Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 30

Sponsored Links

30

Annin na xaune saman kujerun falon tana nunawa magajiya da larai masu aikinta guraren dake buqatar gyaran,ko kadan bata iya zama cikin qazanta duk taron da akayi sai taga gidan ya daidaita take samun sukuni,amal ce ta ukunsu tare suke gyaran falon,duk da cewa dauriya ce kawai take nunawa,ita kadai tasan ya take ji cikin zuciyarta,tana amfani da shawarar sayyada ne kawai qawa a gareta,yau khalipha yayi aure ya auri wata ba ita ba?.

Sallamarshi ta sanya anni daga kai cikin mamaki tana amsawa idanunta a kansu,tun kafin ta qaraso jikinta ya bata ayshan ce,amal dake duqe tana goge glass din center table ta dago da hanzari jin muryarshi tana binsa da kallo itama,gabanta yayi mummunar faduwa ganin mace biye da shi,sai tayi sauri ta koma taci gaba da aikinta,saidai rabin hankalinta da dukkan kunnenta na inda suke.

Related Articles

Miqewa annin tayi har suka iso inda take,ta kama hannunta tana yunqurin zaunar da ita saman kujera,qasan carfet ayshan ta sulale ta zauna,da sauri anni tace
“A’ah…tashi mana,ya zaki zauna a qasa?” Bata damu da wannan ba ta soma gaida annin cike da tsantsar nutsuwa,har a sannan bata bude fuskarta ba bate annin ta ganta,cikin kulawa anni ta amsa sannan ta maida kallonta kan khalipha dake zaune dai dai saman kujera,gajiyar da yayi na bayyana qarara
“Lafiya khalipha,me ya fito daku cikin wannan daren?” Yan aikin dake falon ya kalla sannan yayi gyaran murya,jiyowa sukayi suna dubanshi ya musu inkiya da su wuce,duka suka fice daga falon har amal wadda ta aje duster din hannunta ta haura saman anni,saidai kasa wucewa tayi ta tsaya daga can step din qarshe yadda zata iya jin duk abinda ke faruwa daga parlour din.

“Ta zabi zama a nan anni”shiru annin tayi tana duban ayshan cike da mamakin yadda taqi nata gidan ta zabi zama tare da su,sannan ta daga kai ta dubi khalipha
“Anya khalipha….ita da kanta ta zabi haka?”
“Gata nan anni ki tambayeta,Allah bani nace ba…” Ya fada yana dan bata fuska alamun da gaske yake
“Aysha….yaya zaki qi gidan da akayi donminki?…” Shuru ayshan tayi,tana kunya da nauyin annin duk da bata taba ganinta ba
“Shikenan kuje ku huta…zuwa safiya saimu gaisa tunda naga diyar tawa kunyata take ji” ta fada tana murmushi,harga Allah taji dadin hakan,kodon zaman kadaici da yadda takeson ayshan ta dauketa kamar mahaifiya ta kuma saba da ita,daya daga cikin masu aikin ta kira tace takai ayshan wani dako a bata duk abinda take buqata,a nutse ayshan ta tashi tabi bayanta tabar khaliphan da annin a falo.

“Khalipha anya kuwa babu takura ga yarinyar nan?”
“Ina shiga gidan abinda tace min kenan anni”
“Shikenan saida safe ma tattauna,jeka kaima ka huta nima tashi zanyi” amsa mata yayi sannan ya miqe yana ficewa daga falon,shima burinsa kawai ya samu waje ya huta,don har yanzu ciwon kan bai sake shi ba.

A sanyaye ta juya tabar wajen zuwa dakin anni dake sama hawaye nabin kuncinta,kenan a gidan matar khakiohan zata zauna?,anya kuwa zata iya ci gaba da zama da su?,anya ko burinta zai cika?,da wannan tambayoyin amal ta qarasa dakin ta samu waje ta zauna tana qoqarin controlling hawayenta.

Yana shiga dakin kayan jikinsa kawai ya fidda ya shige toilet,haka ya sakarwa kansa ruwa idanunshi na rufe ruwan na kwaranya tun daga saman kashi zuwa qafafunshi,sanyin ruwan na ratsashi yana masa dadi a jiki saboda zafin da ake dan tabawa kwana biyu,sai a sannan ya soma jin qwaqwalwarsa na komawa kan saitinta,nauyin daya dinga ji saman kanshi da qirjinsa na sauka,nutsuwa ta soma ratsashi,ya jima sosai qasan shower din sannan ya fito ya tsane jikinsa ya sauya kaya kawai yabi lafiyar gado,don hatta shafa’i da wuturin ma ya kasa yi yau,hannunshi saman kanshi yana shafawa kadan kadan,yana son hana kanshi yin kowanne tunani burinsa kawai bacci yayi awon gaba da shi.

Qarar wayarshi da ya manta shaf ba manta ba ta katse shi
“Ya salam” ya fada cikin salo na qosawa,ya saba idan yana so ya huta yakan kashe wayarshi ne a dare har sai gari ya waye don kada wani abu ya bullo da zai hanashi samun hutu,miqewa zaune yayi ya miqa hannunshi saman side drower ya dauko wayar,number ce babu suna,a gajiye ya daga ya kara a kunnenshi,kuka ya soma ji kafin daga bisani ya gane wace,zeenart ce,kuka take masa sosai
“Meye haka ne zeenart…me kike yi ne haka?” Ya fada cikin baci bacin rai
“Yanzu ya khalipha tsakani da Allah saboda bare shine ka gujemu ka zabi bare a kanmu?…mu ‘yan uwanka ya khalipha?…” Ta qarashe maganar tana sake fashewa da kuka
“Stop it zeenart…..bana son shirme don Allah da tsakiyar daren nan” yana gama fada ya katse wayar yana sakin dogon tsaki,ba don anni bama da duk cikinsu a yanzu babu wanda ya isa ya rabo kusa da shi,baijin akwai wanda zai sake kalla a cikinsu koya mu’amalancesu.

Yana shirin sake kwanciya wata wayar ta sake shigowa,tsaki ya sake ja kaman bazai daga ba sai yaga lambar data jibanci kamfaninsu ce
“Am verry sorry sir….” Ya fada cikin ladabi mai maganar ya fadi haka
“Ba matsala joe….me ya faru?”
“Sir…ka duba email dinka,zancan kwangilar nan ne nake ga kamar akwai matsala,na tura maka komai ka duba ka gani”
“Ohk…ohk” ya fadi da sauri yana kashe wayar,sannan ya sauka a nutse ya binciko inda ya aje system din nasa,sai daya kunnata sannan ya koma saman gadon ya zauna.

Aiki yayi sosai mai yawan gaske,tun yana yi cikin marmari har idanunsa suka soma nauyi suna lumshewa,tilas ya katse duk wani aiki ya zube saman gadon ba tare daya ma samu ya kashe cumputer din ba.

Daga bangaren aysha kuwa tunda mai aikin anni ta kaita dakin tana zaune daga bakin gadon,saidai zuwa yanzun ta janye mayafinta baya sosai yadda zaka iya hangen fuskarta,a hankali take qarewa dakin kallo…,dakine falle daya mai hade da toilet,akwai gado mirrow da wardrobe a ciki,komai na dakin ruwan madara ne hakanan tsarin da aka yiwa dakin dole ya burgeka,sosai ya yiwa aysha kyau ba kadan ba,shi kadaine a rea din sauran dakunan suna daga farko.

Amal ce data kasa zama tafe a gaba,kishi sosai take ji yana cik zuciyarta saidai tana qoqarin danneshi,ji take sam ba zata iya kwana ba bataga fuskar amaryar ba,tana fata bata fita da komai ba saboda watan watarana ta fata itama ta zama mata a gareshi,mai aikin anni na biye da ita dauke da kwanukan abinci,kayan tea da flask din ruwan zafin da anni tace a kawo mata ko zata buqata.

Qarar bude qofar ya sanyata saurin sunkuyar da kanta,idanun amal qyarrrr a kanta tayi sallama aysha ta amsa,suka qarasa gabanta mai aikin ta aje kayan ta fita,kusa da ita amal ta zauna cikin salon barkwanci tace
“Haba matar ya khalipha,ban taba ganinki bafa,nima rowar ganin fuskar taki zakiyimin,ai ni ba baquwar kunyarki bace saiki bude fuskar taki na gani” ta fada tana ja mata mayafin baya fuskar ayshan ta fito,sosai gabanta ya fadi sanda aysha ta dago suka hada idanu fuskarta qunshe da murmushi,bata taba tsammanin ganinta haka ba,lallai tabbas dole khalipha yaqisu kafataninsu,ko ita da take mace ba qaramin kyau ayshan tayi mata ba balle da namiji,ba shakka ko itace zata qisu din ta zabi ayshan,da qyar ta hadiye wani abu daya tsaya mata a wuya ta miqe tana cewa
“Ni suna na amal,cousin sis din ya khalipha,ga abincin nan ko zaki buqata,akwai toilet gashi can cikin dakin,akwai kayan bacci a wardrobe,ki kwanta ki huta matar ya khalipha” ta fada taba murmushin yaqe tare da juyawa zata fice daga dakin,banbarakwai aysha taji da sunan da amal din ta bata na qarshe,wai matar khalipha
“Na gode” ta fada a hankali,sai amal din ta juyo tana kallonta, sannan tace
“Babu komai” ta qarasa ficewa daga dakin gami da ja mata qofa,kuka sosai ta rushe da shi sanda ta shiga dakinta,bata ga wata hanya ba,bata ga wata kafa da zata shigewa khalipha ba,ko ina a toshe yake.

Aysha kuwa bandakin ta shiga tayi fitsari sannan ta daura alawa,bata buqaci kayan bacci ba ta ware mayafinta da yake babba ne mai kauri tayi shafa’i da wuturi ta maida kanta ta kwanta,tana jin gajiya na nuqurqusarta,duk da cewa ba wani zirga zirga tayi ba don bata dauki hidimar da dumi ba.

To sai nace asuba ta gari ahalin gidan mai goro .

************************

A gurguje ya shirya ganin har sha daya na safe bai fita cikin gida ba,bashin baccin kwana da kwanaki ya tabbata shi ya danneshi,cikin qananun kaya ya shirya ya fito yayi tsaf da shi kamar kowanne lokaci,sannan ya zira takalminsa half cover ya fito zuwa sashen annin.

Falon nata shuru babu kowa,hakan ya alamta masa wataqila itama gajiya ta hanata fitowa da wuri,yana shirin wucewa zuwa dakinta sai gata ta fito,fuskarta wasai da fara’a ta tarbeshi,cikin girmamawa kamar yadda ya saba ya gaidata
“Yau duka munyi nauyin bacci,don har masu aikin basu jima da gama abincin kari ba,yanzu nake shirin kiranka a waya dama,mun bar baquwa ita kadai bamu bata abun kari ba,bamu san yaushe ta saba cin abincin safe ba” murmushi kawai yayi don ko shi dinma baisan yaushe take karyawa ba,kar yaje yayi magana kuma ya kwafsa shi yasa ya zabi yayi shirun
“Dubata khalipha ta fito mu karya baki daya ko?,hakan zaifi” ba haka yaso ba amma bazai iya cewa a’ah ba,saboda haka ya aje wayoyinsa ya wuce zuwa dakin.

Fitowarta kenan daga wanka tana gaban mudubi bayan ta gama shafa mai tana gyara dogon gashinta,wanda ba yadda aliya vatayi da ita a biki ba suje ayi mata gyaran kai amma sam taqi,tafi ganewa ta gyara abinta a gida da kayan gyara na gargajiya,tunda yana santsi da tsaho abinshi,jin ana kiciniyar bude qofa ya sanyata yayar mayafinta ta yabawa kanta baima yafu a dai dai ba,tayi tsan tana jiran taji wanda zai shigo.

Da sallama ya shigo suka hada idanu kasancewar idonta na bakin qofar,amsawa tayi tana saukar da idonta qasa,idanunshi yakai kan saman goshinta dake kwance da sumar da bai taba gani ba,tunda ko yaushe cikin hijabi da dankwali take bata bari sumarta ko daya ta fito,dauke kanshi yayi yana jingina da bango
“Ina kwana” ta gaidashi da muryarta mai sanyi,masa mata yayi da
“Lpy lau ya kwanan baqon waje….anni tace ki fito mu karya”
“Toh” ta bashi amsa,saidai bata iya motsawa ko ina ba saboda tana son ta qarasa shiryawa ne,ya karanceta sai ya juya yaba yunqurin bude qofa yace
“Idan kin gama ina qofar dakin” ya qarasawa fice,a gaggauce ta daure gashinta ya daura dankwalinta sannan ta gyara yafen mayafin nata ta fito.

Yana gaba ne tana binsa a baya har zuwa cikin falon,kallonta anni take fuskarta qunshe da murmushi ,tausayinta ayshan na sake ratsa zuciyarta
“Kyakkyawar yarinya mai shekarun da basu haura a shirin ba,ya ilahi ko meye aibunta oho?” Anni ke tambayar kanta,tamkar aysha zata nutse haka taji sanda anni ta miqa mata hannu suyi musabaha,sai ta rasa inda zata tsoma kanta,khalipha na jingini saman kujera kamar mai shirin yin kwanciyar rigingine yana noticing abinda yake faruwa,murmushi anni tayi
“Ki daukeni kamar uwa wadda ta haifeki aishatu kinji,daga yau nan gidanku ne,bana so ki sake tuna wani abu daya faru dake a baya,ya zama tarihi daga yau da yardar Allah” kai ta gyada cikin tsananin kunya,har yanzu ta kasa kallon annin
“Muje muci abinci…..bansan me ya hana amal fitowa ba har yanzu,duba min ita khalipha” ba’a son ranshi ba ya miqe zuwa dakinta,a lokacin tana zaune saman kujerar mudubi bayan ta fito daga toilet data shiga ta wanke fuskarta saboda kukan data ci,knocking yayi mata ta tambayi waye
“Ki fito inji anni,tym for breakfst” daddadar muryarshi ta daki dodon kunnenta,saita lumshe ido kamar yana tsaye a gabanta,lumshe idanun daya fito da wasu sabbin hawayen,tuni yayi gaba bai tsaya jin me zata ce ba,saidata sake wanke fuskarta ta goga hoda da kwalli sannann ta fito.

Dauke idanunta tayi da sauri sanda idonta ya sona tozali da aysha daje zaune saman kujerar dining idanunta a qasa ta kasa sakewa,fresh skin dinta,manyan idanuwa da zara zara eye lashes,qaramin bakinta komai dai dai kamar wadda ta zana,kai ko ita ta zana bata jin zata zana mai kyau kamar wanda Allah ya bata din,sai data zo gab da su sannan ta iya dauke idanunta,ta qaqalo murmushin dole ta sorawa fuskarta tana jan kujera daya wadda ke daura da khalipha ta zauna tana fadin
“Amarsu ta ango” kunya maganar ta baiwa aysha,gaisawa sukai sannan amal din ta gaida anni,annin na tamabayarta ko gajiya ce ta hanata fitowa,amsa mata kwai tayi da eh amma ita kadai tasan meke cin zuciyarta,kusan dai cin abincin su uku suka yishi banda aysha,ta kasa taba komai,ji take kamar kowa ma kallonta yake,amal dinma kawai qarfin hali take tana tsakura tare da basarwa,har suka gama babu abinda aysha ta iya kaiwa bakinta,anni nata qorafin hakan khalipha na jinsu,kusan baida wata idea kan halayyarta shi yasa baida abun tofawa.

Sanda ya miqe ne anni tace masa
“Ya kamata ka wuce sashenka da ita sai ta samu taci wani abin a can tunda a nan ta kasa sakewa taci komai,zan turo muku badi’a ta tayaku gyaran wajen ko?”
“Ohk…zanyiwa kamfani magana ma akwai gyare gyaren da za’a yiwa wajen”
“Ya kamata….aysha kuje yanzun zan turo badi’a”amsawa tayi sannan ta miqe tabishi a baya suka fice.

Kamar mai tsoron wani abu haka take biye da shi a baya,tana jin fargaba da tsoro hakanan,a haka suka isa sahen nashi ba wanda yace komai da dan uwansa.

Kallon farko wajen ya burgeta sosai,komai a tsare a tsaftace kamar sashen mace,qamshi yake fiddawa sosai da alama qamshin ya kama wajen,babban parlour wanda ke tsare da kujeru blue black,rugs da curtains dun falon duka kalarsu kenan,sai kayan kallo daga gefe daya wanda aka musu bango gudada yasha ado mai daukan hankali,daga kowanne kusurwa na falon manyan hotunan khalipha ne window size kaman zaiyi magana,wanda suka fitar da ainihin halittar da Allah yayi masa,kowanne hoto akwai murmushi kan fuskarshi,akwai dakuna guda uku,daya bedroom ne biyun suna rufe batasan ko meye a cikinsu ba,saidai dayan dakin study room ne da wanda ya maidashi kaman qaramin office dinshi na gida wanda aka daga bayanshi aka yiwa wata qofa ta glass da zaka iya habgo bayan gidan dake cike da shuke shuke,isaka mai kyau takam shigo masa shi yasa yake jin dadin zaman wajen sosai,dayan kuma ya barshi ne a dakinsa na motsa jiki wanda shima yana da wata qofae daban bayan ta cikin falon.

Dubanta yayi har yanzu fuskatta na qunshe yace mata
“Ga guri ki xauna…..” Soma takawa tayi a hankali wanda ada tana tsaye daga bakin qofar falon,cikin rashin sani santsin door mat din dake bakin qofar ya debeta
“Subhanallahi” ya fada da sauri,Allah ya taqata ta dafe qofar qirjinta na bugawa,tsayawa yayi cak sannan ya sake dubanta
“Ki cire wannan lullubin haka….ni wanki ne ba wani abu ba” ya fada ranshi daya
“Me dame kike buqatar a dauko miki a can gidan?” Ya tambayeta yana jin banbarakwai don bai saba hada daki da kowa ba bare mace bayan ta zauna kan daya daga cikin kujerun
“Kayan sawa na suna nan cikin akwati”
“Kawai?” Ya sake tambayarta,kai ta kada masa sai ya juya ya fice,dai dai sanda mai aikin ta sako kai da kayan abincin,cak ta tsaya ta duqar da kanta cikin girmamawa ba tare da tace komai ba,hannu ya sa ya karbi farantin daga hannunta ta juya ta koma dama tasan dokar ba’a shiga mishi bangare.

Da sallama ya sake shiga ta amsa tana dubanshi,sai suka hada ido,ta sake jan mayafin nata gaba kadan,tabe baki yayi cikin ranshi yana fadin
“Sai wani faman rufe fuska kaman mara gaskiya,ko tana tunanin ina kallonta ne?” Itako cikin ranta cewa take
“Me yasa yakemin hidima da kanshi” ta fadi haka ne saboda matsayin data lura yana da shi,saman dan teburin dake daura da ita ya dora farantin sannan ya juya ya fice.

Sashen anni ya koma,tana zaune yanzun saman kujerar falo,dubanshi tayi
“Sai ina kuma?,zama ya kamata kayi khalipha sosai da ita har ta sake damu,na lura tana da baqunta sosai”agogonshi ya duba sannan yace
“Ba abinda aka taho dashi daga can gidan anni,dole naje naga me za’a dauko din kafin agama gyaran nan,sannan kuma ma ina da baqo…..na masa alqawarin zamu hadu yau,ina zaton kin sanshi abokin hudar abba ne tun yana raye….saidai kaman yaro yake a wajenshi,so sun saba tun a sannan abba na ara mishi kudade daga bisani ya maidowa abba da kudinsa idan ya juya an samu riba,to yanaso ne yanzun yaci gaba da wannan mu’amalar da ni,ina da dan alamun tambaya ne akan kasuwancin nashi,sannan ina tantama kan yiwuwar harkar tamu da shi saboda yanayin yadda na lura da rashin iya tattalinsa,da kuma rashin qwarewarsa wajen juya kudi gaskiya akwai matsala”ajiyar zuciya anni ta sauke
“Tunda har yana hurda da mahaifinka a baya bai kamata ka hanashi ba,abinda zakayi shine ka bashi a matsayin gwaji…sai kaga me zai biyo baya ko?” Kai ya gyada
“Haka ne anni….sai aci gaba da yi mana addu’a”
“In sha Allah….Allah yayi jagora”
“Amin” ya amsa sannan sukayi sallama ya fice.

Ruwan tea kawai ta iya sha cikin kayan da aka kawo din don ba kasafai ta fiye ciye ciye ba,hakanan ma ita sam yau bata jin yunwa,da haka ta hade kayan waje guda ta jingina da kujerar,zuciyarta da gangar jikinta najin gajiya na sauka kadan kadan daga jikinta,idanunta na gilmawa cikin falon tana yaba tsarinsa da kyansa,kwata kwata baiyi kama da falon namiji ba,da daya da daya tana kallon komai har idanunta ya sauka kan hoton khalipha wanda yake opposite dinta.

Yana sanye da kufta ruwan hanta,da hula dara da rufaffen takalmi,yayi murmushi sosai yana kallon kyamarar ya daga hannun damanshi sama kaman yana yiwa wani bye bye,sosai take kallon hoton tana qarewa khaliphan kallo,karo na farko data taba tsayawa ta kalleshi tun daga kanshi zuwa qafa
“Fatabarakallahu ahsanul khaliqin” ta furta a ranta,sai yanxu ta yadda da zancan aliya data ke gaya mata khalipha mai kyau ne,irin kyan da ba kasafai ake samun maza da shi ba,banda yau da zata iya rantsewa shacu fadin aliya ne tunda bata taba tsayawa ta kalleshi haka ba,a karan kanta taji tana jaddawa dawa kanta tayi iyakar iyawarta wajen tsayawa a matsayin qanwarsa,tabbas koba dade koba jima matar khalipha na tafe.

Daga wannan tunaninta ya gangaro kan mahaifiyarta,tunanin da rana bata fitowa ta fadi ba tare data yishi ba sau babu adadi,a hankali take nazarin labarin da gwaggo asabe ta bata,tana tuna duk wata kalma guda daya ta cikin labarin bata bari ta subuece mata ba,umminta tayi nisa,nisan da ba’ajin kira,abun ya ratsata shekarun da aka dauka ba wasa bane,wa zata kama?,wa zai taimaketa,wa zai taimaka mata ta dawo da umminta hayyacinta?,a qalla a yanzu ta samu sauqin wasu abubuwan ta wasu fannin,tunda har gashi dangin ummin da dangin mahaifinta suka iya tarayya waje guda lokacin bikinta,abinda iya zamanta bata taba gani ba,kusan yanzu babbar matsalarta shine yadda zata farkar da ummin nata,yadda zata samu soyayyar uwa kamar kowanne d’a
“Hasbunallahu wa ni’imal wakil,wa ufawwidu amri ilallah,innallaha basirun bil ibaad” ta shiga maimaitawa sau babu adadi kan Allah ya kawo mata dauki,a haka bacci yazo yayi awon gaba da ita.

Bata tashi farkawa ba sai dai dai lokacin sallar azahar,duka sai take jin wani iri babu dadi jikinta saboda bata saba zaman dabe ba haka ba a gida,toilet ta laluba a nan parlourn ta daura alwala ta tada sallah.

Daga can wajen anni kuwa duka hankalinta na wajen aysha har sanda aka kammala abincin rana,da kanta tasa aka shirya komai tacewa mai aikinta ta dauka ta kai mata,karba amal tayi ta wuce da shi don tana son sake tabbatarwa da kanta haka ayshan take?

Tana shirin fita daga kitchen din haidar ya shigo,baya ta danja kadan ya samu ya shigo din saboda tasan halinshi sarai,haka nan yaqi jininsu batasan dalili ba,saidai dalilin kusa yayi shige dana khalipha ne,a sanda dukkan abinda ke faruwar ya farun haidar nada dan sauran wayo,yana tuna wasu abubuwa daga ciki,yana da zuciya sosai shi yasa shima ya kasa mantawa,dalili kenan ma da sukaqi zaman gidan gaba daya da aka tashi hidimar bikin,suka koma gidan wani abokinsu shi da mus’ab dake bayan layinsu.

A ladabce kaman yadda suka saba ya gaida anni
“Ina mus’ab ne?,ai an gana bikin sai ku dawo gida hakanan ko?”
“Yau in sha Allahu….munyi missing dinki anni…” Murmushi kawai tayi tana dubanshi sanda yake duba abinda aka dafa,donshi ba daga nan ba wajen son abinci musamman mai dadi,kusan halayensa suna mata kamanceceniya dana khalipha.

Sanda ta shiga tana zaune saman abun sallah data samu kan hannun kujera,da murmushi kan fuskar ayshan ta amsa mata sallamar,amal din ta qaraso ciki idonta na kan ayshan wadda,ranta yacu gaba da suya irin na kishi gami da fargaba,lallai adazune ma bata kalleta sosai ba qila saboda kada wani ya gano kallon qurillar da take mata
“Ya bakici komai ba?” Amal din ta fada tana bubbuda abincin,murmushi ta sakeyi
“Naci mana”bata sake cewa komai ba don bata jin zata iya sake cewa din ta aje mata wancan kwandon ta dauki dayan ta fice,sai ayshan ta bita da kallo saboda ta fuskanci kaman ta dan sauya,gabanta ya fadi taji babu dadi a ranta,wataqila taji rashin dadi ne saboda bata ci wani abu ba a dazun,ita kuma taci iyakar cikinta kenan,bazata so ta soma bata musu ba daga kwana daya tak cikin gidan,saboda haka ta sauko ta zuba abincin cikin plate,ita kanta tasan ba zata iya cinyewa ba amma haka ta dinga cusawa har sai data ji tana son yiwa kanta illa sannan ta rufe.

Ba dadi haka cikinta yayi mata,hakan ya saka ta tashi ta soma dan kade kade a falon da goge ko zai zazzage,abinka da wadda ta saba sai kawai ta zarce da shara,ta gyara falon sosai duk da ba’a hargitse yake ba,amma komai nason gyara take ya sake kyau da qyalli,sanda ta gama uku ta gota,sai ta sake alwala ta kuma zama tana jiran sallar la’asar,ita irin wannan zaman sam bata saba da shi ba,shi yasa take jinta kamar cikin kurkuku.

_Ya Allah ka rabamu da sharrin mutum da aljan_

*mrs muhammad ce*??
[3/7, 7:27 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*KO KUMA*
07067124863

*DB*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button