Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 24

Sponsored Links

24

 

Ranar laraba da safen mommy ta kirata dakinta,sanda ta shiga akwai qannen mummyn a ciki da wasu daga cikin ‘yan uwanta zazzaune,wasu a gefan gado wasu saman tiles,binta sukayi da kallo sannan suka soma qus qus a tsakaninsu,hakanan jikinta ya bata da ita suke duk da bata iya jin me suke fada amma jikinta ya bata,tana iya jin sautin dariya dariya qasa qasa daga bakunan wasu daga cikin ‘yammatan dake cikin dakin,saidai batasan meye abin dariyar ba,jikinta dai atamfa ce riga da zani sai hijabi data dora iya gwiwa kanta babu dankwali,sai tudun gashinta dake matse a cikin ribbom.

Related Articles

A ladabce ta tsugunna a bayan mummy wadda ke gaban wardrobe tana fidda kayan da zata sanya anjima,ba tare data waiwayo ba tace
“Gobe wasu daga ‘yan uwanki zasu zo daga qauye,za’a je ayi miki jere….ya kamata ki sanar da shi zuwan nasu,ya bayar da muqullin gidan ko ya rakasu,don ba lallai su su sake gane hanyar gida ba bare gidan kanshi”
“Kawai mummy ya rakamun” inji nusaiba qawar asma’u tayi caraf ta fada,cikin muryarta kana iya jiyo sautin dariyar dakeson fitowa,nusaiban ‘yace ga yayar mummyn,qawancensu yayi daidai saboda hali da yazo daya,tana son harkar girma itama,tana son fantamawa,tana son kuma mu’amala da masu hannu da shuni
“Ko yazo ko ya samo wanda xai rakaku…don ko su halima sunce ma ba zasu iya gane hanyar gidan ba” dariya nusaiba ta sake da alama tasan komai ko an bata labari,sai ta kuma waske tana wa farida cousin dinta dake zaune kusa da ita magana
“Toh mummy” ta fada tana miqewa jiki a salube,tana qirga iya kwanakin daya rage zata sake shiga wata sabuwar rayuwar,ko ya zata kaya da ita ita kuma?.

Zata fice sukayi clashing da naana,qawa ce ga asma’u,amma ta zama kamar ‘yar gida saboda yadda ake buga qawance,duban juna sukayi naana ta saki dariya,abinda tsahon sanin da aysha tayi mata bata taba yi mata ba,face kallon banza da kallon raini dake shiga tsakaninsu,saboda asma’u ta riga ta gama dorasu kan turba
“Amarya amarya” naanan ta fada,kallo daya aysha tayi mata ta dauke kanta ta wuce,karon farko da hawaye taji sun cika idanunta,karon farko data ji damuwa ta sosa zuciyarta,gefan gadonta ta zauna,tana qoqarin tsaida hawayen,saidai bata da wannan ikon,saboda zuciyarta na buqatar rage nauyin da ta jima tana dauka,cikin muryar kuka ita kadai cikin daki take cewa
“Ya Allah…kaine mafi jin qan masu jin qai…kaine mafi tausayin masu tausayi…kaine mai tallafar raunana…ya Allah…ka fini sanin wace ce ni…ka fini sanin dalilinka na sanya rayuwata a wannan bigiren,ka fini sani gobe da jibina har zuwa qarshe na,Allah kai kace mu roqeka zaka amsa mana,ya Allah….kayi ruqo da hannayena…ka yiwa rayuwa ta jagoranci…Allah karka barni dai dai da qiftawar ido ya Allah….” Ta qarashe addu’ar tana fashewa da kuka wanda ya tilastata cusa kanta cikin fulalluka don gudun fitowar sautin kukan nata.

Ta jima tana kokawa ita kadai….ta dade tana fitar da ruwan hawaye kafin ta lallashi zuciyarta.

Qarfe shida na yammaci sanda ‘yammatan amarya ke shirye shiryen zuwa bridal shower aka ce mata ta fito ga ‘yan uwanta nan daga takai,gabanta na dukan uku uku ta zira hijabinta ta tako zuwa falon gidan inda aka aje su don bana ce aka saukesu ba,duba da yadda yawanci mutanenmu na birni ke raina mutanen karkakara,bayan mutane ne da Allah ya musu baiwa iri daban daban masu tarin yawa fiye da mu din,fargabarta na su waye suka zo?,yaya zasu zauna da su a muhalli guda ba tare da bacin rai ko samun wata tangarda ba?.

Murmushi mai tafe da hawaye ne kan fuskarta ganin mutanen da suka zo matan,mero ce da gwaggo asabe,sai inna kulu da kuma karima matar kawunta
“Sannunku da zuwa gwaggo kunsha hanya” ta fada itama tana zama qasan carfet cikinsu kamar yadda ta samesu zaune a nan,ko banza taji dadin gani masoyan nan nata biyu meronta da kuma gwaggo asabe,akace naka naka ne hakan take,sai ta dinga jin dadi da nutsuwa har cikin ranta,bakinta yaqi rufuwa gata ga meronta,falon jama’ar dake kai kawo sunyi yawa,hakan ya sanya ta kwashesu zuwa cikin dakinta,ba wanda ya damu da su don ba wanda ya qara bi ta kansu ma,hira suka balle sosai da ita,kusan duk rabi labarin na garinsu ne,kamar aliya tasan da zuwansu saiga wayarta,ta gaya mata zuwan nasu take tace gata nan zuwa,babu jimawa sai gata kuwa da kulolin abinci,duk da gidan basu da damuwar abinci amma bata son aysha ta damun kanta wajen sai tayi girki,don dama ba’a son ranta ana mata gyaran jiki take shiga kitchen ba cewar aliya.

Sanda ta qaraso gidan an ragu sosai duk an dode zuwa wajen da za’a gudanar da bridal shower din,hakan yasa ta dan jima suna hira da su,da yake itama sam bata da qyamatar mutane,hakan tana da fira fiye da aysha da kuna saurin sabo.

Sunzo mata da gudunmawar da aka tara mata,wanda duka duka abinda suka kawo din bai kai ya kawo ba,ba kuma don basu da shi bane,a’ah…,qarfin abinma dai gwaggo asabe ce da mero,har cikin zuciyarta sai taji dadin gudunmawar duk da qanqantarta,wannan ce rana ta farko da zata bigi qirji tace ga wani abu da suka taba yi mata,dalili kenan data ji dadin abun ta kuma bashi girma.

Dukkan abinda yake gudana kusan yana sane da shi ana gaya masa,kama daga events na bikin da yadda komai na gidan ke wakana,hakan ya sanya qarfe tara na dare yayi kiranta,a sannan tana gyarawa su gwaggo wajen kwanciya suna dan taba hira ita da gwaggon da mero,don karime babu wani sabo tsakaninsu,har gwara inna kulu a kanta,don bata taba fito da muguntarta tsirara ba a kanta.

Bata samu ta dauki wayar ba har sai data gama gyara musu wajen sannan ta duba mai kiran,bin kiran tayi don tana da credit wanda daddy ne yakan sanya mata lokaci lokaci,a cewarsa bata iya tambayarsa komai koda tana da buqatar hakan,ita kuma bata saba bane,tun tasowarta bata saba ayi mata abu na,shi yasa ma bata tambaya
“Anata hidimar biki ko ke babu ke…kiyi haquri” abinda yace da ita kenan bayan sun gama gaisawa
“Yayan naki talaka ne….” Ya sake fada a karo na biyu
“Uhmmm” kawai tace tana gyata tsaiwarta,don ita gaba daya tama mance da ana wani abu a biki banda asma’u na nata taron,dan bata sha’awa ma koda zatayi ma wa zata gayyata wa take da shi?,ita duka wannan ba damuwarta bane
“Kinje wajen ne?” Ya tambayeta karo na farko,don yasan ba lallai tayi magana illa kudin wayar da zaita tafiya a haka
“A’ah” ta amsa masa a taqaice
“Saboda me?”
“Iyayena sunzo daga takai…mummy tace na shaida maka gobe zasu zo jere”
“Gashi kuma inaa…” Katsewa yayi da hazari jin ya kusa baranbarama
“Ohk….shikenan…babu damuwa,Allah ya kaimu,zan aiko wani dan uwa na sai ya rakasu”
“Tohm” ta fada kana tayi shuru tana saurare ba tare data ce komai ba,shima jin shirun daga nashi bangaren yasan hirar tasu ta qare saboda haka ya katse kiran,aje wayar tayi suka ci gaba da hirarsu dasu gwaggo.

??????????????

Tun tara na safe motar kayan jeran aysha take tsaye qofar gidan wanda kayan ta siyesu ne a zooroad maimakon dubai kamar yadda daddy ya tsara a siya musu kowacce set biyu daga waccar qasa,yayin da wadanda zasu jeran suke shiryawa,wanda yawancinsu ba don Allah zasu je ba,zasu je ne kawai saboda gulma,duk da cewa yau ne dinner din asma’un.

Goma da minti biyar kira ya shiga wayarta da baquwar lamba,cikin mamaki ta daga wayar ta kara a kunneta
“Ranki ya dade nine wanda yallabai ya aiko nayi wa ‘yan jere rakiya” cikin mamakin yanda yayi maganar cike da girmamawa tace
“Ohk…to zakayi haquri kadan jirasu na mintina,bari na sanar musu”
“To babu damuwa…” Katse kiran tayi sannan ta dubi inna wadda shigowarta dakin kenan tana taya su mero hada kayan da za’a tafi jeran da su
“Inna….” Ta fada a sanyaye
“Na’am indo”
“Wai wanda zai rakasun ya iso yana bakin gate”
“Toh…toh bari a sanar da su” ta fada tana sakin jakar baccon da take zugewa kana ta fice.

Shiru ayshan tayi kanta a qasa,duk da tana sauraren hirarsu gwaggo asabe jefi jefi,saidai faduwar gaba da damuwa sun mata yawa,fargabar auren take qwarai,gani take kamar zata koma ‘yar gidan jiya,yayin da gefe guda na zuciyarta ke cike da damuwa,ina mahaifiyarta ta shiga?,shin ko labarin aurenta ya isa kunnenta?,tasan aure zatayi kuwa?,tana son tambayar gwaggo asabe tun jiya tana jin nauyi da fargaba,Allah kadai shi yasan yadda take ji a zuciyarta
“Ya dai indon baffale?,ko fargabar auren ce irin ta amare?” Mairo wadda ta dafa kafadarta ta fada qasa qasa yadda su kadai zasu ji cikin murmushi,kai ta daga cikin qarfin hali ta maida mata murmushin
“Karki damu….zaki dace in sha Allahu wannan karon” murmushin kawai ta sake mata,kafin tace wani abu muryar inna laraba ta tsaidasu
“Zasu qarasa shiryawa ne saimu wuce”.

Har suka gama shuryawar su wadan can ‘yan rakiyar basu gama ba,har suka zauna suka huta bayan sun gama nasu aikin suka taba hira shiru kake ji,a qalla saida sukayi jiran awanni biyu sannan suka ce sun gama din su fito.

Da mamaki inna laraba take duban ‘yan zuwa jeran,ko a mafarki bata taba tunanin zasu taka gidan aysha ba bate suyi mata jeran aure,dadewarta a gidan ya sanya zata iya fadin halin kowanne daya daga cikin dangin mummy,kai kawai ta gyada cikin ranta tana tabbatarwa kanta cewa akwai lauje cikin nadi,akwai dalilin wannan gangankon nasu,to koda ma saboda Allah zasun ‘yammata irin wadan nan masu ji da kai da yauqi ina zasu tsaya yin wani jere,haka dai ta barwa ranta suka shiga motocin da zasu kaisu wajen wanda yawancinsu motocin ‘yammatan ne suke ta shewa,duk su qi shiga motar da khalipha ya aiko da sunan wadda zata kaisu sun raina ajinta,sai inna laraba da su gwaggo asabe ne suka shiga.

Yana gaba saman babur dinshi lifan motocin dake dauke da kaya da su inna na biye da shi har suka isa unguwar
“Ya haka?,ya zai kawo mu wata unguwar daban kuma?” Cewar anty halima cikin fushi,da yake gwanar fushi ce ita din,abu kadan yake tunzurata
“Nima dai kamar ba unguwar da asma’u tace mana bace” inji farida tana wulwulga idanu,saboda ita kanta unguwar na daya daga cikin burinkanta a wajen zama.

Shiru ne yaci gaba da wanzuwa har zuwa sanda ya tsaida babur dinshi qofar wani katafaren gida,wanda idan ka tsaya ka qarewa gine ginen kallo kaf layin ba gidan da ya kai girma da tsaruwarshi,suma bakin gidan suka tsaida motocinsu
“Ku zauna…basai kun fito ba” ya fada yana zaro wayarshi daga aljihu,daddadannata yayi sannan ya kara a kunnenshi,waya yayi ta sakan biyar,ba’a cika sakanni goma ba katafariyar qofar gidan ta wangale,mai gadi cikin unifoarm na musamman ya bayyana,daga bayanshi kana iya hanho.

hango makekiyar harabar gidan,wadda ta qawatu da grass carfet da fitilu gami da furanni na alfarma da fitilu dake kunne,da hannu ya musu alamun su shigo,hakan nan suka dinga cusa motocinsu ciki wanda suka tashi laqwam a wajen,ba wanda ya iya magana cikinsu har suka gama dai daita motocin nasu kusa da wadansu kyawawan sabbi fil din motoci guda biyu
“Wai ina ne nan ne?,ina ya kawomu?,karfa yace yana nufin ya kawomu gidan uban gidan sa ne mu soma gaisheshi,an gaya masa mu mabarata ne?….ko qarqashin wani muke ci?” Cewar anty halima sanda suke fiffitowa daga motocin kowa yana qarewa harabar gidan kallo,daga yadda ta tsaru tun daga waje ya isa ya gayawa mutum cewa akwai kallo a ciki ba qarami ba
“Kaga malam mufa ba wasa ne ya kawomu ba muna da abinyi….ba gaida uban gidansa muka zo yi ba wannan matsalarsu,ka kaimu gidan qasa muje mu juye mata kayanta mu wuce”
“Kwantar da hankalinki hajiya….nan ne gidan amaryar” tofa!….sai aka soma kallon kallo tsakaninsu,yayin da murmushin farinciki ya subuce a fuskar mero inna laraba dama gwaggo asabe,duk da mamaki daya cika zuciyarsu fal suma
“Kaman yaya?…mu ba wannan fa gidan ya soma kaimu ba,bashi muka sani ba,sannan yanzu ace nan ne?,hasalima fa wancan gidan gidan qasa ne”
“Gidan qasa?” Mutumin ya fada cike da mamaki yana musu wani kallo
“Boss ne zai zauna cikin gidan qasa?….ai ko masinjansa ke ko mai masa wankin mota yafi qarfin zama cikin gidan qasa ko talauci irin haka,ina tsammanin dai a mafarki hakan ta faru kikai zaton a gaske ne”
“Uwar mafarki nayi….nace maka uwar mafarki nayi ba mafarki ba” ta fada cikin hasalar abu biyu,na farko yana son nuna mata raini raini gaban qannenta,na biyu ta yadda khalipha ya raina musu wayo ya rufesu,tashin hankali ta dinga ji yana rufto mata,ta tabbatar ko asma’u gidanta bai qarasa wannan ba,duk kyan gidanta tasan da zata ga wannan din shi zata fi so,ta yaya hakan ta kasance a kan aysha?
“Allah ya baki haquri hajiya….abun duk baikai ya haka ba…ni dan aike ne….kuma boss yace na girmamaku saboda akwai iyayenta a ciki….ga wadan can” ya fada yana nuna saitin sababbin motocin dake qasan rumfa
“Na amarya ne….ga muqullan idan kuna buqata a baku kukai mata” ya fadi yana ciro muqullan daga aljihunsa,dukkansu mutuwar tsaye sukai ba wanda ta iya magana a cikinsu,baki dayansu ba wadda batasan nawa ne kudin mota duk guda daya ba a ciki
“A’ah ka maida masa ya aje mata….duk randa aka kawo masa ita ya bata da hannunsa” cewar inna laraba da saurinta saboda tsoron karsu amshi key din wani abu yaje ya dawo,sam bata damu da kallon da suka soma jeho mata ba
“To shikenan” ya furta yana maida muqullan aljihun nasa
“Mu qarasa ciki ko?” Ya fada yana yin gaba gami da ciro wasu muqullan daban,inna laraba,mero,gwaggo asabe sune kan gaba,ba abinda bakunansu ke furtawa sai
“Ma sha Allah…alhamdulillah…kai Allah abun godiya” musamman inna laraba da tasan zaman aysha a cikin gidan,muryarta tafi ta kowa dagawa,kuma da biyu take da gayya take,ba qaramin farinciki bane a zuciyarta,ta tabbatar da cewa Allah baya zaluntar bawa saidai bawa ya zalunci kansa,hakanan ubangiji baya mantuwa,karamcinsa baiwarsa da kuma kyautarsa yawa gareta.

Qofar falon kawai tun daga nan suka sallama,inda suka gama miqa wuya sanda suka shiga falon zuwa dakunan baccin dake gidan,gini ne mai kyau mai daukar hankali wanda aka yishi cikin hikima da fasaha,tun daga falon gidan zuwa dakuna zuwa kitchen babu abinda bai saka ba na alatun rayuwa harda ma qaari
“Kai Alhamdulillah…Aysha Allah ya miki baiwa….Allah ya zaba ya baki….Allah ya tabbatar dake cikin wannan gida…yasa tsohuwar gida ce” abinda inna laraba ke fada kenan cikin farinciki suna kewaye gidan,mero ba abinda take cewa ita da gwaggo asabe sai
“Amin…amin” cikin farinciki.

Ta gefan su anty halima kuwa bakuna zuwa jikkuna sun mutu murus,kowacce cikin ‘yammatan zuciyarta ta tafi,xasu iya cewa tsahon zamansu da burikansu basu taba shiga gida irin wannan ba….duk cikinsu babu wadda bata ji inama inama ace itace zata shigo gidan ba
“Kutumar uba….mutumin nan fa DON ne wallahi da alama”cewar mufida qanwar mijin anty halima sanda take qarewa gidan kallo karo na barkatai,batasan sau nawa ta kalli gidan ba,babu lungu ko saqo na gidan da bata kashe selfie ba….bama ita kadai ba har sauran yammatan
“amma asma cin kai ce….tace mana fuqara’u wal maskin ne shi?….inaga dai bata gano dai dai ba wallahi” inji nusaiba
“Ni gani nake anya wannan baifi hamid kudi ba?,ko a ina ta somashi?” Fatima qanwar mummy ta fada
“Da Allah ku yiwa mutane shiru kun cika mana kunne da surutan banza da wofi…….” Anty halima ta fada cikin zafi da qunar rai,lallai ba shakka khaliphan DAURIN BOYE NE,yazo musu ne a duqunqune kenan?,ita a karan kanta tasan cewa babu gami tsakanin khalipha da hamid,hamid eh lallai yana da kudi….saidai duka basu kai yadda suka zata ba,sun zaci yafi haka,fariya da dagawa da son a sani ya qarawa arziqin nasa ado ake masa kallon yafi haka,yayin da khalipha ya iya takunsa,yake dora komai a muhallinsa da mizanin hankali da nutsuwa.

Hannun nusaiba ya kai kan wani daki wanda shi kadai ne basu buda ba bayan na mai gidan,dakin na manne da bedroom din ayshan,binta sukayi duka a baya “gwara mu kashe qwarqwatar idanunmu…kai….wlh ji nake kamar a mafarki….indo?,indon da tazo daga qauye wai itace da wannan gidan?,anya ba qarya mutumin nan yake mana ba raina mana wayo kawai yake don ya burge ya kawomu gidan jama’a?” Inji anty kubra
“Nima tunanin da nake kenan” anty halima ta fada cikin sanyin jiki gami da tausayawa qanwarta,tasan yanzun zata tashi hankalinta matuqar taji cewa gidan ayshan ya kerewa nata.

Daki ne guda wanda aka shiryawa sif ta jikin bango kowanne gefe da tarin hangers na maqale sutturu,sutturu ne sabbi a dinke iya ganinka babu kalar wanda babu
“Innalillahi….oh my god” nusaiba ta fada tana rufe bakinta da hannunta tana fiddo idanunta,abun yayi masifar burgeta da tafiya da ita,ba ita kadai ba kusan duk wadanda suka shigo dakin,saidai hassada data cika zuciyar wasu daga ciki hakan ua gaza tarihi
“Na shiga uku…..indo ina zata kai wadan nan sutturu?….wannan kuwa zata gama saka su harta mutu?” Cewar mero tana dafe qirji,dariya inna laraba ta saki
“Suttura ai itace mutum kuma bata yawa….kuma bai kai mata lefe ba bawan Allah ashe haka ya tsara zaiyi mata” ta fadi cikin murmushi,kayan suka dinga bi daya bayan daya suna tabawa dubawa da fadin kudin wadanda suka san kudinsa,wanda basu sani ba kuwa saidai hasashe kawai da suke,tun suna dubawa suka gaji suka koma kan jakankuna takalma da mayafai,qarshe haqura sukai da qwaqwqwafinsu suka fito daga wajen bayan sun gama daukar hotuna,a falo suka tadda anty halima zaune wanda tunda ta saka kai dakin sai ta fito da sigar amsa waya bata kuma komawa ba,gefanta kubra ce zaune itama cikin sanyin jiki,bala’i ta hausu da shi kan uban meye suka a wajen,kamar basu taba ganin kaya ba?.

“Halima ina zaton saimu koma haka harda motar kaya ko?,tunda naga gidan babu abinda yake buqata ko cokali kuwa”cewar inna laraba,wani banzan kallo ta juyo ta watsawa matar data darawa ma mahaifiyarta a shekaru
“Ke kinga inna laraba,na gama fuskantar take takenki fa…tunda muka shigo gidan nan kike rawar qafa kina neman gindin zama….shine zaki gayawa mutane magana a fakaice,butulu shekararki nawa kina cin arziqinmu daga ke har indon?,ina cewa badon muba da tuni ana qauye ana fama da kirci da faso?,to mu duk girman arziqi bai rudarmu don mun saba gani ba yau farau ba” maganar ta yiwa inna laraba ciwo qwarai,a ganinta ko babu komai haliman ta girmamata ko don furfurarta,cikin murmushi da danne bacin rai tace mata
“Ki adana fushinki don bani nayi ba Allah ne ya nuna ikonsa a kai….duk wani abu da kuka hana aysha sai gashi yau Allah ya bata ninkinsa….duk abinda kuke zaton bata cancanceshi ba sai gashi yau Allah ya bata sama da shi,kun hanata mota qarama qwaya daya sai gashi Allah ya bata manya biyu,kun bata daki mafi qanqanta a gidan sai gashi Allah ya bata masarauta guda….kun siya mata kayan daki a qasar nan maimakon qasar waje kuma saiti daya sai gashi Allah ya bata wasu fiye da daya fin biyu ma,ya qawata mata gidan aurenta da jin qansa da rahamarsa….kinga kenan ba yina bane yin Allah ne…idan kunga dama ku aje abinda ke ranku ku rungumi yarinyar da bata taba taka muku ba bare ta zubar muku,ba sawa ba futarwa sai ku da kuke amfana ma da ita,baky dubi maraicinta ba,baku dubi rauninta ba kuke gallaza mata da gasata a ruwan sanyi ba tare da duk wani mara dogon nazari da tsinkaye ya fuskanci hakan ba,kun manta cewa Allah ke daukaka bawa a duk sanda yaso,kun manta cewa talaka da mai kudi duka Allah ne ya haliccesu badon yafison wani ba sai wanda yafi biyayya a gareshi,kun manta cewa dan kauye mutum ne mai daraja shima kamar kowa….qauye muhalli ne mai daraja tun a zamanin annabawa?,tunda ko annabinmu an bada shi raino a can,ya rayu da su bai kuma taba qyamatarsu ba,halima wannan ishara ce a gareku,ruwanku ku gayara ruwanku ku dora daga inda kuka tsaya,aysha dai tayi gaba amma zaku iya biyota a baya”miqewa anty halima tayi ta soma zuba ruwan bala’i,duk wani bacin rai dake ranta take furtashi a sannan,su anty kubra ke riqeta amma bata ji bata gani,murmushi inna laraba tayi
“Iyaka a dakatar dani bakin aiki ko?….ki sama ranki to daga nan zan wuce cikin nawa ahalin,karki manta yarona da qafarsa yazo zai tafi da ni mahaifiyarku ta dakatar da shi,ta roqeshi ya barni saboda sabo,ina fata baki manta ba?,abu daya zan gaya miki kafin na wuce shine…kibi ko ince kubi duniya a sannu,a yanzu ishara daya tazo muku…idan baku sauya ba sauran isharorin na nan tafe,bikin indo kuwa har qauyen takai in sha Allahu,na barku lafiya” ta fada tana juyawa nan ta fice ta barsu,anty halima naci gaba da kumfar baki.

*mrs muhammad ce*??
[3/6, 9:01 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN BAKI BIYA BA DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING_*

*_LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*_,IDAN KINA BUQATAR SIYA KI TUNTUBI WANNAN NUMBER (08030811300)_*

*KO KUMA*
(07067124863)

*DB*

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button