Hausa NovelsJarabta Hausa Novel

Jarabta 22

Sponsored Links

Maman Miemie da Anty Hindu tasamu a falo gaidasu tayi tawuce sama danyi wanka gashi ana Kiran sallan la’asar hakan yasa ta shiga bayi, muryan Farida dataji itama ta dawo yasa tai sauri tagama wankan ta dauro alwala tafito da saurin ta dan tabama Farida labarin yanda sukai da Fahad akan gadonta taga Farida ta kwanta tana bacci ko kaya bata cireba, murmushi kawai tayi ta girgiza kai tace “lazy gurl” gaban wardrobe taje dan pink rigar ta data kaimata har gwuiwa tasaka sanan tadau zani ta daura tasaka hijab tahau kan dadduma tai sallan la’asar. Koda ta idar sauka kasa tayi dan debo abinci, jellof rice ta debo da fried plantain tadawo sama ta zauna tanaci, ture kwanon gefe tayi ta daura kanta akan gado tana duba watsapp messages dinta.

Sama da awa daya da rabi kenan yana bakin anguwan su dan ko la’asar ma anan masallacin bakin titin yayi, yana sanye cikin wani farin yadi mai kyau ya daura hula akai, agogon dake hanunshi wanda Eesha ta bashi ya kalla 5:25, kunna motar yayi yay kwana ya shigo anguwan nasu yay parking a kofar gidan su shiru yayi yakasa fitowa, toshi yanzu wama zaice yazo nema baima san sunan ta ba, yafi minti uku a zaune ganin zuciyarshi takasa hakura yasa ya fito ya rufe motar. Mai gadi dake zaune kan benci a kofar gidanne yataso da sauri dan yagane shi mutumin daya gani jiya da Islam ne lokacin daya fito daga kewaye, washe baki yayi yace “yallabai barka dazuwa, wajen hajiya kazone?” shiru yadanyi dan baigane wace Hajiya yake nufiba, zaiyi magana mai gadi yace “koba Kaine wanda nagani tareda hajiya jiya kasa kayan kwallo?” murmushi yamai yace “eh nine” mai gadi yace “to biyoni dan Alhaji yacemin na dinga kai baki cikin gida bayason yaran shi na tsayawa a waje” bai jira amsar Khaleel ba yabude gate ya shiga Khaleel yabi bayanshi har suka kai wajen kofar shiga dakin mai gadin ya juyo yace “bari nagaya musu” bude kofa yay ya shiga ciki Anty Hindu da Maman Miemie ne suke dan hira ya gaidasu yace “hajiya dama wanine yake neman hajiya Islam, gashi nan ma” zama Anty Hindu ta gyara tace “okay shigo dashi” fita mai gadin yay yace “ance kashigo” sosai yaji kirjinshi nabugawa ahankali yabude kofar ya shiga mataye biyu yagani Babbar daya gani wacce daga gani kasan tama girmi Ammin shi yadan duka kadan yace “ina yini Hajiya” murmushi Anty Hindu tayi tace “Lpy Lau” ta kalli Maman Miemie dake zaune gefenta tace “jeki kirata” ta kalli Khaleel dake tsaye har lokacin kanshi akasa dan wani irin kunya yaji yakamashi tanuna mai kujera tace “bismillah zauna mana” ahankali ya zauna itakuma ta bude newspapers dake kan table din gabanta ta cigaba da karanatawa.
Bude kofar dakin tayi Islam dake gyangyadi ta shigo ta tabata tareda kiranta tace “Islam Islam” Farida cikin bacci tace “maman Miemie kuna damuna plzz” maganar Farida ne yatada Islam Maman Miemie tace “Anty Hindu na kiranki tana palo” da sauri ta mike tsaye, da dan gown dinan iya guiwa da gashin ta datai parking yana lilo tafito daga dakin, dayake daga sama Anty Hindu kadai zaka iya hangowa danshi yana kan kujeran dake ta ciki sakkowa tayi ta shigo falon kai tsaye tazo gaban Anty Hindu ahankali tace “gani Anty” rufe jaridar Anty Hindu tayi tace “banike neman kiba game neman kinan” ta nuna mata Khaleel da tunda ta shigo idanunshi ke kanta, juyowa tayi ganinshi yasa numfashin ta ya tsaya chak zazzaro idanu tayi tana kallon shi unbelievably, wawwaigawa tayi hijabin Maman Miemie data gani akan stool din dake kusa da Anty Hindu ta dauka da sauri ta saka dan juyawa tayi ta kalli fuskar Anty Hindu ganin ita take kallo yasa ta daburce cikin inda inda tace “uhnn dama dama” ta nunama Anty Hindu shi da hanunta tace “uhn, dama brother yar ajinmu ce, ta turoshi ne yakawo min note ko” ta kallai ware ido yay ya kalleta zaiyi magana tai sauri tace “yauwa ina note din data baka ka kawomin din?” kasa magana yayi dan baima san mezece fa, kara kallon Anty Hindu tayi ganin ita take kallo har yanzu yasa tace “ahhh yana mota? Muje na amsa saika tafi ko” tai hanyar fita daga dakin ahankali ya tashi ya kalli Anty Hindu yace “sai anjima Hajiya” murmushi tamai tace “daga zuwa ka tsaya kasha drinks mana” da sauri Islam tace “yana azumi ko, yau Monday” ta kalleshi gyada kai yayi yana dan murmushi, murmushi itama Anty Hindu tamai tace “to shikenan mun gode agaida su Mum” bude kofa Islam tayi tafito yabiyo ta abaya yana wani irin murmushi.
[6/16, 8:26 PM] Maman Jedda: *JARABTA*

Maman Abd Shakur

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button