Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 2

Sponsored Links

2….

Duka jikinta rawa yafara da sauri ta kalli jakan, kasa taba jakan tayi har wayan ya karasa ringing ya katse, yafara ringing akaro nabiyu, sosai hanunta ke rawa da sauri tajawo jakan tabude taciro wayar tata kirar Samsung A50, Anty Lami data gani a screen yasa kirjinta ya buga da sauri ta dau wayar ta kara a kunenta kafin ma tai magana Anty Lami tace “ina kike Hamida? Nace ina kike?” ta daka mata tsawa, sosai hanunta ke rawa, kirjinta na bugawa dan bamatasan mezatace ba, kasa magana tayi but tana iyajin Maman su nacewa “tamiki shiru halan ko? Ban wayan kigani Anty” karban wayan Mama tayi ta kara a kunenta cike da fushi da takaicinta tace “wlh Hamida inba kinaso ki gamu da fushina da kin dade bakiga irinshi ba ki kamo hanya kidawo gidan nan right this second, dan iskanci ana bikin yar uwan ki kin kama hanya kin gudu, kidawo gida yanzun nan kinajina Hamida?” gyada kai tayi bakinta na rawa sosai tace “t…to Mama” katse wayar sukayi hakan yasa tabi wayan da kallo gabaki daya hankalin ta yatashi cewa da akayi tadawo gida, jakar ta jawo ta saka wayan ciki kafin ahankali ta mike tsaye, doguwar mace ce kyaykyawan gaske, fara ce fat kana ganinta kaga Maman su kaman su harya baci da Mama, tana sanye da fararen eyeglass idanunta ba kawalli saidai eyeliner dataja a saman ido dayama idanun wani irin cool kyau, giranta acike da gashi, gashin bakin kirin, sai dogon hancinta da dan karamin bakinta daya bushe, black hijabi ne jikinta wanda hulanshi ya rufe goshinta sosai dan saura kadan ma yarufe giranta amma dudda haka kana hango kwantaccen gashi a forehead dinta, dogon hijabi ne ajikinta dahar kafafunta ya rufe bama ka hango asalin kayan datasaka, da sauri tadau handbag dinta ta rataya tafara tafiya a natse kaman batason taka kasa ahaka ma wai sauri take tafito wajen da sauri Baba mai gadi ya rage karan radio dayake ji ya juyo ya kalleta yace “har zaki tafi Hamida?” gyadamai kai tayi batare data kalleshi ba tana kakkare fuskarta da hijabi kaman wacce tai laifi tana kara sauri, murmushi yayi yace “shikenan sai gobe tunda baza amin magana ba, gobe ma zaki kawomin tuwon ne Hamida?” gyadamai kai tasake yi still batare datamai magana ba tafice daga wurin da saurin ta, murmushi Baba mai gadi yayi yakomar da kanshi ya daura akan filo yana murmushi ahankali yace “Hamida kenan” yasake yin wani murmushin ya kara karan radio shi yacigaba dasauraran shirin da ake.

Da sauri take tafiya akan titi tana kakkare fuskanta da hijabi, keke napep ta tsayar ta shiga ciki da sauri tana kallon gefe daya batare data kalli mai keken ba tace “j…jan bulo zani” “naira dari uku ne kudin ki hajiya” gyadamai mai kai tayi tana kara rufe fuskarta da hijabi tace “to” tada keken yayi suka fara tafiya har zuwa jan bulo sosai gabanta yafadi dan sosai anguwan su yacika da manya manyan motoci, da mutane ga maza ko’ina, jitayi hankalinta yatashi tunanin ta shine yanda zata wuce mutanen ta shiga gidansu, ahankali tace “yayi nan” tsayawa mai keken yayi ta zage jakanta taciro dari ukun ta bashi sanan tafito tana kare fuskarta da hijabin ta saukar da kanta kasa tafara tafiya ahankali batare data bari sun hada ido da kowaba kirjinta kaman zai fashe zuciyata kaman zai fito waje, a kofar gidansu ta tsaya chak ta leka ciki uban mutanen data gani ciki yasa ta koma gefe jikinta na rawa duk ta birkice, wata yarinya ce kyakyawa da bazata wuce 10yrs ba tafito sanye da doguwan rigan ankon dayamata kyau sosai, ware manyan idanunta tayi ta kalli Hamidan dabama ta lura da itaba sai kakkare fuskarta takeyi tana sake mammanewa ajikin gate dinsu kaman wacce tai laifi ake shirin kamawa akaita ciki, cikin daga murya tace “laaaa Anty Hamida yaushe kika dawo? Ina kikaje anata nemanki? Kinga anma kusa kai Anty Ayush” dan janye hijabinta tayi back jin muryan kanwarta ta kalli kanwar tata dake kallonta, da idanunta dasuka cika da hawaye cikin rawan murya tace “I..Ihsan jeki fadama Mama nadawo ni bazan iya shigowa ba mutane sunyi yawa” juyawa Ihsan din tayi ta leka compound din saikuma ta dawo wurinta tace “wlh Anty Hamida babu wasu mutane fa, su kawayen Mama ne dana Kaka, saikuma su maman Rabi makotan mu, zomuje ki shirya kisaka ankon ki” tai maganan tana kamo hanunta, sake komawa baya tayi tana zaro mata idanu kaman zatai kuka da yar karaman cool voice dinta tace “Ihsan stop dan Allah kunyan shiga nake” daidai lokacin wata budurwa da bazata wuce sa’an Hamidan ba tazo zata wuce ta shiga gidan dan daga gidan Pharty su na kawayen amarya take taci gayu sosai cikin ankonsu na yan mata wani pink ashobi doguwan riga an mata dauri hadadde tadan yafa gyale a kafada, kwala mata kira Ihsan tayi. “Anty Zainab” da sauri budurwan ta juyo ganin Hamida tsaye tana kakkare fuska da hijabi tana komawa baya yasa ta rike waist takaraso wajensu cike da mamaki tana kallon Hamidan tace “Kinga daman dawowa Hamida?” da sauri Ihsan tace “Anty Zainab kinga wai bazata shiga cikiba, kumafa Mama na nemanta tun dazu dasafe, Kaka ma ta aikani nemota yafi sau dari uku” kallonta Zainab din tayi ta harareta tace “wuce mutafi” da sauri ta share hawayen dasuka zubo mata da hijabi tace “Anty Zainab mutane” “to uban me zasu miki? Cinyeki zasuyi?” kallon wajen tayi cikin tashin hankali tace “nidai zan tsaya anan kucema Mama nadawo” ganin kara makalewa take a bango kuma tasan halin ta tsaf inba ka tursasata ba wlh bazata shigan ba yasa zainab ta karasa wajen ta finciko hanunta tajata da karfi, fashewa tayi da kuka sosai tana waigen baya tana neman fizge hanunta daga na Zainab din, da sauri Zainab tace “rikemin dayan hanunta Ihsan mu shiga ciki” da sauri Ihsan din ta rike dayan hanun suka jata zasu shiga ciki, fashewa tayi da kuka duka hankalinta yatashi tanason kwace hanunta takasa dan zainab akwai shegen karfi, cikeda tsoron shiga gidan tace “Anty Zainab dan Allah no, please kinji wlh kunyan shiga ciki nake, ai nadawo kusakeni bazan kara fitaba, kunya nakeji” waigawa baya tana neman abinda zata rike dan karsu shiga da ita ciki karaf suka hada ido da Ya Faruk yana zaune kan white Lexus dinshi yaci farin shadda gizna hanunshi rike da waya yana kallonsu, wani mugun kallo ya watsa mata da sauri ta dauke kai tana share hawayen da sun kasa tsayawa suka shiga gidan da ita da karfin tsiya, kara fashewa tai da kuka sabida yanda ake kallonsu ta rufe fuskanta da hijabinta da sauri hankalinta duk atashe, dakin Mama suka bude suka shiga da ita ciki Zainab tace “Mama gatanan tun tuni tana waje taki shigowa shine na jawota” wani irin kallon takaici Mama ke mata gashi ta tsaya tanama mutane kuka aka hakan yasa wani irin zuciya ya debi Mama ta tashi ta zuba mata mari tana huci, ihu tayi ta tsugunna akasa tafashe da kuka sosai, cikin fushi Mama tace “kukan ubanme kike mana iyye?” zata kara kai mata wani dukan Anty Lami ta riketa tace “ke Maman Ayush dena dukanta, addu’a ake ma yara” cikin tsananin fushi tace “wani irin addu’a Yaya? Kullum Hamida saita jamin cin mutunci, meke damunta ne? Yanzu bagata ananba ta wuce mutanen wani abu yasameta? Wlh Yaya kimata magana kotamin shiru kona sassaba mata Allah bazance ta girmaka duka zan kirba mata kaman yar shekara biyu agidan” hanunta Anty Lami ta rike ta zaunar da ita tace “calm down, ya isa haka, kidena bata rai yau babban ranace kina aurar da ya baikamata kina fushi ba” ta juyo ta kalli Zainab dake tsaye itama tana kallon Hamidan data boye fuska cikin hijabi tana kuka tace “ina ashobin nata Zainaba?” “yana dakinmu” tafada ahankali, “yauwa to jeki dauko ki kawomin tai wanka ta shirya taje wajen kakan ku dake nemanta kafin ku tafi” juyawa tayi dan zuwa dauko ashobi, ta kalli Ihsan datai shiru tana kallon Hamidan idanunta sun cika da kwalla itama kaman zatai kukan dan ta tsani taga an taba Hamida tace “jeki taya Zainab dauko kayan” juyawa tayi tafice tarufo musu kofan hakan yasa Anty Lami ta dawo inda take tsugunne tana kuka ta dagota tana murmushi tace “haba Hamidan Maman ta, mai kama da Maman ta” tsakin takaici Mum tayi ta tashi tafice daga dakin, sakinta tayi ahankali tace “oya cire hijabin kije kiyi wanka kizo ki shirya” gyadamata kai tayi ta zare eyeglasses din idanunta ta sauke handbag dinta tasa aciki tana goge idanunta da bayan hannu da hawaye ke zuba ta ijiye jakan ta mike tana kallon gadon ganin ba Mama, ahankali ta zare hijabin ta ijiye akan gadon, kyaykyawan yarinya ce Hamida bana wasaba, gawani irin shape da Allah yamata mai bala’in kyau tana sanye cikin simple riga da skirt na wani poker dot silk material skirt din yabi jikinta yafito da fine curve hip dinta rigan ma yakamata yay mata shegen kyau, kitson shiku ne akanta manya manya dabaza su wuce guda gomaba, gashinta dogon gaske yay tsufa gashi ya kwanta akan goshinta sosai, babu dan kunne a kunenta,looking naturally beautiful, sake goge hawayen daya zubo mata tayi Mama Lami tace “Ya isa kukan haka wuce kije kiyo wankan ki kinji Hamida” gyadamata kai tayi ta wuce tabude bayin dake nan dakin Mama ta shiga bata wani jima sosai ba tafito daure da zani kayanta dasu Zainab suka kawo Anty Lami ta nuna mata akan gadon, daukan kayan tayi bayan tagama tsane jikinta ta shirya cikin kayan doguwan rigan itama aka mata kaman na Zainab bakaramin kyau dinkin yamata ba yafito da shape dinta sosai, zama tayi kan gadon tana wasa da yatsu Anty Lami tace “tashi zakiyi kiyi kwalliya kije kakan ku na kiranki” gyadamata kai tayi tana kokarin danne kukan datakeji taje gaban madubin Mama ta tsaya, tashafa farin hodan data gani awurin, ta shafa man baki, Anty Lami daketa binta da kallo sabida kyan datayi dudda batai gayuba sosai ba amma tai wani irin kyau tace “bayan kin dawo daga wurin kaka kije dakin ku kihada kayan da zakiyi amfani dashi in kinje Lagos din ance kwana uku zakuyi” hawaye ne suka zubo mata da sauri ta share, hararanta Anty Lami tayi tace “ai kyaji dashi lamarin ki ya tabarbare Hamida wuce kibani wuri danni inzan miki nawa wlh saiyafi na wanda maman ki tamiki, kayan takaici kawai mtsww” taja tsaki, ahankali takoma gaban gadon tadau hijabin ta ta zura, baki Anty Lami ta bude tace “kinsa ashobi ki na yan mata saikin saka hijabi kuma? Lallai Hamida nidai wuce kiyi duk yanda zakiyi kekika sani” ta nuna mata hanyar kofa, ahankali tadau jakanta tawuce tafita daga dakin mutanen data sake gani chaa ana hayaniyan biki yasa taja hijabin ta rufe fuskarta tana tafiya ahankali ko ina na jikinta na rawa, kafin takai falo taci karo da mutane sama da goma sha da kyar tasamu ta fice tai hanyar sassan kaka, karo taci da mutun da sauri tai gaba zata wuce batare data dagokai ba taji an wani irin fizgota, a tsorace tadan dago kai hada ido sukayi da Ya Faruk yadaure fuska kaman baitaba dariya a duniya ba, saukar da idanunta tayi kasa bakinta narawa sosai tace “s…sorry Ya Faruk” wani irin matsiyacin kallo yamata hakan yasa jikinta yadau rawa, cikin wani irin kakkausar murya yace “mahaukaciya kawai” yawani irin turata, ahankali ta dagakai ta kalleshi da idanunta dasuka cika da kwalla shima ita yakema wani kallon tsana, cike da dakewa zuciyarta na tsinkewa sosai tace “niba mahaukaciya bace”.
_🌹IN BANI 🌹_

Related Articles

 

_M. Shakur_

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button