Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 9-10

Sponsored Links

Last Free Page 9-10*

★★★~~~★★★~~~★★★

 

Related Articles

Bai koma gda ba sai yamma koda ya fito daga ma’aikatar yayan nasa tasu ma’aikatar ya nufa amma abin arziki ya kasa hassalawa sai juyi da yake a kan kujera wayar Beebah yaketa kira taki tafiya duk damuwa tabi ta cunkushe masa zuciya sai bayan magrib ya nufi gdan babu wani karfi a jikinsa saina imani wanka yayi yana shirin fita Masallaci sallar Isha wayarsa tayi ruri ya ganin number Mai martaba yasashi haɗa nutsuwarsa ya daga Mai martaba yace “in ka dawo kazo inason ganinka” amsawa yayi tare da fita yaje yayi Sallah sannan ya nufi kiran na Mai martaba ya shiga da sallamarsa yana zaune saman shimfiɗun Kilishi da farin tabarau a idanunsa ya amsa sallamar Habeeb ya nemi guri ya zauna yace.
“Allah yaja kwana gamu mun amsa kira” ɗagowa yayi yayi masa murmushi ya miƙe ya saita zamansa yace “Am dama wani babban uzurine ya taso munason zamu haɗa gwiwa da wani campany dake Japan domin haɓakar masana’antunmu” jinjina kai Habeeb yayi yace “hakan yayi Allah ya taimakeka hakan zai kawo ci gaba ƙwarai” murmushi Mai martaba yayi yace “shiyasa nakeson ka Habibullah to dama ba komai bane yasa na kiraka campanyn sun buƙaci a tura mutum ɗaya daganan domin yaje yayi course na yanda ayyukan suke kasancewa kamar yanda suma zasu turo nasu wakilan don faɗaɗawa juna fasaha.
Na duba naga babu wanda ya dace da wannan tafiya saikai duba da kwazonka da basirar ka saboda haka kaje ka fara shiri nan da sati biyu zaka tafi in Allah ya yarda….”

 

Tunda Habeeb yaji ƙudurin Mai martaba gumi yake karyo masa yasan tabbas da manufa cikin wannan shiri, a sanyaye ya ɗago ya buɗe baki zaiyi mgn Mai martaba ya ɗaga masa hannu yace “banason kace komai kaje Allah yayi maka albarka shekara ɗaya ne babu yawa idan Allah ya amince kafin lkcn zan sama maka matar data dace dakai na aura maka na turota tunda na fahimci yanzu hankalinka ya hadu kana buƙatar auren” a kasalce yace “Habeeban fah ranka ya daɗe….” Shiru mai martaba yayi masa shi kuma ya kasa tashi jikinsa har rawa yake saboda tashin hankali bai iya jurewa ba yace “Na rantse da Allah bazan iya zama da duk wacce zaka aura min ba Allah ya taimake ka indai bazaka amince nayi jahadin janyo Habeebah daga duhun kafirci zuwa hasken musulunci ba idan bazaka amince min na rayu da abinda raina da zuciyata suke muradi ba to ina roƙonka da kayi hkr ka barni na ƙarasa rayuwata ni kadai kamar yanda na shirya yinta a baya….”

 

Tsawa Mai martaba ya daka masa yana huci yace “Ni Habeeb Nine nake faɗa kake faɗa harma na zartar da hukunci kace baka amince ba lallai ya tabbata ka girma kakai shiyasa har kake jayayya dani akan kafira, to na rantse da Allah kaji dai kuma ka sani bana saurin rantsuwa akan lamarin rayuwa to nayi akan wannan yarinyar indai kaga ka aureta to kodai ka canza uba ko kuma bana numfasawa, tashi ka ficemin a daki kafin na nakasaka”
Tsuma jikin Habeeb yakeyi saboda ɗimuwa da gigita rantsuwar mahaifinsa tayi mugun girgiza shi Shikenan ta faru ta ƙare Mai martaba ya gama yanke hukunci yanzu babu bakin da zai iya fahimtar dashi ya gane….”

 

Sashin Hajiya Kilishi ya nufa da ƙannensa biyu mata da suke ciki ɗaya da sauran matan gdan duk suna babban falon suna kallo yazo ya shigesu ya nufi ɗakin mahaifiyarsa ya faɗa kan gadonta saboda mugun sanyin da yaji yana keta ƙashinsa yaja bargo ya rufa.
Kallon kallo sukayi Hajiya Zulai ta dubi Hajiya Kilishi da Hajiya Hauwa tace “Salma?” Dubansu Kilishi tayi tace “Naam Zulai” Hajiya Hauwa ce tace “Soja ƙalau kuwa?” Numfasawa tayi tace “da alamun ba ƙalau ba wato ɗebowa yayi da zafi aure yakeson zaiyi kuma ba musulma bace yarinyar da yakeson aure, nikam na fahimceshi kuma na bashi goyon baya to amma fah tunda mai martaba bai fahimta ba babu wanda ya isa ya fahimtar dashi”
Miƙewa Hajiya Zulai tayi ta nufi ɗakin tace “Babana komansa daban banda rigima irinta tarar aradu daka inashi ina kafira matsayin mata….” Tana faɗin haka ta bude dakin ta shiga yanda taji gadon na rawa yasata nufarsa da sauri ta yaye bargo tace “Innanillahi Ni Zulaihatu Babana meye hakan kuka kamar wani ƙaramin yaro….”
Tashi yayi zaune ya kama hannunta yace “Don Allah ku ceci rayuwata ku faɗawa mai martaba zanje Japan ɗin amma ya barni na auri Beebah Hajiyan soro bazan iya taɓuka masa komai ba indai ya rabani da Beebah nasan itama bazata iya rayuwa babu Ni ba”

 

Numfashi taja tace “Akan mace kakeson kashe kanka dubi fa yanda kake rawar sanyi Habeeb yanzu waye kake tunanin zai iya tunkarar mahaifinku yace zai fahimtar dashi?”
Hajiya Kilishi ce ta cafe da cewa “kaje inda ya umarce ka kayi masa biyayya insha Allahu zaka dace idan kace zakaja yaja kaine zaka faɗi ƙasa” zama sukayi sunata rarrashinsa shikam banda zafin jiki ma babu abinda suke ƙara masa kafin wane wannan zazzaɓi me zafin gaske ya lulluɓeshi Hajiya Kilishi ta shiga damuwa tabbas bada wasa Autan mazan nata ya ɗauki lamarin ba da gaske yakeyi don duk abinda yasa a ransa har yakai masa jinya to ya isa kallo.

 

Ranar sai ɗakin tabar masa bayan likita ya duba shi baccin wahala ya ɗauke shi zuciyarsa taƙi samun sukuni
Washegari da asuba ya duba wayarsa ya zabura ya tashi zaune yana latsa wayar bugu biyu ta daga cikin muryarta me cike da gajiya da kasala tace “Tunda ka tafi nake kiran ka naji ko kun sauka lfy bana samu ɗan birni ina fatan lfy kake…” Wata gwauruwar ajiyar zuciya ya sauke yace “kamar bakida lfy meye yake damunki?” Kukan da ta kwana ta nayi shine ya dawo mata sabo tace “banasonsa wlh tsohone idan suka auramin shi kashe kaina zaiyi ɗan birni kai nakeso….”
“Wa?” Ya faɗa da ƙarfi yana miƙewa daga gadon cikin kuka tace “Sarkin Mahauta….”

 

Miƙewa yayi daga gadon yace “Wa…waye yace zai bashi ke waye….” Kashe wayar tayi yayi bin duniya ta kasa ɗagawa aikuwa ba’a wayi gari dashi a gdan ba ya nufi tasha ya hau mota saboda bazai iya tuƙi ba shata ya ɗauka har garin Tsaunin gawo bai zame ko inaba sai gdan Dagaci a ƙofar gida ya tarar dashi sunashan hantsi ya mike da sauri ya tareshi suka gaggaisa yace “Ina Beebah?” Sunkuyar dakai Dagaci yayi cikin kunya yace “Tana ciki wani abu ta faɗa maka?” Iska ya furzar yace “waye wanda suka bawa ita?” Gabansa ne ya faɗi yace “Mai Tukuba ne nasan kasanshi a zaman da kayi a garin nan don ko zaman yini ɗaya kayi a garin nan indai ka shiga cikin mutanen garin nan zagaji sunan me tukuba ɗaiɗai yarinyar data zama bazawara a garin nan da bashine ya mayar da itaba a yanzu haka matansa na aure sha tara a gidansa Bibo itace ta Ashirin yau da yamma yace zai kawo komai na aure a ɗaura zai ɗauketa su tafi rani nayi iya yina na kasa yanada manya a karamar hukumar nan yanada bokaye sannan yanada kuɗi kaga dole na sakar masa iko….”

 

Numfasawa yayi ya dubi agogon hannunsa 12:12pm ya dago jajayen idanunsa yace “akwai masallaci a garin nan?” Girgiza kai Dagaci yayi yace “Saidai Hayin Fulani” ajiyar zuciya yayi yace muje ka rakani”
Babu musu suka nufi hanyar da zata kaisu Hayin Fulani suna zuwa suka tarar anyi shimfiɗu a ɗan ƙaramin masallacin juma’ar Liman ɗin dakansa ya fito ya taresu yana kallon Habeeb da mamakin abinda ya kawo shi musamman da yaji ance shine baƙon.
Karkacewa yayi masa bayanin komai da uzurinsa liman ya kalli na’ibi suka jinjina sukace “kaiko ɗannan miye naka da auren ɗiyarga ta Jimo kaje ka nemi wata mana ko a rugar nan ne baka mukayi”
Girgiza kai yayi yace “ita nakeso liman taimakon ta zanyi bayan soyayya akwai tausayi kanaganin wanda sukeso subawa aurenta yarinya ƙarama nawa Habeebah take wlh Kona aureta saina raineta kafin ta gama haɗa hankalinta sone yayi mana gaggawa, liman ka yankan sadaki na biya a ɗaura bisa tsarin addinin musulunci”

 

Ɗagowa Liman yayi yace “Duk da inajin tsoro bazanƙi ɗaurawa ba amma hanzari kace ita yarinyar ba musulma bace kaga kenan akwai jumurɗa abinda zaifi indai ta amince zata aureka to ta yarda ta musulunta auren zaifi sauki…”
Gumi ya share yace “zata musulunta daga baya nidai a ɗaura ɗin shine me wuyar” baƙin nacinsa yasa dole Dagaci ya karbi waliccin Bibo na’ibi ya karɓi na Habeeb aka ɗaura wannan rikitaccen aure akan sadaki saniya biyu kamar yanda al’adar Waliyyin angon take.
Wayyoh zo kuga murna gurin Habeeb har sujjada yayima ubangiji na cika masa burinsa da yayi, ya manta da duk wata kwantacciyar ƙura da ɗaura wannan aure zai tayar ya manta da rantsuwar mahaifinsa ya manta da alwashin da yaci akansa muddin ya auri Habeeba, ya manta da ƙudurin Mahaifanta da sukaci alwashin saisun kasheshi sun kashe Bibo muddin ya matsa akan aurenta……
Sai a lkcn abubuwa suke ta dawo masa yayi zugum zuciyarsa ta kasu biyu wani sashi farin ciki wani sashi ɗinbin damuwa, Dagaci ne ya katse shirun da cewa “Mal Balaji tunda dai wannan aure ya ɗauru Habeebah matar Habibu ce to zaifi ya ɗauke matarsa subar garin nan don tabbas maganar zata fasu kuma indai har ta fasu batare da yabar ƙauyen nan namu ba to kuwa ko zai fita zai fita cikin rashin hayyac….”
“Kwarai kuwa munafiki zai fita cikin rashin hayyaci domin kuwa bazamu bawa abar dogaro kunya ba kamar yanda muka alƙawarta zamu kasheshi mu kasheta sayi auren a lahira na rantse indai nine Buba Sarkin Noma to yau saina raba wannan yaron da rayuwarsa bai isa ya auri jikanya ta ba macuci masu shanye jinin bil’adama……”

 

Wani sara ya kaiwa Habeeb daidai lokacin da Habiba ta kwace daga riƙon da yayi mata ta hankaɗe Habeeb suka zube can baya tare sai gashi a ƙasa ita kuma tana kwance a samanshi.
Idanunta ta buɗe cikin idonsa ya sakar mata wani murmushi yasa hannunsa ya riƙe weast ɗinta ta kwantar da kanta luf a ƙirjinsa dagashi har ita wata nutsuwa ce take kwarara a ƙasan zukatansu….
Babu wanda yasan meye yake faruwa saida sukaji Liman yana cewa “Buba Aure ne mun riga mun ɗaurashi Habiba ta tabbata matarsa kada kuja da ikon Allah shine ya hukunta wannan aure kuma babu wanda yasan rabon dake tsakani wannan….
Dakata nace ka dakata Mal Liman kun hana mu taɓashi amma fah ka sani idan har kukaga yabar ƙauyen nan to warware auren nan kukayi….” Janyewa Habiba tayi a jikinsa zatayi magana Uda ya kai mata bugu Mal Liman ya janye ta ya turata gdansa ya dubi Habeeb yace shiga ciki akwai zauren baƙi ka jirani”

 

Zaku iya samun littafin nan ta website na arewabooks ku karanta cikin sauƙi ga waɗanda karatu keyi musu wuya a WhatsApp, ko kuma ku sauke app na arewabooks a wayoyin hannunku ga link ɗin domin shiga ta website ku biya ku karanta cikin aminci👇🏼

https://arewabooks.com

 

*Share please*
[4/13, 8:45 PM] AM OUM HAIRAN: *BAMAGUJIYA*
*(HOT LOVE AND DESTINY)*

NA

*FAUZIYYA TASIU UMAR*
*OUM HAIRAN*

https://youtube.com/channel/UCZ5Vt2–iGyJfTwItSzAnGg

*Paid book*
Kunata cewa promo ɗin dana baku yayi kaɗan to gashi nan na ƙara daganan zuwa jibi zaku sameshi a 200 PC 500
Ki biya ta waɗannan hanyoyin acct details 0255526235 Fauziyya Tasiu gtbank ko ku turo katin waya MTN ta WhatsApp number na kamar haka 09013718241 ƴan Niger kuma zaku tuntuɓi wannan number don biyan kuɗinku +227 95 04 58 22.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button