Hariji Book 2 Hausa NovelHausa Novels

Hariji Book 2 Page 47-48

Sponsored Links

47&48
*Alheri writers asso.*

Watsewa duk dangin ummi sukayi,yayi saura ita kaɗai sai hajjo,da ta janyeta Zuwa part ɗinta,a ƙoƙarinta nason ta gamsar da ita ,cewar duk wannan tsiyan da sukayi,sun yishine na gyaran zama,don sun lura,kishiyoyinta akwai su da damuwa,sosai ta gyarata cikin wani yadi ,samfarin kalar na en indiya ,mai haɗe da tafkeken mayafi ,da ta naɗe jikinta a ciki kamar lafaya.
Duk abun nan ummi da ido take binsu,amma ita sunma kasa gane ciwonta,ace kamarta itace ƙanwarsu,and tayi aure ta barsu a gidan ,dama ace rashin mazane ,amma ba haka bane tsabagen kwaɗayine da huɗubar shaiɗan,wannan lamari nasu in ta tuna yina haddasa mata damuwa ,ya za’ayi a cikin gidan in suka waiga suka ga sai isu ya su,ba me kwa6a masu? Dukda dama ko da take cikinsu nata nasiha ne,matsayinta na qanwarsu,uwace allah ya basu amma son kuɗi ya rinjayi zuciyarta ga iya gane banbancin halas da ɓacuwar tarbiyyar yaranta…Allah see my family through🤲😭 ta ɗaga hannu tana addu’a cikin zubar ƙwalla

sosai hankalin uwale ya tashi ganin ƴar ƙanwarsu na sharar da hawaye,wanda shigowarta kenan tazo tayi wa ummi sallama kuma ta kira hajjo tunda jirgnsu zai tashi

Related Articles

Damuwane ya shigeta sosai,a ranta ta soma raya cewa “Anya zan bar ummieta a wannan gidan ? To waima shi quliyar bayida dangine sai mata da bamuga kowa a danginsa ba? koda shi aminin sarkin kano ne ko? kuma famous person ,in bacin haka da wallahi ba abunda zai hana in dauketa mu koma,saidai yace abiyasa kudinsa mu kuma munci halas!”

“Anty uwale zo in rungumeki ko zan samu saukin zogin da nikeji a raina,wallahi anty uwale inajin tsoron matan gidan nan,amma …” sai kuma taja bakinta ta tsuke

ƙarasowa wajenta uwale tayi da sauri ta ɗaura kanta akan cinyarta,tana ɗan shafa mata kai ,tana ɗan girgiza mata kafaɗa ta sigar rarrashi
“Amma mene?” ta tambayeta da dukkan kulawa

Rawa bakin ummi ya somayi kafin tace”Anty kune kaɗai gatana,dangina ,fukafukaina,in baku bazan taɓa kai labari ba,plx ina roƙonku don allah ,ku fitar da mazaje cikin manemanku kuyi aure,indai har kunason raina ya natsu in zauna a gidan aurena , in fuskanci ƙalubalen cikinta na roƙeku”

Ta fada tana qarashe kalmominta cikin kuka mai haɗe da shasheƙa,,,wanda ke taɓa zuciyar masoya da ƴan uwa masu jin ɗan uwansu a jiki

Sosai jikin hajjo yayi sanyi A hankali takejin rashin kyautawar abunda sukeyi a ranta,to amma ya zasuyi ,meye zatace ya jawo masu ?kasancewarsu mabuqata , *harijai* ko kuwa kasancewar rashi da fafutukar buqatar rayuwa?

gyaran murya tayi sannan ,kamar hadin baki ,suka soma magana suna bata haquri ,da yi mata alƙawarin tsaida mazaje ,matsawar za tayi farinciki da hakan.
Murmushin jin daɗi tayi,kuma at d same time ,wasu siraren hawaye na silalo mata “Nagode yayuna,zan cigaba da tayaku da addu’a daga nan,kuma kuna yimun addu’a allah ya kaɗe fitina a rayuwar aure na da ƴan uwan zamana”
ca6e baki uwale tayi,wai en uwan zama? sai dai tayi shiru ,saboda kar hankalnta ya daɗa tashi,amma ita sheda ce,akan cewa har gaban abadan ,kishiya bata taɓa riƙar kishiya a matsayin ƴar uwar zama.

***

ƙuliya hankalinsa bai kwanta ba sai da ya tabbatar dangin amaryarsa ,sun bar abuja kuma sun sauka kano lafiya,,saidai abu ɗayane ya basa mamaki yanda matansa suka haɗe kai ,yayi kiransu ɗakinsa amma ba wanda yazo ,Amma ya alaqanta hakan ta 6angaren uwar gidansa.

**
*9:00pm*

Quliya wanka yayi sosai ya ɗakko wata tissue yadi mai ruwan milk ,da ya ɓoye tsufansa ,ya fito da kyawunsa ,kasantuwarsa na real balarabe ba algus.

wayarsa ya ɗauka yayi ta kiran matansa ,saidai ba wanda ya ɗauka,wanda ya alaƙanta hakan da kishi,sosai yikejin kansa cikin tsananin farin ciki wanda rabon da ya tsinci kansa a wannan yanayin tun sophy tanada lafiyarta kafin tayi hauka…

A Take tsikar jikinsa ta tashi yarrrr ! Wani baqin cikine ya maye gurbin farincikinsa ,da sauri ya miqe ya fiddo wipes yina tsantsane zufar fuskarsa
“Ya ilahy,yaushe zan saba da wannan yanayi naki sofy na,when?”
Kiran wayarsa ya dawo dashi ,dai dain sa.
A hankula ya sauke ,idonsa da suka shanye saboda amfani da medicated glass ,akan screen din wayar
ɗan murmushi ya saki da ya ƙara ƙawata fuskarsa,tun kafin ya ɗauki wayar yaji ya nema damuwarsa ya rasa
“My son!” ya furta a hankula da kawai zaka iya ganewa a saman la66an sa da ya motsa.

“Assalamu Alaik,son ka huce?” .
“Dad ya amaryan ka?”
murmushi yayi na saman le6e,wanda ya sashi jin farinciki ko banza ,ya damu da damuwata,ya raya a ransa
“Son amaryata,tafi jin lafiyar dad ɗinka?”
Murmushi yayi ,gamida sosa ƙeya,kamar yina ganinsa a gabansa
“No dad,kawai dai auren naka yina ,raina ne,amma plz ka kula da ita sosai dady,if possible duk inda zaka kuje tare,saboda kar en gidan nan su nema cutar da ita”
“Son ance maka wani abu ya faru ne?”
ya tambayesa cikeda mamaki,saboda if zai canka,adnan bai taɓa kawo ƙorafin gidan a wajen ƙuliya ba,amma why wannan maganan?

katse masa tunani yayi da cewa”Dad kar fa ka kawo komai a ranka,na tafi can amma raina na wajen dady na ,feels so worried ,ina nan dawowa a satin nan”

sun cigaba da hira mai ɗan tsawo kafin ,ya katse kiran ,ya zauna turus ,yina saƙa da warwara a ransa ,shin inyi ko in janye?

**
Da sallama ƙuliya ya shiga ɗakinta,hannunsa ɗauke da wani tray na alfarma ,an ɗaura wasu madaidaitan farantai da bowl,sai glass cups biyu a kwance da wuƙa,cokali da fork .
su kuma a farantan ,ɗaya gasashen kaza ne ,sukutum ɗinta ,anyi gashin inji,an kwashe kayan ciki,an replacing da carot,cabbage da green pepper,sai ta wajen an shafeshi da garin yaji da magi,sai ketchup da salad cream,ɗayar bowl ɗin mix fruit mai madara da zuma,sai kwalin hollandia
Tun da taga shigowarsa ,gabanta ya yanke ,gamida bada sautin dam!
amma duk da hakan bai hanata jin nauyin ganin babbar mutum kamar sa yina kiciniya da tray ɗin kayan abinci
batasan sanda ta miƙe taje gabansa ba
saidai ta kasa cewa komai idonta na a ƙasa ,ta miƙa masa hannu alamar ya bata ta taimaka masa

Murmushin jin daɗi yayi,sosai ya sake jinta a ransa
“Amaryata,sha kuruminki yau ranar kine ,bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida” yayi mata magana cikeda zaulaya,sannan ya je ya aza akan center carpet ɗin dake gaban gadon nata

cak ta tsaya a inda take ta kasa motsawa ,itadai nauyinsa take ji…

“To qaraso mana ,ki zauna a gadon mulkinki” hmm abun ,zan kunya ,tsofai tsofai dashi bai kamata yina mata wannan kalaman ba
Batayi masa gardama ba,saidai akan carpet ɗin ƙasan ta zauna a maimakon ,kan gadon ,sannan ta ɓige da gaishesa

Umurni ya bata da taje tayi alwala suyi sallah ,nagodewa allah da ya nuna masu wannan ranar

ɗauke wuta tayi gamida shafa pant ɗinta dake ɗaukeda pad a hankula

“wayyo kunya,zanyi sallah ba tsarki ne,ko kuwa zan ce masa am up ne?”.

jin shiru yasa ya kira sunanta ,”Ummul kulsum,kinaji na?”

Inda inda ta fara yi,”Au ,uhm ,eh ”

“ok to shiga ciki ,kiyi alwalan ko bakisan toilet din bane?”

“Ah ,amma…” sai kuma tayi shiru ,tana jinjina abun a ranta

ɗan tunani yayi kaɗan ,kafin nan,ya zarce da zolayenta ,ta hanyar cike mata maganar da bata ƙarasa ba
“…Amma ina Al’ada,ko ba haka ki ke son fadi ba?”
shiru tayi ,tana ɗan murmushi,ta gyaɗa masa kai,batareda tace komai ba

sosai ta yabawa simplicity ɗinsa,ga barkwanci

“A’ah cire wannan mayafin fuskar taki ki hauro nan ,muyi hira,in san me kikeso ,nima kisan me nike so” ya fada yina nuna mata gefensa a kan gadon

Girguza masa kai tayi,sannan tayi kwa6a kwa6a kamar za tayi kuka

“A’ah bana son gardama,indai kinason in jaki,jikina to ko mai nace banson jayayya”

dole taje inda yace ta zauna,sannan ta sassauta mayafin fuskarta
“Yawwa ko kefa”
A nutse ya matsa kusa da ita ,ya tallabo ginshikin qugunta,da nufin ya manno ta da jikinsa

Ai kamar an manna mata wuta haka taji ,aikuwa ta zabura ,gamida fashewa da kuka
“wallahi da gaske ina period ka yi haquri”

sosai ta basa dariya
“ummu na wauta,ai ban qarya taki ba,kawai ina sone in jiki a jikina muyi fira,kuma inyi feeding dinki,sabida nasan kacaniyar jama’a bai barki kin ci komai ba …amma kin san wancan abunnnn?😉 ”

Cuno baki tayi “wani abu?”
“Abun nan da akeyi in an tare”
girgiza kai tayi cikin shonin “ban gane abun ba dady”
“hhh banda zolaya dai,amma tunda baki gane ba matso in nuna maki yanda abun yike. ”
ai da sauri bakinta ya dauki 6ari
“wallahi nagane”
dariya ya saki ,yanda yaga tayi maganar
“alryt alryt,to nayi maki alqawarin baza muyi ba har sai sanda ke kanki kika shirya agaza na da abun,but amma nima kiyi mun alqawarin sakin jiki dani da tararaya na gamida bani duk kular da ta dace”
“Indai wannan ne na yarda,nagode ”
Tafada cikin zumudi ,har tana en surutai qasa qasa

Jinjina kai yayi sannan suka sauka qasa ya fara feeding dinta,taso tayi masa gardaman ta qoshi,don dai bazata yarda yabata abinci a baki ba,saidai hade rai yayi “yanzu fa kika yimun alqawari”
dole ta bude baki yina bata har saida ta fara yamutsa fuska sannan ya daura masa da hollandia
shikuma ya dauki qaramar spoon ya soma cin mixed fruit din da ya zamar masa al’ada cinsa duk dare.

“Kin ganni ina feeding kaina da kaina,meye amfanin matana,allah sarki gwanin tausayi,inda nine amaryata naga angona a haka amsa zanyi in basa,kuma in ta yi masa tausa in ya gama har yayi barci”

ware dukkan idonta tayi waje kafin tace “hm wallahi karma kace alqawari don kunya nikeji ”

***
Bayan kwana uku

Da rana suna zaune shi yina kan kujeran falonta ,ita kuma tana qasan carfet tana matsa masa yatsun qafarsa da suka ɗan tasa ,sakamakon bp ɗinsa da ya ɗan motsa ,saboda faɗan da sukayi matan gidan ,wanda duk akan yanda ya tare a sasan tane ,itakuma dama duk ta gama tsorata dasu,don haka ta kulle sasansa bugun duniya ,taƙi buɗewa ,shine yaje yayi masu kaca kaca ,ya dawo yina ta haki,saboda fushin da yayi ,shine bp ɗinsa yayi rising ,itakuwa hakan da ya faru shi ya ƙara mata ƙaimi da Azama ,akan taga ta jajirce ta sashi farin ciki,kafin ta fara tunanin hanyar dazata gyara matsalar cikin gidanta da kishiyoyinta.
Adnan ne ya kirasa a waya
“Dad ,Anty yau ciwonta ya motsa ,saidai tanata kiranka all the time,plz dad in zai yuwu kazo …”

“Ta fara magana?”
“eh dad”
“zanzo yau”
“Ah ah ,ka bari sai gobe,zan kula da ita”
“Zan zo nace yau!”
yina faɗan hakan ya kashe wayar yina ƙoƙarin zame ƙafarsa a hannunta
saidai da sauri ta matse ƙafarsa
“Dady cool down first,kana da hawan jini and duk abunda aka fada maka,to ba me daɗi bane,kar ka tashi jiri ya ɗebeka ” sannan a hankali ta miqe takai hannunta kan goshinsa ,zafi zau
da sauri ta watsa yatsunta a gefe dagefen goshinsa ta soma matsawa gamida yi masa addu’ah

kamota yayi sosai ya rungumeta a jikinsa ,jikinsa har rawa yikeyi ,sannan ya lumshe ido yina furzo numfashi a galabaice ,dole yasa ta natsu gamida lafewa a jikinsa ,don ta lura yina cikin zafin zazzaɓi ne

hannunsa ya cusa ta cikin rigarta ,ya ajiye akan fatar cikinta …
49&50

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button