In Bani 33
Ahankali ta shiga falon da sallama tana kallon ko’ina komi nadawo mata kaman wata matsoraciya, daidai Kaka tafito daga uwar dakan ta rike da wani turmi da tabarya na karfe, shigowa falon tayi ta ijiye turmin a tsakar dakin ta kalli Hamidan tace “kin wani tsaya hala nadawo aljana ce ko kike kallona da katun katun idanun ki kaman kwan lantarki, bazaki shigoba” shigowa tayi dakin Kaka kuma tadau ledojin data fito dasu tana budewa tana dubawa tace “yauwa saiwar ce” ta dago kai ta kalli Hamidan data zauna achan gefe tace “tashi ki cire hijabin nan kije fridge ki daukomin nono da kofi da chokali kizo nan” tashi tayi ta cire hijabin ta ijiye akan kujera taje fridge ta dauko nonon dakeda sanyi ta maida fridge din ta rufe ta kawo ta ijiye kusada ita sanan taje ta dauko kofi ta chokali takawo da sauri Kaka ta ijiye dakan ta karba ta zuba nonon a kofi ta zuba wasu magunguna aciki ta juya sosai sanan ta mika mata tace “yauwa shanye wanan kafin gobe suzo su kawomin kudaden saina dauko miki yar buzu tazo ta fara miki gyaran jiki dan wanan fatar taki fatar manya ce dole kiji gyara, ungo” ahankali ta karba tana kallonta dan ko kadan bamata gane metake cewaba ganin bata mata fadaba yasa taji zuciyata tai sanyi tai maza ta shanye batare data damu da dacin maganin ba.
Haka Kaka tarike ta a Sasan batare data bari tafita ba, tabata wanan tabata wanchan har bayan magrib sanan tasata taje tayo wanka, wanka tayi ta shirya cikin doguwan riganta na atampa sanan tasaka hijab tafito tai sasan su.
Falonsu ta shiga, babu kowa sai kamshin turaren wuta dayake yi, ahankali tawuce ciki ta tsaya agaban dakin Mama, sallama tayi chan kasa tanajin wani irin tsoro aranta, daga taciki Mama tace “waye, shigo” bude kofan tayi kaman wata matsoraciya ta shiga tana zare ido hada ido sukayi da Mama dake tsaye gaban wardrobe tana maida wasu kaya dake kan gadonta ciki, kallonta tayi kafin ta dauke kai tace “rufemin kofana sauro, meya kawoki kuma?” mayar da kofan tayi ahankali tarufe sanan tajuyo ta kalli Maman data mayarda hankalin ta kan abinda takeyi kaman batasan da ita a wurinba, jitayi jikinta yadau rawa wani irin kuka yazo mata ta tsani taga Mama na shashareta kotana fushi da ita, abin na mugun damunta arai bana wasaba, batasan lokacin dataje da gudu tawani irin rungume Mama ta baya ba tafashe da kuka sosai tace “Mama kiyakuri dan Allah kiyafemin kinji bazan karaba, wlh, wlh, biyoni yayi, tsoro naji nayi ihu Kaka tazo ta dakeni tahadani da Abba koya Faruk saisa naki fadi, am sorry kinji Maman mu” tasaki wani irin kuka dayasa Mama sakin kayan hanunta kasa ahankali ta lumshe ido tanajin kukan nata akowani jijiya na jikinta, kasa daurewa tayi ta juyo ahankali, hakan yakara bata dama tafada jikinta sosai tasaki wani irin kuka dayake cinta kwana da kwanaki tana shesheka tace “dan Allah ki yafemin bazan karaba, am sorry” ganin yanda take kukan yasa ahankali Mama ta dago kanta daga jikinta ahankali takai hanunta ta share mata idon tana girgiza mata kai tace “ya isa haka kukan” gyadama Maman kai tayi wasu hawayen na sake xubowa, hanunta Mama takama takaita gefen gado ta zaunar da ita sanan ta zauna itama a gefen ta, ahankali tai cupping fuskarta da duka hannayenta takira sunanta chan kasa. “Amatullahi” ahankali akuma natse ta amsa da “na’am” dan Mama bata taba kiran asalin sunan ta hakaba, murya chan kasa Mama tace “wacece mahaifiyar ki?” ahankali tace “kece Mama” zama Mama ta gyara tace “maisa baki bani matsayin ba? Kinada wata kamata ne aduniyan nan?” girgiza mata kai tayi, “kinada wacce zata soki regardless, wacce zatai understanding naki kaman nine a duniyan nan?” sake girgiza mata kai tayi ahankali hakan yasa Mama tace “to mesa baki fadamin matsalar ki? Mesa baki gayamin kowani hali kike ciki? Inaso kifadamin yau mecece matsalar ki tell me everything, tell me anything, tell me the whole thing Amatullahi and your mother will listen to you, mesa bakison mutane? Mesa baki attending lecture mesa? Mesa u are not free da kowa, eh? Talk to me Hamida ina jinki, i want to know your problem” hawaye ta share ahankali sanan ta girgiza kai tace “nima i don’t know Mama, kunya nakeji idan naga mutane dayawa sun taru sai naga anata kallona saina dingajin kunya saikuma nafara jin tsoro idan banvar wajenba sai nafarajin kirjina na bugawa sosai, kaina yafaramin wani iri, kafufuna sufara rawa, nafara ganin jiri, inji kaman kallonsu na shakemin wuya, numfashi na nafita da kyar, banson zuwa lectures sabida yan ajinmu kullum nunani suke yi wai nice maicin 3 da 5 a CA, duk in naje class kallona suke saisa bana zuwa ajin” ahankali Mama na kallonta asanyaye tace “to ina kike zuwa in baki shiga lecture ba?” murya chan kasa tasake share hawayen daya zubo mata tace “old railway station chan nake zuwa?” cikin wani irin yanayi na mamaki Mami tace “old railway Hamida? Bakisan irin wajajen nan matattaran yan shaye shaye bane?” gyadamata kai tayi ahankali tana kokarin fashewa da kuka tace “sunma biyoni ranan nagudu shine harna hadu da mara lafiyan nan shima yadinga bina har gida” ahankali Mama tai salati “innalillahi wa innailaihi raji’un, Hamida all this suka faru baki fadamin ni mahaifiyar ki ba anya kinmin adalci kuwa?” girgiza mata kai tayi tana kuka tace “am sorry Mama bazan karaba Allah kuwan” shiru Mama tayi tana kallonta kafin tace “dena kukan share hawayen ki” share hawayen tayi wasu na zuba, Mama tace “daga yau kome yasame ki any problem at all, ko wani abu dakikeji lemme be the first person to know kina jina” gyadamata kai tayi ahankali kafin ta rungume Maman da sauri tace “am sorry Mama, kiyafemin” kanta ta shafa tace “nayafe miki ya isa kinci abinci” gyadamata kai tayi ta tashi tace “bari na gyara miki kayan” hijabin jikinta ta cire ta gyara kayan ta jerasu a wardrobe din tass Mama nabinta da kallo tana mata addu’a aranta Allah ya shiryata, yakuma chanzata sanan yabata miji nagari, mayarda kofan tayi tarufe sanan tadawo ta zauna kusada Mama suna hira su biyu ahaka bacci ya kwashe ta gyara mata kwanciya Mama tayi taja bargo tarufe ta tana kallon fuskarta, duk cikin yaranta tafijin tausayin ta kodan sabida itace shiru shiru bata saniba amma hakanan takejin wani irin tausayinta da sonta bana wasaba, Hamida daban takejinta aranta tun ranan data haifota duniyan nan, all children are special but deep down tanaji Hamida zata dawo wani abu nan gaba, inka kalli Hamida innocent dinta zaisa ko cizonta bazaka iyayiba.
Sallaman Abba dataji yasa ta kalli agogo goman dare lokacin dawowan shine tashi tayi takara fesa kanta da turare tabude kofan tafita daga dakin dan zuwa tarban mijinta.
Ranan Kaka batai baccin dareba wani hadadden kwaleman dakinta tayi tana masifa ita kadai. “ja’irar yarinya tatafi bata dawoba sun barni nikadai naketa aiki, ai wlh duk kudin dazasu kawo gobe sisi bazasu ciba nikadai nasha wahalata nizan mori kudina, Hamida tasami gidan hutu miji pagal kaman ita chan su karata sa warkar da juna” tai maganan tana tura kujeran falon ta jikin bango ta tsaya tana kallo yanda dakin yay kyau sosai tace “masha Allah komi yay tsaf tsaf, sun gogu kujerun jibi yanda suke kyalli gobe dazaran sunzo shashina zan kawosu darat ayi magana in yanke musu sadaki, sati hudu zan saka biki, babu kyau jan biki yay tsawo ga yaro ma ba lafiya, yar buzuwa ma kudin ta rabi zan bata sai bayan biki zan cika mata rabin, wayyo Allah na bayana” tai ihu tana kokarin zama akan kujera dan tagaji iya gajiya, ko minti biyu batayi da zama ba bacci yay awon gaba da ita.
_🌹IN BANI 🌹_
Maman Abd Shakur