Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 13

Sponsored Links

13….

_This novel is for sale karki karanta in baki biyaba_

_in kinason novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card ta watsapp number na sainai adding dinki a group din danake posting_

Related Articles

 

 

Agaban wani babban gida yasa akai parking, gidan babban gaske ne dan yay girman wani anguwan, fitowa yayi daga mota yabama mai taxi kudi, masu gadin gidan dake sanye da kayan security ne suna ganinshi suka washe baki. “laaaa jikokin Alhaji ne, barka da zuwa oga” murmushi yamusu ya gyadamusu kai dan baijin yin magana suka budemai gate ya shiga, babban gidane dakeda fadi sosai gawani hadadden water treatment plant a tsakiyan compound din dayay kaman round about ta gefe kuma wajejen parking cars ne inda cars sunfi kala goma apake awurin, gawasu irin hadaddun design din flower dayabi ko ina na tsakar gidan babu kowa atsakar gidan kasancewa babu kananun yara a gidan inbadai jikoki sun zo kokuma anyi hutun school shine zakaga yara cike a gidan, da saurin shi yakarasa shiga ciki yay shashin kakanshi bude kofan part dinshi yayi babban falone dayasha hadaddun manyan kujeru sai carpet mai bala’in kyau da taushi dake shimfide akasa, wani tsohone azaune yasha manyan kaya dadan rawani akanshi idanunshi sanye da glasses nakara karfin ido, yana zaune akan wata lumstatsiyan kujera hanunshi rike da jarida yana dubawa gefen kujeran dayake zaune kuma yar sanda ce ajingine awajen wanda daga gani kasa ita ke taimakamai ya tsaya yay tafiya, manyan mazane guda uku a falon zaune akasa wanda suke yaranshi Uncle Suleman, Uncle Muhammad, sai last namijin shi Uncle Mustapha, sai mace guda daya wacce take yayar Mami tana sanye da hadadun kayan kamansu daya da Mami mai suna Asma’u, sunfi kiranta da Big Mum, itama tana zaune a falon suna hira suna shan slice fruits dake wadace agaban su, ahankali yay sallama ya shiga falon yana dan sosa keya dan yasan shima laifine, dukansu dagokai sukayi suna kallonshi cikeda mamaki Uncle Suleman wanda yake babban yayan su yace “kaga daman zuwa yanzu Hussain aika kyauta” kaman zaiyi kuka yakaraso cikin dakin yace “sorry Uncle” cikeda masifa Uncle Muhammad yace “bazaai sorry ba, shine baka fada ka shigo hanya ba kadauko taxi daga Airport kataho wat if something happen akai kidnapping dinka ahanya eh?” sake dan turo baki yayi yana kallon Baffan daya janye jaridan daga fuskarshi yana kallonshi yanamai wani irin calm love look irin na kakanni da jikoki, a sanyaye yay murmushi yanadan sosa keya ya ware hanunshi yatafi wajen tsohon. “oyoyo Grandfather oyoyo Oldman dina” karasawa yayi zai rungumeshi tsohon yadau sandar gefenshi yana nunashi dashi cikeda masifa yace “ka zonan kaga yanda zan kwaleka da sandar nan” da sauri yakoma baya ya zauna kusa da Anty Asma’u dasuke kira da big Mum kaman zaiyi kuka yace “Big Mum kinga grandfather zai bugamin wanchan ugly sandan nashi ko” dariya duka yaran sukayi tsohon yanunamai sandar cikin jin haushinshi yace “kana Nigeria kusan sati biyu saiyau zakazo dan baka da mutunci bakasam mahimmmancin yan uwanka bako, kullum da tunanin ku nake kwana nake tashi aika kyau” kallon Uncles dinshi yayi dake kallonshi cike da so yace “Uncles am sorry kunji, Big Mum am sorry wani assignment fa nazo yi dama nace saina gama zanzo, kema kinsan bazan iya zuwa Nigeria banzo wajenki ba, please Uncles kucema grandfather am sorry” duk dariya sukayi gabadayan su, Big Mum ta shafa kanshi tana kallon mahaifin nata tace “amai afuwa Baba bazai karaba” baban yayansu Suleman yace “Baba amai afuwa ai gashinan yazo, muma madan huta da maganan yan biyun ka dakake ta mana” kallonshi tsohon yayi yanajin wani irin sonshi aranshi tun yana saurayi yaso yan biyu yakeson yan biyu amma Allah baitaba bashi ba sai akan jikokin shi akuma kansu saisa yake mugun sonsu, ahankali yamai alamu da hannu. “yaka” da sauri yatashi yaje yana murmushi rungumeshi yayi ahankali yana dariya yace “My old grandfather kajika fadafa duk randa kabugamin sandar nan ai shikenan sai mutuwa” da sauri yadan zaro mai ido yace “kul denamini maganan mutuwa, sainaga yaranka, naga yaran Hassan dinka ma in sha Allah” dariya duka yan dakin sukayi, murmushi shima tsohon yayi ya nunamai gefenshi yace “zauna anan” ya kalli Asma’u yace “Asama akira masu aiki su kawomai abinci, kice suzo sufarajin meyake so tukunna abinda yakeso shi za’a dafa” da sauri tace “to Baba bari na turosu” tashi tayi tafita, ya kalli Suleman babban danshi yace “Sulemanu akiramin duka jikokina duk suzo gida ayi liyafa na kwana uku tunda Hassan da iyayensu gobe zasu shigo suma” murmushi duk sukayi sukace to Baba, yasake kallon Aabid din dake kallonshi kaman zai cinyeshi dan dudda tsufanshi badai kyauba yace “kaikuma tunanin me kake” shafa kanshi yayi ya kwanta akan kujeran yadaura kanshi kan cinyar Baffan yace “nothing old man” gashin kanshi ya shafa yace “wanan karan bazaka bar garin nanba saida mata namaka alkwari kodai kafito da ita kokuma na nema maka dakaina” sosai gabanshi yaji yawani irin fadi hakan yasa yadan lumshe ido yakai hanunshi yadaura kan kirjin yana ganin Hamida a idanunshi. Hanunshi Baffa daya gani akan kirji yakama yana kallon yar karaman yatsarshi yanda yabar kunba a yatsar yace “kumban nan fa Hussaini zama cikin yaran yahudawa ne yasa zaka fara abu kaman su” dan murmushi yayi yace “ina jirane fa jumma’a nayi na yanke ta” daga kanshi yayi daga kan cinyarshi dan ya tsani ganin mutum da doguwan kumba yace “tashi ka daukomin kayan yanke kumba adakina kazo nan na yanke maka ita” tashi yayi yana dariya dan grandfather is just d best ne, he’s so caring akansu, ga masifa, ga kirki ga korafi ga naci shidai Baffa babu abinda bai hadaba. Dakinshi ya shiga da komi yake a gyare dakin sai kamshi yake yadauko abin yanke kumban yafito yadawo kusa dashi a shagwabe ya zauna kaman wani yaro yabashi yace “please Grandfather karka ciremin kaji” hararanshi yayi yakama hanunshi yana gyara glasses din idanunshi yashiga yanke mai kumban tass har sauran da basukai wanan fitowa ba saida ya yanke, daidai lokacin masu aiki sun shigo dakin sanye da uniform cikeda girmamawa suka gaishe shi suka tambayi mezasu dafamai ahankali yace “just something light” dan bama yunwa yakeji ba yasan idan yace yakoshi ne bala’i zasuyi da Baffa dan dole saiya sashi aci wani abu zaima iya yabashi da kanshi.
Haka ranan yawuni da grandfather banda masallaci babu inda yabari yafita yaje dudda yaso yabi bigmum yaje gidanta hanawa grandfather yayi, koda daddare kin bari yaje part dinshi yayi yace anan part dinshi zai kwana wani hadadden daki dake kusa da nashi ya shiga yana kumbure kumbure hakanan yay bacci awurin.

 

Biyar saura daidai yafito daga dakinshi yana bugan kamshi yasa kananun kaya, Baffa yasamu zaune akan dadduma a falon yana jan charba, komawa daki yayi yadauko daya daga cikin tulin keys din motar Baffa yafito yadawo falon yazo inda yake yace “am going Oldman” shafa addu’a yayi ya kalleshi yace “kaje da driver karka tafi har airport da asuban nan kai kadai, bari ma tsaya nakira Sulemanu da Muhammad subika” kwankwaso yarike yace “waini yarone Baffa, ni gaskiya bawanda zaka kira, airport dinne ban saniba ko banda karfin kare kainane” yanda yake maganan cikin jin haushi yasa Baffa cikeda lallashi yace “a’a maida wukar, idan wani abu yasaman min ku mutuwa fa zanyi, naji kaje to amma kai tuki ahankali kaji, kadanje da driban kaji yaron kirki” to yace yafita daga dakin da sauri dan he’s so eager yaga dan uwanshi, wajen motoci yayi yashiga motar yay warming sanan yay horn aka budemai gate yaja motar yafita daga gidan, minti kusan 20 ya dauke shi yakai airport din ya tsaya agaban arrivals yana jiran yaga fitowa su yana duba wristwatch din hanunshi no rolex.
Kaman daga sama yahango Mami cikin shiga ta alfarma tasa doguwan riga irinta larabawa tana rike da handbag sai Abie dake rike da hanun Aadil dake tafiya ahankali idanunshi sunyi jajir sun kumbura alamun yaci kuka yakoshi acikin jirgi gefensu kuma wani mutumi ne dake tayasu tura laugage dinsu a cart da sauri ya juya ya boye dan bayaso su ganshi, bayan motoci yadinga bi harya kai karshe sanan yaje ya kutsa ta cikin mutane ya zagayo ta bayansu suna cikin tafiya yazo ta daidai saitin Aadil dake tsakiyan su yasa hanunshi yarufema Aadil ido tabaya, ihu Aadil yayi yana turo baki dan dama acike yake daga Mami har Abie da sauri suka juya suka wanda yarufema dansu ido, ganin Aabid ne yasa duk sukayi murmushi duk sukai shiru. Cikeda masifa dakuma shagwaba Aadil yay ihu yana buga kafa akasa yace “open my eyes, leave me eyes alone” yay maganan ya daura hanunshi akan hanun Aabid din yanaja ihu yasakeyi yace “Mami My eyes” da karfi ya fizge hanun ya juyo cikeda fushi dan yaga waye ya kullemai ido Aabid yay wani irin ihu cike da tsantsan murna ya rungumeshi yace “oyoyo you this fight fight yaro” cikin wani irin murna Aadil yasakeshi yana murmushi dake lobar da two sided dimple dinshi yana ware manyan fine lulu eyes dinshi yace “Bid” wani irin tsalle yayi kaman yaro karami kanshi na rawa sosai yanajan riganshi yace “Bid, Bid, Bid, Aa…Bid” shima tsalle Aabid din yayi cikin tsananin farin ciki da mugun son dan uwanshi yanajan white long sleeve high neck Givenchy shirt da Mami tabashi yasa sabida sanyin jirgi yace “yes..yes, my one and only twin Bro, rascal, yes is me, hug me” cikin wani irin bala’in murna da rabon shi da irin murna haka tun Aabid nanan yawani irin fada jikinshi ya kankameshi sosai yana gogamai fuskanshi awuya yana murmushi sosai yana tsalle da kafa, rungumeshi back Aabid yayi yana shafamai baya Mami data gaji da tsayuwa ta ballamai harara tace “tunda bakuda ranan gama oyoyo oyoyon Abie mutafi mudai sa samemu a parking lot” da sauri Aabid yasakeshi yana dariya handkerchief dinshi yaciro daga aljihu yakai fuskarshi yana sharemai fuska da wuya yace “su Mami are jealous banyi hugging dinsu ba saikai My Dil” washemai baki Aadil yayi yana kallonshi, gama gogemai yayi shima ya goge wuyan nashi sanan yarike mai hannu yace “let’s go kaga grandfather, kagaji ko” gyadamai kai yayi batare dayay magana ba dan sosai yaji yawani irin gaji gabanshi sai faduwa yake, hanunshi yakama sukai wajen Mami da Abie dake hiransu saida yafara bude motar yakai Aadil gaba ya zaunar dashi sanan yadawo ya saka akwatinan su a bot yarufe yadawo gaba ya shiga yana waigen su Mami da Abie yace “welcome Abie and Mami hope you all had a smooth flight” yakarshe maganan yana kallon Aadil dayay shiru yanata kallon waje, kunna motar yayi yaja saida suka fara tsayawa a wani masallaci sukai sallan asuba sanan suka dawo motar sukaja sai gida, horn yayi aka bude gate din yaja motar ciki gidan su, Yayin Mami ne da bigMum Dakuma Baffa dayafito daga daki rike da sandarshi kashe motar yayi Mami tafita da sauri ta karasa ta rungume yar uwarta Abie ma fita yayi, juyo dakai Aadil yayi ya kalli Aabid yana daddure fuska yace “who are all this people?” dan shiru Aabid yayi yana kallonshi dan wani zubin idan Aadil yay magana kaman wani Boss wani zubin kuma kaga kaman yaro dan shekara 3, ahankali ganin rigima yakeji kaman bashi yagama murna dazuba yace “gidan su Mami da Abie ne anan suka girma, and ko last year big eid ba anan mukayi ba kaman tane?” yatsine fuska yayi yace “take me back to our house I don’t like here” hanunshi yakamo da sauri yace “iskancin naka yatashi ne rascal? Okay let’s do this look” dan juyo dakai yayi ya kalli Aabid din idanunshi suncika da hawaye sosai suna shirin xubowa, ahankali Aabid yace “how about we just stay here sabida we want to be good children muma su Mami biyayya but kullum kullum am gonna be taking you out kana ganin cool places muna zuwa yawonmu how did you see d idea? Idea yamaka?” shiru yayi kafin ya daura hanunshi akanshi yana yatsine fuska, da sauri Aabid ya matso yataba kan nashi yace “menene ciwo yakema?” gyadamai kai yayi hawaye na xubowa da sauri yace “sorry sorry, tashi muje kaga Baffa sai muje daki kayi wanka kai bacci” fitowa yayi yazagayo ta side dinshi ya budemai kofa, fitowa yayi ahankali yana kallon Baffan su dayagani yana dogara sanda yana karasowa inda suke shima kakan nasu wani irin kallon Aadil din yake wani abu ya tsayamai awuya yaro har yaro amma ba lafiyan kwakwalwa, da sauri Aabid yaja hanunshi kafin kakan nasu yakaraso yace “Dil zokaga old man mai gilas” dariya kakan nasu yayi yadaga sandarshi zai bugama Aabid cike da wasa yadan matsa gefe yana dariyan isgilanci, ahankali ya daga hanunshi yana wani irin kallon Aadil dake kallonshi yana kokarin tunashi ya shafa kumatun shi har zuwa sajenshi yace “Hassan barka da zuwa, menene idanunka sukai ja haka kagaji ko?” gyadamai kai yayi ahankali, murmushi Baffa yayi yace “muje kahuta” ahankali yake tafiya Aabid a gefenshi sukai babban falo inda har ancika ko’ina da abinci, kin gaida kowa Aadil saima kuka daya saki shizai koma gidansu sai lallabashi ake yakiyin shiru, Baffa yacema Aabid yawuce yakaishi dakinsu yay wanka abiyosu da abincin.
_🌹IN BANI 🌹_

_This novel is for sale karki karanta in baki biyaba_

_in kinaso novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_
_you can also send MTN card ta watsapp number na sainai adding dinki a group din danake posting_

 

_Maman Abd Shakur_

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button