Bamagujiya Hausa NovelHausa Novels

Bamagujiya 49-50

Sponsored Links

Tana gama rubutawa ta karanta tare da tura masa sannan tayi maza ta kashe layin.
Habeeb dake kwance saman kujera three sistar yaji shigowar saƙo kamar bazai buɗe ba ya gyara kwanciya, zuciyarsa taƙi nutsuwa ya ɗauki wayar ya buɗe saƙon baisan sanda ya tashi tsaye ba yana duba saƙon number babu suna ya sake duba saƙon yace “Habeebatullah kenan? Kece kika turomin saƙo?”
Da sauri ya fara kiran layin abin takaicin ta riga ta kasheshi wannan tasa shi zama daɓar tare da dafe kansa yana furta Innanillahi wa inna ilaihirraji’un sake gwada wayar yayi har zuwa lokacin a kashe ransa ne ya fara faɗa masa to ko ta koma Tsaunin gawo ne?
Da wannan tunanin ya tashi ya zari key na mota ya fice daga dakin komawa yayi ya zauna tare da duba agogo 3:20am yasani koda yake motar kansa ce ba ƙaramin ƙalubale zai fuskanta a garin Abuja kafin yace zaije Kano daga Kano ya ɗauke hanyar Tsaunin gawo kwanan zaune yayi asubar fari zakara ya bashi saa ya ɗauki hanya wajen goma ya isa Kano ya ɗauki hanyar Tsaunin gawo lokacin daya isa duk maza suna gona.

 

Jumme ya tarar tana shanyar ganyen albasa ya tsaida motarsa ya fito tana ganinsa ta nufi gida da sauri ya bita tare da cewa “Barka da safiya Mama!” Tsayawa tayi ya rusuna ya gaisheta, cike da kunya irin tasu ta mutanen karkara ta amsa ya sosa kansa yace “dama Habeebah nakeson gani….” Da sauri ta juyo tace “Tana ina ɗannan Nima ita nakeson gani”
Wani abu yaji me nauyi ya saukowa ƙirjinsa daƙyar ya miƙe tsaye ya koma cikin motarsa ya kira wani yaro ya zaro kuɗi da baisan adadin su ba ya bashi yace yakaiwa Jumme ya tada motar yabar ƙofar gidan baiyi nisa ba ya tsaya ya ɗora kansa bisa sitiyarin motarsa ya lumshe idonsa hawaye suka fara sintiri Mai Martaba ya cutar dashi duk shine yaja masa amma yanzun wai dashi yake fushi saboda ya sakar masa zaɓin nasa.
Ajiyar zuciya yayi tare da tada motar ya koma cikin garin Kano anan ya samu wani hotel ya sauka ya huta yana kwance wayar Wali ya shigo yana gani amma ya kasa ɗagawa saboda ransa a cushe yake kalma ko ɗaya bayajin zai iya furtawa me amfani.

Related Articles

 

Kira na biyu ne ya sashi ɗagawa Wali yace “nazo gdanka bakanan ina kaje?” Buɗe idanunsa yayi cikin gajiya yace “ina Kano” amsawa Wali yayi yace “Ok dama inason ka rakani gidan Al’Amin ne” a yatsine yace “
Ko kwanaki kace nazo muje nace maka banida interest akan hakan so waima meye Ni sai ka rinƙa jana gidan matan aure?” Murmushi Wali yayi ya riga yasan halin izza da son isa irin ta Habeeb shiyasa yace “Allah ya huci zuciya dama Ahmad abokinka ne ya dameni tun jiya nazo naga bbynsu ƙanwar Mamansu ce dake zaune a gidan ta haihu shine dake naji kace kanason zuwa ka gaisa da Ahmad na sanar dakai”
Numfashi ya aje yace “ok kaje inna dawo ka rakani tunda Ni yanzun saina shiga Dutse zan wutto nan” sallamewa sukayi ya tashi ya fara shirinsa ya ɗauki mota sai dutse koda yaje bai saurari mai martaba ba sashin Kilishi ya shiga suka gaisa cikin watanni biyar ɗin duk ya rame ya susuce sai ido da hanci kawai taja fasali tace “Meye yasa bazaka fawwalawa Allah komai ba Habeebullah ubangiji ba da kansa yake cewa (ashe haka zan barku kara zube? Shin bazan jarabceku ba?) Habeeb Allah nason bayinsa masu haƙuri da fawwala masa komai daya shafesu” hawaye ya share ya miƙe zai bar wajen ta riko hannunsa tace “meye ne?” Ƙasa yayi da kansa

 

Yace “Ta haihu Kilishi yanzu Shikenan yarinyata bazata Sanni matsayin ubanta ba?” Da sauri Kilishi tace “Habeeban? Yaushe ta haihu ina kaji kai ya akayi ka sani???” Ta jero masa tambayoyin cike da ruɗewa ya kawar da kansa yace “yau da asuba naga saƙonta kuma tun lokacin nake kiran wayar taƙi shiga” jinjina kai tayi tace “To a bibiyi number mana ai za’a gano daga inda ta rubuto saƙon” sosai yaji daɗin shawarar Kilishi domin da gaske ya manta da ana wani bibiyar number waya don gano daga inda ake amfani da ita.
Fasa shiga ɗakin nasa yayi ya fito ya kira Najeeb tare suka yini a campanyn layin wayar ba ƙaramin al’ajabu Habeeb ya shiga ba da akace masa Beebah tana garin Abuja inda tayo test ɗin ne suka kasa ganowa saboda layin ba akan waya yake ba.
Jikinsa har ɓari yakeyi da aka sanar dashi inda take ashe zuciyarsa ce a gurin shiyasa ya kasa barin Abuja ko zaman London ya kasa ko yaje baya jimawa yakejin hankalinsa ya dawo Abuja.

 

A ranar bai kwana a Dutse ba ya wucce Abuja ya nemi Wali yayi masa bayanin komai shima ya cika da mamaki nan suka kuma ɗimawa suka fice domin Habeeb ya hanashi kwanciyar hankali gani yakeyi suna fita zasu ganota.
Haka suka shafe kwanaki suna jigilar nema abu kamar wasa sai gashi sun ɗauki kusan sati.
Ranar wata asabar tun safe suke zaga gari yamma suna zaune cikin wani garden Habeeb ya kifa kansa saman tables ɗin abin duniya yabi yayi masa zafi, wayar Engineer Wali tayi ring ya zarota a aljihunsa tare da manna ta a kunnensa suka gaisa yace “kace zakazo taron raɗin suna kuma banganka ba” numfashi ya sauke yace “kayi afuwa abune yayi yawa Wlh amma bari yanzu mu taho dama muna ta arear taku” kallonsa Habeeb yayi kamar yace bazashi ba Wali yace “karkace komi don Allah inci wannan arzikin Dr Amin yafi ƙarfin haka a gurina”

 

Tashi yayi suka nufi mota daga inda suke zuwa gidan Dr Amin babu nisa suna isa suka ishe Dr Amin ya fito raka baƙi suka gaisa yayi musu jagora zuwa parlourn baƙin aka cika musu gabansu da abinci Habeeb dai tsakurar abincin kawai yakeyi Dr Amin ya kira wayar Safeenah yace “A kawo ma su Engineer Wali Ummusalma su sanya mata albarka” Habeeba dake zaune saman gado Safeenah ta duba tace.
“Kanin Dr ne yazo ki kai musu Bbyn su ganta” itadai Beebah hakanan taji gabanta na faɗuwa, ta jima bata tashi ba Saida Safeenah ta matsa sannan Beebah ta tashi ta fito daga dakin ta ɗauki kwalliya ta ban mamaki sai sheƙi takeyi.
Nufar ɗakin bakin tayi idanunta na kan Ummusalma.

 

Ta shiga dakin tare da sallama yana ganinta ya miƙe da mugun sauri ya fara nunata da yatsa itama ɗagowar da zatayi tayi tozali dashi ta sake ware injin idanunta akansa tace “Hab… Habeebullah…..” Saurin juyawa tayi da mugun gudu zata fice a dakin yayi wani kukan kura ya cafkota cikin tsananin farin ciki ya kira sunanta sai hawaye sharrrr a ijiyarsa itakam itama zamewa tayi ta zauna a ƙasa ta rungume Ayyana mikin ciwon dalilin nesantata dashi yana dawo mata sabo ta rushe da kuka me ciwo tare da rungume Ayyana ƙam a ƙirjinta.
Tausayin kansu yaji ya ƙara nunkuwa a zuciyarsa ya zauna yana share hawayen idanunsa yace “Bantaɓa…..” Saurin ɗaga masa hannu tayi tace “Don Allah kada kacemin komai Habeeb basai ka sanar dani halin da zuciyarka ta shiga ba saboda yanayinka ya nuna hakan idan kace zaka sanar dani zaka cusamin tausayinka a lokacin da tausayin bazai mana amfani ba nasan kanasona ka rayu dani a ranka tsayin shekaru ka zaɓi rabuwa da manyan jigogin rayuwarka saboda ni so amma hakan ta gaza samuwa kayi ƙoƙari inada yaƙini bazan taɓa maye gurbinka ba…..”

 

Yanda ya ambaci sunanta da ƙaraji yasata miƙewa yakai hannunsa zai karɓi Ayyana ta janye har zuwa lokacin idanunta hawaye yake zubarwa yace “Meye yasa zaki hanani ɗaukar jinina” girgiza kai tayi tace “Ba jininka bace” daga haka ta nufi hanya ta fice daga dakin da sauri tanaci gaba da kukanta me taɓa zuciya. Safeenah data rako baƙi ta tsaya da mamaki tace “Beebah….” Bata kulata ba ta shige daki ta faɗa gado ta rushe da kuka me sauti tana cewa “Na shiga uku Ni Habeebah ya akayi Habeeb yasan ina garin nan har ya biyoni maɓoyata?”
Safeenah ce tace “Waye shi?” Ɗagowa tayi a gajiye idanunta ya kaɗa yayi jajir tace “Shine wanda nake baki labari mijina a baya uban ƴaƴana, Maman Ahmad nasan mijina yana sona amma inajin kamar mun rabu kenan”
Girgiza mata kai Safeenah tayi tace “ ba zaku rabu ba zakuci gaba rayuwa fiye da baya me daɗi kuma kyakkyawa bari naje naga meye ke faruwa Beebah har abada Habeeb naki ne”

 

Ficewa tayi daga ɗakin ta nufi ɗakin baƙin ta zubawa Habeeb idanu babu ko tantama ga kama nan a fuskar Ayyana.
Miƙewa sukayi dukkansu Dr Amin da jikinsa ya jima da yin sanyi tausayin Habeeb ya cika zuciyarsa tabbas Habeebah ta cancanci soyayya a gurinsa shima ya cancanci ta soshi ashe shiyasa kullum take cikin damuwa, hawayen Habeeb ya share yace “Insha Allahu zaka rayu da matarka da yaranka wannan abu duka ya faru ne a cikin gaibu sama da watanni biyar Beebah take gdana take zaune da iyali na nasani Tanaji da ganin mutumcin Safeenah ita kaɗai ce zatayi maka aikin rarrashin zuciyarta nasan zata sauko”
Kallon Safeenah yayi yace “Mijinta ne kije ki ɗauki masa ƴarsa ya ganta ashe Ummusalma ɗin da ta zaɓawa yarinyar sunan surukarta ne” fita Safeenah tayi ta dauko Ayyana ta dawo ta miƙawa Habeeb ya rinƙa zuba musu hoto shida yarinyar don a yau yakeson zuwa ya dauko Kilishi tazo taga takwararta tunda yasani yanzun ko giyar wake yasha bazaice zai ɗauki Beebah yakaiwa Kilishi ba duk da alamu sun nuna cikin waɗanda ta riƙe a ranta babu Kilishi.

 

Kuɗi ya zara masu nauyi ya bawa Safeenah yace a bawa Beebah kafin yawo sukayi sallama suka tafi zuciyar Habeeb wasai yau yaga abar ƙaunarsa, suna zuwa gidansa ya haɗa kayansa yace da Wali yakaishi airport yau ɗin nan Dutse zai kwana.
Bakwai ya shiga gdansu ya tarar da kowa a babban parlourn ciki harda Khausar tana durƙushe gaban Sarki Khalil tana kuka.
Bai sauraresu ba ya wuce zuwa ɓangaren mahaifiyarsa tana ganinsa tace “Ya kiraka kenan?” Dubanta yayi da rashin fahimta yace “Wa ba?” Kawar da zancen tayi tace “Ina labarin ƴata da jikata” fara’arsa ya faɗaɗa yace “yau naga Zuciyata taganni saidai taƙi aminta dani Kilishi Kinga shaida” nan ya fara nuna mata hotunan ta rungumeshi tana dariya tace “Alhmdllh Ya sunan Bbyn?” Shafa kansa yayi yace “yau da yamma yayan abokina Engineer Wali wato Dr Amin ya kiramu ana suna a gidansa ƙanwar matarsa ta haihu muka tafi domin tayasu murna shine ya kira matarsa domin ta kawo mana Bbyn abin mamaki sai ga Wyf ɗauke da wannan kyakkyawar yarinyar tana ganina ta kira sunana na mike, amma fah Kilishi Wyf ta sanar dasu Ni mijinta ne a baya banda yanzu inda Ni kuma nayi musu bayanin komai yanzu dai sun bani hƙr sunce zasu tausheta”
[5/25, 3:12 PM] AM OUM HAIRAN: _*BMGJY Bonus 51-52*_

_Ku biya ta acct detail 3184512451 First bank ko kati MTN ta WhatsApp number 09013718241._
_Normal 300 PC 700_
_Ƴan Niger zaku biya 500f ta wannan number +227 95 04 58 22_

_Ban amince a juyamin littafi ta kowacce siga ba._

 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button