Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 37-38

Sponsored Links

★★★~~~★★★~~~★★★

Wani mugun tsaki Khausar taja tana yiwa Baba Larai wulaƙantaccen kallo tace “kuma Ni meye nawa cikin haihuwarta zakizo ki dagamin hankali kamar nice Habeebun da yayi cikin…..
Ƙara ƙasƙantar dakai Larai tayi zatayi mgn Khausar ta daka mata tsawa tace “ki matsamin anan munafuka in kinada abinyi kiyi mata in baki dashi ki zuba mata idanu duk abinda Allah yaga dama yayi, Ni banida lokacin batawa akan abu mara muhimmanci…..” Fuuuu ta shige ɗaki Baba Larai ta girgiza kai lallai wannan mata takai mara imani.
Da wannan tunanin ta koma kitchen ɗin ta tarar da Beebah ciwo har yaci uban na baya daƙyar ta iya bata amsa lokacin da take tambayarta wayarta ta ɗauko cikin saa kuwa babu pin a jiki ta miƙa mata, a wahale ta kamo mata number Kilishi ta kirata ta sanar da ita abinda ake ciki, kafin wane wannan sai gata suka tattageta sai asibiti cikin ikon Allah kamar jiran isarsu asibitin ta haifo yaronta sankacece kyakkyawa me kama da ubansa.

 

Related Articles

Murna gurin Kilishi kamar akansa ta fara samun jika, da kanta ta gyara abinta bayan maijego ta huta suka koma gida.
Tun kafin su isa labarin haihuwar ya cika dangi masu murna nayi ƴan baƙin ciki suma ba’a barsu a baya ba suna nasu a bayan fage, kadama Khausar da yan fadarta suji labari sun kasa zaune sun kasa tsaye, duk inda takai ga iya makircinta wannan karon kasa ɓoye baƙin cikinta tayi hatta Habeeb Saida ya fahimceta a kalamanta aikuwa mutuncinta ya ciwu ba ƙarya don Saida ta gwammace dama tsautsayi baisa ta kasance matar Habeeb ba a wannan rana, ya wulaƙantata da gaske.
Gabaɗaya ya ɗauki hankalinsa ya mayar dashi kan Beebah da bbynsu yaso yazo yaga jaririn amma campany sunƙi bashi hutu dole haka ya hƙr saidai hotuna da aketa yiwa yaron ana tura masa da videos, a tsarin gidan sarautar duk jaririn da aka haifa mai martaba ne yakeyi masa huɗuba amma shi wannan jaririn bai samu wannan gatan ba, koda aka faɗawa Mai martaba samun ƙaruwar da ɗan nasa yayi baice komai ba Saida akayi zancen huɗuba nanne ya magantu da cewa ai kamar yanda ya yafewa uwar jaririn ubansa to shima jaririn ya yafesa.
Beebah da taji wannan ɗanyen hukunci Saida tayi kuka kamar ranta zai fita wai akanta itakuwa wacce irin baƙar kadara ce data zama silar rusa shaƙuwa da soyayyar dake tsakanin uba da ɗansa?

 

Kilishi ce ta rinƙa tausarta da samu tayi shiru amma duk jikinta a sanyaye yake musamman lokacin da Yaya Ahmad yazo yima yaron huɗuba tayi nadamar biyewa Habeeb su ɓata ran iyayensu, wai a haka ma gara shi akanta ita batama san makomarta da nata iyayen ba.
Yaya Ahmad dakansa ya shigo har ɗakinta ya tambayeta ko tanada sunan da takeso a kira ɗanta dashi? Girgiza kai tayi tace ta bawa Kilishi zabi.
Kilishi taji daɗin wannan dama da Beebah ta bata tayi murmushi tace “To a kirashi da Ibrahim Khalilullah” ajiyar zuciya Beebah tayi ta rungume ɗanta tana hawaye tace “Allah ka rayaminshi ka tsareshi ka albarkaci rayuwarsa” ranar suna ta zagayo akayi shagalin suna itadai Beebah kawai bin mutane takeyi da kallo komai ba daɗinsa takeji ba hankalinta ya haɗu yanzu iyayenta kawai take kewa da shauƙin gani. Bayan kwanaki da yin suna Kilishi tana kulawa da surukarta sosai kamar yanda zata kula da ƴarta ta cikinta har sukayi arba’in Beebah taci gaba da kula da ɗanta yaronta kyakkyawa me shiga rai.
Zaman nasu yaƙi daɗi kullum abubuwa ƙara lalacewa sukeyi ita Beebah dake ba ma’abociyar son hayaniya bace bata wani biyewa Khausar ko zata kwana tanayi mata habaici da baƙaƙen maganganu, saima dai tayi murmushi ta ɗauki ɗanta tabar mata parlourn. Gashi zuwa lokacin iskancin Khausar kullum ƙara gaba yakeyi har takai ba ko yaushe take zaman gdan ba kuma duk lokacin da taga dama tanada damar shigo da samarinta da ƙawayenta, abin yana damun Beebah saidai batasan ta yanda zata sanar da Habeeb halin da ake ciki ba.
Ana haka kuwa Habeeb yayi musu zuwan bazata, Beebah na kwance a ɗakinta ita da Hudais kamar yanda suke kiransa bacci ya ɗauke ta me nauyi kasancewar daren jiya sun kwana suna fama dashi ita da Baba Larai ciwon ciki ya hanashi bacci.

 

Ji tayi an ɗauke hannunta daga saman cikin Hudais data rungume yana bacci, aikuwa kamar an ɗala mata duka ta buɗe idanunta a razane ta saukeshi akan Habeeb ta tashi da sauri cike da matsanancin farin ciki tace “Hero…..” Yanda ta kira sunansa da yanayin tsananin mamaki ya bashi nishaɗi ya ɗaga Hudais ya cilla sama ya cafe yaron ya buɗe idanunsa yana ƙifƙiftawa Habeeb ya haɗe shi da ƙirjinsa ya ɗora bakinsa a na yaron yana tsotsar lips ɗinsa yana sake saita injin idanunsa akanta.
Ƙasa tayi da kanta tana wasa da zara-zaran yatsunta tace “Sannu da hanya amma ka shammaceni shine ko a waya baka faɗa min zaka shigo ba” ajiyar zuciya yayi ya lumshe idanunsa yace “Yanayin kewarki da nake ciki itane ta hanani faɗa Miki zanzo nafison nayi Miki zuwan bazata” murmushi tayi tace “Ai Shikenan ka kyauta gara da ka dawo dama wannan photo copyn naka ya hanani sakat kwana biyu baya barni bacci da dare”
Kama kunnen yaron yayi ya murɗa a hankali tayi saurin riƙe hannunsa tace “Kay Hero….” Dariya sukayi a tare yace “Faɗa zanyi masa daya hanamin ke bacci” murmushi tayi tace “tab ai ji nayi kamar raina ka taɓa kasan kuwa yanda nakejin Hudais a raina?”

 

 

Tsuke fuska yayi yace “Ya muke dashi a ran naki?” Zama tayi tace “Nifa yanzu ji nakeyi duk duniya zan iya hƙr da komai da kowa akan Hudais kuma zan iya cin mutuncin kowa akan Hudais kasan ma me….”
Ɗagowa yayi fuskarsa babu walwala yace “Harni kenan ko?” Yanda taga fuskarsa a ɗaure yasa gabanta faɗuwa tayi saurin saita nutsuwarta yayi ajiyar zuciya ya miƙe ya fice da yaron a kafaɗarsa hakan ya bata damar miƙewa tasa rigarta ta fito ta nufi kitchen ta haɗo masa kayan sha ta nufi ɗakinsa ta buɗe ta shiga ta aje masa yanata yima yaron wasa yaron bata ɓangale baki.
Tsiyayowa tayi ta miƙa masa ya ɗago yayi mata wani mugun kallo ta sunkuyar dakai jikinta duk yayi sanyi ta miƙe zatabar gurin ya riƙo hannunta ya tashi ya tsaya a gabanta yace “Na shafe tsayin wata shidda da damuwar rashin ki kewarki tana neman ƙarar da numfashina na kasa jurewa saboda damuwa tayimin yawa inason inzo in ganku dawowata ace irin tarɓar da zakiyimin kenan Wyf ɗan da kika sameshi dani yazo duniya ta dalilina wai yau shi kike faɗa min yafini a gunki ko?….”

 

Hawayen fuskarta ta share tace “baka fahimceni bane wlh ba haka nake nufi ba Hero idan da mutumin daya samu daraja da ɗaukaka a duniyata bayanka ne waye na amince na rasa komai akansa kaine Hero kayimin uzuri soyayyarka itace ta sabbaba soyayyar Hudais a zuciyata saboda shiɗin tsatsonka ne jikinka ne wlh da banasonka ba lallai nasoshi ba har na rinƙajin abinda nakeji akansa, kayi hkr idan hakan ya ɓata ranka…..”
Rungumeta yayi yana sauke ajiyar zuciya yana shafa bayanta suka zube a gadon ta janye ta ɗauki cup na juice ɗin takai masa bakinsa ya kurɓa tare da riƙewa da hannunta yayi kissing yatsunta yace “komanki me kyau ne Wyf meye yasa nake sonki ne?”
Dariya tmbyr ta bata tace “Nima ina yawan tambayar kaina meye yasa” dariya sukayi tare ya kwantar da Hudais yace “ki taimakamin wanka nake buƙata kuma na gaji” murmushi tayi zatayi magana ya ɗora hannunsa a bakinta yace “Sai kinyi fah” karyar dakai tayi tace “Lissafina ya kwance kamar ba anan zaka sauka ba ai ko?” Harara ya maka mata ya nufi bathroom ɗin tasan abinda yake zuciyarsa bashida kaɗan wannan tasa tabisa sukayi wankan suka fito ta zaɓo masa kaya yasa bayan ta shafeshi da mai.
Ana shirin suna wasan zilliya so yake ya cafke ta itakuma taƙi sai waskewa takeyi da dabara dai ta bari ya kyaleta sa haɗe da dare.

 

Fita sukayi parlourn tashiga kitchen tana tambayarsa me yakeso ta girka masa? Bin kitchen ɗin ya rinƙayi da kallo cike da mamaki “Wannan sauyin kuma yaushe ya faru?” Murmushi tayi taci gaba da aikinta batare da ta bashi amsa ba, yasan tunda tayi shiru batada amsar badawa ne yaja numfashi yana bin komai da kallo harta gama ta zuba a flat suka koma dinning dake parlourn suka zauna sunacin abincin yana binta da kallo sai yanzu ya lura da ramar da tayi ya kira sunanta ta ɗago yace “Kin rame kuma tun shigowata gdannan nake ganin sauye-sauye da bangane musu ba na tambayeki kuma kinyimin shiru”
Ƙasa tayi da kanta ya kuma kiran sunanta ta ɗago yace “ke fah nake saurara” a gajiye tace “Da kayi hƙr tunda ka dawo kome ke akwai zaka fahimta Hero don Allah ka daina tambayata akan lamarin gidannan” zubanta idanu yayi yana nazarin kalmar ta.

 

Ya daina tambayarta to in bai tambayeta ba wa zai tambaya? Bai kuma mata magana ba har suka gama ya miƙe ya dauki Hudais suka fice daga gidan karon farko da yaron ya fara fita batare da uwarsa ba a cikin watanninsa biyu da sati biyu.
Kai tsaye gdansu ya nufa a hanya Khausar taga motarsa Saida ta kusa yin karo saboda firgici duk da bata ganshi ba kasancewar bakin Glass ne da motar tasani ko tantama babu shine a ciki domin Beebah har yanzu bata wani son hawa mota ita kaɗai takeyi ba, shi kuwa bai gane motar ba saboda ba wani saninta yayi da ita ba koda sukayi clear ɗin sunayin kwana ta tsaya ta sauke ƙawarta Deedah da wani abokinsu tace suyi maza su nemi wata motar mijinta ya dawo zata tafi gida, yawon da baayi ba kenan ta nufi gda.
Habeeb kuwa yana isa gidan sarautar bai nufi cikin gdan ba kai tsaye ɓangaren Mai Martaba ya nufa ya shiga ya ishe shi a zaune saman Kilishi yanacin dabino, sallamarsa ya amsa masa ya gaisheshi da girmamawa amsawa yayi ya tashi zaune tare da zubawa Hudais idanu ya miƙa hannu Habeeb ya miƙa masa shi.
Zubawa yaron idanu yayi yana jinjina kai yace “Shine takwaran nawa?” Shafa sumarsa yayi yace “Shine dama shi ɗaya ne ai” murmushi ya miƙa masa shi yace “yayi kyau yaushe ka dawo?” Amsa ya bashi sukayi shiru na ɗan lokaci Mai Martaba ya miƙe yace “zan shiga ciki a gaida mutanen gidan”
[5/14, 6:24 PM] AM OUM HAIRAN: _

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button