar ta buɗe ta baya ta nufi part ɗinta ta faɗa wanka tana wankan taji shigowarsa ɗakinsa ya shiga yayi wanka ya fara shirinsa ta fito ta tayashi shiryawa.

 

Sallama yayi musu me kyau suka rakashi airport Najeeb ne yake drivern ɗin yana tsokanar Habeebah dake itan ba ma’abociyar son hayaniya bace saidai tayi murmushi wani kuma abin khausar ta rama mata, ita kewar mijinta kawai itane ta dameta musamman da sukaje airport ya matso ya riƙe hannunta ya zubanta manyan idanunsa.
Ya jima da fahimtar yanayinta hakan yasashi ɗago kanta yayi kissing lips nata yace “ko mutuwa nayi kiji a ranki ni nakine Wyf bare ina raye rabuwa ce ta ɗan lokaci, amana nabar Miki kanki da Bbyna da duk abinda ya shafeni ki kulamin da kanki!….” Hawaye ta share masu dumi ta cire hannunta a nasa ta kaɗa masa kai tace “Insha Allahu zanyi bakin ƙoƙarina kaima ka kulamin da kanka.
Sakinta yayi ya juya da sauri ya nufi matakalar jirgin ya shiga itama ta juya tana tsane hawaye da tisue ta shige mota suka juya suka nufi gidan sarauta Gaban Beebah na faduwa suka shiga gdan sukayi parking ya saukesu Khausar dake ƴar gda ce ta nufi part ɗin Hajiyan soro itakam Beebah gaisawa kawai sukayi ta miƙe ta nufi sashin Hajiya Kilishi tana babban parlour tana ganinta ta miƙe ta tarota tana cewa.

 

Sarkin yawo kukan bakwa gajiya Beebah ke ko nauyin jikinki bakiji koda yake ɗaurin gindi kika samu nayi magana mijinki yace motsa jiki kikeyi” ƙasa tayi da kanta cikin ladabi tace “Wlh Kilishi ciwon mara ne yake damuna har bacci yake hanani” cikin jimami tace “Subhanallahi kuma kunje asibiti?”
Ɗaga mata kai tayi tace “Munje sun duba sunce kwanciyar Bbyn ne ba daidai ba amma suna saka ran zai koma daidai kafin lokacin haihuwa” ajiyar zuciya Kilishi tayi tace “To Allah yasa yanzu me kikeso kici me za’a dafa Miki?” Dariya tayi sarai Kilishi tasan halinta itama tayi dariya tace “shikenan in kin gama dariyar sai ki faɗa” rufe idonta tayi tace “Kunun tsamiya nakeso da wainar gero….” Zaro ido Kilishi tayi tace “taɓ amma Wannan jikan namu akwaisa da iya baro aiki bari nasa ayi Miki kije ki kwanta kafin a gama”

 

Ɗakin Kilishi tashige ta kwanta bata kuwa jima ba bacci yayi gaba da ita ba ita ta tashi ba sai yamma likis ta tashi ta tarar duk abinda tace an haɗa mata suka tafi gida sunaci suna hirarsu dare yayi kowacce ta nufi ɗakinta.
Da farko zaman nasu babu wata matsala lokaci guda abubuwa suka rinƙa canzawa musamman lokacin da cikin Beebah ya tsufa duk wani taimako da Khausar keyi mata ta daina saidai tayi idan bazata iya ba tabari gata da zurfin ciki ta kasa faɗa masa tana buƙatar ƴar aiki domin tana ganin hakan a matsayin shiga tsakanin mace da mijinta, musamman da kullum ya kira zaice mata Khausar ta kirashi tace masa anyi kaza anyi kaza, itadai takanyi murmushi kawai ta bagarar da zancen.
Wani abu dayake damun Beebah yawan baƙi da sukeyi ƙawayen Khausar kuma Bama iya mata ba harda maza haka zasu raba dare suna busa musu shisher a gidan itakuma tayita amai saboda bata kaunar ƙamshin flavor ɗin tun tana ma fitowa babban parlourn Saida fitowar ta gagareta saboda wasu abubuwan hankalinta baya iya ɗauka kusan karo biyu tana kama wata ƙawar Khausar Jidda suna romance da wani cikin abokan nasu a cewarsu da faɗa.

 

Abu na biyu da yasa ta daina fitowa indai taji motsinsu yawan kallo da samarin ke binta dashi jin kunnenta akwai lokacin da taji Wani cikinsu na cewa shifa yana haɗiyar yawu akan kishiyar nan ta Khausar ranar baram² suka rabu a gidan tanata fadan ita wlh sai tayi maganin Beebah ace don masifa mijin ta kama ta riƙe abokan nata ma da take samun nutsuwa dasu suma sun fara cewa sun fara haɗiyar yawu.
Beebah bata gane abinda take nufi ba shiyasa bata wani ɗauki abin da muhimmanci ba, itadai kullum burinta da addu’arta Allah ya rabata da cikin jikinta lfy.
Cikin hakan ne kuma ta kama wata rashin lafiya me zafi wadda ta sanya dole Hajiya Kilishi da tazo taga irin mugun zaman da sukeyi ta dauko Larai tace taje ta zauna da ita, Larai na kula da ita Kilishi nayi shikam Habeeb kullum cikin yo aike yake da kiran waya, kwananta takwas a kwance da yamma tana kitchen ɗin sashin nata ranar jikin nata da ɗan sauƙi, kunu take damawa taji bayanta ya wani amsa.
Ai batasan sanda takai ƙasa ba tana keta gumi ashe wasa farin girki lamarin na gaske yana tafe, ji tayi bayan ya ɗan saki ta yunƙura zata miƙe taji mararta ta riƙe babu shiri tayi zaman ƴan bori a gurin ta rinƙa matagugun azaba.

 

Baba Larai ce taji shirun nata yayi yawa ta nufi kitchen ɗin ta tarar da ita cikin mawuyacin hali ai da gudu ta isa kanta ta tallafota tana tambayarta menene? Babu damar mgn sai ido sai hawaye fita tayi da sauri tana ƙwalawa Khausar kira ta fito ɗaure da towel, Baba Larai tace “ko zaki kiramin Hajiya Kilishi Gimbiya Beebah ce batada lafiya ina tunanin haihuwa ce Azo a kaita asibiti…..”
[5/13, 8:06 PM] AM OUM HAIRAN:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button