Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 28

Sponsored Links

Da kyar ya iya gane department dinsu dan duk student din daya gani zai tambaya gudu yake, a parking lot din department dinsu yay parking yafito yana waige waige, few people kawai yadan gani suna gudu dan duk an watse, saikuma wanda yagani sunyi fenta jikin su suna dambe da securities wasu kuma na faffasa windunan aji wasu na kona taya gadai sunan. Da dan gudu gudu yake tafiya yana zagaye wajen da kyar yagano theater din, hayakin dayaga yana fitowa ta windunan yasa yakarasa wajen da gudu, hanunshi yasa ya taushe hancin shi ya shiga baya gani hakan yasa yaciro wayar shi daga aljihu ya kunna yana haskawa some student ya gani sun faffadi ta gaban ajin harda maza suna tari, tadasu yafara yi yana kamasu yana fitar dasu waje, tsayawa yay awaje yana dan fifita idonshi sabida wani irin azaban yaji dayake mai na teargas, bude boturan shirt din jikinshi yay yacire rigar ya kulle hancin shi dashi, haka yadinga fififto da students dayaga sun zuzzube yana hashaska fuskokin su amma bai gantaba, saida yagama fito dasu sanan yafara hawa stairs din yana hashaskawa ga idanunshi dake mai zugi, wasu group din student yagani again anan tsakiyar stairs din wasu akan wasu daddaga suna tari duk sun kasa tashi, daddaga su yay yana kaisu waje, mai Hijabin daya gani a karkarshin su ta kife yasa yaji kirjin shi ya buga dim! ahankali yadan juyo da ita, ganin fuskar Islam jini nabin goshinta idanunta a kulle yasa jikinshi yafara rawa, jakarta data rataya ta wuya yay maza ya cire mata yarike jakan a hannu sanan ya dauketa ya fara sakkowa daga matattakalan, wani kusa kujera ne yaji yawani kece shi acinya saida wandon shi ya yage, bai damuba tafiya kawai ya cigaba dayi yana sakkowa, fitowa yay daga ajin yana kallon fuskar ta, tunawa yay da randa Eesha ta rasu, jijjigata yayi arude yace “dan Allah karki barni, please stay with me” harda gudu yahada yay inda yay parking da ita, bude bayan motar yayi ya kwantar da ita ya rufe, rigar shi daya rufe hanci dashi ya cire ya yar ya bude gaba ya shiga ya zauna tareda ajiye jakarta a kusa dashi, ya kunna motar yabar school din dawani irin mugun gudu, wani hospital yagani akan hanya Salama Clinic da gudu ya shiga yay parking daidai lokacin yaji wayarta dake cikin jaka na ruri bude jakar yayi ya dauko wayar, yasaka a aljihun shi batare dayama kalli screen dinba yafito, bude baya yayi ya dauko ta chak idanunshi sunyi jajir ya shiga cikin hospital din da ita, nurses din dake reception ne suka tashi ganin yanda jini kebin fuskarta, wani gado suka turamai ya kwantar da ita, daya daga jikin su ta ruga da gudu kiran Dr, daya Kuma ta cire mata hijabin jikinta ta mikamai ahankali ya karba yana kallon fuskarta, Dr ne yafito ya karbi handglove yasa yafara kokarin tsayar da bleeding din forehead din yadan waigo yace “maiya faru?” tari yadanyi sanan yace “school dinsu ke zanga zanga shine akasa teargas” Dr yace “okay tana bukatan madaran ruwa kaima haka” sanna sukai cikin wani daki da ita da sauri yabisu Dr ya nunamai kujera yace “calm down sit and relax, zamuyi aikin mune, kaje ka kawo mana madaran” yajuya ya shiga dakin ya rufo kofa, ahankali yakoma ya zauna akan kujera hijabin ta dake hanunshi ya daura akan fuskan shi jin hawaye na neman zubomai, ringing yakara ji wayarta nayi ahankali yacire hijabin daga fuskarta yaciro wayar ya kalli screen din “Abba” yagani, kasa picking yayi harta katse, sake kira Abba yayi hakan yasa yay picking yakai kunne, “Ummi dafatan komi a school lpy, hankalina yaki kwanciya sai tunanin ki nake?” shiru yayi baice komiba, Abba yasake cewa “are u there Ummi?” da kyar ya tattaro courage yace “Abba muna asibiti?” yacigaba da tari adan rude Abba yace “Asibiti? Wani Asibiti? Ina Ummi? Wake magana?” da kyar dan muryan shi ta dinshi makogwaran shi har yaji yakemai yace “salama clinic, riot akayi a school, tadan sami injury, muna asibiti” “innalillahi wa inna ilaihi raji’un, ganinan zuwa” kashe wayar Abba yayi, kasa hakura yay yatashi yaje gaban kofan yadan leka glass din, oxygen yaga an mata fixing, sanan Dr na dressing ciwukan data samu a goshi da gwuwowinta da hannu, komawa yay ya zauna idanunshi sunyi jajir ya dafe kanshi dayaji yana wani irin mugun sarawa. Wani list wata nurse takawo mai tace “ga abubuwan da ake bukata, kaje ka siyo a pharmacy” ahankali ya karba yafita yaje pharmacy ya siyo harda madaran ya kawo ya bata yasake zama dan kanshi bala’in ciwo yake, ringing wayar Islam tayi hakan yasa ya amsa, Abba yace “ina reception din asibitin a ina kuke?” Daidai Abba ya bude kofa ya shigo reception din sanye da manyan kaya, tashi yadanyi tsaye dan baijin zaima iya tafiya ba sabida yanda kanshi ke sarawa, Abba nagani shi yagane shi ganin wayar Islam a hanunshi yakara so inda yake yana kallon kafar shi ganin yanda kafan ke jini yace “subhanallahi basu duba ka bane jibi yanda kafar ka ke jini, nurse” ya kwalama nurse kira, wata nurse data fito daga dakin da aka shigar da Islam ta karaso inda yake tace “thank God kakawota da wuri mun samu mun tsayar da bleeding din she is out of danger, bacci take yanzu sabida duk wanda yasha teargas need sleep sabida system dinshi yay relax” murmushi yama nurse din dan sama sama yake gane mema take cewa sabida yanda yaji kanshi ke juyawa, ahankali yaji jiri na dibar shi yay baya zai fadi da sauri Abba ya rikeshi yace “subhanallahi” turo gado nurse din tayi Abba ya kwantar dashi tace “ai namaga mugun kokarin shi yasha uban teargas dinan har ya iya tuki ma yakawo ta ba abinda ya samai, and I told him yasha madara fa” shigar dashi wani daki sukayi dan bashi kulawa, fitowa Dr yayi yace “Kaine mahaifin ta?” Abba yace “eh, zaka iya zuwa ka ganta she is fine amma bacci take” shiga dakin Abba yayi ya zauna akanta kumatun ta ya shafa tareda sauke ajiyar zuciya yace “Alhamdulillah, banason wani abu yataba samin ki Ummi ke kadai nake gani dakike tunamin da mahaifiyar ki” wayar shi ce tai ringing da sauri ya dauka ganin Anty Hindu ce yace “Yaya ina asibiti fa, Salama clinic Islam ce duk taji ciwo wai students ne ke riot a makaran tarsu, shine wani bawan Allah yakawota shima gashinan ba lpy”.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button