Daurin Boye Hausa NovelHausa Novels

Daurin Boye 52

Sponsored Links

52

Anty halima,anty kubra da anty lubabatu na zaune a falon,da fari sun soma hayaniyar ganin asma’u ganin shigowar aysha ya sanyasu rage hayaniyar tasu,dukkanin idanunsu na kan ayshan,kowa da irin kallo da yake mata,musamman anty halima da komai na ayshan ya tsone mata ido
“Ashe ana ganinku?” Cewar anty luba tana duban ayshan,tana neman abun fada,murmushi ayshan tayi
“Ana ganinmu mana anty luba,makaranta ce kawai ke sakawa wani zubin bana zama available koda yaushe,sai weekens nake dawowa gida” tabe baki anty halima tayi
“Kuma a haka ake zaman auren?” Dubanta aysha tayi,ta karanceta tsaf,ta kuma gogu da zama dasu hanan
“Eh…ba wata damuwa bace ko matsala ai idan akwai fahimtar juna tsakaninka da abokin zamanka”toh baki yasan abun fada baisan me za’a maida masa ba,sai maganar ta dan yiwa anty halima zafi,tunda suke da aysha wannan ne karon farko data soma maida mata amsa dai dai da maganarta,ta fuskanci amsar ta shigeta dai dai yadda ya kamata,don haka saita miqe tana cewa
“bari na qarasa na duba jikin daddyn” ba wadda ta amsa mata.

Da sallama ta shiga falon daddyn,yana zaune qasan carfet ya jingina da kujera,mummy na gefanshi tana hada mishi abinci,a ladabce ta qarasa gabanshi ya zube tana gaidashi da dubashi da jiki,fuskarshi fal da fara’a yake amsa mata,sannan ta waiwaya rana gaida mummy,da qyar take amsa mata,itakam a rayuwa ta rasa me ta yiwa mummyn,idan ma har zamansu ne tare bataso a baya ai zuwa yanzu yaci ace ta aje komai tunda tabar musu gidan,zata tashi daddyn ya tsaidata,hira suke sosai wadda suka jima basuyi irinta ba da daddyn,taji dadin hirar tasu ita kanta ba kadan ba,daga bisani tayi sallama da daddyn bayan ta aje masa kudi masu yawa,da fari qin amsa yayi yace shime bata ne ai
“Nasani daddy kafi qarfinsu,amma abinda kayimin a rayuwa kafi qarfin komai a wajena,badon baka dashi ba na baka,saidon bansan me zan baka din ba,amma wannan ka amsa daddy kasa min albarka ka nuna jin dadinka wannan shine kadai zai faranta min ,ya kuma tabbatarmin da kaji dadin kyauta ta”
“Shikenan indon baffale,Allah yayi miki albarka ya albarkacu rayuwarki,jiyan ma munyi waya da maigidan naki ya dubani da jiki,Allah yayi muku albarka”
“Amin daddy” ta amsa kanta a qasa tana jin wani abu cikin ranta,yaushe khalipha ya kira daddyn amma ita ya shareta,toko laifi tayi masa?,da wannan tunanin ta baro sashen daddyn ta dawo sashen mummy,asma’u ta tadda kawai a falon,sai anty halima dake dakin mummy tana bacci,saura duka sun tafi,da murmushi kan fuskarta ta dubi ayshan
“Ina mai gidan ya kika barshi?”
“Yana lafiya” ta bata amsa fuskarta a sake,saidai zuciyarta cike fal da mamaki,dama akwai sanda asma’u zata tambayi lafiyar khaliphan,tsaki asma’un taja wanda ya katse tunanin ayshan ta sauke wayar data kanga akunne
“Pls aysha bani aron wayarki don Allah zanyi wata waya,bashi nake bin wata mata idan na kira taga numberta ce sai taqi dagawa” wayar tata ta ciro daga jakarta ta miqa mata sannan ta miqe,alwala dama takeso ta daura zatayi sallar la’asar ,don haka ta shige toilet din dake parlour din donta daura alwala.

Related Articles

Cikin hanzari ta dauki abinda zata dauka a wayar sannan ta fita ta aje mata wayar tana murmushi cikin ranta,sanda ta fito daukar wayar tayi ta sanya cikin jakarta sannan ta tada sallah,bayan ta idar ta yiwa mummy sallama ta baro gidan.

Tana cikin revers zata fice daga gidan taga anty halima da asma’u sun fito,da alama wani waje zasu je,hakan ya sanya ta dakata har suka qaraso gab da ita,cikin murmushi tace
“Anty naga kamar wani waje zaku”
“Eh ya akayi?”
“Ku shigo saina rage muku hanya” ta fada tana bude musu qofar motar
“A’ah,jeki kawai” anty halima ta fada tana yin gaba asma’u ta bita a baya,sai dataga sun wuce sannan ta tashi motar itama ta fice a gidan tana girgiza kai kawai cike da mamakinsu,har yau ace jiya iyau alqarasu?,Allah ya kyauta ta furta a sarari sanda take hawa saman titi.

????????????????

Duk yadda yaso daurewa cikin kwanakin gaba daya juriyarshi ta qare,ya tabbatar wa kansa da cewa soyayya ce ta kamashi,soyayya aysha ce ta masa kamu bana wasa ba,irin soyayyar da bai zaci zai bawa wata diya mace irinta ba,cikin daren ya kasa bacci gaba daya sai juyi da yakeyi,ji yake idan har baiji muryarta ba wani abu xai iya faruwa dashi,dole ya janyo wayarshi yayi kiran layinta.

A lokacin itama tana cikin falon sashensu tana karatu,don tun sanda annin ta tafi bata fiya zama a wancan falon ba,don gaba daya ta kame kanta itama saboda su rahama,sai taso ma sannan suke ganinta,tayi qoqarin dai killace duk wani abu daya kamata,tun randa aka rasa atamfar anni daya cikin ukun data bayar akai mata dinki,idanunta ta daga kawai ta dubi wanda ke kiran,sunanshi ta gani saman screen dinta yana yawo,wani abu mai kama da jan aji ya motsa mata,saita share kiran har ya katse,sake kiranta yayi karo na biyu,nan ma tana sane ta basar da kiran,don ta tabbata cewa lafiya lau ya daina kiranta da replying saqonninta.

Zama yayi daram kan gadonshi sanda yake sake kiranta karo na uku,jikinsa har dan rawa yake yana addu’ar ta amsa ba tare ma da yasan yana yi ba,baisan cewa haka ya damu da ita ba,baisan cewa haka yayi kewarta ba,baisan cewa haka soyayyarta ta kamashi da zafi ba sai yanzu,bata daga din ba sai gab da zata yanke ta kara a kunneta hadi da yin sallama,wata ajiyar zuciya ya sauke da qarfi a sarari wadda ta ratsa dodon kunnen aysha,saita lumshe idanu tana jin muryarshi yana amsa sallamarta
“Uwaishah….” Sai taji sunan yayi mata dadi qwarai har data lumshe ido
“Ya Allah,what a nice name” ta fada cikin zuciyarta,tana jin zuciyarta na mata nauyi dauke da wani abu mai wuyar fassara,gaidashi ta soma yi ya amsa murya can qasa sannan yace
“Uwaish bakya kewata ko?,duk yadda naso na daure na kasa,wannan abun ba lafiya ba” idanu ta zaro don bata fahimci kalmarsa ta qarshe ba
“Me ya sameka kuma ya khaliphah?” Yadda ta ambaci sunanshi karon farko saida murmushi ya subucr daga lebansa
“Asiri kika yimin ko ayeesha?” Gabanta ne ya fadi sosai,tsoro ya kamata,sai zuciyarta ta karye,tuni hawaye suka tsattsafo cikin idanunta
“Ya khalpha?,asiri fa?,na rasa wa zan yiwa asiri saikai?,don Allah ka yimin bayani waya gaya maka haka?” Ta qarashe muryarta na rawa,dariya sosai take cinsa saiya kanne
“Ki jirani zan gaya miki” ya fadi yana katse wayar saboda ya kasa boye dariyarsa,baiso kuma taji,wayar na hannunshi yana jujjuyaya yana kallonta,iya muryarta kawai daya ji ta kwantar masa da.hankali sosai,hakanan cikin jikinsa yaji ayshan kuka take,saboda haka saiya rubuta mata texs

_idan kikayi kuka toki tabbatarwa kanki da kanki baki da gaskiya,hakanan idan kika damu to shima baki da gaskiya,just in kin yarda da.kanki fell free kawai,ki tanadi abinda zaki kare kanki idan nazo tuhumarki_

Saqon nashi ta dinga maimaita karantawa,saita samu kanta da share hawayen fuskarta,ta dinga maimaita karanta saqon nashi,ta wani bangaren yana mata kama da gaske,ta wani bangaren kuma yafi mata kama da wasa da tsokana,to amma yaushe suka fara haka da khaliphan?,sai taji matuqar kewarshi,tana son ganin fuskarshi mai kyau da kwarjini,hakan ya sanya ta ture litattafanta ta jawo system dinta ta shiga inda ya adana mata hotunanshi ta hau kalla daya bayan daya.

Nishadi yake ji sosai cikin zuciyarshi,saiya sauka daga saman gadonshi ya soma duba abubuwa masu amfani a wajensa ya fara hadasu waje guda,bayan ya hau net ya duba idan zai samu jirgin da zai tashi gobe zuwa nijeria ya sayi ticket.

Yana tsaka da wannan kira ya sake shigo masa,sai yabar abinda yake ya duba kiran,salim ne saboda haka ya tabbatar kiran mai muhimmanci ne
“Ya salim ya ake ciki”
“Am sorry boss,zarginka ya tabbata kan mutumin nan….yana amsar kudaden ne yana safarar miyagun qwayoyi,idan ya samu ribar yake dauka ya dawo maka da kudadenka,yanzu haka a rahoton da na samu sunyi niyyar fitar da wasu qwayoyi an kama yaransu,suna kuma gab da fadin sunayen su waye” idanunshi ya runtse sosai,dama ya jima yana tantamar bawa mutumin bashi,banda anni ta sanya baki tun a wancan lokacin da bazai bada ba,lallai ya zama dole ya samu mutumin
“Good job salim,ku jira zuwa ne gobe,but bana son kowa ya sani”
“Thank you boss,Allah ya kawoka lafiya”
“Amin” ya amsa yana katse wayar,ya cillata gefa yana furzar da iska mai dumi daga bakinsa,lalllai bazaiwa mutumin nan ta sauqi ba duk tsufarshi saiya gane baida wayo,ya bata mishi rai qwarao,amma daya tuna chaptershi da ayeeshanshi sai ya saki murmushi yaci gaba da shirinsa yana imagining haduwarsu gobe.

????????????????

Kwance take saman gadonta,wanda a sannan kusan sha daya da rabi na dare,har a sannan hamid bai dawo ba,ta riga data saba da rashin dawowar tashi wani lokacima sai tsakiyar dare,a da tana damuwa saidai a yanzu sam babu abinda ya shafeta dashi,neman hanyar rabuwarsu kadai ya rage mata donta cimma muradinta.

Cikin shakku da tantama ta soma kiran number khalipha ta farko,nan na’ura ta sanar mata number a kashe take,hakan ya sanya ta tafi kiran daya layin nashi.

Sha daya da rabi da minti biyar wanda yayi dai dai da sha biyu da rabi da minti biyar a cyprus,kwanciyarshi kenan saman gadonshi,kaman bazai daula ba,amma ganin kiran daga nijeria ne ya sanyashi dagawa bayan tayi kamar zata tsinke,jin muryar mace sai ya bashi mamaki,muryar da bai santa ba
“Amincin Allah ya tabbata a gareka”
“Wa’alaikumussalam warahmatullah” ya maida mata da yaren larabci
“Ina fatan kana lafiya kamar yadda nake,duk da ni din sai a hankali tawa lafiyar”
“Amm,idan babu damuwa da Allah zan iya sanin dawa nake magana”
“Kasha kuruminka,ba wata bace illa asma’u,tsohuwar masoyiyarka”
“Asma’u?,asma’u?” Haka ya dinga nanata sunan a ranshi yana son tuna wacce asma’u,asma’un ce ta fado mishi,saidai ita din a yadda ya sani matar aure ce,akanme kuma zatayi kiranshi a irin wannan lokaci?,hasalima bata da numbersa
“Idan baka gane ba bari nayi maka dalla dalla,asma’u dai wadda ka fara cewa kana so tayi kuskure da gangancin hadaka da aysha bayan ita tafi kowa dacewa dakai” gaba daya sai yaji kaman yana magana ne da zararriya,kodai ba cikin hayyacinta take ba?
“Am lafiya kike kuwa?,” yana nufin cikin hankalinta take,amma fuskanci maganarsa ba
“Lafiya nake,amma ba lau ba” zuciyarshi ce ta bashi shawarar sauraro kafin yanke hukunci,saboda haka yace da ita
“Uhmm….me yake faruwa?,ina kika samu numberta?”
“Khalipha kenan….”
“Point of correction…” Yayi saurin katseta
“Yaron oga dai” a shagwabe tace dashi
“Haba don Allah,na baka haquri fa tuni,amma bai wuce a wajenka ba?kuna yanzu ma kira nayi na sake baka wani haqurin don Allah ka yafemin komai ya wuce” Tsaki yaja a bayyane wanda ya isa kunnenta
“Me kika yimin da zaki bani haquri?,idan ma kina tunanin akwai wani laifi da kika yimin ma to babu,nikam khalipha saidai nayi miki godiya ma,domin duk abinda kike zaton kinyi alkhairi ya zamewa rayuwata da ita wadda kikayi nufin cutarta,karki sake kirana daga yau,don ni bana magana da matan mutane” yana kaiwa nan yayi hanzarin kashe wayar zuciyarsa na masa wasi wasin kiran asma’u,yanayin yadda take karya mishi murya dayi masa magana kadai ya isa ya karantar dashi akwai wata a qasa,yasan halin mata da yawa hakanan dai dai gwargwado ya karancesu,shikam saidai ya bawa wani labari,kiranta ne ya dinga shigowa babu adadi har sai daya gaji ya danna mata block,sai kuma ta koma sms wanda sukayita shigowa a jajjere,tsaki ya saki sannan ya kashe wayar gaba daya,bayan ya sake blocking yadda bata da damar sake tura masa wani saqo.

Kuka asma’un ta sako sanda ta fuskanci dukan abinda yay mata,saita zauna sosai saman gado tana sharban kukanta,tana jin cewa ba zata iya haqura ba dole tayi hanzarin fita daga gidan hamid,tana tsaka da haka ne hamid ya turo qofar dakin ya shigo,kallo daya yayi mata ya dauke kanshi bai tanka mata ba,sai daya gama sabgar gabanshi sannan ya dubeta da qyar
“Ke kuma waye ya mutu kika zauna kina yiwa mutane irin wannan kukan da daren nan?” Harara ta watsa masa,cikin izgili da rashin mutunci tace
“Ban sani ba,aikin banza aikin wofi,wallahi hamid ko kafi quda naci saika sakeni,don na gama zaman aure dakai”
“Ki iya bakinki tun bai jawo miki duka ba”
“Ai wallahi nabar zama ka taba lafiyata tunda bakai ka halicceni ba,banza wawa sakaran namiji dabai da aiki sai dukan matarsa” nan fa ya harzuqa,baiyi wata wata ba ya kasheta da mari sannan ya miqe yana huci
“Laifi nane dana sassauta miki kwana biyu kinga kina ci kina qoshi,to bari na sake jaddada miki tunda dama can ke jaka ce wadda ta fita makaranta da C.O,aure yanzu na fara,babu saki tsakaninmu har abada” ya juya yabar dakin,ashar takeson danna masa amma tana son lafiyarta,haka ta hadiye sai daya fice sannna ta dinga zage zagenta tare da cin alwashin gobe sai gida.

Zaune yake cikin office din nashi wanda yana sauka a qasar can ya soma zuwa,duk da yadda ya qagu matuqa yayi tozali da ita amma dole ya soma biyawa can,yantsunshi harde cikin juna,yayin daya dorasu saman table din gabanshi,ya kuma zubawa aljh kutama idanu yayin da alhj kutaman ya hada gumi sharkaf,ilahirin jikinsa rawa yake,tsananin tashin hankalin da yake ciki bazai misaltu ba
“Alhj kutama” khaliphan ya kira sunanshi kai tsaye abinda kusan bai taba yiba,kasancewar sunyi mu’amala da mahaifinshi kamar yaron mahaifinsa ne,amma hakan baisa ya daina bashi girma ba
“Alhj kutama” ya sake kiran sunan nashi
“Na’am yallabai,ranka ya dade Allah ya taimakeka….” Ya fada cikin dimuwa da rudu
“Duk abinda kake da kudina dana samu ta hanyar halas,nake baka saboda taimako darajar iyali da kake dashi kaje ka juya ta hanyar halas,duk sanda ka samu riba ta halas ka dawomin da kudina,nasan me kake dasu,haka mukayi dakai?”
“Wallahi yallabai akasi aka samu,ba halina bane”
“Alhj kutama”
“Na’am yallabai”
“Na bala nan da jibi ka tattara dukkan kudina dana ranta maka ka dawo min dasu,ban kuma yardaba ban lamunce ka kawomin wadanda ka samu ta qazantacciyar harqallarka ba” juya kai ya soma yi zai soma roqo da bashi haquri,cikin hanzari khaliphan ya dakatar dashi
“Banason naji komai daga bakinka,magana ce munyita dakai tsahon minti ashirin,duk cikin maganarka babu gaskiya a ciki,hakanan kuma ban sameka ba sai dana sanya aka yimin bincike a kanka,so ka riqe duk abinda kake da shirin fada kayi abinda nace maka” yasan halin yaron sarai,kaifi daya ne,ya riga daya karya duk wani abu da zai sanya ya tausaya masa ko ya janye hukuncinsa a kanshi,hakan ya sanya dole ya miqe yana jan qafa cikin tashin hankalin inda zai samo masa kudinsa ya fice,don dukka kudin ya tattara aka sayi cocain dasu da zummar idan suka wuce zasu samu riba mai yawa,sai gashi an kama yaran kuma suna shirin fadar sunanshi,tabbas daga shi har hamid suna cikin masifa,don har hamid din shima ya karbi bashin kudade masu yawa daga wajenshi,yace kuma dukansu su dawo masa da kudin,kuma baya jin a yanzu akwai kudin wajen hamid din shima,yace ya zuba kudin a wani kamfani da zasu dinga bashi ribar kudade mai yawa duk qarshen sati.

Waya ya dauka ya kira hamid din,yace kome yake yabarshi ya sameshi a gida,sannan ya wuce gidan shima afujajan cikin motocin da yake yawo dasu kamar wani gwamna,yaga alama talauci ne yakeson yayi masa saukar gaggawa alhalin bai shirya taryarshi ba daga nan har randa zai bar duniya,haka motocin suka dinga tafiya da sauri sauri,wannan burgar tashi da nunawa duniya shi lallai wani ne yasa sunanshi yayi suna yayi tambari,bayan kuma baikai inda yakeson ace yakai din ba,hakanan a wajenshi dukka yaranshi suka gado qarya da fafa.

Numfashi khalipha ya sauke yana sakin ajiyar zuciya gami da lumshe idanunshi,ya kara bayanshi da kujerar da hake kai yana istigfari,sosai ranshi ya baci matuqa,ya jima yana baiwa mutumin rance ga zatonshi yana amsa ne donya tallafi kanshi,duk da ya dade yana mamakin salon rayuwarshi,ya daukaki komai nashi bayan kusan qashin bayan arziqin nasa bashi ne,saidai ganin komai na tafiya dai dai tsakaninsu ya sanya ya kauda kai daga gareshi,daga bayane yadda kudim suke saurin dawo masa gami da gwaggwabar ribar da yake gaya masa yana samu a lokaci kadan kan kasuwancin da yakeyi ne yasa masa ayar tambaya,don duk abinda khaliphan zaiyi yakanyi takatsantsan da kaucewa haramun,saboda annabi S A W yana cewa haram a bayyane take hakama halal,saidai tsakaninsu akwai al’amura masu rikitarwa da shubha,wanda ya kiyaye wannan shubhar haqiqa ya kubutar da addininsa da mutuncinsa.

Bazai lamunci ko ya yarda ya ciyar da duk wanda ya danganceshi da haramun ba,walau kana aiki qarqashinsa ne ko kuma kankat mai gaba daya mahaifiyarsa da ‘yan uwansa,saboda annabi S A W yayi bayani cewa,duk jikin daya ginu da haram,to wuta ita tafi cancanta da ita(wato wuta ita tafi cancanta ta cinye wannan tsokar,jan hankali a nan a garemu mata shine,muyi qoqari mu dinga tunasar da mazanmu koda yaushe su nemo halal su kawo mana halal,musamman yanzu da babu tayi yawa,albarka ta ragu cikin dukiyoyi da kayayyakinmu,don billhil azim maganar ma’aiki ba zata tashi a banza ba,duk wanda bai kiyaye haramun ba,ya yadda ake ci dashi a tufatar dashi asha dashi da haramun,to babu shakka ranar qiyama ya lissafa kansa cikin wanda wuta zata ci,saboda haka mu yiwa kanmu ‘ya’yanmu da mazajenmu gata mu dorasu kan neman halali domin samun dace da tsira ranar da wata rai ba zata tsinanawa wata rai komai ba,matan sahabbai sun kasance kullum ta Allah idan mazanau zasu fita nema,sukan tsaidasu auce,yakai wane kaji tsoron Allah,ka nemo mana halak,don zamu iya haquri da yunwa amma ba zamu iya haquri da azabar Allah ba,Allah yasa mu dace)mutane da yawa sun shaida sirrin yauqaqar arziqinsa da albarkarsa shine kiyaye haqqin Allah da yakeyi a ciki,sannan kuma biyayya ga mahaifa.

Saida ya shiga toilet ya daura alwala sannan yaji zuciyarshi na sanyaya(ki riqe wannan ‘yar uwa,a duk sanda kike jin bacin rai,ko wani abu ya bata miki rai,walau tsakaninki da mijinki ko wani daban,kije ki dauro alwala sannan kiyita karanta a’uzubillahi minash shaidanir rajim,da yardar Allah zakiji zuciyarki tana, sanyi)shauqin isa zuwa gida ya dawo mishi fil,sai ya zauna kan kujerar sofa din dake office din ya tura gajeran saqo,cikin ‘yan mintina mutum biyu suka shigo,daya ya soma rufe mishi jakarshi,yayin da dayan ke tsaye saman kanshi,duqawa yayi.ya maida safarshi sannan ya saka takalminshi ya miqe yayi gaba suka rufa mishi baya suka fice da kamfanin gaba daya.

*_ZAFAFA BIYAR NA KUDI NE,IDAN KIN GANI DON GIRMAN ALLAH KARKI SHARING,LITATTAFAN SUNE KAMAR HAKA_*

*DAURIN BOYE*
_HUGUMA_

*WUTSIYAR RAQUMI*
_BILLYN ABDUL_

*BURI DAYA*
_MAMUHGHEE_

*SAUYIN QADDARA*
_HAFSAT RANO_

*KAIMIN HALACCI*
_MISS XOXO_

*GA WANDA KEDA BUQATAR SAYENSU SAI YA TUNTUBI WANNAN NUMBER*
08030811300

*ko kuma*
07067124863

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button