Hausa NovelsIn Bani Hausa Novel

In Bani 22

Sponsored Links

22….

_This novel is for sale, karki karanta in baki biyaba, in kika karanta ina binki bashi pay anan ko pay achan_

_in kinaso novel dinan zaki turo 300 access fee to 3107021073 first bank aisha Muhammad, saiki turo evidence of payment ta watsapp number na 07012181461_

Related Articles

_Zaki iya turo MTN card 300 ta watsapp number 07012181461 sainai adding dinki a group din danake posting_

Ko motsi kasawa tayi jin abinda yafadin mata saima wani irin kallon idanunshi datakeyi, ahankali yakamo hanunta yana kuka yana lumlumshe mata ido gwanin ban sha’awa yace “i love you Hamida, and we will marry just like Mami and Abie right?” shiru tayi takasa magana jikinta yay wani irin shegen sanyi tundaga yatsar kafarta, lumshe ido yayi yasake budesu ya kalleta araunane kafin yasakin mata wani irin kuka, ta tsani taga yana mata kuka, sosai kukan shi ketaba mata rai, da sauri ta gyadamai kai tace “yes” wani irin ware mata manyan eyes dinshi yayi yace “yes Hamida my wife, she will marry me like Abie and Mami na yay” yay maganan yana mata fari da ido yana juyawa, tsayawa tayi tana kallonshi sosai taji tana wani irin tausayin shi to wai mutunmin dayake da lafiyan shi meya dawo dashi hakane? Meya maidashi haka? Hanunta taji ya fizgo yace “lets go, bazamu koma dat mugu house bako” ahankali ta karbe hanunta daga rikon dayamata suka cigaba da tafiya, batamasan inda zasuba gashi ko naira daya batadashi tafiya kawai suke yana mata surutu yana kirga hanunshi yana nuna mata yana murmushi, sosai yake wani irin farin ciki yana murna sabida tacemai yes sai tsalle tsalle yake akan hanya yana kallon fuskarta, duk in sukazo wuce bishiyan fulawa saiya katso yabata, karba kawai take tana murmushi amma matsalan datake ciki yawuce tunaninshi.

Gidan data boye jiya sukaje, atare suka shiga yana tsalle tsalle, pure water data gani awurin tadauka da sauri ta bude tai alwala, Aadil dake tsalle tsalle shima yazo da sauri ya tsugunna yana kallonta sai leken fuskarta yake, turo mata baki yayi yace “me too zanyi alwalan” zaro ido tayi ganin saura dan kadan ruwan, mikamishi tayi da sauri ya karba yana murmushi yace “thank you my wife” yafada yana nuna kanshi yana wani irin fikifiki da idanunshi dimples dinshi na lotsawa, tashi tayi da sauri batason tana kallonshi inyana mata irin abubuwan nan dan wlh wani irin kyau da kwarjini yake mata bana wasaba, karasawa dan filin dakin tayi ta gyara kasan wajen da hanunta sanan ta yafa dan kwalin kanta da kyau ajikinta ta kabbarta salla sai alokacin taji zuciyarta yarage mata nauyin dayake mata na kunci da azaba sosai, yay wani fayau kaman an kawad da damuwanta, salla tayi tai addu’a Allah ya bayyanar da yanuwanshi burinta kawai bai wuce yaga yan uwanshi yatafi gidaba ita saita tafi gidan Anty Lami yayar Mama, zuwa yayi shima ya tsaya a gefen ta yafara sallan murmushi kawai tayi tacigaba da addu’oin datakeyi.

Jinginar da bayanta tayi da bango ta daura kanta akan guiwowinta tai shiru idanunta sun cika da kwalla sosai, alamun mutun dataji akanta yasa tabude ido ahankali, hada ido tayi da Aadil daya leko da kanshi yana wani irin kallonta, ganin yanda hawaye yacika idanunta yasa duk yabi ya damu, zama yay a gefenta ya daura hanunshi akan kadadarta yawani irin dago kanta daga jikin kafafunta da karfi, kallonshi tayi shima kallonta yake ya daure fuska sosai, akumbure yace “why do you want to cry?” dan lumshe ido tayi da sauri tana kokarin ture hanunshi daga kafadarta takasa sabida yanda yarike ta gam, jiyayi kanshi yadau zafi da sauri ya fada jikinta yakai fuskarshi saitin nata, arude tabude idanunta dake gab da zubar da kwalla tace “Aadil kadena stop, kasakeni” makemata kafada yayi yakai hanunshi ya daura akan saman idanunta yana leka idanun kaman maison gano wani abu, murya chan kasa yace “you want to cry” girgiza mai kai tayi zuciyarta namata rawa sosa tace “n…no Aadil am not cr..crying, kaga….ni” saikuma tasaki kukan da karfi sosai sabida yanda zuciyarta kemata zafi, bamatasan tasaki kukan ba kawai kukan ne yazo uncontrollably, Kaka ta koreta daga gida batada gida ina zata, rudewa Aadil yayi sosai dan yatsani yaga ana kuka barinma na Hamida dayakeji har kasan zuciyan shi, wani irin rungume yayi yasata ajikinshi yana jijigata muryanshi shima narawa sosai yace “d…on’t cry, i will call police for them, they will arrest them, they beat you and injury you i will go with police and beat all of them, stop crying Hamida” yanda yake maganganu dabama ta ganewa dan dukya rude muryanshi narawa sosai yana breaking kaman shima yana shirin kukan yasa tai shiru tana tureshi tana kokarin tashi daga jikinshi, make mata kafada yayi yana kallon idanunta dasukai jajir sun kumbura sosai, hanunshi dake rawa sosai yakai kan fuskarta yay cupping face dinta yana share mata hawayen dake kan fuskar yana yana turo baki kaman zai fashe da kuka yace “i will beat them for beating you, stop crying, don’t cry again kinji” gyadamai kai tayi ta hadiye duka kukan datakeji tamai murmushi tace “am fine” ahankali yana kallon idanunta batare dayasaki fuskarta ba yace “are you sure?” gyadamai kai tayi tama kasa magana kirjinta na bugawa sabida wani irin kallo dayake mata daya bambanta dana koda yaushe da sauri ta runtse idanunta gam tafara kokarin fita daga jikinshi, make mata kafada yayi yasata a kirjinshi ya kankameta yay shiru kirjinshi nawani irin bugawa, shikanshi baisan meyakejiba kawai yanaso yacire mata damuwan datake cikine, ganin ko motsin kirki takasa yasa dan bebata daman ba yasa tai shiru gabanta na faduwa tana sauraron yanda jikinshi kewani irin daukan zafi heart dinshi na beating da karfi and fast fast…

 

***
“Mami, Mami na” da kyar ta iya bude idanunta dasuka mata nauyi sosai tsabagen kukan datake sha ta kalli Aabid daya rame shima duk yay wani iri hanunshi rike da mug din hot tea yana kallon mahaifiyar nashi dake kwance kan gado ta lulluba da bargo, kaman zaiyi kuka yace “Mami please tashi kisha tea kinji Mami na, please sweet Mum” girgiza mai kai tayi muryanta narawa sosai tace “bazan iya shaba, bansan ina Aadil dina yakeba, bansan ko yasamu abinci yaci ba, am sure my baby is hungry yanzu haka, bansan wani hali Aadil dina yakeba, tayaya zan iyacin abinci bansan wani hali my poor innocent boy yake cikiba” hanunta Aabid yakamo yarike zaiyi magana Baffa da shigowan shi dakin kenan kusan shi yamafi kowa damuwa ya nunata da Sanda cike da masifa yace “tashi ki karbi shayin nan kisha, kashe kanki zakiyi tunda yaro yabata babu abinda kika sama bakin salati, tashi ki karbi shayin nan kisha Maryama kona mugun saba miki wlh” cikin kwantar da murya Suleman yace “ya isa Baba muje kahuta kaima bakajin dadin, yanzu nida Abdullahi zamu koma police station din da Hussain” wayar Aabid ne yay ringing da sauri yaciro wayar daga aljihu ya kalli screen din, da sauri yadaga kai ya kalli Abie dake kusa dasu Baffa yace “Inspecta ne” da sauri Mami ta yunkura ta tashi zaune tanajin wani irin masifaffen ciwon kai tace “dauka hala anga Aadil dina ne” da sauri yay picking call din yakai wayar kunenshi daga tachan bangaren inspecta yace “yallabai…” da sauri Mami da jikinta har bari yake tace “sa, saka a speaker Son” zare wayan yayi daga kunenshi yasa a speaker yace “i can hear you inspecta kace mene?” “yallabai jami’an tsaro damuka baza a kowani anguwa ne muka sami wani information da safen nan dayasa muke bukatar kuzo kuyi comfarming ko shine” da sauri Mami ta fizge wayar daga hannun Aabid tsabagen yanda jikinta ke bari tace “inspecta anga d’ana?” anatse inspecta yace “abinda yasa nake neman ku kenan anga wani amma shi gaskiya ga dukkan alamu ba kidnapping dinshi akayiba kaman yanda muke zargi ba, dawata mace muka ganshi yanzu haka suna under our watch suna wani uncompleted building da ba’a gamaba awata sabuwar unguwa, na zuba jami’an tsaro da yawa a anguwan tayanda bazasu fitaba harsai kunzo kun tattance idan shine na hoton dakuka bamu, dan gaskiya wanan yay datti sosai yay budu budu kaman mahaukaci ko takalmi babu akafarshi kawai nadai ga dan kamaninsa da wanan saurayin daya kawo case din offis ne saisa mukace bari mukira” da sauri Mami ta share hawayen dake zubo mata tace “i…ina…inane wurin?” “zan tura muku address din yanzu” ya katse wayar saukowa Mami tai daga gadon tai baya luuu zata fadi sabida rashin karfi babu abinci acikinta tun jiya da sauri Aabid ya riketa, Baffa ne yace “ki zauna agida bari mu muje” fashewa tayi da kuka tace “Baba dan Allah zanje” share mata hawayen Aabid yayi yadau mayafinta ya yafa mata yace “muje grandfather muje da ita” fita dukan su sukayi harda big mum, Kafin ma su shiga mota har inspecta ya tura musu address din location din suka shiga manya manyan jeep dinsu kusan guda uku sukaja suka sukabar gidan.

Tafiyan wurin 25min yakaisu anguwan, parking sukayi agaban junction din anguwan nan inspecta da sauran yaranshi suka fito daga inda suka boye, fiffitowa daga mota sukayi inspecta yakarso wajen yace “muje”…..

 

Yanda yake wani irin shishigewa jikinta yana numfashi da sauri da sauri yasa ta tureshi tace “stop” make mata kafada yayi da idanunshi dasukai ja sundan kankance kaman zaiyi kuka yace “am sleepy” matsawa gefenshi tayi da sauri tace “to sleep ga fili nan” make mata kafada yasakeyi hawaye ya cicciko a idanunshi yace “i want to sleep on your body” yay maganan yana matsowa kusada ita gabaki daya idanunshi sun chanza kala, da sauri ta mike tsaye adan tsorace ganin yanda ya chanza, kadangare tagani abango da sauri ta matsa baya tace “wayyo lizard” kallon bangon yayi kafin ya fizgo riganta tabaya juyowa tayi da sauri ta kallai tamai pointing lizard din tace “come let’s play with lizard, kadangaren babba ne sosai ko” tashi tsaye yayi shima batare daya saki riganta ba ya kalli lizard din sanan ya kalleta yanda yaga tana kallon kadangaren tana komawa baya alamun tsoron kadangaren take yasa yaturata da karfi yace “lizard catch her” ihu tayi sosai takoma bayanshi da gudu ya kyalkyace dawani irin dariya yana clapping hands dinshi yace “Hamida my wife is afraid of lizard” kaman daga sama idanunshi suka sarke dana Mami data fara kunno kai dakin.
_🌹 IN BANI 🌹_

 

Maman Abd Shakur

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button