Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 32

Sponsored Links

32

 

Khalipha ne ya soma miqewa daga zaman cin abincin,anni ta dubeshi
“Ka gama kenan?”
“Eh..ban jima da cin abinci ba ai…”
“Ko amarya dai ta cika maka cikinka?” Rahama ta fada da salon bin qwaqwqwafi,wani kallo yayi mata kawai ya dauke kai ya soma sauka daga wajen,ture plate din aysha itama tayi wadda bata ci wani abun arziqi ba sam,don ko yunwar ma bata ji batasan me yasa ba
“Aishatu kardai ace kema kin qoshi?” Kai ta gyada a kunyace
“Don dai ya khalipha ya qoshi ne shi yasa” amal ta fada can qasan ranta tana jin kishi,dariya suka saka tsakanin mus’ab da haidar,murmushi anni tayi sannan tace
“Saiku wuce hakanan ku samu ku huta ko muhammadu?” Anni ta fada
“Ohk…ohk” khalipha ya fada cikin dan daburcewa kadan wanda ba lallai ka lura da hakan ba,yayi zaton anni zata bata daki ta wuce ta kwana a nan,amma sai ya raya a ransa me yiwuwa saboda idon yaran ta gwada hakan
“Aishatu wuce ku tafi sai da safe”kunya ta sakata ta kasa motsawa daga nan,idon rahama na kanta haka ma amal na satar kallonta,tsaf anni ta lura kunya take,sai tace da khalipha
“Wuce amal ta rakota”
“Ohk to…” Ya fada yana jin dadi cikin ransa,don baisan yadda zai kwana daki daya da mace ba.

Yana fita daga falon anni ta dubi amal
“Qarasa ci ki rakata..”
“Toh” ta amsa wani abu yana dunqule mata a maqoshi,hakanan amal ta dinga yangar cin abincin da gayya tana sani,bata gama ba har sai da khalipha yaci wajen awa daya da tafiya sannan ta sha ruwa ta miqe hakanma ba don taso ba
“Allah ya bamu alkhairi”
“Amin” aysha ta amsawa anni.

Kaman tafiyar kurame haka sukayi,ita aysha baqunta amal kishi har suka isa qofar part din nashi,amal na shirin juyawa aysha tayi qarfin halin cewa
“Ba zakiqaraso ba?” Idanu ta waro tana dubanta
“Ko da can ba’a shiga masa sashe any how ina ga yanzu?,sai da safe” ta fadi tana yin gaba,sai dataga wucewar amal din sannan ta tura qofar ta shiga tana tunani
“Komai nashi a tsare take sarkin tsari me da alama wannan mutumin” bashi a falon sai wasu jaridu dake zube gefe daya da alama dubasu ya gama yi ya tashi,daga can wani side din idanunta suka gamo mata qyallin wasu akwatuna,irin wanda ya bata dazu sak saidai su manyansa ne guda goma sha biyu,gefe daya ta samu ta zauna qasan carfet na tsahon minti talatin sannan aka turo qofar bedroom din aka fito,sanye yake da jallabiyya baqa sai zabga wani qamshin yake daban,dan tsaiwa yayi da ganinta a zaune,ya zaci anni ta riqeta kenan?,hannun rigarshi dake nade ya soma saukewa yana jin wani bawai,ya saba bararrajewarsa shi daya a sashensa ta yaya zai iya zama da wata,agogon dake maqale a bangon falon ya kalla,goma da arba’in sha daya saura kenan,din shirin kwanciya ma yake ya dawo cirar wayarsa ne
“Ammm…” Ya fada kana yayi shuru
“Inaga muje wajen anni ko akwao wani dakin spare ki kwana a can,zuwa lokacinda zanga ya za’ayi a gyara inda zaki zauna a nan” ya qarashe yana goge gargasar jikinsa dake jiqe da ruwa da qaramin towel.

Yana gaba tana baya har sashen anni,babu kowa a falon,sun kashe ma duka wutar falon alamun sun kwanta saishi ne ya kunna,saman anni suka haura kai tsaye har zuwa qofar dakinta yayi knocking,daga ciki ta bada izinin shigowa,tana zaune saman abun sallah da hijabi a jikinta,haka take duk dare bata wani barcin arziqi,tana raye darenta da salloli da addu’o’i ma yaranta da mai gidanta daya rasu,shi yasa yawanci take bacci tsakanin sha biyu na rana zuwa azahar haka hakadan,wanda irin wannan baccin sunna ne,annabi S A W yayi umarni da yinsa,yace saboda shaidan baya irin wannan baccin,yawanci hausawa muna kiransa da qailula,da ido ta bisu sannan daga bisani ta saukewa khalioha kallon baki daya,dai ya dan dirirce daga jisani ya tattara hankalinsa yace
“Anni…cewa nayi akwai sauran dakin da za’a ara mana zuwa sanda za’a gyara sashen nawa?” Wani irin kallo tayi masa kafin ta dauke kanta ta.mayar kan casbahar gabanta me dubu da take ja
“Babu,saidai wannan nawan da nake ciki”
“Subhanallah”ya fada a ransa cikin fargaba
“sai da safe”ya fada da sauri yana duban aysha tare dayi mata umarnin ta taso su tafi,batasan me yake faruwa ba itadai ta tashi ta bishi,a son ranta itama a samu inda zata kwanna a can,har su fita ta qwalo masa kira,shi kadai ya koma aysha ta jungina da makarin silver na matattakalar
“Daga yau karka sake yawon neman dakin da zaka aje matarka…karkayi kuskuran dako sau daya zata ji cikin ranta ita ba komai bace a cikin gidan nan,bata da cikakken matsuguni,bangarenka shine nata,shine cikakken ‘yancinta,yanzu ba mallakinka bane”
“In sha Allahu anni” ya fada cikin nuna ladabi
“Tashi ka bani wuri sai da safe”
“Na gode” ya fada yana fita,suna tsaka da ficewa suka jiyo muryar rahama
“Yawon me angwaye suke haka alokacin daya kamata ace suna tsaka da morewa lokacinsu?” Ta tambayesu tana qarasowa cikin kayan bacci,dauke kai khalipha yayi ya juya baya kafin ya bata amsa
“Ina tunanin tsananin sa idonki ne ya hana kowanne saurayi tararki yace zai aureki sanoda yana gudun shegen qwaqwqwafinki” tilas ba don ya shirya ba yasa hannu ya damqo hannun aysha,ya hade yatsunsa da nata ya jawota yana fadin
“Sai da safe idan kin gama tambayoyin kya iya tafiya” sukayi gaba suka fice daga falon.

Bai saki hannunta ba duk da yadda wani abu ke ratsashi tun daga yatsanshi zuwa qwaqwalwarsa don yana gudun sa idon rahama,tsaf zata iya leqensu,sai da suka shiga falonshi ya maida muqullin ya rufe sannan ya zame hannunshi daga nata,wanda zuwa wannan tuni ta daskare a wajen,bata taba aikata hakan ba bata kuma tabajin irin hakan ba,tsoro da fargaba jikinta har dan rawa yake saboda tsoro da rashin sabo,guri ta samu ta zauna ba shiri zuciyarta na bugawa,tuni ya wuce bedroom sai ya tsaya ya rasa me zaiyi,tafin hannunsa ya duba kamar me neman amsa sannan ya hadashi da daya hannun nasa ya murza su sosai ko zai daina jin abinda yake ji idanunsa a lumshe yana furzar da iska mai dumi daga bakinsa,tsahon minti biyar yayi a haka sannan ya haura gadonshi ya ciro blanket da pillow qwaya biyu,yana jin bai kamata ita ta kwanta a falon ba saboda yadda anni ta nuna kulawa a kai shima ya kamata yayi komai saboda annin
“Ki shiga ki kwanta” yace da ita yana zube pillows din a qasa tare da shimfida blanket din kan kujera,kanta ta daga ta dubeshi,har ya gama shimfidar ya dora pillow bata motsa ba
“Nace ki shiga ciki ki kwanta” ji tayi hakan bai dace ba sam,karon farko data bude baki
“Babu komai zan kwanta a nan kai ka kwana a dakinka”
“Ba zaki iya ba”
“I can do it…ka manta,daa a tsakar gida nake kwana ma gaba daya kusa da turken dabbobi?” Ta fada qwalla ma shirin taruwa a idonta,sai ya daga kai kawai yana dubanta jin abinda ta fada,baisan me ya tuna mata da wannan rayuwar ba a dan tsukin nan,kawar da kallonshi yayi daga gareta sannan yace
“No,kiyi kaman yanda nace miki” zamanshi yayi saman daya kujerar yaja magazine din yana dubawa,wanda talla ne na wasu kamfanunuwa da sabbin gine gine ake masa,a nutse ta miqe ta nufi dakin gadon a karo na biyu,sai data shiga ta maida qofar ta tura ta yadda ta ganta,gadon ta qarewa kallo sosai,bata jin zata iya hawa gadon daba nata ba ta kwana bayan ta kori mai gadon zuwa falo,tana jin kamar tayi zalunci ne,bargo itama ta cira ta shimfida a qasan gadon ta saka pillow,tana dora kanta tunanin mahaifiyarta ya dawo mata sabo fil,’yan sa’o’in data yi da anni da khalipha tafa yadda uwa ke nuna qaunawa yaranta,taga yadda uwa ke zama wani abun alfahari a wajen yaranta,duka cikin abinda ya zama musabbabin faruwar komai bata ga laifinta ba ko qwaya daya,me yasa abun yafi shafarta fiye da kowa?,me yasa abun yafi illatata,sakamakon ya koma gareta duka da nauyin laifin daba ita ta aikata ba,bata bada shawarar kan kasancewar haka ba?,idanunta ta lumshe hawayen dake maqale a gashin idanunta ya sauko zuwa kuncinta.

????????????????

Tunda ta idar da asuba idanunta biyu bata koma ba tana ta rabo ido cikin dakin nashi,ba abinda bai burgeta ba a dakin,komai sai data qare masa kallo kafin ta dauke kai,bata taba gasgata zata kwana a irin dakin ba a rayuwarta,qarfe takwas na safiya tayi karambanin shiga wanka,sanda ta fito taga wani qaramin akwatin da yafi na jiya girma a gefen gado,batasan ya akayi ya shigo dakin ba,amma koma.meye tana da buqatar kayan sawa,data bude komao da komai akwai a ciki,saidai sabanin na jiya wannan harda soson wanka water soap,brush da toothpaste,sai setin rollon,body spray powder da sauran tarkacen kwalliya da qamsasa jiki,mai ta shafa kawai da powder,sai jikinta data bude da turare saboda qaunarta da qamshi itama,kayan dake cikin akwatin ta buda tana dubawa,qarshe ta zari wata atamfa ta saka set da mayafinta da komai.

Ita kanta data tsaya a jikin mudubi sai taga kaman ya zira jiki da yawa,ba wata kwalliya tayi ba amma kyanta ya fito sosai,atamfar holland ce pink me adon fari da blue zanan manyan ganye,cikin ranta take tasbihi da godiya ga ubangijinta wanda yake sauya mata rayuwa daga wannan bigiren zuwa wani a sanda baka zata ba,maida komai muhallinsa tayi ta gyara dakin zuwa bedroom din sannan ta maida mayafinta ta fito.

Babu kowa a parlour din sai tarkacensa da kayan shimfidarsa na jiya,saidai tana iya jiyo motsi cikin daya daga cikin dakunan dake falon,wala’alla tayi tunanin yana ciki,gyare falon tayi tas har ta gama bata daina jiyo motsin ba,saboda haka ta bude qofar kawai tayi cikin gida,don yau batason wannan wunin waje guda,ita sam takura take tunda bata saba da shi ba.

Tana shiga falon anni tayi kacibus da daya daga cikin me share sharen gidan riqe da mopper,cikin girmamawa ta gaida aysha ta amsa tana jin kunyar yadda tayi matan tare da mamakin ta santa ne?
“Anni ta tashi?” Kai ta girgiza
“Ai sai goma da rabi sannan take saukowa qasa ayi karin safe idan ba yunwa kaji ba ko uzuri gareka” kai ta jinjina sannan ta tambayeta kitchen,jagora tayi mata zuwa kitchen din ta qofar ta nan cikin falon zuwa wani corridor na musamman inda kitchen din yake.

Mutum biyu ta tadda suna aikin abincin safe,suma gaidata sukayi cikin girmamawa ta amsa musu kaman waccan karon,sai taja kujera ta zauna tana kallon yadda suke gudanar da ayyukansu,take kewar gida ta taso mata,sabo turken wawa,da tuni i yanzu itama tana can tana tata sabgar,duk motsinsu tana biye da su,a nan taga kurakurai da dama daya kamata su gyarashi yayin girkinsu,saidai bata ce musu komai ba saboda tana ganin hakan bai kamata ba daga zuwanta a matsayinta na baquwa bazatayi musu shishshigi ba.

Tana nan zaune har suka gama komai,saidai duk abinda sukeyi suna yine cikin tsafta daya daga cikin abinda ya burgeta kenan,da alama sun horu da tsafta daga wajen anni,dawowa sukai suna gyara wajen da wanke kayan da sukayi amfani da shi,zata kama musu saida kowa ya zabura suna fiddo da ido
“Ki rufa mana asiri…inamu ina saka matar boss aiki,kiyi haquri don Allah” suka fada a marairaice,karo na farko da aka soma girmamata a rayuwarta,karon farko da aka nuna ita din mutum ce mai wata daraja ta daban,dariya suka so bata,lallai qaramin sani qunqumi,lallai basu san ita din wace ba da basu wani gigice haka ba.

Katsam saiga anni a kitchen din ta shigo riqe da wani jug a hannunta,cikin ban girma aysha ta miqe ta amshi jug din daga hannunta tana shirin gaidata annin tace
“Aysha harkin tashi?”
“Ai hajiya ta jima a zaune a nan tana kallon aikin girki”kallonta annin tayi
“An tashi lafiya ya baqunta” kamar zata nutse haka taji,ita annin ke gaidawa,russunawa tayi sosai ta gaidata ta amsa tana jin dadi a ranta,kallon daya daga cikin masu aikin tayi
“Atika karbi jug din ki hadamin wani,kinsan ina gama cin abinci nake sha”
“Toh hajiya…da alama kinji dadin jikinki”
“Sosai ma…kedai Allah ya biyaki”
“Ameen hajiya” ta fada cikin farinciki
“Bari naje nadan watsa ruwa kafin sarakan baccin su tashi muyi break”
“A fito lafiya” aysha ta fada cikin girmamawa annin ta amsa sannan ta juya ta fice.

Inda ta tashi ta koma ta zauna tana kallon atika na yin wasu hade hade cikin jug din,ta gane me take hadawar saidai taga kamar akwai kura kurai a ciki,taso yin shuru sai kuma ta kasa
“Ko zaki dan aramin jug din kadan naga ko na iya hadawa?” Waiwayowa tayi tana duban ayshan tana murmushi
“Kai hajiya wannan hadin mutanen qauye mu muka fi saninshi ai,ina ku kuma ina qauye” murmushi tayi kawai tana saukowa daga saman kujerar da take kai ta nufi inda take
“Ba wanda bashi da qauye…duk wanda yace baida qauye ka tuntubi asalinsa” sosai zancan ya yiwa atika da sauran biyun dadi,basu zaci haja daga gareta va,sun saba ganin qyama da kallon banza daga gun duk baquwar fuskar data zo gidan,abinda ke kwantar musu da hankali da sake basu qwarin gwiwar zama da mutanen gidan shine basu taba jin ko ganin maganar banza ba daga wajensu

Cikin minti goma kacal ta gama hadawa,atika duka na kallonta cikin mamaki
“Kai hajiya….ya akayi kika iya wannan hadin kamar ma yafi nawa kyau?” Murmushi kawai ayshan tayi ba tare data bata amsa ba,kusan tasan magunguna sosai,saboda inna yelwa tayi sana’ar saidasu kala kala,kuma babu maiyin wahalar sai ita,wani lokaci ma ita ke shiga jeji ta sassaqo abinda ya kamata,ta gada ne itama daga wajen mijinta wato kakan ayshatu bayan rasuwarsa,wanda ya rasu ne tun kafin a haifi umminta.

Tana aje jug din rahama na shigowa cikin kitchen din,ta tsuke cikin shirt da dogon skert tana takawa dai dai,ganinta duk sai su atika suka nutsu,suka soma gaidata tana amsawa dai dai tare da cewa
“Ku samamin wani abun,duka abinda kuka dafa din yau bana jin cinshi” kai aysha ta daga tana dubanta cikin mamaki,a qalla an dafa abu yakai uku kuma duka tace babu na cinta a ciki?,idanunta ne ya sauka kan ayshan,ta dan kalleta na minti biyu,yanayin halittarta tayi mata sosai,ta yabawa tsarinta saidai tana kishinta
“Amaryarmu…ya da fitowa da safe haka?,ke daya kika bar angon naki?”
“Tare muka fito nina rakota saboda ta damu taga anni,komawa nayi in dauko wasu takardu dana manta” muryar khalipha ta ratso kitchen din a sanda take takowa zuwa kitchen din,cikin yadin kufta baqi wanda iyakar rigar qasan gwiwa sai dogon hannu da take da shi,aikin sarauta aka yi masa sosai wanda ya dace da hula dara dake kansa,ba qaramin kyau suka yi masa ba,sai ya tashi tamkar wani jinin sarauta,kwarjininsa ya qaru sosai,sunkui da kansu atika sukayi sannan suka rusuna suna gaidashi,ya amsa musu suka lalubi qofa suka fice,kitchen din ya rage saura su uku,hannyensa harde a qirji ya zubawa rahama ido,wanda a take ya ladabtar da ita,ta dauke kanta tana basarwa
“Princess” yayi qarfin hali fada yana duban aysha,sai tayi wuri wuri da ido cikin mamaki da tambayar kanta dawa yake,hakan sai yayi kama da kamar ta kada mishi idanunta ne a ganin rahama,hannunshi ya miqa mata yana cewa
“Muje muyi break anni tace na kiraki” dubanshi take,ta fuskanci abinda yake nufi,amma sai take jin ba zata iya ba,har yanzu kallonta yake yana fatan ta dago abinda yake nufi ko don rahaman,iya matakin da zai dauka a kanta kenan ta rage sawa rayuwarsa ido da matsanta masa,ganin ayshan nason karya plan din sai kawai ya saqalo tafin hannunta ya janyota zuwa kusa da shi tamkar zasu hade,sannan ya soma takawa ba shiri itama tabi sahunsa yana fadin
“Rahaman kike jin kunya….idan baquwarki ce toni ba baquwata bace…muje kici wani abu na lura bakison cin komai,bana son wannan baquntar taki fa” da idanu rahama ta bisu ranta na suya,bata taba sanin haka khalipha yake ba sai yau,ashe duk sauqin kanshi da take gani da sakin fuska ta wani fannin baida kirki,ita zaiwa haka?”qwalla ce ta cika mata ido tayi hanzarin maida ta,a hankali ta soma takawa tabi bayansu,ta fasa canza abun karin,zama taci ko meye.

Gab da zasu isa qofad da zata sadasu da ainihin falon taso ta zame hannunta,turasu yayi ita da shi cikin wani daki wanda sai da suka shiga taga store ne na kayan abinci,idanu ya tsareta da shi sannan ya soma cewa
“Na gaya miki tun ranar farko ni dake,karkiyi wani abu da zai saka baqin fuskar dake yawan zuwa gidan nan su dora ayar tambaya a kanki ko akanmu,ke matata ce wadda na aura saboda ina sonta,ta aureni auren ‘yanci da soyayya kuma akan radin kanta,a haka kike a idon family na….kiyi qoqarin ci gaba da kasancewa a haka,bana son ki bada qofar zargi” kalma ta qarshe data shiga kunnen rahama kenan wadda tazo wucewa,tsai tayi tana jira ko zata sake jin wani abu,saidai ba abinda khaliphan ya sake cewa,illa handkherchief daya ciro daga aljihunsa ya miqawa ayshan yana cewa
“Goge hannunki da kyau,baki tsaya kin wanke ba muka fito,ga gefan fuskarki ma ya dan baci kadan” a sanyaye ta saka hannu ta karba ta goge duk inda yace din,gefan bakinta ne kawai bai gama goguwa da kyau ba,dole ya karba ya sake matsawa gabanta kadan yasa handkherchief din akan yatsanshi ya soma goge mata,numfashinsu ne ya soma gauraya da juna saboda kusancin da hakan ya kawo tsakaninsu,idanunta ta daga saita saukesu fes cikin na khaliphan,ja baya yayi da sauri kaman wanda aka jonawa shock,cikin aljihunsa ya saka handkherchief din sannan ya juya ya soma yunqurin ficewa,hakan ya sanya rahama qara wuta tabar wajen kafin su fito su cimmata.

Duk kowa na saman tebur din kusan kaman qarasowarsu ake jira,ja mata kujera yayi ta zauna kafin shima ya zauna,hakan ya yiwa anni dadi sosai,yayin da amal ta dauke ido zuciyarta kaman zata fito,rahama kam hararar khalipha take a fakaice,wanda ko giyar wake tasha tasan bata isa ta harareshi ba gaba da gaba,haidar ne ya soma gaidata sannan mus’ab,dukkansu ta amsa cikin fara’a da jin kunya,don dukkansu sun girme mata amma suke girmamata kamar itace gaba da su,shikam haidar ganin qimarta yake tun waccar rana a capteria,abinda tayi ya tabbatar masa ita din nutsatstsiyar macace,sai gata a amatsayin matar wanshi hakan ya masa dai dai,a nutse ake cin abincin babu yawan surutu kaman jiya,tsakiyar shurun muryar rahama ta ratso
“Ya kamata amarya ki fadi abincin da kika fiso tunda kin shigo cikin iyalin da kowanne lokaci ake daukar abincin da kowa yafiso a girka”
“Karki damu….abun mamaki duka choice din anni akan abinci irin na aysha ne….” Ta wutsiyar ido aysha take satar kallonshi,itadai tasan basu taba magana makamanciyar haka ba,hasalima koda za’a titsiyeta batasan choice din anni ba a yanzu,dan sauya fuska rahama tayi sannan tace
“Haba ya khalipha…ka barta ta fadi da kanta mana…,wai haka ne?”murmushi ta saki wanda dan fitar sautinsa yasa khalipha daga kai ya dubeta sannan ya maida kan plate din gabanshi yaci gaba da juya abincinsa
“haka ne”ta bata amsa a taqaice,kafada ta daga tana tabe baki
“sai kace mutuniyar qauye?….”
“Suba mutane bane?,abincin da suke ci duka yafi namu lafiya,mu kusan duk kame kame muke,ko a qarfi idan kija hada yaron qauye saiya kada na birni guda uku shi kadai” anni ta bawa rahama amsa tana murmushi tare da son nusashsheta,sosai amsar ta yiwa aysha dadi ta kuma qarawa anni qima da martaba a idonta,khalipha ma yaji dadin hakan,saboda baison aysha tayi wani abu da zaisa rahama ta dauki haske kan wani abu daya shafeta ko ya shafi rayuwarta,daga haka bata qara tankawa ba kowa yaci gaba da cin abincinsa.

_Ya Allah,ka rabamu da sharrin mutum da aljan_????????

*mrs muhammad ce*??
[3/7, 7:28 PM] Binta Mustapha: *_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_SAFIYYA HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*KO KUMA*

07067124863

*DB*

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button